Showing 45001 words to 48000 words out of 153980 words

Chapter 16 - AUREN WATA TARA COMPLETE HAUSA NOVEL

30 Sep 2024

16338

had'a ta shiga saida ta gasa jikinta sosai kafin tayi wankan tsarki ta fito tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ganin idonshi lumshe kamar mai bacci ya sanyata saurin cire towl din tare da mayar da doguwar rigar jikintaba ta yafa beil din irin nad'in larabawa a dardumar da ta gani shinfid'e ta tayar da salla saida tayi magriba Har isha i ta na cikin nafilfilu bacci na wartarta tana Tasbihi a haka har baccci barawo ya saceta a kan sallayar duk abunda take MD akan idonsa saida yaga har bacci ya d'auketa kafin ya Mike toilet ya fad'a Bayan Shima yayi wankan ya fito ya shirya cikin shigar bacci Kallonta ya tsayayi yanda ta takure waje guda kamar bazai tab'ata ba sai kuma ya yunkura a hankali ya d'auketa tare da kwantar da ita kan gadon yayi mamakin yanda bata tashi ga Alamun ta na da nauyin bacci kwance yayi kan Doguwar kujera wani bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi Wanda ya jima baiyi irin sa ba........lokacin da ya tashi Tuni gari har ya fara Haske sosai yayi mamakin makara sallah da yayi duba Agogon bangon dake manne a d'akin yayi Yaga har 7:16am cikin Sauri ya Mike Tare da shiga toilet Ya dauro alwala Bayan ya gama salla kallonta yayi da har lokacin Bacci take Tsaki yaja tare da karasawa Inda take Da Hannu ya bubbugi kafarta tare da cewa "Keeeeee" Cikin gigin bacci Zarah ta tashi Dan ba k'aramar gajiya ya Tara mata ba dak'yal ta iya Mikewa da Addu'ar tashi daga bacci a bakinta tare da Yin wata irin mik'a gabak'i d'aya ta bankaro da kirjinta saurin kauda kai MD yayi Dan muddin yaci gaba da kallonta akwai matsala tsaki yaja a ranshi Dan daukarshi da gangan tayi itako bama tasan da wanzuwarshi wajenba Saida bacci ya saketa kafin ta Kalleshi Sai Kuma ta kauda kai tana jan tsaki MD yajita sarai ya nuna baiji ba saboda tsawon rayuwarsa Ba abunda ya tsana sama da ayi masa tsaki Toilet ta shiga Bayan tayi alwala tana gunguni ta fito najin haushin makara salla da tayi Bayan ta gama salla ta zauna tana lazumi tana idarwa ta mik'e taga harya fita zaunawa tayi tare da Yin tagumi Tana karewa d'akin kallo Hankalinta ne ya kawo mata su Asmy kila na chan suna nemanta ga wayarta silent take Jakarta ta hango Chan kasa cikin Sauri ta k'arasa tare da daukowa ta dawo ta zauna tana fito da wayarta wara idanu tayi ganin missed call d'in Asmy kusan sha biyar har wajen karfe ukku ana kira ga na Chuchu ma Yafi goma Banda na Hafiz Shima rututu gabanta ne ya bada daram To me ma zata ce Musu ina zatace ta kwana tsaki taja ta ce mugu azzalumi kawai ya satoni Dan zalinci tana juyi da wayarta kiran Hafiz ya shigo kamar bazata dauka ba saikuma ta d'auka cikin sanyin murya tana ji daga bangarensa ya sauke ajiyar zuciya Tare da cewa "My luv ina kika sanya wayar jiya nayi ta kira Baki d'auka kinsan kin sabarmun sai Naji muryarki nake iya Bacci "cikin sanyi ta ce " Sorry ya Hafiz nayi bacci ne da wuri jiyan ina kwana"Lafiya qalau my love fatan kin tashi lafiya "Alhmdllh yau baka da lectures safe ne " Yanzu nake shirin Tafiya Hankalina bai kwanta bane sai yanzu ya kwanta da Naji muryarki gimbiyar tawa "kasaitaccen murmushi ta saki Wanda ya lotsar da dimples d'inta " Daidai shigowar MD da leda a hannunsu kallo d'aya yayi mata yaga yanda take magana kasa kasa tana murmushi Ledar ya Aje tare da Yin hanyar fita kamar bashi yayi maganarba ya ce"Idan kin shirya kya iya fitowa "bai jira me zata ce ba ya fice katse wayar Zarah tayi Bayan sunyi bankwana taje ta daga Ledar daya shigo da ita latsetsiyar doguwar Riga ce mai.kyau da gyalenta sai brush da kuma take away din Indomie da kwai" tsaki taja tare da cewa "ko wa yace masa ina buk'atar Wasu kayan inbanda tsabar kinibibi har wata indomie ce a take away " ta fad'a tana kuma Jan wani tsakin Brush tafarayowa Bayan ta fito ta Dauki indomie d'in taci Dan yunwa take ji cikinta banda karan yunwa ba abunda yake Tana gamaci cikin minti baifi sha biyar ba tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar daya sayo mata ta ninke tata tare da sakawa cikin Ledar waccen wayarta da d'auka ta hand bag d'inta ta rataya Bayan ta yafa beil din rigar sosai rigar tayi mata kyau ko madubi bata tsaya duba ba ta fito Zaune ta tarar dashi Da kayan exercises jikinsa yana rik'e da remote hankalinshi na kan tv gefenshi taja tsaya ta hade rai kamar bata tab'a Dariya ba Shiru tayi batayi magana ba Ganin Shima bazai yi mata magana ba agogon dake manne a palourn ta duba taga 8:40 gashi 10 take da lectures ya sanyata cewa "ka budemun Na tafi ina da lectures " Baice mata uffan ba kusan 5 minutes hakan sosai ya k'ara Kular da Zarah Chan kuma taga ya Mike yayi Hanyar Bedroom dinsa ta na tsaye ta cika tayi Fam gajiya tayi da tsayuwar ta zauna ta sawa sarauta Allah ido tayi tagumi Ba ayi 10 minutes ba Taji fitowarshi Ta gefen ido ta Kalleshi taga ya shirya cikin wasu K'ananan kaya kauda kanta gefe tayi hanyar kofa taga yayi tare da cewa "follow me" Yayi ficewarsa tsaki taja ta ce "Aikin banza Sai wani shan k'amshi Da gadara da isa yake saikace ba shine jiya ya gama....saikuma ta rufe bakinta ta tashi cikin Sauri tabi bayansa Parking space Taga ya nufa Tana nan tsaye har yazo Inda take daidai Inda take Ya tsaya Tare da bude mata front sit ta ciki Ajiyar zuciya ta sauke Tare da shiga Suka d'auki Hanya cikinsu bamai cewa uffan " Ina ne Inda kiken"ta tsinkayi muryarsa "tana kauda kai ta ce " A B U"Daga haka ba Wanda ya k'ara cewa uffan har Suka isa Bud'ewa tayi ta fita tare da banka masa kofar da karfi kamar zata karye tayi gaba da Kallo ya bita Tare da Jan tsaki Ya ce "Stupid Matsala kawai"Allah ya sanyama tinted ne motar ba Wanda yasan shine ya juya yabar sch din.
Zarah ko tana fitowa daga motar taci.karo da Asmy da Chuchu Alamun sun fito daga lectures Bin motar da Kallo Chuchu tayi Itama Asmy haka Zarah ko gabanta saida ya fad'i ganin irin yanda Chuchu kebin motar da Kallo Har sukaga ficewar motar daga wajen da mamaki suke Kallon Zarah Chuchu ce tayi k'arfin halin cewa ..โœ๐Ÿฟ

07026166536

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐Ÿ‘ฏโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘Ž๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*


1, *MU GANI A ฦ˜ASA...*๐Ÿ”ฅ
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ฦ˜WAI..*๐Ÿฅš
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*๐Ÿ’ฅ
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐ŸŒŽ
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huษ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษ—aya N300

*DOMIN TURA KUฦŠIN KAI TSAYE*๐Ÿ‘‡

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya๐Ÿ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTN๐Ÿ‘‡

0814 179 9224

ฦณan ฦ˜asar Niger zasu tura nasu anan.๐Ÿ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huษ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษ—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐Ÿ”ฅ๐Ÿฅš๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŽ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ



_*Miss Hajo ce*_๐Ÿค™๐Ÿฟ
[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy: ๐Ÿ…ฟ๏ธ...........*35 & 36*


Sosai zuciyar Zarah ta karye Batasan lokacin da ta Rungume Asmy ba saikuma ta sanya kuka Itama Asmy hawaye take tare da cewa"kiyi hakuri ki yafeman Zarah"tsagaita kukanta Zarah tayi ta ce "ban kullaceki da komai ba Asmy komai ya wuce Saidai takaicin abunda ya faru yaki barin kwalwata" zaunawa sukayi Asmy ta Goge mata hawayen ta ce "Ki cire wannan tunanin a ranki Zarah Dan Allah ki d'auki hakan a neman lafiyarki ne komai ya faru kuma ai ba zina kikai ba a bisa Aure komai ya faru" murmushi mai ciwo Zarah tayi ta ce "Amma dai kinsan na rasa budurcina dame kike tunanin zanyi tak'ama dashi gidan Aure na Asmy wani tanadi zanjema mijina dashi Bayan budurcin da ko wace y'a mace mai mutunci ke San kaiwa gidan Aurenta na rasashi ga Wanda baisan Darajarshi ba" ta k'arasa fad'a ta na rufe baki sakamakon kukan da yazo mata"Rungumeta Asmy tayi ta ce "ki daina damuwa da wannan Zarah Zamuje ayi miki d'inki kafin lokacin bikin bazai tab'a fahimta ba sannan Allah zai rufa maki asiri tunda yasan da niyyar da hakan ta faru" da mamaki Zarah ke kallon Asmy ta ce "d'inki kuma Asmy kina ganin to ba matsala bazai fahimta ba" Ta na kama hannunta ta ce "E insha Allahu bazai fahimta ba bazaima tab'a fahimta ba saboda A budurwa zai sameki " Boyayyar Ajiyar zuciya Zarah ta sauke saitaji kashi Sittin na cikin Darin damuwarta ta ragu Itama Asmy Ajiyar zuciya ta sauke Zarah ce ta ce "To yanzu yaza ayi ku farke Auren nan Asmy please tunda Mai faruwa ta Riga ta faru kawai a farke " Karki damu zanyi waya da Jaber akan Baki amince da *Auren wata taran* da suke ikirarin an daura ba kawai su Aiko maki takardarki"Tsaki Zarah ta ja tana tunowa da bayanin da Dr yayi mata wai akan matarshi na karatu "Asmy ce ta kira Jaber Bayan sun gaisa tayi mashi bayani akan Suna buk'atar takardar Zarah " Da mamaki jaber ya ce ,"Amma dai kinsan ba haka mukayi dake ba Wata Tara mukayi daku please Asma'u kar a dinga maida hannun agogo baya tunda Kinga Duka abunnan taimakon juna ne akayi tunda shi ya taimaketa ya biya mata bukatarta Karku kasance masu San kanku mana Kenan shikenan ku bukatarku ta biya shi ko oho ko"Sosai ran Asmy ya b'aci.cikin tsananin b'acin rai Ta ce "to yi mana Gori jaber sannan bazamu yarda da wani *Auren wata Tara* ba dole ne zai saketa komai zakuce Saidai kuce a lokacin ma tashin hankali ne ya sanya har na Amince muku Dan haka wlh dole ya saketa " Daga bangaren jaber Shima cikin b'acin ran ya ce "Daman ance d'an adaman butulu tunda munbiya muku bukatarku y'ar uwarki ta fita daga halin mutuwa ko rayuwa dole ki fad'i haka" Zarah ce ta Goge hawayen dake zubo mata Dan tanajin komai amsar wayar tayi tare da cewa"Allah ya kaimu wata Taran da rai da lfy "Sannan ta katse kiran kallon Asmy tayi dake huci ta ce " ki rabu da su sis yana da Gaskiya tunda kin Riga kunyi yarjejeniya Kinga harya farayi mana gorin sun biya mana buk'ata ki rabu dasu Allah ya kaimu wata taran"Sosai Asmy tayi sanyi ta ce "Amma dai Zarah ai basubi ba ta yanda zamu amince ba farawa da iyawa Anfara da kwanciya gadon asibiti na tabbatar da karfi yabi dake please ki barni dasu daidai nake dasu" A ranta Zarah ta ce "Inma kasheni yayi aike kika jamun tunda da baku had'a baki kin turani d'akin ai da haka bata faru ba a fili kuma cewa tayi " kawai kibar maganar ta wuce ki barsu wata taran,"Asmy ce ta ce "To shikenan sadakinki fa 500k na account d'ina na tura miki ko?cike da takaici Zarah ta ce " kibarsu a account d'in naki sakin hirar sukayi Dan Zarah bata ma son yawan firar...."Daga ranar Asmy da Zarah suka shirya kamar basu tab'a samun sabani ba Chuchu ma taji dad'in shiryawar tasu dukda batasan dalilin da ya had'asu fad'a ba....yau perioud din Zarah yazo Wanda sosai tayi mamakin neman ciwon mararta da tayi ta rasa sai Kad'an Kad'an da takeji Asmy ma sosai taji dad'in hakan Zarah ko sai yanzu ta k'ara gaskatar da maganar Dr d'in da duk daukarta Had'in baki ne kawai kwance tayi Kamar mai bacci nanko tunani ne kawai ta ke saitaji damuwarta duk ta ragu Cikin kwana Ukku Ta gama perioud dinta hankali kwance ita kanta hankalinta ya kwanta Asmy ma sosai hankalinta ya kwanta Dan tsoranta Allah tsoranta ace Ciki ya shiga Dan tasan sau d'aya ma.ana iya d'aukar ciki itakam Zarah Daman ko Kad'an bata kawo wannan tunanin a ranta ba ta cigaba da harkokinta tayikamar komai bai faru ba nan ko abun yana nan k'asar zuciyarta...

MD na Kwance around 9:50pm yaji kiran jaber kamar bazai d'auka ba sai kuma ya d'auka daga bangaren jaber ya ce "Bloody bansanka Da Rashin tausayi ba a sanin da nayi maka Kayiwa yarinya irin wannan Abun Dan Rashin tausayi Ka tsallakema kabar k'asar kaje Chan kaci gaba da rayuwarka ita ko oho ko wani hali ma ta shiga kenan ko,to yanzu ka na neman ka bata mana shirin da mukayi Dan wlh daga wannan Karin kuma bazan k'ara sa baki na a case dinka ba Inma y'ar kauye Hajiya zata aura maka Saidai ta aura maka wlh ga babbar dama ta sameka kana wasa da ita ya rage naka sauran sannan harsun fara zancen ka sake ta dak'yal na samu na lallaba dukda bansan sun hakura ba ko oho"tsaki MD yaja cikin d'aga murya ya ce " To saime Jaber Mtwsss a saketa din mana kowa ya kama gabanshi Dan ni hankalina ba wani kwanciya yayi da wannan Auren ba"Da mamaki jaber ya ce "Oh haka kace kenan okay yayi kyau ina jiran sakin Alhmdll daman haka nakesonji kowa ya kama gabanshi kuma na fitar da hannu na Daga Lamarin nan daga yau" ya na Gama fad'ar haka ya katse kiran"MD ko tunani ne ya shigayi"Tabbas gaskiyar jaber ne wannan dama ce ta k'arshe idan baiyi abunda ya kamata ba yanaji yana gani Hajiya kaka zatayi abunda taga dama a kanshi"To yanzu yaza ayi Bayan yarinyar yasan fushi take dashi"Tsaki yaja mood d'insu na ranar ya shiga dawo masa lokaci guda kuma yaji wani fitinannen feeling na taso masa harga Allah bai isa yayi karyaba a mu'amularshi da yarinyar yasan meye gamsuwa rumtse idonsa kawai Yake Kallon Amera yayi dake gefenshi tana bacci Tare da rungumota ko Dan ya rage zafi cikin bacci Amera taji irin abunda MD keyi mata cikin Masifa ta ce "Wai meye haka honey bacci fa nake meye haka Kasan dai a gajiye nake tunda na kwanta tun 10pm " MD da a matuk'ar bukace yake kwantar da murya yayi yana kissing d'inta ya ce "Please my merah help me I need you ki bari Kad'an zanyi" ya fad'a cikin Wata irin kasalalliyar murya Amera ko Mikewa tayi tare da cewa "nidai wlh na gaji Haba Ayi mutum bashi da aiki sai Abu d'aya wannan jarabar dame tayi kama.shekara Tara ai yaci ace yanzu ka fara hakura da abunnan kai dama baka gajiya" ta fad'a cike da Rashin kunya"MD ko ranshi ne ya b'aci sosai Cikin fad'a ya ce "Get out Ki fitarmun daga daki Kuma ki rubuta ki Aje daga rana irin ta yau Bazan k'ara neman wani Abu wajenki ba zakisan ni in d'ane ki jika jikin naki kisha me nake moruwa da jikin naki daman stupid kawai marar Ilimi ko aikin Ubanme kikayi da zakice kin gaji in banda yawan birthday da dinner da yawo gidan kawaye da bama musulmai ba ubanme kika iya ibadarma yinta kike yanda ya kamata "kuka Amera ta fashe dashi Tare da cewa " Ni kake cewa haka yau MD Daman nasan zuga ka ake kwanannan kakemun Rashin mutunci to duk ubanda ke zuga ka dinma zanganshi sannan jiki ai nawa ne kuma nace banaso daman ance d'an Adam butulu shekara Tara kana moruwa dole ka fad'i haka idan bani ba wace mace ce Zata zauna dakai a irin wannan yanayin naka kullum Abu d'aya ba sassautawa in banda ina da kwarin arziki ta tuni ban rarakeba To wlh bazan iya ba Ai bani kadai bace mace a duniya"ta k'arasa fad'a ta na Jan tsaki"Idan ran MD yayi dubu ya b'aci baisan lokacin da ya wanke ta da Mari ba tare da nuna ta da yatsa ya ce "Ni kike fad'awa haka Amera Dan baki da Ilimi mijinki na Aure na sunna Aiko zakisan na haihu zakisan ni d'ane sannan zakisan ba ke kad'ai bace mace a duniya " Sosai Amera ta tsorata da mijin nata abar kaunarta Tsawa ya k'ara daka mata ba shiri ta bar d'akin hada tuntube MD ko ranshi ne yayi mugun b'aci ranar bacci sai barawo yana dawowa daga Sallar asuba Bayan yayi wanka Ya shirya tare d'aukar password d'inshi ya bar gidan Gaba d'aya baima waiwayo Amera ba Dan ta gama bata masa rai Kai tsaye Aiport ya nufa.

zaune take Gaban Lecturer d'insu Bayan kiranta da yasa akayi tunda Ta shigo tayi k'asa da kanta ta na wasa da y'an yatsun hannunta shiko wani irin kallo yake binta dashi Na kurulla har wani Had'iye yau Yake "ya ce " Zarah Yusuf ko"?eh"ta fad'a gabanta na fad'uwa Dan kar ace wani abun tayi "Murmushi Sulaiman yayi ya ce "Ki saki jiki mana sai d'ari_d'ari Kike Ni ba mutum bane mai tsanani ina da saukin kai daman Kiranki ne nayi Dan na fad'a maki sirrin dake zuciya ta a Gaskiya Zarah tun sanda kika shigo makarantar nan Naji kin kwantamun arai nake sonki soyayya ta Aure bata yaudara ba Tun kina aji daya naso Na fad'a maki amma kwarjinin da kikemun yasanya na kasa Sai yau Allah yayi na fallasar da sirrin zuciya ta fatan za'a amshi tayina hannu bibbiyu" sosai Zarah tayi mamakin jin maganar da ta fito daga bakinshi da mamaki take binshi da Kallo tama rasa abun cewa sai k'asa da kanta da tayi gabanta na fad'uwa Suleman ya ce "Yadai kinyi shiru Zarah ko baki amshi tayin da nayi maki bane" Batasan lokacin da ta furta Kalmar "zanyi tunani tukun" ta na gama fad'ar haka tabar office d'in gabanta na fad'uwa "kawayenta ne hibba Da Jamcy da suka rakota suna ganinta sukayi kanta hibba ta ce " Lafiya me ya ce maki naga kin fito a rikice kinsan mutumin nan ba mutuncin kirki ya isheshi ba"Ajiyar zuciya Zarah ta sauke tare da cewa "Kudai kawai muje wlh abun yaban mamaki wai mutumin nan zaice ya na sona" wara idanu sukayi a tare suka ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login