Showing 120001 words to 123000 words out of 153980 words
gidan Dan son shawo kan Ammy amma bata kulawa wani lokacin ma tashi take ta basa wajen Dan ba abunda yafi mata ciwo kamar idan ta tuna wai Dan Matar d'aya aura a boye ta haihu suce mata Dan ko d'iyar ya mutu ya kaiwa Amera ace ita ta haihu idan ta tuna wannan Abun sosai takejin zafi a ranta tana tunanin yaushe MD ya zama marar imani haka a saboda da matarsa ya saka wata cikin wani hali hakan yasa ko tayi shirin sassauta masa take fasawa sosai MD ya shiga damuwar da bai tab'a shiga irinta ba ga sosai yakeson ganin Zahra saboda ya ganta kullum yana gidan Amma ko giccinta baya gani mamaki yake to ina Ammy ta kaita yauma yana zaune a palour shida Ammy dake kallo tayi banza ta kyalesa cikin dauriya ya ce"Ammy bazan gaji da baki hakuri ba Dan Allah ki yafemun"Kallonsa ta k'asar glass Ammy tayi taga harya rame.sosai yaso bata tausayi amma ta fusge ta ce "Na fad'a maka ka daina bani hakuri me kayimun " Shiru yayi yana sauke numfashi kafin ya d'ago ya ce "To Ammy Ina Mamyn ina kika kaita" wacece haka?Ammy ta tambayesa dukda tasan da wacce yake Dan baya fad'ar mai irin sunanta "Saida tadanyi shiru kafin ya ce " Takwarar taki"Wani irin kallo Tayi masa ta ce "Ina ruwanka da ina take ai babu wani abu tsakaninka da ita Illa iyakar ta Haifa maka abunda ke cikinta a ranar ta mik'a maka Ka kaiwa Matar gold Matar so da tafi duka mata kyau da Asali "Innalillahi " MD ya fad'a a ransa Kafin ya ce "Ammy ba haka bane Dan Allah"Tsaki Ammy taja ta mik'e ta ce " idan kagama zaman ka rufemun palour "Dafe kansa dake Sara masa MD yayi Yasan tsananin fushi Ammy take dashi kafin ya ce " Allah yasa basu fad'a mata haka ba ta k'ara kullatuwa dani"Tunani yake ina take,sosai yakeson ganin ta yanda shi kanshi baiyi tunanin zaiso ganin wani Abu da yayi kewa kamar yanda yake son ganinta ba wayarsa ya janyo tare da kiran Chuchu yace "Kizo ina son ganinki palourn k'asa" koda Chuchu tazo sosai tayi mamakin Ganin ramar da Yayan nata yayi Daka Kalleshi kasan baya cikin yanayi mai dadi dukda yaji haushin abunda yayi kusa dashi ta zauna ta ce "Ina yini Yaya" Lafiya qlau "ya bata amsa a takaice tana ganin yanda ya had'e fuska tamau" Ina Mamy"ya tambayeta"Shiru tayi tana nazarin. Wa yake nufi da haka Kallonshi tayi ta ce "Yaya ko Momcy kake nufi " a takaice ya ce "Eh " Ohh tana sama Bacci ma take"Nauyayyar Ajiyar zuciya taga ya sauke kafin ya Mike ya nufi hanyar sama "binshi da gudu Chuchu tayi ta ce " Dan Allah karkaje Ammy ta hana fad'a zatayi mun"Hararar d'aya watsa mata ce ya sanyata Jan bakinta tayi shiru yana haurawa sama kai tsaye d'akin Chuchu ya nufa Yana shiga ya sameta kwance tana bacci hankali kwance daga ita sai wata doguwar rigar Chuchu kasancewar rigar bata da nauyi yaba cikinta damar bayyanuwa a hankali MD ya zaune gefen gadon saitin da take kafeta yayi da Kallo bako k'iftawa beauty face d'inta kawai yake kallo Ajiyar zuciya ya sauke koba komai ya rage damuwar dake cinsa a hankali ya shafa cikinta tare da sumbatar cikin ya ce "I love you more my unborn Allah ya fito mun da kai/ke Lafiya Ganin tayi motsi kamar zata tashi ne ya sanyasa saurin matsawa ganin ta koma bacci ne ya sanyasa sauke ajiyar zuciya saida MD ya shafe 20 minutes a d'akin yana kallonta kafin ya Mike ya fito a palour ya samu Chuchu na chart hanyar fita yayi " Zey na gida"Yafada kamar bashi yayi maganar ba"Eh yaya tana gida Sundawo "bai amsa mata ba yabar gidan kai tsaye MD gidan Zey ya nufa Wanda harya mance rabonshi da gidan Palourn ya zauna yaranta duk sun baibayeshi suna murnar ganinsa sai tsalle suke mai yana musu murmushi da wasa jin suna oyoyo uncle ya sanya Zey ganewa yaya md ne da Fara a tashigo d'akin ta ce " Yaya yau Kaine a gidan namu kamar kayi Batan kai"b'atan kan nayi Shiyasa kika ganni"ya fad'a yana sanyawa Mimi da Daddy sweet a baki "Dariya Zey tayi tana zaunawa ta ce " ina yini Babban yaya"Bayan sun gaisa Ana shirin gabatar masa da abinci ya ce "Ki barshi ina Sauri magana nazo muyi" Kallon su Mimi tayi ta ce "My Daughter My son ku wuce waje mai lesson dinku yazo" Suna barin d'akin MD ya sauke ajiyar zuciya kallonta yayi ya ce "Nasan kunyi magana da Ammy kinji duk abunda ya faru" Jim tayi kafin ta d'ago ta ce "Eh Tun a waya ta kirani ta sanar mani to kasan bama k'asar Duka sai shekaranjiya muka dawo ina ma son zuwa gidan to dadyn su Mimi na gida pull time sai yanzu ya fita ina shirin injema gidan kazo"Okay kinsan da Ammy fushi take dani taki saurarata shine nazo wajenki nasan zaki iya taimakamun wajen shawo kanta" numfashi zey taja kafin ta d'ago ta ce "Insha Allahu Yaya Amma kaima yaya sai nakega baka kyauta ba lokacin da ammy ta labartamun ba karamun mamaki nayi ba wlh Naji yarinyar ancema kawar Chuchu ce " Numfashi yaja ya ce "maganar kyautawa da Rashin kyautawa Duka wannan ya wuce tunda Mai faruwa ta Riga ta faru " Hakane.kam yaya Allah ya kyauta insha Allah zamuyi magana da Ammy"yawwa Zey Thnks ya fad'a tare da mik'ewa yayi mata bankwana ya wuce Abuja wani meeting da aka kirasa a ranar Zey tazo gidan koda ta fara bawa Ammy hakuri Akan ta janye fushin da take akansa ce mata tayi "Zainab ba fushi nake dashi ba ina kwatarwa yarinyar nan hakkintane yasan darajarta tafi yanda yake Tunani" numfashi zey taja ta ce "Kuma fa hakane Ammy Tabbas ciwon y'a mace na y'a mace ne Amma a sassauta masa " Shiru Ammy tayi ta kyaleta "Mikewa Zey tayi ta ce " bari naje mu gaisa"lokacin da ta isa palourn Sama Zahra na saman sallaya tana karatun qur'ani Chuchu na gani Zey ta guda da gudu ta Rungumeta ta ce "oyoyoy My Aunty nayi missing naki sosai ya Paris din " Murmushi Zey tayi tace Alhmdllh Auta "ina su Mimi" Ta tambayeta"Suna gida Ana musu lesson shiyasa bantaho dasu ba dayake ba jimawa zanyi ba "ayya naso ganinsu Ina Tsarabata" Tana Chan kije ki amsa da kanki kinsan dai ba kawo maki zanyi ba y'ar rainin hankali ina yayarki a gari amma saikiyi watanni bakije Inda nake ba ni bama wajenki nazo ba wajen Auntynmu nazo"Dariya Chuchu tayi sai sannan ta kalli Chuchu da ta Aje qur'anin ta ce "momcy ga fa Aunty Zey yayatace daga yaya sai ita saini" Murmushi d'auke da fuskar zahra ta ce "Ina yini" Cikin fara'a zey ta ce "Lafiya qlau momcyn mu ya jiki" Alhmdllh "ta fad'a kasa_kasa" masha Allah Allah ya k'ara sauki bari na wuce saina dawo ina Sauri"Murmushi Zarah tayi ta ce "A gaida gida Kallon zahra Chuchu tayi ta ce " ina zuwa momcy bari na raka aunty"gyada mata kai tayi"Suna fitowa Zey ta kalli Chuchu ta ce "Wlh yarinyar tayimun ji nutsuwa da hankali gata da kyau masha Allah jifa duk yanda ciki kesa ayi muni Amma ita kyanta na nan " Dariya Chuchu tayi ta ce "Ai da tafima haka kyau wlh Aunty bari ta haihu kiga ta koma asalinta " Har suka Iso palour Zey na yaba zahra Zaunawa tayi gefen Ammy ta ce "Wlh Ammy Yaya ya rasa wannan ya yi Babban rashi da asara Dan wlh bazai samu kamarta ba Dan Allah Ammy karki yarda Su rabu Tunda gashi hada rabo tsakaninsu" Harararta Ammy tayi ta ce "Ke daman ai Chan bakinku d'aya babu ruwanki da duk hukuncin da zan yanke dole ya rabu da ita tunda ba kaunarta yake ba jira nake.kawai ta haihu na amayar da duk abunda ke cikina a kansa " Jan bakinta Zey tayi shiru ta ce "Amma Ammy sainakega kamar ba yaro d'ayane cikinta ba jifa girman cikin yakamata ayi scanning asan meye cikin Dan mufara sayayya kar wuri ya K'ure Dan daga gani ta kusa" Nasa Dr yayi mata scaning Nasan komeye ciki harma na sanya ayo order kayan daga Dubai jibi ma zasu iso "Ammy nawane?basaikinji ba ta haihu kingani" Marairaicewa Chuchu tayi ta ce "Dan Allah fad'a mana nima inason na fara sayayyar kayan baby" Jin haka ya sanya Ammy cewa "Triplet ne amma Karku fad'awa kowa koshi ko ita kada Wanda Naji kun fad'awa" Sosai suka Zarah ido a tare sukace y'an Ukku Ammy"Dariya Ammy tayi ganin yanda sukayi Chuchu ta buga tsalle ta ce "Wayyo Allah dadi wlh Ammy karkiji yanda na k'agara Momcy ta haihu naga jinin yaya wayyo Allah y'an Ukku a gidannan" Zey ko hamdala tayi ta ce "Allahsrk yaya Double Allah yayi masa Ammy Banmasan wani irin farinciki nake cikiba" murmushi d'auke da fuskar Ammy tace "baku kaini farinciki ba Zey ranar da aka fad'amun kwana nayi ina Godiya da Allah Dan al'amarin nan gaba d'aya ikon Allah ne Amma Karku fad'a musu Kuyi sayayyarku kawai" Insha Allah Ammy bazasuji ba "Tundaga ranar Zey tahau uwar sayayyya komai Ukku takanas ma kawarta takira dake Paris tatura mata kudi akan tayi mata sayayyar kayan jarirai na triplet yawan kudin ma data tura mata saida nayi mamaki yanda kasan ita ce Zata haihu cikin sati uban kayan suka iso akwai kusan goma banda abun goyon jarirai na ciki irin na turawan nan shima komai ukku Chuchu ma Sosai take jibgarta sayyya itadai zahra nata ido bata tab'a tanka mata akan sayayyar dataga tana lubgowa ba Ammy ko ba amagana Dan har kekunan wasa yara saida ta sayo daki guda ta ware ta cika kayan jarirai dashi da gadon kwanciyarsu keken koyon zama kai komai Wanda wani ma baka tab'a ganinshi ba saida Ammy ta had'o mai gayya kwa mai aiki kwata kwata hankalinshi baya jikinshi baimayi tunanin fara wata sayayya ba duk yanda yaso koda ganin Zahra Ammy ta kasa ta tsare bangaren zahra ba laifi zaman gidansu Chuchu yayi mata dadi saboda wata irin kulawa da suke bata a halin yanzu cikin zahra ya shiga watan haihuwa sosai Ammy da Chuchu suka ninka kulawar da suke bata kaffa kaffa suke da ita sosai dan sosai Ammy ke tausaya mata nauyin cikin yara Ukku ba wasa yau zahra tunda ta tashi takejin sauyi tattare da ita Hakanan dai ta daure batare da ta nuna komaiba tun safe tun tanajin Abu Kad'an har yazo yayi yawa Sosai take zufa a d'akin tana yarfe hannu tuni ta fara fita hayyacinta sunan Allah kawai take Ambata a haka Chuchu ta shigo ta sameta tana ganin haka a d'imauce ta ruga wajen Ammy ta ce "Ammy kizo kiga yanda momcy take zai zufa take kamar ta mutu" ba shiri Ammy ta mik'e ta sanya hijab d'inta ta ce"inaga haihuwarce tare suka koma d'akin Inda suka tarar da Zarah na murkashi Sannu Ammy tayi mata tare da kamata ta kalli Chuchu tace "yi Sauri D'auko hijab d'inta Da Sauri Chuchu tasa mata hijab tare da takalmi su biyu suka kamota har wajen motoci Inda Chuchu ta kwalawa driver kira ba shiri yatado mota Tare suka shiga su Ukku Chuchu dukta rude asibitin mafi kusa dasu suka nufa da ita Inda suna isa aka wuce labour room da ita zirga zirga kawai Ammy take da Chuchu Sosai zahra take karb'ar wuta tayi awa guda tana wahaltuwa sosai takejin wata irin azaba da tunda uwar da ta haifeta bata tabajin irinta ba D'aya Daga cikin likitan d'aya duba ta ya fito ya kalli Ammy ya ce " A Gaskiya Hajiya Kuyi hakuri Ayi mata cs bazata iya haihuwa da kanta ba sakamakon Rashin bud'ewa da batayi ba na Auna bata Inda zata iya haihuwa Inma akace dole saita haihu da kanta Gaskiya zata wahala over sannan abunda ke cikinta Shima zai wahala"Innalillahi Ammy ta fad'a ji take kamar ta fashe da kuka ta ce "Dr Kuyi mata Cs din kawai Kar wani abun ya sameta" Chuchu ko kuka ta fashe dashi Okay "Zamu shirya yi mata yanzu amma ana buk'atar ganin mijinta da mahaifinta da Susa hannu" Ba matsala dr ku shiryata yanzu mijin nata zaizo saiya wakilci nbaban nata tunda emergency ne cikin Sauri Ammy ta kira MD Cikin tashin hankali ta ce "Ka sameni a asibiti" Bayan ta fad'a masa sunan asibitin ta kashe ba ayi 20 minutes ba saiga MD yazo afutatan wajen Ammy ya nufa ya ce "Lafiya ammy" Da sauki Zahra ce Zata haihu muka kawota sunce bazata iya haihuwa ba sai anyi mata cs shine muke buk'atar sa hannunka"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Ammy yanzu tana ina Ina ne za a sa hannun"Sosai MD ya rikice ya rude Shi ya sanya hannu kuma shi ya bada jininsa kasancewar group o garesa suna gani aka shiga Theater room da zahra sosai Chuchu ta fashe da kuka Ganin kamar zata rasa kawartata Ammy ma hawaye take tana addu'ar Allah sa ayi aikin lafiya MD ma addua kawai yake hankalinshi a matuk'ar tashe yake "Ba ayi 30 mminutes ba sukaga fitowar dr D'auke da jariri a hannu fuskarshi d'auke da Fara'a suna ganin haka suka Kallesa Ammy ta ce " An sauka"Alhmdllh Dr ya fad'a yana mik'a mata jaririn"Amsar jaririn Ammy tayi "Allahu akhbar Allahu akhbar" kawai Ammy ke fad'a ganin yau ita ce rik'e da jinin MD a hannunta shiko gogon har yanzu gaba d'aya hankalinshi yana kan ga wani hali zahra ke ciki Nurse biyu suka ga sun Kara fitowa rik'e da wasu jariran a hannu"sai sannan MD ya kusa daskarewa ganin sun nufo su da Yaran Daya daga cikin nurse ta mik'awa MD.jaririyar ta ce "Congratulation Sir Allah ya raya" d'ayar kuma ta mik'awa Chuchu da itama ta daskare a wajen Kallon y'ar MD Yayi ya kalli sauran yaran dake hannun Chuchu da Ammy kamar Wanda bakinshi yayi masa nauyi ya ce "Kuna nufin Duka yaran nan aka ciro kuma Duka nawa ne" Murmushi nurse din tayi ta ce "Triple ta haifa gasunan Allah raya "farincikin da MD ya shiga fadarsa bata baki ne ji yake tamkar a mafarki wai yau shine Allah yaba yara har Ukku baisan lokacin da wasu hawayen farinciki suka zubo masa ba ya goge ya ce " Alhmdll.......✍
*Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536*
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
_*Miss Hajo ce*_🤙
[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy: 🅿️.........*85 & 86*
Amera koda isarta jikin dadynta ta fad'a ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah dad ku fad'amun me yake faruwa bansan abunda ya faru ba hankali na bai kwanta ba " Lallashinta ya dingayi akan ta nutsu ba komai bane ta Bari ayi bincikike tukwana washegari dak'yal ta Bari gari ya waye ba yanda Mamanta batayi.da ita ba akan ta Bari a bincika aji gaskiyar Lamarin ta kiya ta ce "saitaje gidan Ammy tunda shi tayi ta kiransa kusan 1 week baya dagawa abunda baitab'a yi mata ba " girgiza kai mamanta tayi ta ce 'Ai daman Amera na fad'a maki tun ba yanzu ba akan ki tsaya kiyi zaman Aure kwata kwata rayuwar da kika zab'awa kanki ba rayuwar y'a mace mai mutunci bace"da Allah mom Ni kibarni Naji da abunda ke damu na fisabilillahi"ta fad'a tana yin gaba tana gunguni "Girgiza kai Hajiya Farida tayi ta ce "Allah ya kyauta"Dadynta ko zirga zirga kawai yake...k'arfe 7:am zaune suke a palourn Dagashi sai Ammy Bayan kiran gaggawa da tayi masa shiru yayi ya maida hankalinshi ga sauraron abunda take son fad'a masa fuska ba wasa Ammy ta ce " d'ago ka.kalleni babana"ba shiri ya d'ago yana fuskantar mahaifiyar tasa "Hannu Ammy ta mik'a masa ta ce " bani takardar Saki ukkun zahra "Lokaci guda MD yaji wani irin tashin hankali ya ziyarce sa a matuk'ar rude ya ce"Ammy saki kuma" Eh saki ko kana da wata maganar ne daman ba Dan ka saketa ka aureta ba,ba Dan ta Haifa maka d'a ko y'a ka aureta ba to ai burinka ya cika ta Haifa maka yara har Ukku kaga ko amfaninta a wajenka ya k'are dan haka ka saketa ta kama gabanta itama taje tayi Aurenta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa "Cikin tsananin tashin hankali ya ce "Ammy kiyi hakuri kibar maganar nan please ni har yanzu Mamy matsayin mata ta take kuma haka zataci gaba da zama insha Allah please Ammy kiyi hakuri kawai ki barmun matata kodan yaran nan Ammy kinsan d'an sai uwa please Ammy ina begging d'inki kidaina maganar sakin nan ba Ni Gaskiya bazan iya sakin Uwar y'ay'a na ba" ya fad'a kai tsaye "Sakato Ammy tayi tana kallon ikon Allah kafin ta tab'a hannu ta ce " ikon Allah daman Kasan da ruk'on d'a sai uwa ka shirya rabata da Y'ay'anta ka kaiwa Matarka Matar so da.kafi sonta da kowa inbanda asirinku ya tonu to wlh baka isa ba saika saketa"Hankali tashe ya d'ago ya ce "Ammy Dan girman Allah ki daina maganar sakin nan nifa bazan saketa ba period magana Zan zauna da ita na bata kulawa kodan yaranta Dan Allah Ammy naci darajan yaran nan"baka isa ba wlh watau nufinka Zama ka zauna da ita zaman Y'ay'anta lallai Babana kai harka isa ka zauna da zahra zaman Y'ay'anta zahra harta isa tayi zaman ,y'ay'a to bazata zauna dakai ba sannan