Showing 6001 words to 9000 words out of 153980 words
nan idan ba Dan kin sameta mai hakuri bata fad'amun shiyasa kika maida ita jakar ki to hakuri na ya fara kaiwa Bango daga yau Zahra'u bazata sake Wani aiki a gidan nan ba su d'iyanki aikinme suke idan bazasuyi aikin ba gidan ya rube karewar kazanta kumasannan daga yau Kika Kara d'aga hannu kika daki yarinyar nan kin daki igiyar auranki a bakin aurenki"
Nuna kanta Rabi tayi ta ce "Ni kake fad'awa haka Malam " Amfad'a maki ko akwai abunda zaki iya"jinjina kai tayi ta na girgiza k'afa na borin kunya Dan Malam bai tab'a mata haka ba tasan yakai bango Har ya iya d'aga baki ya furta mata a igiyar Aurenta tofa ya fara gajiya da ita hakan yasanya ta yin lakwas Dan Tasan ta rabu da Malam asirinta ya gama tonuwa Dan duk cikin mazajenta biyar da ta aura babu mai hakurin Malam bazata tab'a yarda Auransu ya lalaceba
wucewa ciki tayi kamar zata tashi sama Baba ko Kallon Zarah yayi ya ce "Tashi ki shiga kici gaba da hakuri kinji wataran sai labari " Mikewa Zarah tayi ta ce "Toh Baba nagode " tare da shiga d'akinta tana hawaye har bacci ya d'auketa.
Washegari koda ta tashi bata sa ran Bata abinci ba Ta na nan zaune wajen 10 koda ta lek'a ta tambaya ina abincinta Da masifa Mama Rabi ta korota ta ce Daga yau bazata k'ara cida ta ba Tunda ubanta ya hanata ta girka to itama bazataci shi ba ta nan zaune ta na hawaye taga shigowar Asmy dakin maza tayi ta goge hawayenta Murmushi suka sakarwa juna "Zarah ta ce
" yanzu nake tunaninki Besty"wlhko nima tunaninki ya sanya na taho ta fad'a tana zaunawa gefen katifar da take kallonta tayi ganin yanda fuskarta ta kumbura Alamun Tasha kuka kamata tayi ta ce "Mai ya faru Besty " kirkira murmushi tayi ta ce "Bakomai me kika gani"?hmmm karkiyimun karya Zarah ina gane halin da kike ciki ko baki fad'amun ba nakanji a jikina fad'amun meyake faruwa "
nan Zarah ta fad'a mata abunda ke faruwa Mikewa asmy tayi tare da dura ashar ta ce "Wlh iskancin Matar nan yayi yawa bari zan gwada mata ni y'ar zamani ce “
" ta fad'a tana niyyar fita kamota Zarah tayi cikin Sauri ta ce 'ki Rufamun asiri sis Dan Allah karkije ki k'ara jamun ni komai tayimun na barta da Allah .
dak'yal Zarah ta samu Asmy ta hakura Kama hannunta tayi ta ce "Taho muje gida ki karya " tare suka fito " Mama Rabi ta bisu da harara da tsaki suna isa gidan su asmy nan Zarah ta karya Dan tare suka shiga kitchen suka dafa indomie Bayan sun karya gadon d'akin asmy suka kwanta Dan su huta daman Zarah da gajiyar jiya bata saketa ba Aiko kafin kace me bacci yayi awon gaba da ita itace bata tashi ba sai wajen Azahar
tana tashi tayi wanka ta sanya kayanta a gidan Anko sukayi da asma u da Yamma Mama ta aikesu gidan babbar yayar Asmy dake Aure wata unguwar Gyara fuskarta Zarah tayi tare da shafa hoda Wanda Asmy ce ta sanyata shafawa Bayan ta sanya doguwar Hijab d'inta mai hannu tana shirin daura nikab asma u ta rik'e tana Dariya ta ce "Haba Kinga yanda kikayi kyau kuwa please muje a haka Dan Allah "
tana murmushi ta ce "Allahko Besty" Eh mana ai nikab bakoda yaushe ake sanya shiba itama kalar hijab din ta Zarah ta sanya Bayan sun fito Mama ta basu kudin napep tare da cewa kar kuyi dare to suka fad'a tare da fita basu jima ba Suka samu napep koda suka isa gidan Hauwa'u daman sun saba zuwa tare sai nan nan take da Zarah kamar ma itace kanwartata Zarah ko sai wasa take yiwa k'aramun d'anta ganin magriba tana gabatowa ya sanya su mata bankwana Suka fito
d'ari biyu ta basu waigawa sukayi unguwar suka ga ba Alamun Abun hawa Tafiya suka fara Kad'an kad'an parking d'in mota sukaji daga bayansu hakan baisa sun juya ba saima cigaba da Tafiyarsu da suke Zarah ta ce
"Wannan tafiyar da mukayi ai daman karasawa mukayi a k'asa munkusa fa Rabi" Wlhko ai inbanda magriba da kawai a k'asar muka tafi muka ma sai awara da kud'in napep din wlh "cewar Asmy " Assalamu alaikum warahmatillahi ta ala wa bara katuhu “
"Suka tsinkayi Muryar wani saurayi daga bayansu " Zare idanu sukayi tare da Kallon juna ta wutsiyar ido Asmy ce tayi k'arfin halin amsa masa sallamar yayinda Zarah ta k'ara yiwa saurinta mai "matashin saurayin ne ya ce " Dan Allah y'an mata idan ba damuwa minti biyu zaku bani muyi y'ar magana
"Asmy ce kamar zata tsaya Zarah ta juyo tare da banka mata harara cikin siririyar muryarta ta ce Kiyi Sauri mana mu tafi munyi masa kama da matan da za a Tara a titi ta fad'a tana turo baki" Tare da tsaida napep da sukaga zata wuce "maza tayi ta shiga Asmy ko girgiza kai tayi tare da Kallon matashin saurayin ta ce " Kayi hakuri Malam ba mutunci bane tsare mace a titi shiyasa “
"tana gama fad'ar haka itama ta shiga cikin napep d'in Cizon yatsa Hafiz yayi zazzak'ar muryarta na dawo mashi har tsakiyar kansa kyakyawar fuskarta ce ta shiga yi masa gizau rumtse idonsa yayi da karfi tare da bud'ewa ganin napep d'insu na shirin yi mashi nisa ya sanyashi saurin komawa mota ya tada tare da binsu Dan shifa ya ga Matar Aure.
Koda suka isa gida Ana gama Sallar magriba Suna isa salla sukayi Bayan sunbawa mama sak'on da itama ta bayar a kawo mata ana isha'i nan sukayi sallah Wutar da aka maido ne ya sanya Asmy saurin Mikewa tana murna ta ce " alhmdllh daman yanzu ake tsaka da series din da nake kallo a zeywood “
Ta fad'a ta na kunna kallo Zarah ko na kwance a doguwar kujera nan Asmy ta zauna tana cigaba da Kallon Indian series din da ake hankalinta duk ya na wajen Zarah da ba kallo take ba Ganin yanda Asmy ta maida hankalinta a wajen ya sanyata Fara kallo Sosai taga ana zuba romance love a film d'in Tuni taji wani irin feeling ya bijiromata tun daga tsakiyar kanta Rumtse idonta tayi sosai tare da matse cinyoyinta lokaci guda mararta ta fara mata wani irin murdawa
Cikin karfin hali ta na murya dak'yal ta ce "Sis ki kashe Dan Allah ki kashe" ta fad'a ta na rumtse ido"Cikin Sauri Asmy ta kashe shataf ta mance da yanayin kawar tata da bata kunna ba cikin Sauri ta je Wajenta tare da kama hannunta ta ce’
"Sorry sis Na manta larurarki ne kuma banzata zaki kallaba shysa " murda kawai Zarah take cikinta na mata wani irin murdawa "tuni ta fara shafta uwar zufa cikin kid'imewa Asmy ta mik'e Dan bata mance irin bak'ar wahalar da tasha ba kwanaki Wanda har saida akaje Asibiti shawarar da doctor ya basu ta fad'o mata a rai cikin Sauri ta mik'e tare da...........✍🏿
*Domin magana da marubuciyar sharhi tambaya ko kuma Karin bayani 07026166536*
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
*_Miss Hajo ce_* 🤙🏿
[8/22, 13:59] ❤️❤️❤️: 💑 *AUREN WATA TARA* 👨❤️👨
MALLAKAR
*Hajara L Sadeq*
*TEAM GAWURTATTU BIYAR*💃
🅿️.........*7 & 8*
Tare da rugawa Dakinsu maganin baccin da Dr ya basu akan idan ta fara haka a bata zai iya taimaka mata ta maza ta fito tare da bude kwalbar maganin Tado kanta Kad'an tayi tare da sanya mata kwalbar maganin a baki
Saida Tasha kusan rabi tukwana Asmy ta janye Ba ayi minti goma ba wahalallen bacci ya kwashe Zarah Ajiyar zuciya Asmy ta sauke tare da zaunawa gefen kawartata .
Mama ce ta shigo kallonta ta yi ta ce "Lafiya asmy naga Zarah kwance kamar bata lafiya " kasa da kanta Asmy tayi ta ce "Eh Mama bacci ta ke " Okay ta fad'a tare da komawa kitchen Dan ta dagosu tunda taga kwalbar maganin bacci hannun Asmy .
zarah ita ce "bata tashi ba sai wajen la asr ta na tashi taji sauk'i.
Haka rayuwar Zarah taci gaba da wakana da dadi ba dadi danma yanzu ta samu sassauci tunda Baba yayima Mama Rabi wannan Abun bata Kara yunkurin dukan ta ba.
sannan daman su habiba ba wani harkansu take shiga ba Dan magana ma saita kama take had'asu gwarama khairat itace Dan Safiya ma dukda yarinyartarta ta fara kwatsawa dasu Habiba shekararta 13 amma rannan ta hangota suna tafiya da wani wai Saurayi har yana rik'e hannunta.
irin dabi'ar yaran gidan nasu Sosai take mata ciwo dan ma Baba yana bakin kokarinshi Amfi karfinshine saboda yanayin aikin da yake ba na zama bane.
Neco d'in su Zarah ta fito masha Allah ta samu 9 credit ranar zokuga irin farincikin da ta shiga ita da kawarta sai tsallen murna suke Suna cikin murna gidan su Asmy aka Aiko wani yaro aka ce Ana kiran " Zarah
"jekace bana nan " Zarah ta fad'a tana yamutsa fuska mamansu Asmy ce ta ce "je kace gata nan" Kallon Zarah tayi ta ce "y'ata jekiga waye ne Ai ba a haka "
",to Mama ta fad'a tare da mik'ewa ta sanya hijab d'inta har k'asa ta fito Rungume da hannayenshi ta sameshi A jikin motarshi kirar corolla L E sanye yake cikin shadda ash Bak'ine amma coculate colour bashi da muni haka bazaka kirashi da kyakyawaba.
" k'arasawa wajen Zarah tayi tana jin d'ari_d 'ari Hafiz ko tunda ta fito ya kafeta da idanu ya na k'ara yabawa da zubi da kyan sura uwa uba kyau irin na Zarah dan tunda ya ganta a wajen safka ya kwallafa rai a kanta.
Dan lokacin da suka haduma arashi akayi yaje unguwar wajen wani abokinshi Hakan yasa ya bi mai napep din Har ya gano gidansu Zarah Inda ya nemu information a kanta kuma ya samu bayanin komai a kanta.
tundaga tarihinta da irin wahalar da take sha sosai ya tausaya mata hakan ya k'ara sawa yaji soyayyarta a ranshi.
"Da fara'arshi yayi mata sallama tare da cewa "fatan na sameki lafiya sarauniyar mata "
Batasan lokacin da murmushi yazo mata ba ta ce "wa'alaikumussalam yaushe na samu wannan mukami haka Ba nad'i ba komai a nadani har sarauniyar mata anma bansaniba wannan mukamin ai sai manya ".
“ai kin fi ma a kiraki da sarauniyar mata saboda ked'in ta musamman ce a cikin mata"K'asa da kanta zarah tayi ta na wasa da zoben hannunta.
"Da farko dai su na na Hafiz ma'aruf Mahaifina tsohon Dan kasuwane kuma.manomi a wannan garin namu nine Third thild d'insa A yanzu na kammala Degree d'ina a Umyuk Inda yanzu ina shirin jonawa masters wannan shine takaitaccen tarihina"
"Tsaki Zarah taja a ranta ta ce " ji shegen surutu kowa ya tambayesa a fili kuwa cewa tayi"masha Allah Nice to meet uh".
gyaran murya Hafiz yayi ya ce "da farko dai tun ranar da na fara ganinki Naji kin tafi da imani na kuma ina sonki so na aure inason ki zama uwar y'ay'ana duba da tarbiyarki,hankalinki da nutsuwarki a Gaskiya Zarah ki godewa Allah a zamaninnan samun kamarki sai antona Allah yayi miki komai a rayuwa kina da kyau tarbiya ga kuma ilimin addini both side boko da arabi kafin nazo wajenki saida nasan wacece ke ina fatan za amshi tayin soyayya ta"
" uhm Zarah kawai tace tare da cewa"Gaskiya zan fad'a maka ka fara zuwa wajen mahaifi na ka nemu izini a wajensa Dan bai bani ikon kula kowaba har sai an nemu izininshi sannan nagode da soyayya"
"ta na gama fad'ar haka ta juya ta shiga gida Dan ta tsani namiji mai yawan surutu .
" Hafiz ko yaji dadi a ranshi tunda da kanta ta ce yabi ta iyayenta hakan ba k'aramar dama ce ta sameshi ba".
"Zarah na komawa gida Nan Tabawa Asmy labarin yanda sukayi ta na Jan tsaki " Dariya asmy tayi mata ta ce "Uhm nikan banga makusha a wajensa ba wlh daga gani yana da nutsuwa"
Harararta Zarah tayi ta ce "Ke wani ganin baki da hankali ma wlh Haba mutum sai shegen surutu ke nifa sanin kankine bansan surutu " .
Chab nikam zanso naga mijinki zarah kowa yazo saikince ga aibunshi Asa Nura ma wannan ba Mate d'inki bane amma hakafa kwanaki wani daga katsina yazo wajenki saida kika koreshi Kinga Zarah kiyiwa kanki fad'a ".
Kamar yanda ta fad'a masa da daddare yaje ya samu mahaifinta a waje Inda Yayi mashi bayanin abunda ke tafe dashi Malam yaji dadi sosai Dan dukda a dare ne baiga fuskarsa ba kasancewar duhu amma a kalaman yaron yasan yana da nutsuwa".
ce masa yayi ba damuwa zai iya fara zuwa Wajenta hakan sosai yayi wa Hafiz dad'i.
Washegari Baba saida ya sanya aka masa bincike akan Hafiz kuma aka tabbatar masa da yaro ne mai hankali da nutsuwa hakan yayiwa Baba dadi sosai .
Ranar da daddare ya samu Zarah a d'aki Inda ya shiga mata nasiha tare da cewa " Kinga Zarah yaron nan da alamu ya na da hankali kuma na bincika an bani kyakyawan zato a kansa zai dinga zuwa wajenki har Allah yasa ku daidaita kanku kinji"
Dagowa tayi kamar zatayi kuka ta ce "Bab." shit karkice komai Zarah kice "Allah ya zab'a miki alkhairi Dan ba abunda nake da burin gani a rayuwa da raina sama da aurenki na k'agu naga ranar da zan Aurar dake zarah kema ki huta da wahalar gidannan shi yasa kullum Addua ta da buri na naga ranar Auranki Allah ya baki miji na gari Wanda zai rikemunke da amana"
kasa da kanta Zarah tayi Bayan Baba ya fita daga d'akin saida tayi hawaye ita harga Allah Hafiz d'innan bai mata ba Amma yanda taga Baba yana yabonshi kuma ya nuna yanason alakanta dashi dole ta kula shi ko Dan son farincikin mahaifin nata.
Soyayyace da shakuwa ta fara shiga tsakanin Zarah da Hafiz Sosai yake nunawa Zarah soyayya da kulawa a nata bangarenma ta fara sabawa dashi saboda mutum ne mai barkwanci kullum yazo sai ya sanyata Dariya hakan yasa ta fara sabawa dashi Saidai duk wata sayayya ko kudi da zai bata bata tab'a amsa ba ba yanda baiyi da itaba amma bata amsar abun hannunshi.
ta bangaren Mama Rabi ko bakinciki take da Hafiz d'innan dake zuwa wajen Zarah ba irin Karfar da batayiwa Zarah a wajenshi ba Anma yace Eh yaji ya Gani yana sonta Dan kafin yazo wajen Zarah an bashi labarin Mama Rabi ko ita wacece da samarin da take korarwa Zarah.
Washegari Zarah ta tashi da ciwon Mara Wanda hakan ya tabbatar mata da perioud d'inta na kusa sosai hankalinta ya tashi Dan duk wata a darura takeyi saboda tsananin wahalar da take sha cikin Sauri ta sanya hijab d'inta tare da fitowa ta nufi gidan su Asmy
Dan bata mance irin sharrin da Mama Rabi take mata ba akan ciwon marar da take akwai lokacin da tace k'ilama cikine aka zubar mata ake mata rufe rufe hakan yasa ta maza ta zame tana zuwa gidansu Asmy Bayan ta gaishe da Mama a daddafe ta shiga d'akin Asmy Inda ta sameta ta na guga kwancewa tayi kan gadon ta na maida numfashi .
"Asmy ce ta ce " Lafiya Besty"Gyada mata kai Zarah tayi tana ida kwanciya kan gadon ta ce "Da sauki dai perioud d'ina ne zaizo wlh na farajin ciwon Mara" Cike da tausaya Asmy ta ce "wayyo my Zarah Allah dai ya yaye maki wannan larurar Dan larurace wlh ace duk wata sai ka sha bak'ar azaba hada su suma " .
bata Kara cewa komai ba Zarah saboda murdawar da cikinta ke mata ruwan zafi Asmy ta d'auko tare jika tsumma take Dan shafa mata a ciki sannan ta had'a mata tea mai zafi ta bata ta sha ciwon sai gaba yake Inda Zarah duk ta firirice ta fara fita hayyacinta kafin ka Ce me sai amai nan ta fara kwararashi Asmy dai Sannu kawai take mata Bayan ta gyara wajen mamansu Ce ta shigo ta ce.
"Lafiya Asma'u" cike da damuwa ta ce "Mama perioud din Zarah ne yazo" cike da kulawa Mama ta ce "wayyo Allah sauwake amshi ki maza ku tafi Asibiti ayi mata allurar ta fad'a tana mik'a mata d'ari biyar amsa tayi tare da kama Zarah dake murkashi .
mai napep ta fara tarowa tukwana ta zo ta kamata suka tafi asibitin da suka saba zuwa suna zuwa nurse din tayi mata allura daman ita ke mata duk wata ita kanta tana tausayawa irin wahalar da yarinyar takesha.
Sai wajen magriba Zarah ta samu kanta Taji ciwon ya lafa Asmy itake jinyarta kamar kowani lokaci harta gama perioud d'inta.
Yau ta na zaune tsakar gidansu ta na sintar gashinta aka Aiko akace ana kiranta " to ta amsa "
Mama Rabi na banka mata harara saida ta ida sintar tukwana ta mike tare da sanya Hijab ta fita .
" kamar yanda tayi tunani shi d'inne dai murmushi ya sakar mata Itama ta mayar masa da murmushin yak'e sun tab'a Hira sosai kasancewar yamma ce Sai wajen magriba da zai tafi kwalin waya kirar hot10 ya mik'o mata ya ce.
"tata ce saboda su dinga waya ko baya nan" nanfa Zarah ta ce bata San wannan zancen ba ba irin yanda baiyi da ita ba akan ta amsa amma takiya saboda bata da sha'awar abun hannun namiji kuma Baba ma yayi mata wannan kashedin