Showing 117001 words to 120000 words out of 153980 words

Chapter 40 - AUREN WATA TARA COMPLETE HAUSA NOVEL

30 Sep 2024

16343

" Saura kakirasa ka fad'a masa munyi haka tunda kunsaba munafurci tare "Kasa yayi Jabir da kansa yana muzurai saurin barin palourn Ammy tayi Chuchu dake tsaye duk tayi shock kafafuntama ji tayi sun kasa daukarta sosai Abun yazo mata yanda bata tab'a tunani ba wai Yayanta ne Mijin zahra kuma shine uban cikinta Shine sukayi *Auren wata tara* da ita idan ta tuna saitaji kamar almara Kallon screern din wayarta tayi ganin kiran da Asmy ke mata mema zata ce mata " Muryar Jabir ce ta dawo ita daga dogon tunanin data Lula ya ce "Chuchu please waya fad'awa Ammy zancen nan taya tasan wannan din" Turo baki gaba tayi Dan duk haushinshi takeji har yayan nata ta ce "Saika bi Ammyn ka tambayeta" tana gama fad'ar haka ta juya "Mikewa Jabir yayi zuciyarshi chunkushe da tunannika ta wani bangaren kuma yaji dadin da Ammyn sukasan da maganar ko ya fita daga sarkarkiyar d'aya shiga tsaka Baiyi yunkurin kiran MD ba Koda wasa Dan yasan yana fad'a masa guduwa zaiyi da ita koma subar k'asar Wanda bazaiso hakan ba Tunda asiri ya tonu gwara kawai ta fanjama " Ammy sosai ranta ya b'aci Hijab kawai ta sanya da takalmi ta fito Chuchu ta biyota ta ce "Ammy ina zaki kuma Yamma tayi fa" daga mata hannu tayi ta ce "Ki koma yanzu zandawo zanje na taho da yarinyar nan tun yanzu kafin abokin munafurcin nasa ya kirasa " Ajiyar zuciya Chuchu ta sauke Ammy na fita ta kwalawa driver kira Ta ce ya kaita Abuja cikin Sauri "Ba bata lokaci motarsu ta dauki hanyar Abuja ana gab da magriba Suka isa Kai tsaye buzu quarters suka nufa......MD na zaune a Palour ya na dafe da kansa Saboda yau ba k'aramun kuka zahra tayi masa ba akan ya maida ita gidan iyayenta ga Allah ya isa da ta dinga ja masa yau ko.abincin kin ci tayi duk ta chaza masa kai yajiyo knking Kamar bazai Mike ba saikuma yaje ya bud'e gabansane ya bada daram cin karo da Ammy tsaye fuska ba wasa lokaci guda Alamun Rashin Gaskiya suka bayyana k'arara a fuskarsa a rarrabe ya ce " Am my "ka bani hanya na wuce " Ammy ta fad'a a tsawace 'sosai yayi mamakin abunda baitab'a gani daga Ammyn nasa ba Hankalinsa sosai ya tashi waigawa yake Kar zahra ta fito Ammy ta ganta asirinsa ya tunu"tsawar da Ammy ta daka masa ce ta sanyashi matsawa ba shiri daidai sanda zahra ta fito daga daki cikin doguwar Hijab Fuskarta jab'e jab'e da hawaye Tsaye Ammy tana kallonsa tana kallon zahra sosai zahra tayi mamakin Ganin Ammy a gidan Gabanta banda fad'uwa ba abunda Yake Sosai ran Ammy ya k'ara b'aci tunkarar wajen zahra Ammy tayi tare da kama hannunta tajata itadai zahra binta kawai take har suka isa Inda motar take ammy ta ce "shiga " ba musu zahra ta shiga motar Kallon Ammy MD d'aya biyosu yayi cikin tashin hankali ya ce "Ammy" Daga masa hannu tayi cikin Tsawa ta ce ..............โœ


*Domin magana da marubuciyar 07026166536*



*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐Ÿ‘ฏโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘Ž๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*


1, *MU GANI A ฦ˜ASA...*๐Ÿ”ฅ
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ฦ˜WAI..*๐Ÿฅš
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*๐Ÿ’ฅ
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐ŸŒŽ
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huษ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษ—aya N300

*DOMIN TURA KUฦŠIN KAI TSAYE*๐Ÿ‘‡

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya๐Ÿ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTN๐Ÿ‘‡

0814 179 9224

ฦณan ฦ˜asar Niger zasu tura nasu anan.๐Ÿ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huษ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษ—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐Ÿ”ฅ๐Ÿฅš๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŽ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ


_*Miss Hajo ce*_๐Ÿค™
[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy: ๐Ÿ…ฟ๏ธ.......*81 & 82*



"karka Cemun komai baka da bakin da zaka fad'amun wata magana "Sannan ta kalli driver tace jamu" Bayan Inda Zahra take Ammy ta zaga ta shiga "Motarsu ta tashi sosai zahra tayi mamakin Ganin Ammyn Chuchu me ya kawota gidan meye alakarta da Musty" Ganin ba amsa ya sanyata hade kai da gwuiwa tana hawaye "A sanyaye Ammy ta ce " Kidaina kukan nan kar kanki yayi ciwo"Duk yanda zahra taso shiru kasawa tayi Ammy na ganin haka ta janyota jikinta tare da Fara Lallashinta ta ce "Kiyi hakuri insha Allahu komai yazo karshe " Shiru zahra tayi tunani chunkushe a kwalwarta kafin bacci ya kwasheta a jikin Ammy tayi baccinta kallonta kawai Ammy take tana jin tausayinta na ratsa ta yarinyar abar tausaya wa ce Kamar yanda Chuchu ta bata labari ga maraici ga kuma halin da MD ya jefata Har mahaifinta ya shiga wani hali banda zargin mutane Har suka isa gida zahra batasani ba saida Ammy ta tasheta ta ce "Tashi Daughter munzo" a sanyaye zahra ta fito daga motar sosai tayi mamakin Ganin saukarsu gidan su Chuchu dan bazata mance gidan ba kama hannunta Ammy tayi a hankali take binta saboda cikinta da taga yayi girma har suka isa Babban palourn ita dai zahra na biye da ita Suna shiga palourn zahra tayi ido hud'u da chuhu Da gudu chuhcu ta Ruga tare da Rungumeta Da karfi saikuma ta sanya kuka Ammy ce ta ce "Ki bita a hankali Maryam bakiga yanda take " tsagaita kukan sukayi suka zauna Kan sopa Chuchu na dubar zahra dake hawaye Goge mata hawayen tayi ta ce "Kina.Lafiya sis?Gyada mata kai tayi har lokacin hawaye zahra take " Ajiyar zuciya Chuchu ta sauke ta ce "Kiyi hakuri momcy insha Allah komai yazo karshe Mikewa Chuchu sukayi tare da zahra Kallon Ammy da har lokacin ranta b'ace yake tayi ta ce " Ammy zamuje ciki"Okay tafada maki abunda take so a girka mata sannan ta huta sosai "To Ammy " Chuchu ta fad'a tana kama hannun zahra "Ki bita a hankali fa wajen hawa stairs " To Ammy Chuchu ta fada "koda suka isa d'akin Chuchu kasayin shiru zahra tayi Dan tun d'azu zuciyarta cike take da Tambayoyi Kallon Chuchu tayi ta ce " Sis Dan Allah na.tambayeki"Murmushi Chuchu tayi mata ta ce *bama saikin tambaya ba zanyi maki bayanin komai yanzu dai kiyi salla ki fad'a abunda kike so kici "numfashi zahra taja ta ce " Banason cin komai "wara idanu Chuchu tayi ta ce " taya zakice bakisoncin komai inke bakya so Unborn d'inmu yana so"Hararar wasa zahra tayi mata ita kunyar cikin nan ma take ta kauda kai Chuchu ta Kalleta ta sake cewa "please me kike son ci Dan Allah kinsan Na fad'awa Ammy Bazakici abinci ba fad'a zata maki " nafa koshi "ta bata amsa " okay bari naje na fad'awa ammy"Chuchu ta fad'a tana Mikewa saurin Rikota Zahra tayi ta ce "Ki bari mana karkije ki fada mata naji zanci koma meye " a a a ki fad'a a girka maki"girgiza mata kai tayi ta ce "Duk abunda kukayi zanci" Shikenan Chuchu ta fad'a ta ce "Bari naje na had'o maki ruwan wanka" gyada mata kai zahra tayi har lokacin mamaki take "Bayan Chuchu ta fito daga bathroom d'in Kallon zahra tayi ta ce " na hada kishiga kiyi bari naje na dawo"Okay "ta fad'a tana Mikewa a hankali Ta shiga toilet din sosai taji dad'in Wankan saboda ruwan dumin da Chuchu ta had'a mata Bayan ta gama ta d'aura towel a bakin gadon taga kaya marassa nauyi da Chuchu ta Aje mata d'auka tayi ta sanya tare da sanya Hijab tayi magrib da isha'i tana lazumi Chuchu ta shigo da plate din Farfesun naman rago d'ayan kuma lafiyayyan shinkafa da miya ce Samanta anyi yanke yanken kayan lambu da itama Tasha naman kaji a sama y'ar aikinsu da suka shigo Tare tazo gabanta ta Aje jug din dake d'auke da kunun Gyada da yasha madara cikin girmamawa ta ce " Ina yini Hajiya"Ina yini Zahra ta mayar mata Bayan barin mai aikin d'akin nan Chuchu ta tisata gaba saida ta kusa cinye naman shinkafarce ma ta kasa ci saboda kunun gyadar da ya cika mata cikin Dan sosai taji dad'inshi wajen 10 harsun kwanta ganin Chuchu bata da shirin mata wani bayani ya sanyata cewa "Baki fad'amun komai ba Chuchu" Shiru Chuchu tayi tanajin nauyin ta fad'awa zahra Yayanta ne yayi mata haka dak'yal ta iya tattaro jarumta ta ce "Tun ranar da yatafi dake Asmy tafadamun komai na *Auren wata taran* da kukayi wlh sis bantaba sanin yayana bane yayi miki haka sai dazu" mamaki cike da Cikin zahra ta ce "Kamarya Yayanki" Shiru Chuchu tayi kafin ta labartawa zahra komai d'aya faru har suka gane Yayanta shine ya aureta shiyasa har Ammy taje ta d'auketa sannan Chuchu ta Goge hawayen da suka zubo mata tana kama hannun zahra ta ce "Dan Allah sis kar dalilin wannan yayi sanadiyar shafar zumuncin mu nasan a halin yanzu ba Wanda Kika tsana sama da yaya na Dan Allah kiyi hakuri kar abunnan ya tab'a zumuncinmu" Sosai zahra tayi mamakin jin cewa Yayan Chuchu da take yawan musu zancenshi shine Mustaphan wannan shiru tayi mamaki duk ya gama cikata kenan d'an Ammy ne "Kinyi shiru sis bakice komai ba " Chuchu ta fad'a"Sai sannan zahra ta d'ago ta kalli Chuchu ta ce "Nayi mamaki ne sis Inajin bacci mu kwanta " Shiru Chuchu tayi duk tayi sanyi ganin yanda zahra tayi ta ce "Dan Allah sis kiyi hakuri ki daukeni tamkar y'ar uwa kar laifin yayana ya shafeni" Kirkirar murmushi Zahra tayi ta ce "Kibar maganar nan Chuchu babu abunda kikayimun mubar maganar kawai" Chuchu najin haka ga sauke ajiyar zuciya kwanciya zahra tayi kan makeken bed din Chuchu ta lumshe ido bacci take so ya d'auketa amma tunani ya hana....bangaren MD tashin hankalin daya shiga bana wasa bane cikin Sauri ya kira Jabir a waya bai samesa ba Innalillahi wa inna ilaihiraji'un kawai yake maimaitawa kafin yayi Sauri ya fito ya kwalawa driver dinsa kira kai tsaye Airport ya nufa ya wuce Kaduna koda isarsa gidansa dake nan din g r a ya nufa Yana son zuwa gidan Ammy amma baisan me zata masa ba saboda yasan tsananin fushi Ammy take dashi sosai yayi mamakin ya akayi Ammy tasan da maganar nan d'ayar number Jabir ya kira nan yaci sa. a ya d'auka baima jira komai ba ya ce "Kana ina Jabir ka maza kazo gidana dake gra ina kd akwai matsala babba" Daga bangaren jabir yasan daman da haka Koda Jabir yazo gidan Cikin tashin hankali MD ya ce "ya akayi Ammy tasan da maganar nan Jabir Bayan kasan dagani saikai sai Dr Aliyu sai ALLAH daga bangarena suka san da maganar nan taya akayi ta fita" Nan Jabir ya bawa MD labarin yanda sukayi da Ammy Shima yayi mamakin yanda sukasan maganar"Sosai MD ya shiga tsananin damuwa Daren ranar da idonsa bacci gagararsa yayi....washegari Around 9:am Ammy ta sanya Chuchu ta kira mata zahra tare suka isa palourn da Ammy take Wanda zahra kasa yarda ta had'a ido da Ammy tayi saboda wani irin nauyinta da take ji "A sanyaye kanta a k'asa ta ce " Ina kwana Ammy"Lafiya qalu takwara ya bakunta"Ammy tafada fuskarta d'auke da murmushi"alhmdllh "Zarah ta fad'a a hankali" shiru Ammy tayi kafin ta ce "D'ago ki kalleni zahra zamuyi magana" Sai sannan zahra ta iya d'agowa amma bata yarda sun had'a ido da Ammy ba tana wasa da yatsun hannunta ta ce "Tohm Ammy"saida Ammy taja numfashi kafin ta fara magana da cewa" Nasan Chuchu tayi maki bayanin komai Ba saina Kara maimaitawa ba ina mai baki hakuri akan dukkan abunda Babana yayi miki Dan banga laifinki ko Kad'an ba Kiyi Hakuri ki d'auki hakan a matsayi jarabawa ce kuma insha Allahu kinkusa cinyeta abunda nake so dake ki kwantar da hankalinki waje Daya ki nutsu kiyi hakuri Nasan anyi miki ba daidai ba ki daukeni tamkar mahaifiyar da ta haifeki karkiyi d'ari_d'ari dani ina son ki zauna a wajena ne Har ki haihu kafin muga yanda Allah zaiyi na bincika na samu labarin mahaifinki yanzu yaji sauk'i yana garin danginsa kiyi hakuri ki zauna damu har zuwa lokacin da zaki haihu saimuje tare ayiwa iyayenki bayani sannan a basu hakuri Sannan Abu na gaba da nakeson fad'a maki Ko babana yazo gidannan kar wani Abu ya k'ara hadaki dashi ko ganinsa kikayi kibar wajen kada wata alaka kota magana ta kara hadaki dashi karki sake ki sake masa fuska koda wasa kinji na fad'a maki " gyadawa Ammy kai tayi Alamun taji"Ajiyar zuciya Ammy ta sauke ta ce "Yawwa to Allah yayi miki albarka ya Rabaki da abunda ke cikinki lafiya " Shiru tayi Chuchu ta amsa da ameeen "ga Dr nan zaizo ya duba ki yanzu ki tabbatar kin karacin abinci sannan ta kalli Chuchu ta ce " ki kulamun da ita sosai Kuje Kuyi break fast an shirya muku a dining dake sama "Daman zahra so take Ammy tace Su tashi saboda jinta take kamar a k'aya tare sukayi break fast da Chuchu kafin Su fara hira sosai Chuchu ta dinga Jan zahra da Hira Wanda har saida ta samu da wartsake wayarta Chuchu ta jawo ta ce " Bari na kira Asmy nayi mata albishir"Lokacin da Chuchu ta kira Asmy tana kwance zazzabi ya rufeta daga bangaren Asmy ta ce "Tun jiya nake jiranki bakya d'auka nakagara Naji yanda kukayi dashi" murmushi Chuchu tayi ta ce"AI Albishir na kira na miki gama momcyn nan a kusa dani"Asmy batasan sanda ta mik'e ba ta ce "Da gaske ko wasa" Dariya Chuchu tayi ta ce "Ga kat ki gani" ta fad'a tana bawa zahra wayar murmushi tayi ta k'ara wayar a kunne a hankali ta ce "Hello sis" Ai Asmy batasan sanda ta buga ihu ba ta ce "wayyo Allah Alhmdll Alhmdllh Zahra kece kuwa" Murmushi zahra tayi ta ce "Karki batamun dodon kunne da Allah Malama " Dariya Asmy tayi ta ce "ba dole nayi murna ba karkiga yanda nayi kewarki Kina ina" chuchu ta mik'awa wayar Chuchu ta ce "tana gidannanmu" Gidanku kuma ina kika sameta "Dariya Chuchu tayi ta ce " akwai labari baya fad'uwa a waya"Aiko gani nan zuwa yanzu"duk daukarsu wasa take basu yarda ba da zatazo sai Bayan two hours data kira Chuchu ta ce "Na Iso kizo ki tafi dani security sun hanani shiga" Da mamaki Chuchu tace "waida da gaske kike gani nan" Tana fita suka shigo Tare da chuchu Asmy na ganin Zahra batasan lokacin da taje ta Rungumeta ba ta ce "I really miss you so much My Dear nayi kewarki over kafin kuma ta Goge hawayen da suka zubo mata ta ce " kina ina tsawon watannin nan zahra"Shiru zahra tayi mata saikuma ta sauya hirar da cewa "Yagida yasu Mama Ya jikin Baba" murmushi d'auke da fuskar Asmy ta ce "kowa lafiya qalau Baba yanaji sauki yana Batsari jiya ma su Mama sunje duba sa sunce ya warke sosai Dukda yana tambayarki " Goge hawayen da suka zubo mata zahra tayi sosai takeson ganin Baban Nata ko taji sanyi a ranta Sosai suka sha Hira da Asmy Sosai sukaji dad'in ganin juna dukda Zahra bata da wata sakewa sosai da fara'a fuskar asmy ta kalli cikin zahra ta ce"tubarakalla sis ji yanda cikinki yayi girma saikace yanzu ne lokacin haihuwar"Harararta Zahra tayi tare Jan tsaki ta kauda kai "Dariya Asmy tayi ta ce " Daga magana Sorrry Harna k'agara naga Unborn d'innan Na *Auren wata Tara* sosai zahra ta k'ara shakuwa tsaki taja tare da mik'ewa ta shige ciki Dariya Asmy tayi ta ce "Wlh Chuchu zahra duk ta sauya hali dukta zama wata jarababbiyar karfi da yaji" inaga fa Cikin nan ne ya sanyata haka"Uhm kuma hakane Allah dai sauketa lafiya "Ameen Chuchu ta fad'a Asmy ce ta ce " bakiban labarin yanda akayi kuka sameta ba "A sanyaye Chuchu ta labartawa Asmy cewar yayantane " Sosai Asmy tayi mamaki jin cewar da Yayan Chuchu akayi haka no wonder kamarsu da Ammy daman ta baci Dan tun sanda sukaga Ammy suka San tana tsananin kama dashi ta wani bangaren Asmy taji dad'i da abun yazo da sauki tasan Ammy mutuniyar kirki ce Zata kula da Zahra sannan zata fahimtar dasu Baba Ita yanzu chuchu Tsoranta bai wuce Zahra ta gane Yayanta shine MD d'innan data tsana tasan tsanarsa ninkuwa zatayi a ranta "Sai yamma Asmy tayi musu bankwana zata wuce bayan taje ta gaishe da ammy Inda Chuchu ta sanya driver ya kaita har gida sosai Asmy taji Kashi tamanin na damuwarta ya ragu zahra ko saitaji ba dadi da asmy ta tafi koda taje gida ta yanke shawarar fad'awa iyayenta Maganar Gaskiya dukda tasan zasuyi mata fad'a mamanta ta samu a tsorace ta labartawa mata komai " salati mamansu tayi ta salamce "sosai ta shiga yiwa Asmy fad'a kamar ta doketa ta ce " daman ashe kece kikayi silar shigar zahra wannan halin kece silar komai Dan Ubanki ita kuma ta biyeki to ai gashinan kinja mata "fad'a sosai maman su Asmy take Inda asmy ke bata hakuri daga karshe kuma ta godewa Allah da Cikin zahra ya kasance ta hanyar aure aka samesa ba hanyar banza ba dukda dai tasan mutane ba kowa zai fahimta ba har videon d'aurin Auren saida Asmy ta nuna mata Dan ta tabbatar.....Shiru MD yayi gaban Ammy yama rasa abunda zaice mata saboda tun gaisheta da yayi ta amsa a takaice bata Kara ce masa komai ba " Dak'yal yayi jarumtar cewa "Ammy Dan Allah kiyi hakuri" Me kayimun da zaka bani hakuri "Ammy ta fada'"Shiru ya sake kafin ya ce " Ammy nasan fushi kike dani Dan Allah kiyi hakuri Bazan iya jurar fushinki ba "murmushin da yafi kuka ciwo Ammy tayi ta ce " Ah ah ni ai baka tsoron fushi na ga Amira uwarka data haifeka ta kawoka duniya ita kake shakka kake tsoron fushin ta baniba "Omg MD ya fad'a ya ce " Ammy ba haka bane nasan ban kyauta ba ki tsaya nayi maki bayani"Daga masa hannu tayi ta ce "ba bayanin da zakayimun " duk yanda yaso Ammy ta sauraresa kin sauraransa tayi kullum.MD saiyayi zarya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login