Showing 57001 words to 60000 words out of 153980 words

Chapter 20 - AUREN WATA TARA COMPLETE HAUSA NOVEL

30 Sep 2024

16367

sun fara zarginta Tsaki taja tanajin haushin Abunda yace mata wai villager A sanyaye ta mik'e tabar office d'in Bayan ta mayar wa da Mlm Umar wayarsa kai tsaye hostel ta nufa a sanyaye daka kalleta kasan tana cikin damuwa shiru tayi tare da Yin tagumi Asmy ce ta ce "Lafiya naga tunda kika dawo kinyi shiru" Tana turo baki ta ce "da sauki dai" Satar kallon Chuchu tayi taga hankalinta nakan waya chat take tana Dariya ya sanya Ta fad'awa Asmy Yanda sukayi a waya k'asa da murya Asmy tayi ta ce "Ki shirya ki tafi kawai karki yarda yana zuwa school d'innan Dan last time ma da aka saukeki wlh wasu harsun fara cece kuce wai daman ustazan nan Kunfi iskanci a boye har fad'a saida mukayi da wata Kiyi Sauri" Ajiyar zuciya Zarah ta sauke ta ce "To shikenan Chuchu fa yazamuyi da ita" Ki barni nasan Abunda zance mata "Cewar Asmy cikin k'ank'anin lokaci Zarah ta shirya cikin atamfarta Riga da sicket Ta d'ora hijab d'inta doguwa mai hannu Pink Fuskarnan tata fresh ba komai sai kwalli Bayan ta dauki hand back d'inta da wayarta zata fita Chuchu ce ta ce " ina zuwa momcy"Asmy tayi. Charaf ta ce "Cikin gari zataje gidan kanwar mamanmu Mijinta yayi tafiya zataje ta tayata kwana" okay Adawo lfy"cewar Chuchu"Koda Zarah ta isa cikin gidan tayi minti biyar tana tsaye ta kasa knoking Dak'yal dai ta tattara jarumta tayi knoking sau d'aya Saida a ka dau kusan Minti Bakwai kafin taji karar bud'ewa duk Haushi ya isheta tana Jan tsaki tsaye ta ganshi kamar kullum sanye cikin K'ananan kaya "tana ganinshi ta murtuke tare da hade rai " Shiko murmushin gefen baki yayi tare da raba mata gefe Alamun tazo ta wuce Kamar bazata wuce ba sai kuma ta shiga tana turo baki Dan tadau aniyar wata magana bazata had'ata dashi ba Tunda Dan wulakanci ne Kan Sopa ta zauna tare da d'ora kafa d'aya kan d'aya ta kauda kai Shima zaunawa yayi kan sopa Yana kurbar drink a cup hankalinshi nakan Kwallo da ake nunowa a gidan television Sunkai minti Ashirin cikinsu ba Wanda yayi magana Shi MD harma ya manta da halittarta a wajen saida yaji ringing d'in wayarta d'an satar kallonta yayi yaga tana Zage jika tare da dauko wayarta cikin Sauri tayi murmushi tare da d'aga kiran cikin cool voice d'inta ta ce "ya Hafiz Ina yini" Shidai MD yana satar kallonta yanda Take wayar tana lumshe ido Baidamu da hakan ba kiran Sallar magriba ne ya tayar dashi Tare da barin gidan ya wuce masallaci Zarah ma wayar tayi masa bankwana saijan tsaki ta ke ta ce "Mutumin nan ya rainama mutane wayau wlh mtww " Toilet din palourn ta shiga tayi alwala Bayan ta fito ta tada salla a carpet din dake palour tayi sallarta bataji shigowar MD ba sai Bayan isha'i itama Bayan ta gama isha'i nan ta zauna tana latsa wayarta Tana chat "Keee" ta tsinkayi muryarsa daga samanta"A ranta ta maimaita keee lallaima watau bazai iya Fad'ar sunanta ba Aiko bazan amsa ba ta fad'a tanayin kwafa tare da cigaba da chat dinta kamar ma ba da ita yake ba "Saida MD ya ce keeee sau Ukku batare da ta d'ago ba hakan sosai ya bakanta masa Yunkurawa yayi tare warce wayar Dake hannunta ya ce " Ba magana nake maki ba"Dagowa tayi ta tsatsareshi da dara daran idanunta tare da turo baki ta ce "To ai banji ka kira suna na ba ?Ohh saina kira sunanki kenan zaki amsa mun? " Eh saboda ba Suna na kee ba Suna na Zarah"Binta da wani irin kallo yayi kafin yaja k'aramun tsaki ya ce "To bazankiraki da sunan naki ba da ke din nayi niyyar Kiranki "Zarah da ta cika tayi Fam Tsaki taja tare da kauda kai " murde mata baki yayi da karfi Wanda saida ta k'walla Kara kafin ya saki ya ce Daga yau ki karayimun tsaki kiga abunda zanyi maki stupid kawai "Idanun Zarah na zubar da hawaye ta ce " Allah ya isa"Wara idanu yayi tare da nuna kasa ya ce "Ni??Tana kuka Ta ce " Eh "Ganin ya yunkuro zai chafeka ya sanyata saurin Mikewa tare da rugawa tayi hanyar fita tana murdawa taji a kulle gashi ya biyota da gudu ta Ruga Tayi Wani Bedroom taja zata rufe kenan Ya turo kofar da k'arfin Kara ta fasa tare da rugawa tayi karshen d'akin tana kuka ta ce " Dan Allah kayi hakuri bada kai nake ba"wani murmushi yayi wanda bazata taba cewa yayishi ba tare da cewa "Na lura baki da kunya saina saita miki zama" Ya fad'a tare da binta chafka d'aya yayi mata ya damkota Tare da bajewa kan Gado a tare suka sauke wata nauyayyar Ajiyar zuciya kafin Zarah ta fara kiciciniyar kwatar kanta amma ta kasa Cikin salo MD ya fara romance d'inta Wanda tuni jikinta ya mutu batasan lokacin da Fara mayar masa ba Dan tama mance da Wanda take tare sun dau Minti arba'in suna romance kafin labari ya sauya salo wannan Karin kam Zarah ko Kukan babu Dan Abun dadi yayi mata sosai Suke Abu D'aya MD bai sarara mata ba sai kusan 1:00am Bayan komai ya lafa kankameta yayi a jikinshi kafin wani bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi duk yanda Zarah taso ta cire jikinta daga jikinshi kasawa tayi Dan karfinta da nashi ba d'aya ba haka dai ta hakura itama har baccin ya kwasheta.....a hankali yake bud'e idanunsa harya k'arasa budesu Kallonta yayi dake jikinshi Wanda baisan ma yayi hakan ba A hankali ya zame jikinshi daga nata toilet ya shiga saida ya fara wanka Kafin ya daro alwala ya fito jallabiya Ya sanya tare da tada sallah Bayan ya gama zaune yayi wajen ya na istigfari A hankali ta bud'e idanunwanta Hasken data gano daga Window ne ya tabbatar mata da Safiya tayi mik'ewa tayi zata zauna Dan ta mik'e Daidai idonsu Ya startse Cikin na juna cikin Sauri ta koma ta rufe jikinta har fuskarta Dan ba komai jikinta batasan ya akayi ba Yau wata irin kunyarsa takeji shiko girgiza kai kawai yayi tare da mik'ewa yabar dakin Tanajin fitarsa Ta sauke Ajiyar zuciya tare da mik'ewa cikin Sauri ta fad'a toilet tayi wanka tare da brush da alwala Tana fitowa lotiion da ta gani a jikin mirror din ta hau shafawa tayi mamakin yawan Kayan shafar kamar na mace Bayan ta gama Kayanta na jiya ta Mayar Tare da tada salla cikinta banda karar yunwa ba abunda yake yi mata Palour ta fito Inda ta samesa waya k'are a kunnansa ga alamar waya yake kujerar nesa dashi ta zauna tana kasa da kanta Bata yarda ko ido biyu su hada Bayan ya gama wayar kallo d'aya yayi mata sai kuma Ya kauda kai ba ayi minti goma ba Sukaji knoking Mikewa yayi tare da zuwa ya amso take away din Ajewa yayi kan table batare da ya Kalleta ba ya ce"Zoki d'auka kiyi break fast"A sanyaye ta mik'e shi kanshi har mamakin wannan kunyar data tashi da ita yau yake tana bud'ewa taga taliya ce lafiyayyan Samanta da kifi cikin Sauri ta rufe tare da Ajewa ta ce "Na koshi?For why ?Hakanan bana cin Kifi " kamar bazai amsa mata ba saikuma ya ce alright ga dayan take away din d'auka "Na koshi idan nakoma school zanyi break fast a Chan " Dagowa yayi ya Kalleta ya ce "Zaki iya girkawa a kitchen akwai komai" kamar bazatayi magana ba sai kuma ta Kalleshi ta ce "Ina kitchen d'in" da yatsa ya nuna mata hanya Inda ya nuna matan ta nufa cikin k'ank'anin lokaci ta fara sarrafa Dahuwar indomie Dan itace Abu mafi sauki da zata ce Zata girka Wayarshice take ta ringing yana ganin Amera ce ta isheshi da kira ga text message d'inta rututu tsaki yaja Dan har yanzu kule yake da ita daga karshe ma kashe wayar yayi Dan karta dameshi ba ayi minti Goma ba ta fito hannunta dauke da plate din Indomie Da ta sha vegetables ta kwai a Samanta Tunda ta shigo k'amshin girki mai dadi ya cika masa girki har wani lumshe ido yake Zarah ko ba b'ata lokaci ta fara cin abincinta Saida ta kusa rabi tukwana ta d'ago ta Kallesa taga hankalinshi na kan laptop tabe baki tayi ta ce "Bismillah " Harara ya banka mata Tare da cewa "Nayi maki kama da Wanda zaici wannan jagolgwalon naki" Murmushi kawai tayi tare da cewa "Ai daman fita hakkinkane nayi na musulunci tunda bakaci ai shikenan " ta fad'a tana cigaba da cin abincinta hankali kwance MD ganin Tana gab da cinyewa gashi har ga Allah Kanshin abincin Ya Dakeshi da yawa zaizo yayi taste kallonta yayi yaga ta kusa cinyewa gashi baison Raini daga wajen yarinya hakan ya sanyashi linke Laptop d'inshi tare da cewa "Zoki kaimun laptop d'innan daki" kamar zatayi bataji ba saikuma ta mik'e taje ta d'auka tare da nufar d'akin yana ganin shigarta ya sauke ajiyar zuciya Tare da yunkurawa ya kai one spoon bakinsa lumshe ido yayi jin special girkin da ya mance yaushe ya tab'a cin irinsa Dan dadi dukda yana yawan cin indomie amma zai iya cewa bai tabajin mai dad'in wannan ba "Jin Fitowarta ya sanyashi saurin komawa kujerar da yake ya wani had'e Rai itako murmushi tayi dukda bata ga sanda ya ciba D'aukar plate din Tayi Tare da nufar hanyar Kofa Dan takaiwa mai gadi ta Riga ta k'oshi" ina zaki?Ta tsinkayi muryarsa "Mai gadi zan kaiwa sauran na k'oshi" Dawo ki Aje Ba sai kinkai masa ba ki kai kitchen ki Aje Ko ki zubar "Amma ai fariya ba kyau ma bari na kai masa "wani kallo ya watsa mata turo baki tayi dayin gunguni " Nuna kanshi da hannu yayi Alamun ni"Cikin Sauri ta ce "To me nayi maka kuma " Ta fad'a tana Kara turo baki"Okay zakiga abun da kikamun ya fad'a yana Mikewa cikin Sauri ta hade rai Tare da cewa "Nifa ba abunda nayi maka Saidai kawai idan Zalina kake son ci " ganin ya nufo ta ya sanyata saurin Aje plate din kasa tare da rugawa tayi bedroom murmushi Kad'an yayi tare da d'aukar plate din indomie d'in yakoma kujerar da yake Ya zauna ya fara ci a hankali yana lumshe ido Alamun dad'in ya kai masa karo Zarah jin shiru bai biyota ba ya sanyata sauke ajiyar zuciya Wayarta da taga Ya aje kan centre table ta d'auka da Jakarta daman hijab d'inta na jikinta ta fito wara idanu tayi ganinshi zaune ya na cin indomie d'in da tayi saura yana ganinta Ya wani had'e rai Itako Dariya ta babbake da ita hada rik'e ciki kallonta ya tsayayi da mamaki yanda take dariyar shi kanshi saida ta bashi mamaki daman tana Dariya har haka kenan?ya tambayi kanshi sai kuma ya kalli indomie d'in hannunshi ya tabbatar da ita takewa Dariya Kara hade rai yayi tare da cewa "Keeee meye haka" Cikin Sauri Zarah ta daidaita nutsuwarta Tana Boye sauran dariyarta ta ce "Bakomai naga kana cin jagolgolo ne shiyasa Nayi Dariya" Tsaki yaja tare da banka mata wata Hararar ya ce "Da yake ke Kika zo da indomie d'in da bazanci ba ko?Tana boye dariyarta ta ce " A a a yi hakuri kayan Kane nima arziki ne naci Thnks "ta fad'a tana daidaita tsayuwar Hijab d'inta tare da Yin hanyar Fita tana turawa taji arufe ta waiga ko zataga makullin amma babu Kallonshi tayi da ya mik'e ta ce " Zan tafi school ina da lectures Yanzu karna makara please zoka budemun "ba inda zaki Bazakiyi lectures d'inba Yau "yana gama Fad'ar haka yayi shigowarshi bedroom batare da ya waiwayeta ba..........โœ๐Ÿฟ

*07026166536*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐Ÿ‘ฏโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘Ž๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*


1, *MU GANI A ฦ˜ASA...*๐Ÿ”ฅ
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ฦ˜WAI..*๐Ÿฅš
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*๐Ÿ’ฅ
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐ŸŒŽ
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huษ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษ—aya N300

*DOMIN TURA KUฦŠIN KAI TSAYE*๐Ÿ‘‡

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya๐Ÿ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTN๐Ÿ‘‡

0814 179 9224

ฦณan ฦ˜asar Niger zasu tura nasu anan.๐Ÿ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huษ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษ—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐Ÿ”ฅ๐Ÿฅš๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŽ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ


_*Miss Hajo Ce*_๐Ÿค™๐Ÿฟ
[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy: ๐Ÿ…ฟ๏ธ........*45 & 46*


Sak taga Matar kamarta daya Da ya Musty kamar yanda take ce masa ba banbanci kamar an tsaga Kara an karya lallai Allah yayi kama a nan ta fad'a cikin ranta
Cikin fara a Ammy tayi welcoming d'insu Bayan ta zauna Har kasa suka Duka suka ce "Ina yini Ammy ya jiki" Alhamdulilla jiki da sauki ya hanya kunshawo tafiya ko sannunku ko "Murmushi sukayi Chuchu ce ta shigo Tare da maid house din gidan ubayen kulol A hannunsu da kayan makuleshe daka Kalleta zagaka tana cikin farinciki zaunawa tayi gefen Zarah tana kama hannunta ta ce " Ammy Kinga takwarar taki fa "Cikin fara a Ammy ta ce " Ah masha Allah Ba shakka takwara taho kusa dani "ba musu Zarah ta je gefen Ammy ta zauna kallo d'aya Ammy tayiwa Zarah taji yarinyar ta shiga ranta over duba da irin nutsuwarta ga hankali uwa uba tarbiya sosai Ammy ta kwadaitu da hada zuri'a a Zarah taji inama tana da wani d'an namiji da ta had'ata dashi Sosai Ammy ta dinga nan nan da su Zarah an cika musu gaba da abubuwa Wanda suka rasa ma yanda zasuyi da su Sosai Chuchu da Ammy suka karrama su a gidan kamar wasu sarki Sai wajen La'asr Sukayi musu bankwana Ammy ta ce " Har tafiya yarana ai na zata Kwana zakuyi mana"murmushi Zarah ta yi ta ce "Ai zamu dawo Ammy Allah ya k'ara sauki" Ameen y'an kirki mungode mungode Allah bar zumunci nagode sosai wlh"Murmushi sukayi su kansu har mamakin irin godiyar da Ammy take musu suna nan tsaye Chuchu ta fito da k'atuwar leda a hannunta har rinjayarta take Hijab a jikinta Tana kwabe fuska ta ce "Muje to momcy amma wlh ni nafison ku kwanar mana fa" Hararar wasa Zarah tayi mata ta ce "Bana fad'a maki zamu dawo ba" Badan Chuchu ta so ba ce "Muje to driver ya kaiku" Dubu ashirin Ammy ta zago ajika tare da mik'awa Asmy ta ce "Gashi nan kunyi transfort" girgiza kai sukayi suka ce "Allah Ammy ki bari " ba yanda Ammy batayi dasu ba su amsa sai Chuchu ta amsar musu da niyyar idan sun fita Ta basu suna fita Chuchu ta hau kwalawa driver kira Yakai nawa amma bata ganshi ba Kallon Mai bawa flowers ruwa tayi ta ce "Wai ina sani ya shiga ne " cikin girmamawa ya ce "ranki ya dad'e ya fita ba jimawa gidan marayu mai gida ya aike sa"okay Yayan bai dawo ba kenan" Eh ya fad'a "Kallonsu Asmy chuchu tayi ta ce " Dan Alla ku jira yayana ya dawo ku gaisa"gwalo idanu Zarah ta yi ta ce "Ki duba time fa Chuchu karfe biyar saura kinsan hanyar nan tayi dare ba kyau ki bari sai wani time d'in kawai " cikin shagwaba Chuchu ta ce "Amma banso baku gaisa da yayana ba wlh To ku bari driver ya dawo yanzu saiya mayar daku har Zaria " Asmy ta Kalleta ta ce "Ki bari Chuchu kawai mungode mun koma a motar haya wlh kar dare yayi "to ku bari na d'auko mota mana na kaiku garrage din Kunga kun rage tafiya" Dariya Zarah tayi ta ce "Ai bazan hau tukin ki ba wlh " itama dariyar Asmy tayi ta ce "Chab Bafa zanhau ba wlh nima in kin ganni lahira kaini akayi kawai kina wannan rawan kan ki kifar damu" Dariyar da bata shirya ba Chuchu tayi ta ce "Wlh na iya shekara nawa ina driving Kudai kawai tunda kunkawo k'abli da ba Adi muje na rakaku " A tare suka fito Su Ukku suna tafe suna Hira Sosai sukayi nisa amma basu samu abun hawa ba Daman kuma haka yanayin unguwar yake samun abun hawa akwai wahala musamman magriba tayi "Kallon Chuchu take hucin gajiya Zarah tayi ta ce " ki koma Chuchu mungode wlh Kinga mu biyu ne ke kuma ke kad'aice jifa tafiyar da kikayi zamu samu abun hawa fa "Tana hak'i Chuchu ta ce " kuma hakane Amma nafison naga samun abun hawanku tukwana "murmushi Zarah tayi mata ta ce " karki damu dia zamu samu"Ledar hannunta Chuchu ta saka kudin aciki Dan karsu gani tare da dungurawa Asmy ta ce "Hajjaju amshi ke zakiyi dakon kayan nan Dan wlh momcy na bazata wahala ba " Harararta Asmy tayi ta ce "Sannu mai momcy kinjama bazan dauka ba saidai momcyn taki ta d'auka"marairaicewa Chuchu tayi ta ce " Sorry Besty wasa nake maki "Saida sukayi hug din juna tukwana Chuchu ta juya tana musu Godiya Suma suka kama hanya Inda idan Zarah ta gaji Asmy ta amshi Ledar Dan akwai nauyi kayan saida suka daga sukaga atamfofi ne da shaddoji sai kayan costimetics jinjina kai Asmy tayi ta ce " Gaskiya ammyn nan Nada kirki wlh basu da girman kai Sam na masu kudi"Itadai Zarah murmushi kawai tayi sosai suka tsorata har bayan magriba basu samu abun hawa ba ga tafiyar da suka sha Dan ko gidansu Chuchu basa hangowa zarah sai hak'i take ta ce "Wlh na gaji nikam" Daurewa zamuyi muyi ta tafiya ko Allah yasa a dace Haka suka dinga tafiya ba Alamun abun hawa Sai manyan motoci jefi jefi dake gittawa titin suna tafe sukaga wata mota dalleliyar mota har tayi gaba sai kuma suka ga ta dawo gabansu ta tsaya gefensu inda suke sauri_sauri gudu gudu sukayi Dan a tsorace suke "Mamy " ta tsinkayi muryarsa saida tayi shock a wajen jin muryar da batayi tsammani ba ko a mafarki cikin dauriya da k'arfin hali ta juyo Idanunsu ne ya sartse cikin na juna ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login