Showing 105001 words to 108000 words out of 153980 words
sannan MD ba boyayyan mutum bane dukda yayi mamakin Kawo yarinyar da yayi Saiya d'auka matarsa ce tunda bakowa yasanta ba " Bayan shigar md d'akin da zahra take kan kujer dake gaban gadon ya zauna kallonta ya shigayi ba kakkautawa kwance take tana bacci hankali kwance Fuskarnan tata tayi fayau yanayin yanda take baccin sosai ya basa sha'awa a hankali ya kamo hannunta mai d'auke da bakin lalle da ratsin ja sosai lallen yayi masa.kyau Kallon lallen ya shigayi ba kakkautawa yana Dan shafa lallausan hannunta a hankali A rayuwar MD yanason yaga matarsa na masa lalle wayarsa ce tayi ringing ganin jaber ne yasanyashi saurin picking Daga bangaren jaber ya ce "Yadai najiki kamar baka cikin yanayi mai dadi"da sauki ya fad'a yana matsawa daga Inda take ya ce " ya ake ciki kaje asibitin?Eh naje komai ya tafi yanda akeso kuma sun bada Had'in kai Sunji dadi sosai da taimakon sannan munyi magana da Dr d'in a jiya ma ina Chan yace Zuciyarsa ke ke shirin kamuwa da ciwo amma idan aka tallabi abun da wuri bazai kamu ba "Innalillahi MD ya maimaita a ransa duk shi yayi sanadin shigar mahaifinta wannan halin kafin ya ce " Dan Allah Jabir kamun kokari duk yanda za ayi ayi kar wani Abu ya samu mahaifinta muddin wani Abu ya samesa bazan tab'a yafewa kaina ba duk yanda za ayi ayi chuku_chukun da za ayi kafin gobe a fitar dashi daga kasarnan na shirya kashe ko nawa ne wajen nema masa lafiya"insha Allahu babu abunda zai samesa amma ga shawara mezai hana a jaraba akwai wata Dr Najmat Kwararrar likitan zuciya ce har daga kasashe kawo masa patient ake Inma anfitar dashi wajen tofa abunda zatayi zai iyafin ma na Chan din saboda itama gwanace har Asibiti gareta a India a Gaskiya indai muka sameta tofa insha Allahu za a dace "cikin Sauri MD yace " To yaza ayi a sameta cikin Sauri kar wani Abu ya kuma samunsa sannan wani gari ne take "a nan kaduna itama take gidansu shima cikin GRA yake babu matsala insha Allahu saboda akwai abokin mijinta Habib to Abokina ne kuma matarsa Amera Y'ar uwar ita Dr najmat d'ince yanzu insha Allah zankira Habib din zanje har gidansa ta hanyar amerar zata hadamu da Najmat d'in Insha Allahu" (Only najmat abiy fans can related😝masu buk'atar cmplt book din *Najmat Abiy* su tuntub'eni akan wannan number 07026166536 Na Batin ne😝)Ajiyar zuciya MD ya sauke ya ce "Nagode Jabir komai Kenan ka sameni a waya zan maka transfer kudi kome ya kamata ayi sannan Dan Allah ka sayi kayan abinci da komai na Buk'ata ka kai gidansu ka d'ora musu da isassun kudi kayi abunda koda ina nan haka zanyi Dan Allah" Bayan sun gama wayar kujerar da yake ya koma ya kafeta da idanu kamar zai cinyeta yana jiran farkawarta da akayi Sallar Azahar yaje yayi salla d'aya daga cikin restaurant dinsa ya kira drivern sa akan yaje ya amso abinci Bayan ya fad'a masa asibitin d'akin da take ya koma kafin 1hour drivern ya kira number d'akin ya fad'a masa Akan idan yazo yayu knoking karya shigo haka ko akayi yana zuwa yayi knoking MD yafita ya amso warmers din yazo ya Aje sai wajen la'asr zahra ta farka dak'yal ta iya bud'e idanunta saboda wani irin nauyi da sukayi mata Ga jikinta da duk yayi tsami takejin ko tashi bazata iya ba MD yana lura da tashinta Ajiyar zuciya ya sauke suna hada ido hud'u zahra ji tayi kamar ta kashesa saboda a halin yanzu ba Wanda ta tsana sama da mutumin nan da yayi silar rugujewar farincikinta Dana mahaifinta "MD na shirin tab'ata cikin b'acin rai Ta ce " karka sake hannunka ya tabani"Kamar Wanda aka tsaida haka MD yayi dukda yaji ciwon abunda tayi masa Telephone din dake d'akin ya d'auka tare da kiran Dr din akan yazo ya duba ta ta tashi ba dau lokaci ba likitan yazo Nan yashiga tambayarta irin yanda takeji tana basa amsa a takaice Dan duk haushin kowa takeji "y'an rubuce rubuce dr yayi a paper tare da mik'awa MD ya ce " gashi a saya wannan magungunan ta fara sha daga yanzu amma kafin nan a tabbatar taci abinci "kin amsar paper MD yayi ya ce "a saya a pharmacy din asibitin bani acco no dinka zanmaka transfer kudin"take MD yayiwa dr din transfer kudi masu yawa dukda Dr baiyi mamakin hakan ba Dan MD zaiyi fiye da haka ba dukda asibitin mai mugun tsadane dan kwana daya ma kudin gado kaji kudin saikayi mamaki amma saida ya ninka kudin sau hud'u dr din na shirin taba hannun zahra dan ya cire mata karin ruwan da ya kare md ya daga masa hannu yace " kaje zancire mata"okay dr din ya fada tare da yin hanyar fita zahra ta ce " Dan Allah Dr cikin ya fita"Murmushi yayi mata ya ce "Ki kwantar da hankalinki madam ba abunda ya samu cikinki ya na nan Saidai ki k'ara kula wajen rainonsa " Wani irin bak'inciki ne ya tokare zuciyar Zahra batasan sanda ta fashe da kuka ba Ta ce "wannan wani irin jarababben makwawacin ciki ne Ba irin bugun da banmasa ba Dan ya zube Amma ya like to duk jarabarsa wlh saiya fita Dan Allah dr ka fitarmun da Cikin...bata k'arasa fad'ar abunda take son fadaba sakamakon kwabe mata baki da karfi MD yayi Kallon Dr yayi yace " ka wuce kawai"Dr na fita cikin b'acin rai MD ya Kalleta ya ce "Wlh kika kara aibantamun ko yunkurin yimun asarar ciki zakiyi mugun mamaki na waike wace iri ce da bakisan lallashi ba ba irin Lallashin da ban maki ba cikin nan ko shege ne iya wulakancin da zaki masa bare cikin halak mai matsayi da gata kamar kowani d'an sunna " wani irin banzan kallo zahra ta bishi dashi kafin ta ce "kai harka samu bakin magana an aibanta cikin kayimun abunda zakamun macuci kawai" Kafin ta hade kai da gwuiwa ta fara rera kuka "Tsaki MD yaja yana dafe ka kansa yace matsala " Mikewa yayi Tare da kama hannunta yana kokarin cire mata Karin ruwan Ta fusge a murtuke ya ce "Ki tsaya na cire maki karya ja miki jini" a hankali ya samu ya cire mata Wanda har lokacin jin kukan nata yake na dakar masa zuciya komawa yayi kujerar da yake tare da bude warmers din d'aya Lafiyayyan sakwarace da tasha Miyar ja sai d'ayar kuma pepper chicken ne sakwarar ya zuba a plate tare da d'ora naman a kai sama yayi da plate din tare da Ajewa gabanta yace tashi kici "Cikin kuka ta ce " Bazanci ba Ka maidani gidanmu naga halin da mahaifina yake ciki "Ba irin Lallashin da MD bai mata ba Wanda shi kanshi baisan ya iya lallashi haka ba akan taci amma taki " Omg ya fad'a yana buga kansa da hannu ya ce "Ya kike so dani ne Wai Mamy kwana nawa bakici komai ba Zai iya shafar abunda ke cikin ki?Tsaki taja cikin Masifa ta ce " ina ruwanka Yama shafi kome zai shafa cine bazanyi ba saika kaini naga halin da mahaifina ke ciki"kwantar da murya yayi ya ce "Indai kikaci zan kaiki wajen mahaifin naki" lokaci guda ta d'ago ta ce "Ka rantse " Yanda ta fad'ar ne yaso bashi dariya ya fusge ya ce "saina rantse zaki yarda " Eh saboda kaid'in ba abun yarda bane"dukda MD yaji zafin abunda ta fad'a Hakanan ya sasa daurewa Dan yanzu ya zama dole ya lallab'ata kodan cikinsa dake jikinta da take shirin yi masa asara "kwantar da murya yayi ya ce " indai kina cin abinci da magunguna har aka sallameki wlh zan kaiki ki gansa"Sai lokacin zahra ta d'an yarda amma da sharadin yau a sallameta cemata yayi ba yanzu ba saikinji sauki sosai kafin ya d'auko sakwarar a spoon ya fara kokarin bata da farko kin amsa tayi saida ya k'ara rantse mata akan Zaikaita data warke taga Baba tukwana ta yarda dukda tace zataci da kanta ya kiya shi zaiyi feeding d'inta shi kanshi yayi mamakin akan yarinyar yakeyin abubuwan da bai tab'a yinsu ba a rayuwa wannan ne karo na farko daya tab'a feeding d'in mace sosai ya samu taci abincin Sai sannan hankalinsa ya kwanta magungunan da Nurse din ta kawo ya b'alla mata Tasha sai sannan ya iya Mikewa Dan yaje ya gabatar da salla da harara zahra ta bishi kafin taja tsaki ta ce "mugu macuci azzalumi wlh na tsaneka " Dak'yal ta yunkura tashiga toilet ta dauro alwala ta gabatar da salla dukda batasan tana da tsarkin yin sallarba Dan bataga komai ba yanzu sab'anin idan bata manta ba kafin hankalinta ya gushe...bangaren Jabir sosai yayi kokari akan Baba kamar yanda MD ya umarcesa haka akayi ya samu yarda sosai daga wajen dangin Baba bisa ga taimakon da yayi musu baisha wahala ba ya samu appointment da Najmat a ranar aka maida Baba asibitin dr Najmat Wanda d'aya daga cikin y'an uwanshi ne kad'ai zaiyi jinyarsa bisa ga Dokar asibitin ko dubiya ba a barin mutane shiga saboda masu irin ciwon basasan hayaniya....bangaren Mama Rabi saida akayi mata dinki.kwana tayi tana tsinewa zahra da kawayenta Asmy ko har gida taje ta samu mamanta Tayi mata tas Wanda Bata biye ta ba nanfa mutane aka shiga binciken ina Zahra tayi tsegumi saiya dawo sabo wasu na cewa guduwa tayi Mama Rabi ko itace uwar zazzakewa wajen bada labarin abunda ya faru dukda wasu daga cikin mutane basu yarda zahra ta aikata hakan ba Sosai Mama Rabi ta dinga mamaki lokacin da aka fara shigowa da libgin kayan abinci kamar za a bud'e wani store tsakar gidan saida ta kusa cika da kaya Bayan anyiwa Jabir Iso ya shigo Mama Rabi har kakkarwa take wajen shimfida masa tabarma a takaice suka gaisa kafinma ya fara mata bayani ta ce "yaron nan wannan kayan fa ko b'atan hanya kukayi" Murmushi d'auke da fuskar Jabir ya ce"a a a nan aka kawo Oga na ne ya sanya na kawo muku ga wannan anyi cefane ya fad'a yana mik'a mata y'an Rafar dubu"ai irin godiyar da Mama Rabi tayi kamar tayiwa Jabir sujjada kira take "Kinji Allah Mai iko tsuntsu daga sama gasashshe amma Allah ya sakawa ogan nan naka da alkhairi ya bashi abunda yake nema duniya da lafiya Allahsa ya gama da iyaye lafiya sai kuma kuka ta ce " Allahsrk wai yau nice Rabi da rik'e irin wannan kudin Wanda tunda nake bantab'a rik'e ko rabinsu ba ga kayan abinci Wanda ko buhun shinkafa ba a tab'a Aje mana ba Sosai Mama Rabi Tasha sabbatu daga baya kuma Bayan fitar Jabir tahau rawa da guda yanda.kasan anyi mata albishir da gidan Aljanna..bangaren Asmy kullum cikin kuka take ta rame Ba irin tambayar da Mamanta batayi mata ba akan ta fad'a mata abunda ke damunta ta ce "Bakomai" Dukda ta fahimci akwai abunda ke damunta Ganin ba fad'a ba zatayi yasanyata rabuwa da ita ta sanya mata ido....bangaren Chuchu ma tunda ta dawo bata da walwala sosai labarin da Asmy ta bata ya burkita mata kwalwa sosai takejin tausayin zahra har cikin ranta Dan Asmy ta bata labarin irin bak'ar wuyar da tasha wajen Mama Rabi itamadin wani time d'in kukan tausayin zahra take yanzu bata da burin da ya wuce na Tasan Inda take Ammy itama tayi tambayar duniyar nan akan tafada mata abunda ke damunta Saidai ta ce Bakomai amma daka Kalleta kasan tana tare da damuwa....kwanan zahra hud'u a asbiti aka sallamesu Wanda MD shi yayi jinnyarta harta warke dukda wuyar da take basa na gardama da fad'a masa bakaken maganganu tun a mota zahra ta tubure ta ce "Wlh saiya kaita taga mahaifinta " ba irin yanda MD baiyi da ita ba akan ta Bari idan ta huta saitaje ganin tana shirin Tara masa mutane ya sanya bama su koma gida ba ya d'auki hanyar kd sai sannan hankalinta ya Dan kwanta suna isa kd ya kira Jabir ya turo masa address din asibitin da room d'in Suna isa asibitin MD ya sanya facemask Dan kar a ganesa cike da mamaki zahra ta ce "Yaya zaka kawo ni nan asibitin Bayan yana funtua" A takaice ya ce "ya na nan asibitin ki biyoni " binshi ta dingayi suna zuwa daidai Wani waje aka Hanasu shiga Dukda Dan basu gane MD bane da zasu iya mai alfarma dukda Dokar asibitin ce haka dak'yal fashewa da mai gadin wajen kuka zahra tayi ta ce "Dan Allah ka taimakeni ko ganinsa ne nayi" Hakan yasa ya tausaya mata ya ce "Zan iya muku wani taimako mu zagaya ta k'ofar baya akwai tagar da zaku hangesa ta nan amma karkuyi magana" Cikin Sauri zahra tace "bazanyi ba ngd" Kofar dake baya ya zagaya da su Tare da bude musu Kad'an nan zahra ta Hango Baba kwance Bisa makeken gadon da baiyi kama da na sauran asibitoci ba ga AC har biyu data sama data k'asa banda fanka ga k'atuwar plasma a d'akin kamar wani hotel batasan sanda wasu hawaye masu d'umi suka zubo mata ba ta ce "Dukni nayi sanadiyar shigar ka cikin wannan halin Baba na cuceka bansan da wani ido zan Kalleba ka yafemun Baba ...kuka ne yaci karfinta sosai Kamar daga sama tajiyo tarin Baba yana kokarin farkawa zara idanu tayi ta murza ganin yana bud'e ido Kasancewar ko ina na asibitin ctv camera ce ya sanya daga Chan office d'inta take gane wadanda ke buk'atar taimako ba ayi minti biyar ba saiga Najmat Ta shiga d'akin Sanye cikin farin glass dayayi mugun amsar kyakyawar fuskarta sosai naga ta k'ara kyau da wayewa fiye da wacce take da ita a baya tana sanye da labcoat kai tsaye Inda Baba yake ta nufa Fuskarta dauke da Fara a ta ce " Alhmdllh "Kujerar dake gefen Baba ta zauna Ganin ya farka nan ta fara aikinta Ta tambayesa me yakeji a jikinsa Girgiza mata kai kawai yayi kafin a hankali ya ce " Ina Zahra "Zahra najin da sunanta Baba ya farka batasan sanda kuka Ya Kubce nafa ba rufe mata baki MD yayi tare da girgiza mata kai sosai taji tausayinta da na mahaifinta Yasan akwai shakuwa da k'auna tsakaninsu cikin hikima irin ta kwarewar aiki Najmat Ta kwantar masa daa hankali dukda batasan dalilin shigarsa cikin wannan halin ba ta ce " y'arka ce Baba?gyada mata kai yayi"murmushi tayi masa ta ce "ta na nan jiyama tazo ganinka Yanzu haka tana gida na idan ka warke zatazo ganinka" Ajiyar zuciya Baba ya sauke yanajin damuwarsa ta ragu Saikuma yayi shiru tunowa da abunda Akace zahra ta aikata wanda har yanzu bai gama gaskata hakan ba Najmat na ganin ya fara tunani tayi saurin katsesa Ta fara masa labarai na sanya Dariya da zai hanasa tunani kafin ta kunna masa kallo Na abunda zai basa nishad'i Likita guda takira akan ya zauna dashi pull time kar a sake A barsa yayi tunani ko na minti d'aya ne kafin tabar room d'in ta koma duba wasu Duk akan idonau MD hakan ya faru Ajiyar zuciya zahra ta sauke tana jin k'aunar Dr d'in ganin yanda ta kula da mahaifinta Sosai ta tsaya Kallon Baba ji take kamar ta fasa kofa tashiga taje ta Rungume mahaifin nata dukda tayi mamakin waya sauya masa asibitin daga wancen zuwa wannan Babban asibitin da daga gani za a chashi kudi masu yawa Wanda yayi musu jagora ne yace "Ya isa Haka su tafi kar wani ya gansu a ja masa ta aikinsa "hawaye d'auke da fuskar zahra ta ce " nagode "kudin da suka rage a aljihunsa MD ya basa masu yawa kafin Su koma mota sosai jikinsa ya mutu gaba d'aya kamar Wanda aka zarewa lakka Har suka isa motarsa nanfa zahra ta tubure tace batasan wannan ba ba Inda zata koma hankalin MD nanfa ya k'ara tashi yahau Lallashinta amma ta tubure ganin tana shirin guduwane baisan lokacin da karfi yazo masa ba ya fardota tare da sanyata mota yayi Sauri ya zagaya yayiwa motar lock kai tsaya ma bai tsaya saurarar komai ba ya juya Abuja sosai zahra ta dinga fasa masa kuka kamar ranta zai fita har suka isa Abuja tana kuka tana tsine masa Daren ranar sunsha dabu da ita Dan burkucewa tayi ya ce Wlh saiya maida ita gida kota jaza masa bala i dak'yal ya samu baccin gajiya ya kwasheta ....sosai Baba yake samun sauki a asibitin Dr Najmat kulawa.sosai Jabir yake basa bisa ga umarnin MD Bayan sati biyu jikin Baba ya warware Ranar da aka sallamesa y'an uwansa sukayi shawarar awuce dashi Batsari ya karajin sauki saboda sunsan halin Mama Rabi sarai zata Kara tayar masa da hankali ne akan zahra ta gudu Bayan sun boye masa sunce tana gida zuciyar Baba chunkushe da tunanin zahrarsa .....Cikin satin nan ba k'aramun dabi zahra da MD suke sha ba Sosai zahra ta birkitawa MD tunani ne yau inya tallabota nan gobe ya tallabota Chan sosai yake hakuri da jure irin abunda take masa shi kanshi baisan yana da hakuri har haka ba abinci ko Sai yayi kamar zai mata d'ure tukwana yake samu taci da bala'i da masifar saiya maida ita gida sannan ancire mata cikin nan har sukayi wata guda a gidan Wanda MD ko kd baisamu yaje ko gaishe da Ammy yayi ba Saidai ya kirata a waya ya ce uzuri ne yayi masa yawa .yauma yana zaune a palour around 9pm yana waya da Ammy tana masa complain Chuchu ta kasa gane kanta indai bashi ba yazo babu Wanda zata fad'awa damuwarsa"numfashi yaja Dan yasan damuwar Chuchu bata wuce ta abunda ya samu kawarta ba ya ce "Badamuwa Ammy Zankirata waya Naji meke damunta insha Allah zansamu nazo " Daga bangaren Ammy ta ce "Hmmm haka dai kake cewa Na rasa wani irin aiki ne wannan da zakayi wata guda kana k'asar bakaga ammynka ba " Shafa lallausan sumar gashin kansa yayi yana murmushi ya ce "Ba haka bane Ammy insha Allahu.muryarsa