Showing 48001 words to 51000 words out of 153980 words

Chapter 17 - AUREN WATA TARA COMPLETE HAUSA NOVEL

30 Sep 2024

16352

"so " Sai Kuma hibba tayi Dariya ta ce "chab Wlh ki amince masa idan ba haka ba Zai Kadake a last paper baida mutunci wlh kuma d'an iskane na Bugawa a jarida haka sukayi Da wata budurwa yayata ta na bani labari daga tak'i amince masa wlh Ya kada ita a last paper kuma da gangan Dan Ance kokari gareta" wara idanu Zarah tayi ta ce "Na shiga ukku kuma shine kike cewa Na amince masa Bayan kinsan d'an iska ne " jamcy ce ta dafa ta ta ce "Karki damu ai ba kowa ake Kalla ayima zancen iskanci ba yanzu dai fad'a mana yanda kukayi dashi...nan ta basu labarin yanda sukayi hibba ta ce " To wlh tunda kikaji ya ce Aurenki zaiyi ki rabu dashi bazai maki zancen banza ba sannan kuma yana ganinki amerar makaranta kinsan ance d'an iska baya Auren y'ar uwarta y'ar iska Shima tagari yake nema wlh da gaske yake Dan tun sanda ake lecture na lura da irin kallon k'urullar da yake maki nasan sonki yake ki rabu dashi kawai kuyi soyayya "tab'e baki Zarah tayi ta ce"Bama sai Inda ya k'ara gani na ba.....Koda Tabawa su Asmy labari suma irin yanda Su hibba suka fad'a mata haka asmy ta bata shawara ita dai jinsu kawai take Amma batajin zata iya soyayya da wannan Bayan akwai baikon Aurenta da Hafiz (Nikam nace again kuma ga auran md akanki)Chuchu kuwa cewa tayi"Karki biyeshi momcy bazai kada ke ba Inma ya kada ke ai akwai Allah Duk mutumin da Akace Dan iska ne kaji tsoransa kinganninan bana k'aunar Dan iska shiyasa ko huld'a banayi dasu tunda nazo makarantar nan ba kowa nake abota dashi ba Saboda tsaro ku kadaine zance aminai na kuma Dan na yarda daku 100% na tabbatar kudin mutanen kirki ne kuma tare na daku na k'aru da abubuwa Dan haka Ina baki shawarar kawai kice masa an sanya miki Aure a wuce wajen"Zarah ta ce "Daman Chuchu duk jinsu nake wlh shawararki ita ce shawarar kirki sai sannan Asmy ta ce " Kuma fa hakane "a zuciyarta Asmy ta ce " Astagfurillah to ya matsayin Auren nan na Zarah yake a musulunce laifi ne tayi mu'amula da maza"wata zuciyar ta ce "Mata ai Aure duk Aure ne ko wayar da take Da hafiz haramun ne" Sosai taji gabanta ya bada daram Zarah ko bata tab'a kawo wani Aure a kanta ba harkar gabanta kawai take Dan mancewa ma take da wani Aure a kanta Dan bata d'auki Auren Aure ba dukda ta na da ilimi....Yau Zarah ta shirya tayi kyau sosai Cikin doguwar rigarta Abaya Black mai shegen kyau hijab ta d'auko zata sanya Chuchu ta rik'e hijab tare da cewa "Haba Momcy kici gayun nan ki sanya hijab Allah ban yarda ba gyale zakisa ai ba matsatsun kaya bane sannan Ko larabawa ai sanyawa suke har suyi salla ma dashi please ki yafa gyalen wlh sai kinfi kyau" Badan Zarah taso ba dole ta yafa gyalen nanko Chuchu ta shiga koda da tana cewa "Wow Momcy wlh kin hadu yanda kikasan wata first Lady taho muyi hoto ta fad'a tana shiga snap" Murmushi kawai Zarah tayi nan ta shiga kashe musu hotuna masu kyau chuchu ce ta ce "Wlh momcy karkiga yanda kikayi kyau aikedin Matar manya ce wlh ba yara ba da yaya na kika dace bada kowaba" Harararta Zarah tayi ta ce "ba nace ki daina had'ani da Yayan naki ba ni ta Hafiz ce ta fad'a tana mata far da ido" Dariya Chuchu tayi ta ce "Ki dai bar cika baki kika sani ma ked'in ko rabon Yayan nawa ce Saikiga Hafiz dinma ya mutu" Wara idanu Zarah tayi tare da Kai mata Dukan Wasa a baya ta ce "Ta Allah ba taki ba muguwa Ya Hafiz dina bazai mutuba sai yaga ma Auren jikokinmu" Dariya Chuchu tayi ta ce "Ah su jikoki manya sai mu gani Har na hangoki gidan yayana " Sanin Zarah ta biyewa Chuchu sai ta fasa fitar ya sanyata girgiza kai kawai ta fita ta ce "Dan yanzu Sauri nake ai zan dawo tare da fita daman Asmy ta fita yi musu chefane kai tsaye napep ta Tara Inda ta fad'a masa sunan unguwar da zai kaita kamar yanda Dr Halima ta turo mata sunan unguwa ta na isa Ta kirata ta ce " Aunty na iso nan tayi mata kwatancen Inda take"Dr Halima ta ce "okay ga yarinyata nan zata zo ta taho dake" Zarah na nan tsaye taga wata yarinya da bazata wuce sa'ar khairat din gidansu ba Ta na ganinta ta gane y'ar Dr Halima ce saboda kamar da suke Yarinyar ta gaishe da Zarah ta amsa mata da murmushi Tare da kama hannunta har suka Isa gidan Cikin mutuntawa Dr Halima ta tari Zarah tare da cewa"oyoyoyo Amarya Yau dai Allah yayi Gaki a gidana "Murmushi Zarah tayi tana zama ta ce " ina yini Aunty munsameku lfy"Alhmdllh Zarah ya kwana da yawa kin bace ko ya amarci"Murmushi kawai Zarah tayi ta na kasa da kanta kafin kace me an cika mata gabanta da abubuwa har mamaki tayi irin tarbar da aka mata Inda Dr Halima ta tsareta saida ta cicci wasu sosai Zarah ta yaba da kirkin Matar wajen magriba Zarah ta ce mata zata tafi sosai Dr Halima ta cikata Da abubuwan Arziki su turarruka masu kamshi sai Godiya take mata akan ziyarar da ta kawo mata ita dai murmushi take har waje ta rakota tare da cewa"A dai cigaba da hakuri Zarah zaman Aure d'an hakuri ne Sannan ki dinga yiwa mijinki biyayya Allah babu ruwansa da bakyason Auren zai kamaki da laifin hakkin mijinki muddin kina tauye masa"da mamaki Zarah ta d'ago ta na kallon Dr Halima gabanta na fad'uwa ta ce "Dr kina nufin kinsan komai " Ganin yanda ta rikice lokaci guda ya bawa Dr Dariya ta dafa ta ta ce "Baki d'auke ni y'ar uwa ba kenan ina son ki daukeni yar uwa a garin Nan kamar yanda dr aliyu ya fadamun bakisan kowa nan garin ba Aure ne ya kawoki sannan shima mijin aiki ne ya kawoshi garin Zarah Ai Dr ya fad'amun komai ya ce " Auren ne bakiso shysa ma ranar Har hakan ta faru kiyi hakuri ki zauna da mijinki lfy kinji kanwata "Boyayyar Ajiyar zuciya Zarah ta sauke a zuciyarta ta ce " Dr d'innan Allah ya hore masa iya tsara karya Munafiki da Aikin lawyer ko jarida ya dace bada Asibiti ba a fili kuwa murmushi tayi ta ce "Insha Allahu Aunty ki koma zan samu abun hawa" To nagode a gaida mai Gidan nima saina shigo gidan naki insha Allah"sannan ta mik'a mata 500 tace gashi kiyi abun hawa"Kin amsa Zarah tayi ba yanda batayi da itaba amma taki amsa Cikin unguwar taci gaba da tafiya Dan bataga Alamun samun abun hawa nan kusa ba ga kiraye kirayen magriba da Aka fara tana cikin tafiya Taji parking d'in mota bayanta bata waigaba saboda a matuk'ar firgice ta ke "keeeee" Ta ji anfada Wanda ya tabbatar mata da ita ake da wata zazzak'ar murya Saurin Juyawa tayi Ganin fuskar da bazata tab'a mantawaba da ita ba a rayuwarta ya sanya gabanta fad'uwa tare karawa saurinta volume Binta yayi yana kiran keeeee amma bata waigo ba Zarah batayi aune ba saiji tayi anyi charab an d'auketa wutsil wutsiltu ta fara tana yagushinshi tuni hawaye harsun wanke mata fuska ta ce "Meye haka Malam ka ajeni " Baimasan tanayiba bai direta ko ina ba sai Gaban mota tare da rufewa ya zagaya tashiga driver sit ya tada motar a guje yabar wajen.....✍🏿
_Ki saya da zuciya daya y'ar uwa Dan girman Allah kar a fitarmun da Littafi kud'in karantawa kuka biya ba na mallaka ba_
*07026166536*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*


1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨




_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy: 🅿️.........*33 & 34*


"Kana nufin Dr Had'in baki kukayi batare da izini na ba kuka dauramun Aure ?daman lokacin da Asmy tayimun maganar nan kunrigama kun gama komai sannan ta fashe da kuka ta ce " Wlh Dr banyarda ba Saidai a farke.Auren "Lallashinta sosai suka shigayi cikin magana mai dadi da kwantar da hankali har Dr ya samu Zarah ta tsagaita kukan Dagowa tayi da rinannun idanunta da sukayi mata ja ta ce " ya na Ina Dr ku sa ya rubuta takardar saki ya bani kamar yanda kuka k'ulla Auren haka zaku since Dan wlh bazan iya kai tsawon wata Tara da Auren mugun azzalumi macucin mutumin nan ba"numfashi Dr ya ja ya ce "Karki damu Zarah zai sakeki Ai ba Aure bane kamar ko wanne Aure ne akayi a bisa larura insha Allahu karki damu baza akai wata Tara ba sannan ya d'ora da cewa Dan Allah karki kullaci y'ar uwarki batayi hakan Dan komai ba saidan k'aunar da take maki ki nutsu kiyi tunani Zarah Asmy bata chanchanci haka daga gareki ba" Zarah batace uffan ba Dan har yanzu Abun nan ciwo yake mata sai Mikewa da tayi Dr ya bita da Kallo ya ce "Ina zaki kuma" Hostel "ta fad'a ta na kauda kai" d'an murmushi yayi ya ce "to Malama Zarah kin Sallami kanki Da kanki kenan" Turo baki tayi batace uffan ba "Jaber ne yayi murmushi ya ce " Muje na saukeki "wani banzan kallo ta watsa masa tare da Jan tsaki ta ce" bana buk'ata "Saida ya kumshe dariyarsa Dr ne ya ce " To ni na kaiki ko nima fushin ake dani"Ta na kauda kai ta ce "Zan tari napep naje ba sai an kaini ba " da kyal Dr ya samu ya shawo kanta ta yarda shi ya kaita amma jaber firr kiyawa tayi a lokacin da Aka sallameta Dr Halima bata kan Aiki Taso suyi bankwana amma kuma bakomai ai tunda suna da number wayar juna sun dinga gaisawa.
Har suka isa makaranta Zarah bata magana shine de sai zuba yake ya na bata kamalai masu kwantar da hankali akan wannan din ba wani Abu bane Tayi hakuri ta dauki hakan ba komai ba ita dai jinshi kawai take ya na sauketa Ya ce "To Malama Zarah sai ankawo mana ziyara k,o?,Wani kallo tayi mata tare da kauda kai tayi gaba batace uffan ba Dan Shima mugun haushinsa takeji shikam murmushi yayi harga Allah yarinyar na burgesa sai yanzu yake Danasanin k'in Aurenta shi da kanshi da yayi (Nikam nace Gaskiya Dr da jaber kun rainawa zarah wayau )
Zarah na isa hostel bata iske kowaba hakan ya tabbatar mata da Suna lectures Cire hijab d'inta tayi Tare da hayewa Gado Bayan ta jona wayarta chaji da tayi kwana hud'u rufe Ta na nan Kwance ba bacci take ba tunanin rayuwarta take tun daga farko tanajin zafi a cikin zuciyarta Ji take inama tana da wanda zata fadawa sirrinta taji sanyi Goge hawayenta tayi ta ce " Allah ya jikan ki Mamana ke kad'aice sirrina kuma a halin yanzu bakya raye dukda ban sanki ban san wani naki ba ko da danginki na gani da zanji sanyi a raina"
Around 2pm Chuchu da Asmy suka shigo Bayan dawowansu daga lectures sosai suka yi murnar ganin Zarah da farinciki Chuchu ta ce "Kindawo kenan momcy Sannu da dawowa ya mai jikin" Dagowa tayi ta Kalleta tunani tayi wane ba lfy Hakanan dai tayi mata murmushi ta ce "Da sauki" Allah ya k'ara sauki Ai Asmy ke Cemun Matar babanki ce ba lfy "jinjina mata kai kawai Zarah tayi Asmy ce ta ce " kindawo lfy Zarah"banza zarah tayi mata tare da Juyawa ta lumshe ido kamar mai bacci sosai hakan ya bawa Chuchu mamaki Dan tsawon rayuwarta bata tab'a ganin haka tsakanin wannan y'an uwanba Dan ita duk daukarta cousin sisters ne badai tayi magana ba.
Tunda zarah ta dawo bata da wata walwala sanyinta ya karu fiye da Wanda take dashi Batayiwa Asmy magana Wanda hakan sosai yake damun Asmy Chuchu ma harta fahimta koda ta tambayi Asmy me ya had'asu cewa tayi sundanyi fadane zasu shirya.... yau Zarah Bayan fitowarsu daga lectures zaune tayi bakin wani block book ne hannunta amma kwata_kwata Hankalinta baya ga littafin ta Lula duniyar tunani har abokinta Yusuf yazo ya zauna bata sani ba saida yayi mata tabi tukwana ta dawo hayyacinta kirkirar murmushi tayi ta ce "yaushe kazo" Zaunawa yayi ya ce"tund'azu naga kina ta tunani wai Me ya faru ne daughter naga kina yawan tunani kwanannan baki da walwala"Murmushi kawai tayi ta ce "Bakomai wai muna da lectures Anjima kuwa?Girgiza kai yayi ya ce " a a a malamin ya d'agata ya maida gobe da Yamma kuma ya ce C a zaiyi"okay to daman nazata za ayi shiyasa na zauna bari na wuce hostel Dan na gaji "tare suka Mike suna tafe ya na mata hira harsuka isa hostel bata iske su Asmy ba hakan ya sanya ta d'ora indomie a gas Dan yunwa takeji ta na gamaci ta lalubo wayarta ta kunna waya sosai suka sha waya da ya Hafiz d'inta Wanda duk yawaici shine mai maganar tun a wayar ya lura da Kamar bata cikin yanayi mai dadi cewa yayi wai me yake faruwa ne my Zarah kwana biyun nan bana gane maki" murmushi ta kirkira ta ce "Bakomai ya Hafiz wai saura wata nawa ka gama school din nasan ai zaka rigani gamawa" Daga bangarensa ya ce "Saura shekara daya da Dan wani Abu my amarya ko harkin kagarane kema Kamar yanda na nakagara naga zuwan ranar Aurenmu Zarah Allah kadai yasan kalan son da nake maki duk ranar da Allah ya cikamun burina muka.mallaki juna matsayin mata da miji bansan wani irin farinciki zan shiga ji nake ranar kwana zanyi ina maki kukan farinciki" sosai gaban Zarah ya fad'i tayi Sauri ta fusge ta ce "Uhm ya Hafiz kenan kuka kuma sai kace wani yaro" eh mana my Zarah ba dole nayi kukan farinciki ba Allah ya mallakamun ke.matsayin mata ked'in ai allurace a cikin ruwa "Murmushi kawai ta kirkira gabanta na fad'uwa ta ce " Uhm ina zuwa na daura girki karyayi 'kauri "tukwana ta katse in banda Fad'uwa ba abunda gabanta yake Tunani take Ya Hafiz Idan bai sameta a budurwa ba ya zatayi Bayan Ya yarda da ita 100% batasan lokacin da wasu hawaye masu d'umi zuka zubo mata ba ta ce " Allah ya isa budurcina da Wani marar sanin darajar mutum ne ya amsheshi ba ya Hafiz mai kaunata ba ,"ta jima ta na kuka.

Zaune yake a palour ya na operating system Yaji shigowar Amera Ido kawai ya d'aga ya Kalleta daga sama har kasa tare da maida kanshi ga abunda yake sosai Amera tayi mamakin MD ba tare da damuwar komai ba ta k'arasa gabanshi tare da Rungumeshi ta gefe ta ce "My honey yaushe ka dawo I really miss you so much Wlh duk kewarka ta isheni" Dagowa yayi tare da kallonta fuskarshi ba walwala ya kira sunanta ya ce "Amera" Na'am my honey"ta fad'a ta na Lafewa jikinshi "Sau nawa zan hanaki shigar banzan nan kina fita da su sannan yawan nan da kike barkatai batare da izini na ba ya fara isata" Cikin shagwaba ta ce "Haba honey please me shigar nan tayi sannan baka taba yimun maganar fita da nake ba sanin kanka ne dai bazanyi abunda baida kyauba tunda kafi kowa sanin halina haba saikace dai ana zugaka fisabilillah naga kwanannan Duk nema kake ka shigo mana da dabi'un hausawa gidan nan Gaskiya ni banaso ka bari muci gaba da rayuwar turawanmu kawai" Kallonta kawai ya tsayayi da mamaki Yama rasa amsar da zai bata girgiza mata kai kawai yayi yaci gaba da abunda yake.kwabe fuska tayi ta ce "Haba honey ko dokin gani na bakayi sai wani shan k'amshi kake"Mikewa yayi ya ce " please merah ki barni ina buk'atar hutawa ya fad'a tare da barin Wajen ya haye stairs ya wuce Bedroom dinsa Ganin haka ya sanya Amera binshi ta ce "Wai meye haka Honey Sai wani chanzamun kake " MD ya ce "Amma dai na fad'a maki ina buk'atar hutawa ko ?Ta gefe ta Rungumeshi ta ce " amma dai kasan ina buk'atar hakkina ko?da mamaki ya bita da Kallo sai kuma yayi wani murmushi Alamun na mugunta.....ranar Amera ta gurzu iya gurzuwa Dan MD bai saurara mata ba kuka kam da Dana sanin me ya kaita ta shashi ba Adadi Bayan komai ya lafa ya wucewarshi toilet Bayan yayi wanka ya ya fito Gado ya tadda ita ta na maida numfashi tama kasa Tashi batare da ya ma sake waiwayarta ba ya bar gidan zuciyarshi chunkushe ba dad'i Amera ko dak'yal ta yunkura ta shiga toilet ta na Jan tsaki ta ce "mugu kawai jarababbe ko uban me ya kaini neman wani hakki wajen wannan da daman jira yake ya turmusheka da mugunta".. ..

Zarah na zaune a wajen hostel ta na karatun alqur'ani Asmy ta zo ta zauna wajen Ta na kallon ta zauna Zarah ta mik'e da niyyar zata bar wajen Mikewa Asmy tayi tare da Rik'e mata Bayan hijab cikin kuka ta ce "Ko wani bazai fahimceni ba bantaba tunanin ke zaki kasa fahimtata ba Zarah bakyamun magana dakin ganni waje zaki tashi me nayi maki na baki hakuri akan abunnan da ya faru wlh tallahi Zarah banyi abunnan da wata manufa ba sai Dan Soyayyar da nake maki wacce nakejin bazan jure ganinki cikin wani hali ba ko kuma na rasaki nayi hakan ne saboda ganin shine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login