Showing 81001 words to 84000 words out of 153980 words

Chapter 28 - AUREN WATA TARA COMPLETE HAUSA NOVEL

30 Sep 2024

16358

to saikin fito "Murmushin yake kawai Zarah tayi tare da nufar d'akin da yake Kamar ko yaushe aikin d'aya daban ne yake using da system karasawa dakin tayi cikin nutsuwa ta ce " gani"Bandir din y'an dari biyar dake gefenshi an fiddosu ya mik'a mata tare da cewa "Anshi kiba bakuwar taki tayi kudin transport" saida Zarah ta Waro ido ganin uban kudi a ranta ta ce "Shi wai baisan darajar kudi ba " a fili kuwa cewa tayi sunyi yawa ai"Harararta yayi ya ce "Ke naba?tana turo baki ta amsa ta ce " Angode "kina turomun bakin nan na kusa maganinsu" Dan murmushi tayi tare da ficewa daga d'akin Inda ta samu Dr Halima na shirin fita mik'a mata kudin tayi ta ce "Gashi Aunty ya ce Kiyi kudin transport" Girgiza kai Dr Halima tayi ta ce "a a a wlh nagode kanwata bazan k'arba ba ai gobe bana dawo ba ana irin haka" Marairaicewa Zarah tayi ta ce "Dan Allah Aunty ki amsa bazaiji dadi ba Dak'yal Zarah ta samu ta amsa hijab d'inta ta sanya tare da fitowa Dan ta rakata cewa tayi ki koma basaikin raka ni ba " girgiza kai Zarah tayi ta ce "a a a Aunty muje" tare suka fita Inda a hanya Dr Halima sai nasiha take mata akan tabi mijinta "ita dai Zarah shiru tayi tana jinta a ranta ta ce " bakisan ciki ba Aunty da kinbar wa azin nan Auren da na lokaci ne kuma lokacin ya kusa karewa "sannan ta kara da cewa "kardai ki karashan maganin nan zai miki illah" nan nema zarah ta ce "insha Allah aunty bazan sake sha ba "ba suyi nisa ba ta samu napep Inda Zarah tayi mata Godiya tare da shaida mata zatazo insha Allah tare da Juyawa Dan ta koma gida Tazo tana gab da shiga gidan taji an kira sunanta daga baya Juyawa tayi Ganin Mlm sulaiman ne ya fito daga mota saida gabanta ya fad'i Dan ta manta rabon da ta ganshi ko a makaranta ma ta hangoshi sauya hanya take karasowa Inda take yayi tare da cewa " Malama Zarah kinyi wuyar gani"Kasa tayi da kanta Tare da cewa "Ina yini mlm" lafiya qalau me kikeyi anan"waigawa tayi ta kalli gidan saikuma ta dago ta rasa k'aryar da zatamai kawai sai ta ce "nazo wani gida ne " Okay muje na saukeki "saida ta d'an Zara dara_daran idanunta kafin tace " a a a Malam zankoma da kaina"saboda me?,saboda bana hawa motar maza"Dan murmushi yayi yana Kara Matsowa kusa da ita ya ce "Ga Alamun har yanzu ba a amshi tayin da nayi ba ko" gabanta na fad'uwa ta ce "Ba haka bane Malam an sanya Ranar Aure na ne" lokaci guda fuskarsa ta sauya a sanyaye ya ce "Allah sarki ashe na makaro Allah ya sanya alkhairi amma Gaskiya duk Namijin da ya sameki ya gama morewa a duniya Zarah ba k'aramun dace yayi ya more da komai na taya koma waye murna Gaskiya Dan samun kamarki cikin mata Sai an tona "" kasa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannun ta ce "Nagode Malam zan wuce" Murmushi yayi ya ce "Bazaki yarda na rage maki hanya ba kenan" girgiza kai tayi ta ce "hakan ma nagode Mlm"to shikenan bari na wuce daman gidana yana nan sama da wancen layin zankoma gida ne na hangoki Sai Anjima ki k'ara dagewa dai wannan shine mai matsalar na karshe " Murmushi tayi ta ce "Insha Allahu ngd " ta juya zata shiga ta Hango Motar MD Na fitowa daga gidan ta Cikin mota ya dinga mata kallon mamaki yana karewa saurayin kallo tsaye yayi lokaci guda naga fuskarsa ta sauya har lokacin baibar kallonsu ta Cikin motar dashi yake kallonsu su basa ganinsa Zarah ko kallo d'aya tayi wa motar ta kauda kai Jan motarsa MD yayi da karfi tare da barin Wajen ya nufi gidan gonarsa Zarah ko saida taga tafiyar malaminsu kafin tashiga cikin gidan a ranta ta ce "Ji a baka kamar mutumin kirki k'ilama.sharri ne ake masa saikuma.tace " kodan a fuska ba a ganewa"MD shine bai dawo gidan ba sai Bayan isha'i lokacin Zarah harta kwanta kan bed din da littafin hisnul Muslim a hannunta tana karanta adduo'i shigowa MD yayi d'akin kallo d'aya tayi masa ta wutsiyar ido ta maida kanta ga abunda take sosai ya had'e rai tahau ba alamar wasa a fuskar tasa karasowa yayi d'akin ya Kalleta a murtuke ya ce "waye na ganku a kofar gida" Dagowa tayi tare da Kallonshi irin kallon mamaki kafin ta kauda kai ta ce "Meye ruwanka da koma waye?" ni sa'ankine zaki fad'awa maganar rainin hankali zakiyi mamakin abunda zan maki wlh kina mayarmun da magana son ranki "Murguda baki Zarah tayi tana Kara kauda kai"batai aune ba saiji tayi ya murde mata baki" ihu ta fasa tuni hawaye harsun wanke mata fuska Inda take ya zauna tare da matseta jikin allon gadon Dan Kara ta saki Cikin kuka ta ce "Me nayi maka kuma " Zaki fad'amun waye shi ko saina maki abunda bakiyi tunani ba "Malamin mu ne" ta fad'a cikin kuka"tsaki yaja tare da cewa"shine dan iskanci zaki Fara kawomun kazaman kartin maza kofar gida dan iskanci"Dukda tanajin zafin matsar da yayi mata bai hanata cewa ba "Nidai ba y'ar iska bace " wa yace maki yar iska?Kai "ta fad'a tana cigaba da kuka" Tsaki yaja tare da cewa "ke kikaji ai" Turo baki gaba tayi ganin ya d'an tashin daga wajen "kasa kasa ta ce " Allah ya isa?Jin abunda ta ce "ya sanyashi juyowa tare da nuna kansa ya ce " Dani kike"Girgiza kai tayi ta na hawaye ta ce "Ni ba abunda nace"aini Naji me kikace ya fad'a yana Kara matseta " ya ce maimaita abunda nace "cewa nayi akwai Allah" sassauta matsar da yayi mata yayi tare da Jan tsaki a ransa ya na shirin Mikewa a ranta ta ce "Mugu Azzulumi macuci Allah saiya sakamun" Zaro ido MD yayi tare da kallonta ya ce "Ni kike fad'awa haka?Sai sannan Zarah ta tuna a fili tayi maganar ja da baya tayi tare da cewa " Nifa Bada kai nake ba "Dan murmushin gefen baki yayi ya ce " zanyi maganinki yanzunnan"yana gama fad'ar hakan ya fara rage kayan jikinsa Zarah na ganin haka tasan yau shikenan ta shiga hannu"Tana shirin sauka daga gadon yabi ya danneta......sosai Zarah ta karbi wuta a wajen MD bata tabajin gundurar abun irin na yau ba Dan cike da mugunta MD ya dinga binta saida yayi awa biyar a kanta tun 9 sai 2 ta samu ya rabu da ita Shima Dan ta dinga fasa.masa kuka ne shi kanshi yasan yau ya kurewa yarinyar daman haka yakeso shiko ranshi fesssss Zarah ko tuni baki ya mutu ta k'ara tsorata da mutumin nan kwata_kwata bashi da wasa washageri gashi suna da lectures safe tun asuba bata koma bacci ba ga baccin dake idonta bana wasa bane ga gajiyar da MD ya Tara mata shiko yana kwance kan bed a gaggauce ta shirya Bayan ta had'a ruwan liptop bako madara haka Tasha saboda sauri take tana komawa d'akin hijab d'inta ta sanya Harzata fita ta tsinkayi muryarsa da cewa"karfe nawa zaki dawo "A tunaninta ma bacci yake saita taja gunguni a ranta kafin ta ce " 4 Kuma 2 suke da lectures ta fad'a masa hakane Dan ta sarara"Okay "kawai ya fad'a " tana fita driver har yazo Dan tuni yasan lokuta da take Da lectures koda Zarah ta gama lecture hostel ta wuce kallo d'aya zakayi mata kasan ba daidai take ba saboda ba k'aramun bacci bane a idonta tana shiga ta samu su Asmy na lunch kasancewar 2 lokacin suma basu jima da dawowa daga lectures ba kai tsaye bed ta haye tare da sauke ajiyar zuciya kwanciya tayi Chuchu ce ta ce 'Lafiya dai momcy"lafiya qlau bacci ne kawai nakeji wlh "ta fad'a tana juya musu baya tare da kwanciya ta cire hijab din jikinta Da kallo Asmy ta bita kafin ta ce "Ki sauko kiyi lunch tunda nasan daga lecture kike bakici komai ba " idan na tashi naci ta bata amsa bacci ne mai nauyi ya d'auki Zarah ita ce bata tashi ba sai 4:30 Dan koda Asmy ta ce Zata data ita chuchu tace ta rabu da ita tana tashi salla kawai tayi sai sannan taci abincin da su Asmy suka rage mata a cooler tana gamaci time.ta duba taga har biyar saura tunani tayi tasan drivern yazo kila harya tafi tsaki taja a ranta ta ce "Yau ba Inda zani wlh mugu kawai" har dare ganin Zarah bata da niyyar tafiya ya sanya Chuchu cewa "wai yau nan zaki kwana amma" Eh nan zan kwana"Alhmdllh daman ina son ki jiye mun harda Dan so nake na sauke kafin mu gama sch d'innan wlh"Murmushi Zarah tayi ta ce "Insha Allahu zama ki sauke kafin lokacin tunda Kinga yanzu hizif shida ya rage maki" Da daddare Zarah ta amshi haddar Chuchu Inda ta kuma Kara mata wani shafin driver ko tunda yazo yayi ta jira yaga bata nan ya koma ya fad'a ma ogansa bai ganta ba "Okay kawai md yace " Kd ya wuce Ranar Dan yanason ganin Ammynsa "washegari ya koma Zaria Bayan yayiwa Ammynsa bankwana " Zarah ko ranar ma so tayi ta k'ara kwana dandai kawai tana fitowa lectures ta had'u da driver da ba abunda zai maida ita tana zuwa ta samu MD ya hakimce a kan kujera a takaice ta gaisheta tare da wucewa ciki....after 3 weeks Rabin rayuwar md yanzu kam ta dawo Zaria saboda koda yaushe yana nanike da Zarah yana kwasar romo ko sch yanzu dak'yal yake barinta ta tafi Zarah ko tana nan tana lissafin sauran wata guda ra rage yarjejeniyarsu ta kare inda karatunsu ya rage wata biyu su gama tun daga lokacin da ta zubar da maganin nan bata Kara waiwayar sha ba kwata_kwata tunaninta ma baikawo mata komai a ranta ba harkar gabanta kawai take "Yauma dak'yal MD ya rabu da ita Dan a safenma yanzu ba d'aga mata yake ba cikin Sauri ta gama shirinta Zata wuce sch tana shirin fita Ya ce " kijira na saukeki hanyar nayi"to"ta fad'a a hankali tare da zaunawa gefen gadon tana nan harya gama shirinsa ya fito Cikin shigarsa ta alfarma da gayu sai baza k'amshi yake kallo d'aya Zarah tayi masa tayi kasa da kanta saboda gabanta dake tsananin fad'uwa a tare suka fita Inda ya shiga driver sit ta zaga ta shiga gaba sun fara tafiya kenan ta Hango wata yarinyar mai tallar ta aya a faranti cikin Sauri ta d'ago tare da cewa "Dan Allah ka tsaya zan saya abunchan" Kallonta yayi tare da Kallon abunda take nuna masa ya ce "me zakiyi da abunchan ya gama shan kura a titi jifa " Tana Shagwabe fuska ta ce "Nidai ina so" parking yayi tare da mik'a mata 1k ya ce Amshi ki saya zage glass din motar tayi cikin Sauri ya sadda kansa Dan karma wani ya gansa a ganesa Zarah ko mamakinsa tayi kamar wani marar Gaskiya Juyawa tayi ta kira mai ta ayar Inda ta saya ta 500 ta bar mata chanjin a leda aka sanya mata har lokacin kan MD sadde saida ta Zage glass din kafin ya d'ago ya tada motar sukayi gaba kasayin shiru Zarah tayi ta ce "Wai Dan Allah me yasa baka San ana ganinka yanzuma ka sadda kanka " Is not your business "ya fad'a yana cigaba da driving" Turo baki gaba tayi tare da Fara cin ta ayarta har wani lumshe ido take Dan sosai tayi mata dadi ita kanta mamaki take da bata tabajin sha'awar wannan Abun ba Amma yau sosai taji dadinta Ta wutsiyar ido MD yake kallonta yanda ta dage take gintsar Abu da shi baimasan menene ba "bismillah" ya tsinkayi muryarta"Alhmdllh kici kayanki""Ka dandana kaji da dadi "Girgiza kai yayi a takaice ya ce "Banajin irin abubuwan nan" tab'e baki tayi tare da cigaba da cin abunta har cikin makaranta ya kaita Daidai gab da hostel d'insu yayi parking sauran ta ayar ta sa a jaka tana shirin fita Ya ruko hannunta Tare da damk'a mata 5k a hannu ya ce "Ki dawo da wuri yau please da yazo ki biyosa kidaina tsaidasa" Kasa tayi da kanta Tare da cewa"Toh ngd"har lokacin bai saki hannunta ba Ganin irin yanda yake kallon hannun tare da murzasa tanason tayi magana amma kwarjini yau da yayi mata ya hanata Chan Bayan few minutes ya ce "Kidingayin lalle zaiyiwa hannunki kyau inason ganin lalle a hannun mace"gaban Zarah na fad'uwa ta d'ago ta Kallesa saikuma tayi saurin kasa da kanta samun kanta tayi da cewa " To kace Matarka ta dinga yi maka mana"Murmushin da bai shirya saki ba ya saki ya ce "Kenan sai matata zatayi mun" Eh"ta fad a hankali"wani murmushin ya k'ara saki ya ce "To Matar wata Tara nace ta dingayi yimun ba ta gidan ba" ba tare da ta Kallesa ba ta d'an turo baki gaba ta ce"Matar wata d'aya dai ai wata Tara baya ne yanzu saura wata d'aya ko ka manta"ina sane harkin k'agara lokacin yayi mu rabu ko"D'ago da dara daran idanunta tayi ta sauke a kansa saitayi saurin kasa da kanta ta ce "Ina makara karya hanani shiga" Okay "ya fad'a yana sakin hannunta bud'e motar tayi tare da fita Daidai idonta ya sauka akan Hafiz dake gaban motar Kad'an sosai taga ya kara kyau da kiba yasha shaddarsa ash mai shegen kyau Ya harde kafa d'aya kan d'aya a jikin sabuwar motarsa sosai gabanta ya tsananta fad'uwa da karfi dafe saitin zuciyarta tayi daidai sukayi ido hud'u da shidinma ita yake kallo bako k'iftawa sannan yana bin motar da ta sauka da Kallo a matuk'ar rude ta juya ta kalli MD dake cikin mota har lokacin yaki tafiya Shima Inda take kallon yake Kalla Juyawa tayi ta k'ara kallon Hafiz da Shima motar MD yake kallo dukda baya ganin Wanda ke ciki lokaci guda Zarah taga fuskarsa ta sauya Wanda Bata tab'a ganin hakan a tattare dashi ba kamar wacce kwai ya fashewa haka ta k'arasa Inda yake ta kalli bayanta ta kalli gabanta haka ta dingayi ga MD yaki tafiya cikin jarumta ta k'arasa Inda Hafiz yake da har lokacin kallonta yake ya kalli motar da ta sauka dak'yal ta iya tattaro jarumtar da bata San tana da ita ba ta ce " Ya Hafiz Kaine da gaske kuwa"Juyowa yayi ya kafeta Da idanu tare murtuke fuska tamau nuna motar da ta fito daga ita yayi cikin muryar b'acin rai ya ce...........✍🏿

07026166536 domin neman Karin bayani
_Tofa ya kenan Ga MD ga kuma Hafiz_🙆

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*


1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨



_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy: 🅿️.........*69 & 70*


Da taimakon Asmy da mamansu ta gyara jikinta sosai ta d'an galabaita sannun kawai maman Asmy ke mata ta ce "Baki da lafiya daman?Gyada mata kai tayi ta ce " amma ba Sosai ba "Ikon Allah ai bamuga ta zama ba amarya ba lafiya maza shirya mu tafi Asibiti" A sanyaye ta ce "Mama Bafa wani Abu bane kaina ne kawai ke ciwo kuma nasha magani basai anje Asibiti ba " A a ban yarda ba shi kuma aman na meye ?rasa me zatace tayi ta ce "Wannan maganin ne Mama daman banason shansa shine kawai ya kawomun Tashin zuciya har nayi aman" to shikenan tunda kinki Aje asibitin Maganin nan kam dole ki dinga shansa saboda yafi kowanne amfani bazaki gane amfaninsa ba sai nan gaba "shiru tayi tana kasa da kanta Asmy da duk gabanta fad'uwa yake itafa zargin ciki takeyiwa Zarah Dan duk wasu alamomi na masu ciki take gani a tattare da ita tun a sch bare yanzu da suka dawo gida abun yayi gaba kama hannun Zarah tayi suka koma daki tare da rufe d'akin cike da damuwa Asmy ta ce " Zarah yaushe rabonki Da Perioud? saboda me kikamun wannan tambayar?saboda cire kokonta ki fad'amun Gaskiya "Ajiyar zuciya ta sauke ta ce " Rabon dai da nayi cikakken perioud wata Ukku idan yazo Kad'an yake zuwa kuma kwana daya ya tafi wata biyu baya nayi irin haka Wannan watan ne banyi ba ko kadan kuma naga lokacin ma da zanyi kamar ya wuce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Asmy ta shiga nanatawa ta ce " na shiga ukku Zarah Kardai ace ciki ne dake"a matuk'ar rude Zarah ta ce "Ciki kuma?Eh ciki ni duk alamomin masu ciki nake gani kamar tattare dake " dukda gabanta dake fad'uwa bai hanata Jan tsaki ba ta ce "Lallai baki da hankali Asmy me zai had'ani da ciki nikuwa Bayan nafada maki Watanni biyu baya nayi perioud kuma rabo na da Azzalumin mutumin nan wata Ukku taya kuma zan dauki ciki please kibar maganar nan kar tashin hankalin yayi mana yawa ga wancen bamu gama ba ki b'ullo wani"tagumi Asmy tayi ta ce " Zarah Bazan tabbatar ba har saimunje asibitin ki tashi muje a gwadaki idan akaga babu sannan ne hankalina zai kwanta Amma yanzu babu ni babu kwanciyar hankali"tsaki Zarah taja ta ce "Ba Inda zanje wlh Kuma ba wani ciki jikina Allah ya kiyaye Ya tsareni da Cikin azzalumin mutumin nan macuci ya cuce ni ya yaudare ni Allah ya isa tsakani na dashi " ta k'arasa fad'a hawaye na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login