Showing 153001 words to 153980 words out of 153980 words
wajen Tana zuwa ta Kama hannunsa ta Ce "Ina kaje Akhbar tundazu muke nemanka ka bamu wahala so kake ka b'ace a wajen Nan"Akhbar na hawaye Cikin shagwaba ya ce "Mom wadannan ne sunki bani babynsu "ya fada Yana nuna Mata wadanda ke tsaye dagowar da Zahra zatayi idonta ya sauka akan Hafiz Dake rike da karamar yarinya da bazata wuce sa'ar amera ba sai karamun yaro da bai wuce shekara biyu da rabi ba waro idanu sukayi a tare Zahra ta Ce "Hafiz"Shima Cikin muryar mamaki ya ce "Zahra Daman Rai kanga Rai"Mamaki dauke da fuskar Zahra ta Ce "wlhko ya Hafiz kwana da yawa"a sanyaye ya ce"Kinyi wuyar gani Zahra saidai muji labarinki"Murmushi kawai Zahra tayi Tana kallon matarsa ta Ce "Ko matarka ce"Eh Matata ce sunanta Aisha wadannan din Kuma Yara na ne Babban sunansa haidar wannan Kuma takwarar Kice Na Sanya Mata "Kai Masha Allah Ubangiji ya Raya Mana su Gsky Ina gdy da takwara Ta fada Tana Mika hannunshi ta amshi y'ar Akhbar na Ganin Haka yayiwa hafiz gwalo ya ce "Yeyeye ka gani mom Dina ta amso Mana babyn Kuma da ita zamu tafi gidanmu tunda Ni ka hanani"Dariya Hafiz yayi ya ce "Ohh itace mom din take kenan "Eh saura dad Dina Shima Yanzu zaizo mu tafi da babyn "Hafiz najin kishi a ransa da yanzu wadannan yaran duka nasa ne in Banda kaddara ta rabasu ya kalli Zahra ya ce "Akhbar yaronki ne kenan "Eh Ya akai kuka hadu"Murmushi hafiz yayi ya ce "Tun dazu yake binmu Wai saimun basa Zahra Yaatafi da ita gidansu Karkiga har kuka ya dinga Mana Allah sarki Ashe rabon mu hadu ne"Yar dariya Zahra tayi ta ce "Alhbar kenan ko har yayi kamu To ai shikenanma tunda ta dawo gurin Mamanta kaga gaka ga babynka ko"ta fada Tana kallonshi tsallen murna yayi ya ce "Yesssss mom "kallon matarsa Hafiz yayi ya ce "Wannan ita ce zahrar da nake ta Baki labarin"Aisha da fara'a a fuskarta ta ce "Allahsarki itace kenan Ina yini"ta fada Tana kallon Zahra "Lafiya qalau momyn takwara ygd "Saida suka Dan gaggaisa da Zahra Hafiz jikinshi gaba daya yayi sanyi yasan duk duniya Babu macen da yaso kamar Zahra Amma yanzu tayi Masa Nisan da har abada shida ita saidai kallo a sanyaye ya ce "Zahra Ina son Daman haduwa Dake domin Baki hakurin abunda ya faru wlh kaddara ce ta raba mu lokaci guda kawai naji an chusa mun tsanarki a Raina Wanda Saida na dawo hayyacina na shiga tashin hankalin da bantaba shiga ba Jin cewar Kinyi aure harkin haihu Wanda har Saida na kwanta ciwo kafin na warke har na auri Matata Aisha cousine sister Dita ce yaranmu biyu da ita Wanda itama Ina yawan Bata labarinki tun Tana kishi har tazo ta daina dalilin kaunar da nake maki ya Sanya har nayi Miki takwara "Sosai jikin Zahra yayi sanyi Bata iya cewa komai ba sai Murmushi da tayi ta ce "yanzu kana wani gari"Ina Nan garin Anan na samu Aiki"Masha Allah Ubangiji ya taimaka "Zahra ta fada daidai isowar MD wajen Zahra na ganinshi taga yanda ya sauya fuska Saida taso tayi dariya tasan ba komai bane sai Ganin Hafiz da yayi Hafiz ko da kanshi yaje sukayi musabaha suka gaisa a wayance Zahra ta gwadawa MD takwarar da MD yayi Mata nannema ya saki fuska harya dauki babyn Wanda Hafiz ya dauki amera Musayar number sukayi tsakanin Aisha da Zahra Akan zasuyi zumunci bandir din 1k MD yabawa takwarar. Matar tasa kuka Akhbar yasa musu da zasu Tafi Shi sai Antafi da babyn duk dariya sukayi Masa dakyal aka samu ya hakura Shima Dan anyi mashi wayau da cewar za'a kawo Masa ita Saida suka biya Gidan chuchu da itama Tana da yaronta guda Sadiq yanzu Kuma Tana da wani Cikin Asmy ko yarinyarta daya itama Zahra aka Sanya Mata gidansu Dake Nan Abuja suka wuce Koda dare yayi Ganin yanda MD ke Shan kamshi Zahra ta gane na ganinta dasu Hafiz ne da yayi Dan a zaman ta da mijin Nata tasan Yana da tsananin kishi Wanka taje tayi na birkitawa Bayan ta feshe jikinta da turrarruka ta baya taje ta rungomosa Cikin muryar shagwaba kamar zatayi kuka ta ce" waya tab'amun Kai Sweetheart yau zaman garin Nan ya gagaresa "Dariyar da bai shirya ba MD yayi tare da janyota jikinsa ya ya rungumeta tsam a jikinsa ya ce "Waya Isa ya tab'a d'an Zahra Mijin Zahra Baban Zahra ya Zahra ukku ya kwana lafiya"kafin ya hade bakinsu waje d'aya su Lula Duniyar ma'auratan......✍️
*TAMMAT BI HAMDULILLAH*
Alhmdllh Alhmdllh Alhmdllh I am grateful to God for giving me the ability to finish this book a Nan ne Ni Hajara L Sadeq na kawo karshen wanna littafin Mai dogon zango Kura Kuran da nayi cikinsa Allah ya yafemun Allah ya bawa Al'umma damar fad'akuwa da sakon da nake son isarwa banida bakin magana wajen gode muku masoya bisa ga nunawa book dinnan tsantsar soyayyarku wajen sayansa da Kuma nuna kulawarku a gareshi Nagode ngd ngd bansan da wasu kalmomi zanyi amfani dasu wajen fad'a muku farincikin da kuka sanyani da dalilin book dinnan Kun nunamun tsantsar soyayyar da ba haufi a cikinta ku sani Ni hajara l sadeq taku ce ta har a bada masoyan Asali na gskiya da gaskiya Ina muku son fisabillah wolla inaji daku har Cikin kokon zuciyata zanyi missing dinku over Y'an amana Saimun hade a new book,
*NA SADAUKAR GA LITTAFIN NAN GA DUKKAN MASOYANA NA DUNIYA ALKHAIRIN ALLAH YAJE MUKU HAR GADON BACCINKU INA MUKU SON DA BAYA FADUWA A BAKI SAIDAI A ZUCIYA*
*ALHMDLLH LITTAFIN AUREN WATA TARA YA KAMMALU CIF INDA YA ZAMA COMPLETE DOCUMENT ZAKU SAMESA NE AKAN 500 KACHAL GA MASU BUKATAR SAYA SU TUNTUBENI AKAN NUMBER WAYATA KAMAR HAKA 07026166536 HAKA ZALIKA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DINA NA WHATS APP SUMA SU TUNTUBENI AKAN NUMBER WAYATA 07026166536*
_MA ASSALAM_
_*Miss Hajo Ce*_🤙