Showing 96001 words to 99000 words out of 153980 words
abunda aka fad'a ta ce " Ikon kaji mai mugun hali ayi maka wannan Babban Albishir da muka dad'e muna jira ka zauna haka sototo ko fara'a babu a fuskarka"Sai sannan MD ya kalli Hajiya Yana hade fuska ya ce "me kikeso nayi nagodewa Allah a cikin zuciya ta Bayan haka me zanyi kuma"tsaki Hajiya taja ta ce Wlh tunda nake rayuwa bantaba ga mutum mai irin bakin halinka ba shekara goma Kana neman haihuwa yanzu Allah ya kawo kaki nuna farincikinka ai nazata likitan dinnanma yau sai anyi mishi tukuici babba" Shiru MD yayi baice komai ba danshi hankalinshi ba anan yake ba "Ammy tayi mamakin yanda MD yayi da murmushi a fuskarta ta ce " Congratulations Baba na Allah ya rik'a"Ameen Ammy"ya fad'a ba walwala a fuskarsa "Zey ce ta ce " Congratulations yaya Gaskiya munyi murna wlh Allah ya raba lafiya"Murmushi itama ya sakar mata ya ce "Ameen sis" Cikin farinciki Chuchu ta ce "Congratulation yaya nayi farinciki Sosai wlh kaima zaka zama Daddy harna k'agara naga fitowar Babynka" Murmushi ya sakar mata Itama Mikewa yayi Ya ce "Ina zuwa Ammy " yana fita da Kallo Hajiya ta bisa tare da tab'e baki ta ce "Allah ya yaye maka wannan mugun Abu" nan fa Amera taga tarairayar wajen Hajiya da da bata kaunarta yanzu ita ce hada cewa me take so a girka mata Chuchu ma dukda basa shiri da Amera sosai taji dad'in samun cikin nata kuma ta tayata murna MD na fita suka had'u da Dr Jinjina masa yayi ya ce "Nagode Dr Dan Allah wannan din ya zama sirri tsakaninmu" Karka samu matsala ranka ya dad'e insha Allahu daga wajena bamaijin wannan maganar"Ajiyar zuciya Md ya sauke Bayan yayi de transfer 200k motarsa ya shiga tare da hade kansa da sitiyarin mota Jaber ne ya fad'o masa arai Tabbas dole ya neme sa dukda yasan har yanzu fushi yake dashi amma dole ya nemesa Dan shine kawai zai iya sama masa mafita dukda waccen mafitar tashi ita ta ruguza komai..
Yau tunda ta tashi takejin jikinta ba dadi ga wata irin kasala da takeji haka dai take daurewa amma ita kadai takejin yanda takeji ga bata iya cin abinci yanzu Kowa daka Kalleta saikagane ta zama so silent ga wani fari da kyau data Kara kowa sai ya lakanta hakan da dilkan amare ce da aka fara mata Sosai hankalinta yake tashe kasancewar Bikinta da Hafiz dake k'aratowa Dan yanzu idan bazata mance lissafin ba saura kwana goma ba wani shiri da take daga bangarenta Dan ko Anko bata fiddo ba haka rabon invitation daga ita har aminiyarta ta basa cikin walwala Musamman Asmy da har wata irin rama tayi Dan kullum da abunnan take kwana take tashi sai kowa ya lakanta hakan da rabuwa ce da zasuyi ya sanya sukayi sanyi yauma Zarah tana kwance Kanta keyi mata ciwo sosai Kamar zai tsage da gudu taji shigowar khairat tana cewa Aunty Zarah"Dukda ciwon kan da Zarah take bai hanata farincikin tarbar y'ar uwar tata ba Rungume juna sukayi Zarah ta ce "Badai har kunyi Hutu ba " Eh Aunty dawowata yanzu kenan bakiga ko unifoam ban cire ba ke na fara nema "Kama hannunta Zarah tayi ta ce " Gaskiya ne Autar Baba Ke boarding dinma amsarki tayi naga hada su kiba kikayi"Dariya tayi ta ce "Kai Aunty wlh ba dadi boarding din Bari naje na cire kaya akwai labari Allah ya taimakeni Ina nan za ayi bikin ki " Murmushi kawai Zarah ta mata tana barin d'akin ta koma ta kwanta koba komai taji dad'in zuwan khairat Dan ta samu Mai d'ebe mata kewa dukda Asmy kullum tana gidan ko kuma idan taje gidansu amma khairat ita har daki daya zasu iya kwana "ya rage saura sati d'aya biki aka kawo Lefe Sosai kowa ya yaba irin kokarin da Hafiz yayi kala hamsin ya zuba mata a akwati dangin babanta da makwafta sai yaba kayan suke Mama Rabi ma ko itace uwar zakalkalewa hada guda " A lokacin Zarah na kwance a gidan su Asmy Dan yau da zazzabi ta tashi Kiran Hafiz ne ya shigo wayarta Bayan ta d'auka ya ce "My love Kinga kaya sunyi maki dai ko ko a sauya sannan dinkunanki da zakisa da biki suna wajen tela katsina insha Allah gobe zasu Iso ina fatan suma zasuyi miki Dan na lura baki da shirin badawa shiyasa na bada maki"Banshiga gidan ba na Kalla ya Hafiz amma nasan sunyi Allah ya k'ara budi " Ai komai nayi maki ban fad'i ba Zarah kin chanchanci fiye da haka "Bayan sun gama wayar sosai Zarah ta fara hawayen tausayin kanta Hakika ta cutar da Hafiz ,ta yaudareshi,taci amanarsa ,batayi masa halacci ba yayi mata Rana tana shirin yi masa dare "dukda tasan ita kanta bada son ranta Hakan ya faru ba K'addarar ce ta zaba mata hakann taya zata iya fuskantar wani da wannan Maganar?Taya Kuma zata yarda A daura mata Aure kan Aure ?wannan wace irin kaddararriyar rayuwace ta tsinci kanta Batasan lokacin da hawaye masu d'umi suka shiga zubo mata ba Maman su Asmy ce ta shigo d'akin da take kwance kasancewar Asmy ta fita Sayayya kasuwa cike da kulawa ta ce "Taso Zarah ki daure kisha Maganin nan " Goge hawayenta tayi tare da mik'ewa zaune ta ce "To Mama" Girgiza kai Mama tayi ta ce "Yauma kukan ne kikayi ko Zarah?na rasa abunda yake damunki keda Asma'u tunda kuka dawo daga makarantar nan bana gane kanku idan tunanin rabuwa kuke ai baku rabu ba kuna tare Har abada Aure baya raba Abuta to na lura abun naku ma ya wuce yanda nake tunani" Shigowar Asmy d'akin ya sanya Mama kallonta tare da cewa "kema shigo" a sanyaye ta shigo d'akin duk ta rame itama zaunawa tayi gefen gadon dukansu sukayi kasa da kansu kamar wasu munafukai "Mama ta d'ora da cewa " Dan Allah ku saki jikinku ayi bikin nan cikin walwala Ke yanzu Asmy bake ce aminiyarta ba ko ita bata saki jiki ba aike yakamata ace kinzama kirjin biki kin jajirce a bikin kawarki amma sainaga kema din kamar kin fita solancewa sakarcine yanzu ina tsammanin ko rabon katin gayyata baku kaiwa kawayenku ba bacin Anko da baku raba ba wannan Asama kun lakanta hakan da kurewar lokaci To wlh nidai ina fad'a muku tun wuri ku nutsu kusan abunda kuke"a sanyaye Zarah ta ce "Insha Allah Mama" Asmy ma ta ce "Insha Allah Mama zamuyi rabon IV din Tunda da sauran time" Da dai yafiye muku maza ki Shanye ta fad'a tana mik'awa Zarah cup din da tunda taji warin abun taji zuciyarta na wani irin tashi tana kafawa a baki kurba d'aya tayi taji wani irin amai na tunkaromata a Guje ta tashi tare da rugawa tsakar gidan a makwararo ta durkushe nan ta fara sheka amai kamar zata amayar da y'ay'an cikinta daga Asmy har Mama biyota sukayi Inda suka sameta durkushe sai kwarara amai take kamar zata amayar da y'an cikinta.........✍
*Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536*
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
_*Miss Hajo Ce*_🤙🏿
[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy: 🅿️ .........*75 & 76*
Cikin Sauri MD ya zame bakinsa dukda yaji zafin cizon da tayi masa amma bai nuna ba har suka isa Abuja zahra a hauka ce take lokacin da suka isa 11pm harta gota kin fita tayi daga motar bayan isarsu gidansa dake Buzu quarters sosai take kuka tana ja masa Allah ya isa Wanda sosai yakejin zafin hakan a cikin ransa Saida ya ciccibeta tukwana ya samu ya fito da ita zullewa take amma ya ki sakinta ya Rungumeta jikinsa sosai yayi Hanyar part din da ita shidai driver kanshi gaba d'aya kulle yake Dan yayi mamakin abubuwan da suka faru yasan dai uban gidan nasa mutumin kirki ne to me zai hadasa da wannan yarinyar har tana ikirarin yayi mata ciki"Sauri barin wannan tunanin yayi ya ce "Ba abunda ya shafeni bane inje inyi ta aiki na " MD bai dire ta ko ina ba sai tafkeken bedroom dinsa dake gidan zahra na ganin haka ta zabura ta mik'e kamar mahaukaciya ta ce "me kake nufi da satoni da kayi Bayan tozartani din da kayi bai isheka ba wlh wannan Karin baka isa ba Saidai duk abunda zai faru ya faru Ka cuce ni Allah ya isa tsakani na dakai Daman kasan da cikinka jikina ka bari na koma gidanmu dashi Dan na wulakanta a idon iyaye na da jama'a sannan kak'i saki na kawai d'anka wulakanta ni nasan Duka da gangan kayi wannan din Allah ya isa tsakani na dakai kuma wlh saina zubar da tsinannan cikin....MD baisan lokacin dayayi saurin rufe mata baki ba cikin muryar tashin hankali ya ce " Karki tsinewa Cikina Mamy look ki tsaya mu fahimci Juna "fusgewa tayi da karfi tace " wace fahimtar juna,ai ba wata sauran fahimta ni dakai Wlh tallahi kaji na rantse saina zubar da kaddararran cikin nan mugu azzalumi macuci Alla ya isa tsakani na dakai"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un MD ya shiga maimaitawa Dan a halin yanzu ji yake babu abunda yake so yake k'auna kuma yasa guri akansa kamar cikin nan dake jikinta da ya tabbatar yanzu sosai yaji k'aunar cikin na musamman Wanda yakejin bazai tab'a iya jure rashinsa ba ga zafin irin yanda take ja masa Allah ya isa "Toshe kunnuwanshu yayi tare da rumtse ido Dan bayajin zai iya jure kalaman da take danganashi dasu " Zarah wata tsanar MD takeji wacce bata tabajin irinta ba A matuk'ar haukace ta mik'e tare da kalle kallen Inda zataga mabugi Dan zuciyarta wata irin tafarfasa take "gaba mirror ta ruga kamar mahaukaciya ta fara warwatsa abubuwan da ta gani a kai tare fara tillawa MD Sosai yakeyi mata kallon mamakin abunda take" Mikewa yayi yana shirin nufar Inda take ta tilla masa.kwalbar turare a kafa ji kake tassss "Auchhh ya fad'a yana kallon kafarsa da ta fara fitar da jini Kallonta yayi yaga yanda take kuka ganin tana shirin Bugawa cikinta wata kwalbar baisan lokacin d'aya take kwalbar ba ya chafke ta hannunta Tare da janyota jikinsa cikin b'acin rai ya ce " Baki da hankali ne.wai Mamy me kike haka illata kanki zakiyi"ka sakeni ina ruwanka da rayuwata ina ruwanka da koma meye zanyi wlh na tsaneka na tsani cikin nan "ta fad'a tana bugar cikinta da k'arfin gaske " a d'imauce MD ya rik'e hannayenta sosai baimajin zafin yankan da yayi yana gani ido biyu tana shirin yi masa asarar ciki"Gado ya nufa da ita ta karfi tana fusgewa ya kwantar da ita fusgewa take sosai Kamar mai iska tana kai masa Duka da Allah ya isa "har 3:PM MD da zahra ba Wanda ya rintsa sosai ta haukace masa da tayi nan ta tallabosa dak'yal ya samu ya matseta jikinshi sosai ya rasa yanda zaiyi da ita addu'ar ko yayi ta ba adadi yana tofa mata matseta yayi sosai a jikinsa yanda Bazata iya motsi ba tun tana Kokarin kwacewa harta kasa jikinta ya mutu muryarta ta dishe da kuka a haka ya samu bacci ya kwasheta MD na ganin tayi bacci Ajiyar zuciya ya sauke dukda farincikin cikin dake jikinta bai hana zuciyarsa shiga damuwa ba Ganin irin tsanarsa a idon yarinyar k'iri k'iri kallonta ya dingayi yanda take baccin kasan baccin wahala na kallon cikinta yayi da yaso fitowa Wanda ba kowa zai fahimta ba a hankali ya shafa Cikin ya ce " Allah ya fito mun da ke Ko kai lafiya"Kwata kwata ji yayi bacci ya kauracewa idonsa ranar a zaune MD ya kwana rik'e da zahra da har lokacin take jikinsa duk yanda yaji ta motsa sai yaji har cikin ransa.....bangaren Asmy tunda taga tafiyar zahra ta zaune wajen ta fashe da wani irin kuka Nan Chuchu ta dawo ta isketa ta ce "Ina momcy din "" Ganin yanda take kukan ne ya tsoratata da Chuchu ta ce "Ki fad'a mun Inda take karkice mun sunzo sunkoma da ita" ta fad'a cikin daga murya sai sannan Asmy ta d'ago cikin dakiya ta ce "Wanda yayi mata ne yazo ya tafi da ita " What ya tafi da ita kuma kika zauna a nan kina ganin ina ya tafi da ita"ruko hannunta Asmy tayi ta ce "Na yarda ya tafi da ita d'in ne badan komai ba saidan hakan zaifi mata sassauci iyayenmu bazasu tab'a fahimtar mu ba Chuchu duk nice silar shigar zahra halin nan da take ciki Nina cuceta na zalince ta " ta fad'a tana fashewa da kuka "Sosai kwalwar Chuchu ta chushe ta ce " me kike nufi Asmy Dan Allah ku fiddani cikin duhu kuna rud'ar dani Na kasa fahimtar komai"Ruko hannunta Asmy tayi tana zaunar da ita gefenta ta ce "Chuchu cikin dake jikin zahra ba cikin shege bane cikin sunna ne kamar kowani d'a Saidai nasan ba kowa zai fahimci hakan ba " ta fad'a kukan nadama nacin karfinta karfinta "Da mamaki fuskar Chuchu ta ce " me kike nufi Asmy bangane ba taya zakice haka Bayan ba Aure tayi ba kin sanyani cikin duhu"Goge hawayenta Asmy tayi ta ce "Zanfada maki sirrin da muka jima muna boye miki badan komai ba Saidai bamuyi tsammanin zuwan wannan ranar ba Chuchu zan fad'a maki labarin nan saboda na yarda dake kuma zamu iya magance matsalar nan mu Ukku tunda dukanmu mun yarda da juna kuma munzama tsintsiya madaurinta d'aya amma kafin nan kiyimun Alk'awarin bazaki fitar da maganar nan ba tsakaninmu zaki barta a cikinki kamar yanda muma muka barta cikinmu batare da sanin kowaba" kama hannun Asmy tayi ta ce "karkiyi shakkar fad'amun koma meye Asmy wlh nayi maki alk'awarin bamaiji hatta mahaifiyar da ta haifeni bare wani ki daukeni tamkar yanda kuke da zahra " numfashi Asmy ta ja kafin ta fara labartawa chuchu komai daya faru bata boye mata komai ba har alakarta da zahra Sosai Chuchu ta girgiza dajin wannan al'amarin tamkar almara bata tab'a tsammanin hakan ba Sosai zuciyarta ta girgiza dajin wannan bak'ar chakwakiyar da suka shiga "a Gaskiya Asmy kinyi wauta kawai dai mutanen nan yaudararku sukayi Amma wlh akan wai ciwon cikin perioud karyane Ace anyi aikin million's har Talatin a tunani na kawai suna da wata manufar tasu na Auren a Gaskiya a lokacin da kinyi shawara dani wlh da hakan bata faru ba mai faruwa ta Riga ta faru Saidai a kokonci gaba yanzu ina mafita?,Goge hawayen da suka zubo mata Asmy tayi ya ce " ba wace mafita data wuce mu roki Allah ya warware mana wannan sarkarkiyar "numfashi Chuchu taja wayarta Ce tayi ringing dubawa tayi taga ya jaber ne " Cikin Sauri ta d'auka Daga bangarensa ya ce "Kina ina nazo daukarki ina daidai gaban general din ?waidaman Kaine zakazo shine dazu yaya Ya kirani yace yazo harna tafi nemansa bangansaba daman Nasan da wasa yake bazaizo garin nan da Daren nan ba ka jira ni gefen asibitin Kad'an gani nan" tana gama fad'ar hakan ta katse kiran Tare da Kallon Asmy ta ce "Sis muje na d'auki kayana gida zantafi" Haba Chuchu da Daren nan saikace wacce aka kora ai Ammy ma taganki bazataji dadi ba ki barwa Safiya"Girgiza mata kai tayi ta ce "Bazan iya kai gobe garin nanba sis wlh a tsorace nake Matar nan kinajin tana zata hadamu da y'an daban gidansu Gwara na tafi gida, banso kika bari macucin mutumin nan ba ya tafi da momcy naso mutafi gida tare Ammy bazata tab'a kasa fahimtarmu ba amma dai kome kenan zamuyi waya ki taso muje" Goge hawayenta Asmy tayi tare suka jera Chuchu sai leke take Dan har lokacin a tsorace take Hango Motar jaber da tayi yasa hankalinta ya kwanta Jabir na ganin Asmy saida hankalinsa ya tashi tsoronshi d'aya karta ganesa dayake Chuchu ta shiga gaba Asmy ta shiga baya kwata kwata hankalinta ma baya jikinta Hakan yasa bata gane Jabir ba gashi daman dare ne jakar kayanta kawai Chuchu ta d'auko daga gidan su Asmy tayi musu bankwana suka juya Kd ita da jaber da Daren nan Asmy ko Daren ranar kuka ta kwana tanayi bangaren Chuchu sosai Ammy tayi mamakin dawowar tata cikin dare ga yanda ta dawo duk a firgice ba walwala koda Ammy ta tambayeta meke faruwa ce mata tayi ba komai yin duniyar nan Ammy tayi ta fad'a mata abunda ke damunta ta ce Bakomai "To ya akayi kika dawo yanzu bacin ko d'aurin Auren ba ayi ba " Amfasa "ta bata amsa kai tsaye " subhanalla garinya"a Shagwabe Chuchu ta ce "Dan Allah Ammy mubar maganar nan " Hmmm Allah kyauta "kawai Ammy ta fad'a ta rabu da Chuchu Daren ranar da abun Chuchu ta kwana a ranta sosai labarin da Asmy ta bata ya tsaye mata a rai Juyi kawai ta dingayi amma bacci kam Saidai barawo ya d'auketa...bangaren Zahra koda ta farka ta ganta a hannun MD sosai taji takaici da bak'inciki kamar taga kashi haka ta tashi daga kanshi Tana Danasanin saninsa da tayi a rayuwa Toilet ta nufa MD na ganin haka ya sauke ajiyar zuciya Tare da fita Bayan ya rufeta Dan karma ta gudu ta sanyashi cikin wani hali itama ta saka kanta Sai sannan ya samu damar shiga bedroom dinsa yayi alwala Zahra ko a toilet dinma saida Tasha kuka ba wanda take tausayi take tunawa kamar Baba" yana wani hali?ta tambayi kanta"Sosai ta dinga kuka har ciwon kanta ya dawo sabo kafin ta daure