Showing 138001 words to 141000 words out of 153980 words

Chapter 47 - AUREN WATA TARA COMPLETE HAUSA NOVEL

30 Sep 2024

16346

tashi zaune kamar ba shine aka kawoshi Rai hannun Allah baisan Wanda wasu irin hawaye masu d'umi suka zubo Masa ba tare da gark'ame hannunta yayi sosai Yana hawaye ya ce"Dan Allah Mamy kiyi hakuri karki rabu Dani wlh Ina sonki har cikin zuciyata banajin Zan it's rabuwa dake Kuma na rayu please ki tausayamun"ya karasa fada Yana kuka kamar ba namiji ba "Komawa kirjinshi Zahra tayi Tana shashskar kuka ta ce"Kayi hakuri duk Abunda nayi maka Dan Allah Abban triple na shirya rayuwa dakai na har abada Ina sonki Nima Kuma zankoma maka please ka warke banason ganinka cikin wannan halin "a matukar zabure MD ya rukota ya juyota Yana kallon fuskarta ya ce"Ke kike fad'ar maganar Nan da bakinki Mamy da gaske kike kina Sona ko ko kunnuwanane suka jiyemun ba daidai ba "Zahra na hawaye ta gyada Masa Kai "Ai MD baisan lokacin days sake rungumota jikinshi ba cike da farinciki da tun haihuwar triple bai Taba shiga irinshi ba ya ce "Thanks you thanks you so much my all above ngd Mamy da amincemun da kikayi Zaki koma gareni nagode "Lafewa jikinshi Zahra tayi Tana Murmushi Tana Jin wata nutsuwa na Kara ratsa ta tanajin Kamar ta sauke want gagarumin nauyi a kanta it's kanta sai yau ta fahimci irin son.da take Masa batare da ta sani ba mamaki take har yaushe ta Fara sonshi haka Bata sani ba "Gyaran muryar da Ammy tayi ne ya dawo da su daga duniyar shaukin kaunar junan da suka lumtiya a hankali Zahra ta zame jikinshi daga nashi Tana dagowa ganin Ammy da Baba(kakanta) da tayi ne yasanyata Jin wata irin kunya tamkar ta nutse a Wajen Ammy ko da baba hamdala kawai suke Kallonta days zakayi musu kasan suna cikin tsananin farinciki haka chuchu da it's da jabir da suke bayansu da gudu chuchu ta ruga ta rungume Zahra cikin farinciki ta ce "Thnks you so much momcy kin ceci rayuwar Dan uwana ngd "Murmushi kawai Zahra tayi Tana kasa da kanta karasowa dakin sukayi inda MD yake baba ya zauna ya ce "Ashe jikinshi da sauki jikana hankali na duk a tashe da jabir ya fadamun zuwana kenan Masha Allah "Murmushi MD.yayi Wanda Ammy harsun mance yaushe rabon da yayi irinsa ya ce"Alhmdllh"Jaber ne Yana harararsa ya ce"Yana ganka ka Mike Haka kamar ba Kaine muka kawo Rai hannun Allah ba"Yana Murmushi ya ce "To bakaso kaganni haka ba na warke kaga silar ciwon Daman Kuma tayi magani"ya fada yanayiwa Zahra want shuumin kallo"Ammy na Murmushi ta ce"Babana baka ma karar muna Wajen ko"Sosa keya yayi Yana y'ar dariya"Bayan dr ya shigo ya ce To ya patient Kuma har ana dariya jiki yayi sauki kenan"Mikewa Md yayi tsaye kamar ba shine marar lafiyar ba ya ce "Ku taho mu wuce na warke"Dr ne Yana driya ya ce "To ranka ya Dade baka jira a sallameka ba"Na sallami kaina "ya fada Yana Sanya takalmi"duk dariya sukayi gaba daya gidan mama Habi suka koma Tunda suka shiga suka Fara jiyo kukan triple da gudu Zahra taje ta amshesu shataf ita Tama Manta da zasuyi kuka Dakyal ita da chuchu suka lallashesu har sukayi shiru tukwana tayi feeding dinsu chuchu sai tsiya take Mata Tana ciccijewa"Sosai mama habi taji dad'i da su Zahra suka sasinta kansu Nan aka Fara maganar yaushe zata koma number wayar Baba ta Kira Bayan sun gaisa take mashi bayanin komai cewa "yayi ba matsala habiba duk yanda kukayi daidai ne Ki barmusu ita su tafi kawai Allah ya bada zaman lfy"bayan tayi musu bayanin Abunda ya faru sosai kowa yaji dadin hukuncin na baba a ranar Suka juya kd Tare da Zahra da yaranta MD jinshi yake cikin wani irin farinciki Koda suka koma ya zaci Ammy bashi ita kawai zatayi su koma gidansu saiyaga sabanin haka ta wuce da ita bangarenta Nanfa MD.ya b'ata fuska Ganin Yana Shirin yin wata rashin kunyar gaban baba tsoho ya Sanya Ammy harararsa hakan yasa yaja bakinshi yayi shiru Koda Ammy ta Kira Hajiya Kaka ta fada Mata a waya An daidaita komai sosai tayi farinciki sannan ta Kara sanyawa aurensu albarka Dan ta koma maiduguri tun last week tundaga Zahra ta dawo Ammy ta shiga gyarata ciki da bai kamar wata sabuwar amarya har dilka da tsumin kamshi ake Mata gashi Ammy ta kasa ta tsare Akan md ta ce sai Y'arta ta Kara nutsuwa ta gyarata tukwana zata bashi Ita yaranta ko sosai suke wayau gasu Basu da kiyiwa Gata da soyayya suke Sha a gurin family din nasu ta musamman kayan wasa kuwa saisun ture idan yaran ka gansu saikace sunyi 7 months Nan ko watansu hudu daka kallesu kasan suna da tsananin lafiya irin zubin turawan Nan garesu"bangaren MD Shima Shirin yake sosai Dan Sabon gida ma ya bada kwangilar Gina Masa na gani na fada dan yace a Sabon gida Amaryar tasa zata zauna Banda lefe da suke shiryawa shida zey Dan makudan kudade na ban mamaki ya Bata Akan ta fita waje ta hadowa y'ar gold din nasa lefen da ba a taba yiwa wata y'a mace irinsu ba,yau Ammy ta Shirya bawa MD matarsa Bayan ta Sanya anzo an yarfa Mata Lalle dayayi mugun amsar fatarta kitso ta Sanya akayi mata shima Mai shegen kyau Tsadadden lace da yasha dinki Ta Sanya da yayi mugun yi Mata bala'in kyau simple make_Up asmy da tazo tayi Mata sai zolayarta suke ita da chuchu suna ce Mata amarya saidai ta hararesu ko ta musu Tsaki"Sosai ta fito tayi kyau kamar wata wacce zata zaben sarauniyar kyau ni kaina Saida na ce"Tubarakallah Masha Allah "saboda wankan ta wanku kallo daya zakayi Mata kasan eh ba karya ta cika Mrs MD a palour Ammy ta zaunar da su ta dinga yi musu nasiha sosai gami da nusarwa cikin hikima Ta dinga Musu nasihohi bayan nan ta ce "Iyayen Zahra shekaranjiya sunzo sunyi Mata jere dukda ba yanda bamuyi da su ba Akan su Bari karsu wahalar da kansu sukakiya jiya sunje sunyi Mata jere a Sabon gidanka daka cemun chan zaku tare sannan Nima nayi Mata nawa Allah yayi muku albarka yasa mutuwa ce zata rabaku"kafin Shima baba data Kira Dan yasa musu Albarka ya Dora Akan nashi Saida suka gama musu wa'azi sannan baba ya Kara Masa da nasiha akan yayi adalci a tsakaninsu duka matansa "Sai sannan ya tuno da Amera "Bayan sungama yi musu Nasiha Zahra kanta na kasa Ammy ta ce "Allah yayi muku Albarka "Kutashi ki tafi"A sanyaye Zahra ta Mike ta Ce "Nagode Ammy " MD ko jinshi yake cikin wani irin farinciki marar musaltuwa ya kasa kyafta Ido da kallon Zahra Masha Allah kawai yake fada a ransa Dan shikanshi yasan sai yanzu yayi Mata d'aya da d'aya rike hannun Zahra Ammy tayi har bakin labceciyar motar MD Zahra Tana tunanin Ammy batayi Mata maganar yaran ba MD ya kasa daurewa ya ce "Ammy Triple fa"Ga sunan su chuchu sunshirya su Marar Kara"Ammy ta fada Tana Kai Masa dankwashin wasa"d"an Kara yayi tare dayin dariya ya kauce "Suna tsaye Chuchu Da Asmy suka fito rike da yaran Sunsha Kayansu Suma masu mugun Kyau iri daya sosai sukayi bala'in Kyau chuchu ce ta ce "Wow Yaya gaskiya sainayi muku hoto irin wanna show haka"Murmushi yayi ya ce"Yi sauri kiyi to Kinsan banason hoto sosai"Hannunshi chuchu ta hada Dana zahra ta ce "Yawwa Ku rike a Fara muku Ku biyu"Nan chuchu ta shiga kyalla musu hotuna masu mugun Kyau a dalleliyar wayarta Kafin a Basu yaran a musu Baki d'aya wa'iya zubillah zo kuga irin kyaun da wanna couples din sukayi da yaransu kamar ka sacesu ka ruga Saida chuchu ta Gama kyallarasu kafin ta barsu sai dokin hotunan take Ganin Ammy tabar Wajen ya Sanya Zahra sakin jiki kallon asmy tayi kasa kasa ta ce "Dan Allah Anjima kuzo"Dariya asmy da chuchu sukayi suna tabawa asmy ta ce "So kike ya koromu da karnika kenan ana Shan amarcin Rana kawai zaimuzo muku ai harya hadomu da Kare"Dariya chuchu tayi ta ce kinsan ko yaya wlh ya aika"harara Zahra ta Galla musu kadin ya tsunkini Asmy ta ce "Saura ki tafi yau"Horn din da MD yayi Mata ne ya sanyata rabuwa dasu chuchu Dan ta lura shegantaka suke Shirin yi Mata kafinma ta bud'e taga ya bude Mata Shiga tayi tare da rufewa kallonshi tayi day rike little a Gabansa a ranta ta ce "Da itazaiyi tukin kenan it's kanta tasan cikin yaran yafison Little saidai ilimi yasa baka taba ganewa "motar yayiwa horn a hanya sai kallon Zahra yake da take d'an yiwa amar da Akhbar wasa dukda ya lura kunyarsa takeji kallonta kawai yake gwanin burgewa Yana Murmushi ji yake abun tamkar almara hannunshi daya ya saki tare da Kamo hannunta daya dake dauke da Lalle Abunda yafiso kenan Yana Murmushi yayi sama da hannun tare da kissing din hannun ya ce "I love this"Ganin Yana Shirin karkace tuk'in ya Sanya Zahra Jujjuya Masa idanu tare da shagwabe fuska ta ce "Karka kadamu fa"ai MD ji yayi kamar zai narke Saida tsikar jikinsa ta tashi irin yanda tayi maganar sosai ta rikita Masa lissafi lura da hakan Saida yasanya Zahra ta kusayin dariya tare da zame hannunta "Shima marairaicewa yayi ya ce "Zaki rikitani da yawa babe kija na kadamu a mota"d'an Murmushi Zahra tayi batace komai ba "Har suka Isa Yana kallonta gwanin burgewa yanda take komai cikin class sosai yake son komai nata musamman class dinta Dan shikanshi yasan ajin Zahra bana kananan Yara bane yana son mace Mai aji Daman Shi a rayuwarshi Koda suka isa Sabon tafkeken gidanshi da Shima anan gra din yake ni kaina Saida nayi kauyanci ganin irin wannan gidan aljannar duniya kenan ai duk yanda nake santin gidan md wancen wannan ya Shanyeshi ya Dame ya gidan yanda kasan kazo wata katafaren compony ko Kuma villa tafkeken gidane daya more da kayan alatu da more rayuwa girman gidanko bazan iya cewa ga kwatankwacinshi ba unguwa guda ita kanta Zahra Saida ta tsorata da ganin kyau da girman gidan yanda kasan wata tafkekiyae estate Yana rike da hannunta har suka nufi parlourn bayan ya umarceta da ta shiga da kafar Dama ai shigowar Zahra parlourn Saida ta raina kanta ganin irin turkey da Korea furnitures din da aka lafta a dakin to ai ko gidan shugaban k'asa kayan Nan da gidannan sai Haka rufin selin din dakinma kanshi abun ayi masa kauyancine tiles din Zahra ta kalla Taga Tana ganin kanta Kamar madubi Murmushi kawai MD keyi bayan isarsu tsakiyar palourn A lausassan carpet din da Saida na kusayin sumar tsaye danaga zai Dora twins kanshi ganin yanda yake sawaya ita kanta Zahra Saida ta kusa tsorata ajesu yayi gabaki daya a wayance ta take carpet Jin laushi ya sanyata sauke ajiyar zuciya itadai a rayuwarta Bata Taba ganin duk Abunda ta gani a palourn ba Bata karasa tunanin Nan ba taji ya janyota ya rungumota ta baya tare da rankwafar da kansa Yana shinshinar wuyanta ya Ce "Alhmdllh thanks you so much my all above kingamayimun komai a rayuwa Babu Abunda zance da ubangiji sai hamdala sannan nace ya barmu tare na har abada "Murmushi kawai Zahra tayi Tana kasa da kanta "Marairaicewa yayi ya Ce "please muje ciki muyi sirri aji Dani"RauRau tayi da idanu tare da juyasu ta shagwabe fuska "Suma Ce kawai md baiyi Ba ai baima tsaya wata wata ba yayi sama da ita bai direta ko Ina ba Sai bedroom ya sauketa a kataferen bedroom dinta...sosai ma'auratan Nan suka jiyar da junansu Dadi Kamar zasu cinye juna kunsan mutanen namu duka gwanayene a fagen Nan mD ko haukane kawai baiyiba Jin yanda Zahra ta Kara nice ta dawo Masa sabuwar budurwa Ai iya rikicewa ya rikicewa Zahra sai Wajen magriba suka samu komai ya lafa, fitowa Zahra tayi daga Wanka kallon MD tayi da har lokacin Yana gado kwance, wardrobe ta d'aga sosai tayi mamakin ganinta cike da Kaya na sawa wata Riga marar nauyi a cikin English wears din da ta gani iya gwuiwa ta Sanya sosai rigar tayi Mata kyau musamman data Dame ta bawa albarkatun jikinta damar bayyanuwa jikin mirror taje handrayer ta jona ta Fara busar da lallausan Gashin kanta cikin nutsuwa Daga kwancen da yake ba Abunda yake in banda kallonta Yana Kara godewa Allah d'aya mallaka Masa ita a matsayin Mata Shi kansahi yasan yanzu yayi aure yanzu yasan menene aure Yana Murmushi ya Ce "Kingamayimun komai Mamy bani da kudi ko bakin dazan iya biyanki da alkhairan da kikayimun shigowarki rayuwata kinsauya komai kedin haskece a cikin rayuwa ta data iyalaina kin bani farinciki da ba a taba bani Shiba a rayuwa kedin Allura ce cikin ruwa Ni Allah ya bawa damar chafka I love you so much my wife Ina sonki sosai Ina sonki son da Ni kaina bazan iya kwatanta adadinshi ba "kalamai masu sanyi da sanyayar zuciyar masoyi MD ya dinga zuba Mata Kuma sosai suke tasiri a zuciyar Zahra Saidai kunyarsa ta hanata mayar Masa saboda wani irin nauyinsa takeji Ganin magriba na Shirin gotawa ya Sanya Zahra Ce wa"Za ayi magriba fa ya musty kana kwance"Murmushi yayi tare da mikewa ya Ce "sorry malamata yaufa sai kinyimun karatun Nan Nak'i Mai narkar da zuciyar Mai sauraro cikin zazzakar muryar Nan Taki har nayi bacci sannan ki chanza sunan Nan kibani wani"Murmushi kawai Zahra tayi ta Ce "Uhm"kafin ya fito daga Wanka Harta tada sallar Magriba ganin Tana salla ya Sanya md Shima Sanya jallabiya lokacin magrib ya gota dan yasan yanzu masallataima sun Gama yasanyashi tada Salla a kusa da ita Zahra ta rigasa gamawa a ranta ta Ce"Insha Allah saina sauyaka daga sallar gidan Nan Dan ta Lura ko da sukayi zamansu a gidanshi na Zaria akwai lokutan da yake salla a gida dukda dai taga Yana da kokarin ibada sai idan ya makara Saida suka Gama salla md ya tuno da yaran mikewa yayi ya Ce "Subhanallah na Manta munbar yaran Nan a palour "a rude Zahra ta Mike ta Ce "Sai yanzu na tuna" ta fada Tana nufarr palour da gudu binta yayi kasancewar akwai tazara tsakanin parlourn da bedroom din ya Sanya basuji irin kukan da yaran sukayi ba wajensu suka karasa inda sukaga fuskar little Zahra zabe zabe da hawaye ita da Amar sun hade waje guda suna baccin wahala daga gani ba karamun kuka suka Sha ba Akhbar ko sai tsala kuka yake har Yana kakkafewa a matukar rude Zahra ta daukesa ta Fara jijjigashi da lallashinshi dakyal ta samu ta lallasheshi harta samu ya karbi mama ajiyar zuciya ta sauke MD ko little da Amar ya dauka a hankali ya Ce "Sorry my kids parent din ku sunbarku a palour sunmanta daku "Daidai lokacin da little ta farka itama ta tsala kuka dakyal suka samu suka lallashi yaran sai Wajen isha'i suka samu sukayi shiru bayan kowa ya koshi su kansu sai sannan suka tuna da yaran sunjima a palourn dole susha kuka su suna chan wata duniyar bama suji kukan ba "Da Dare Ammy ta Aiko driver da cooler abinci MD ya fita ya amso Bayan Zahra tayiwa yaran Wanka Wanda MD ya taimaka Mata da shiryasu Kaya ta Sanya musu Bayan ta feshesu da turarruka na Yara masu santin kamshi itama Daman tunda tayi Wanka ta feshi gashi Daman a gyaran da Ammy tayi Mata hada na kamshi Dan ko wake ta zauna saiyayi akamshi Koda suka samu yaran sukayi bacci wata duniyar suka lumtiya daren ranar dai Zahra ta raina kanta Dan MD ba wasa kishirwarshi ta watanni ya sauke a kanta Washe gari ma a palour suka aje yaran da safe Bayan an shiryasu suka babbaza musu kayan wasa Suma iyayen sunyi breakfast MD ya sungumeta suka koma ciki Suna chan suna zuba love dinsu Kamar zasu cinye junansu.
chuchu da asmy da sukazo tun a waje suka Fara jiyo kukan yaran da gudu suka karasa suka daddaukeau sosai suka Sha dabi kafin su samu suyi shiru Shima Saida suka goye biyu tukwana suka samu bacci ya dauke su sunyi minti talatin a polourn Amma Basu fito kallon asmy tayi ta Ce "Jifa Dan girman Allah yanzu mintinmu nawa anan Wama yasan dadewar yaran a palour ga kofa ba rufe da key ba Dan Allah want mugun ma basai a sache yaran suna chan ba wlh saina fadawa ammy "Ta fada Tana lalubar number ammy "Asmy Ce ta Ce "Karki kirata Dan Allah "Allah saina fada Mata ba iya rainonsu zasuyi ba "Ammy na dauka chuchu ta Ce "Kinganmu Nan ammy munzo gidan muka iske Yaran a palour kofa a bude ba key sai kuka suke har yanzu Kuma Basu waiwayesu ba "Subhanallah irin ta'asar da zasu tafka kenan Daman Ina Shirin kawo masu aiki su taimaka.mata da aiki da Kuma nanny din yaran Bari yanzu yanzu nakira Mai samamun y'an aiki ta samo wacce xata dinga kula da Yaran"Ajiyar zuciya chuchu ta sauke ta ce "To Ammy"Saida su chuchu suka kwashe awa guda kafin suga fitowarsu hannunsu sartse cikin na juna MD yasha bak'ar shadda da tayi mugun amsar farar fatarsa har wani shining shaddar take tana walkiya Zahra ko sanye take cikin atamfa super Holland Wanda duk a cikin kayan data gani a wardrobe ne duka size dinta ne tasan aikin Ammy ne Dan Bayan dawowarsu ta taba amsar size dinta Zahra na Ganin su chuchu ta saki hannunshi wajensu ta nufa cikin farinciki ta na murmushi ta Ce"Yanzu kuka zo"Harararta asmy tayi ta Ce "a a a Nan muka kwana"y'ar dariya Zahra tayi ta ce"Sorry maida wukar sauke lillte a bayanta da tayi bacci Asmy tayi ta kwantar da ita chuchu Daman tunda Amar yayi bacci ta saukesa kallon MD sukayi suka gaisheshi ya amsa musu cikin sakin fuska "Kallon Zahra chuchu tayi ta Ce "Ina kwana auntynah"Harararta zarah tayi "y'ar Dariya chuchu tayi "MD dai kallon matar tasa kawai yake Wajen Yaran yaje kowanne ya Basu peck a kumatu kafin ya juya ya kalli chuchu ya ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login