Showing 114001 words to 117000 words out of 153980 words
tsinci kanki sannan ina son ki nemu yarda a wajen Allah ko Duka mutanen duniya basu yarda dake ba indai Allah ya yarda dake kingama samum komai a wajen Allah ake neman yarda ba d'an Adam baa sannan ba mutumin banza Allah yake jarabta ba ni kaina bada son raina nayi doguwar tafiyar nan Ba batare da na rayu dake ba kiyi hakuri da rayuwa kiyi hakuri da rayuwa y'ata ki sani ked'in Haske ce a cikin duhu Ked'in alkhairi ce a rayuwar duk wanda kika rayu dasu zahra ina matuk'ar alfahari da kasancewar ki y'a gareni ina matuk'ar kaunarki kedin yace ta gari " Rungumeta sosai tayi tana kuka ta ce "Mama Dan Allah karki sake tafiya ki barni" murmushi tayi tana Hawaye ta ce "taso nayi miki Albishir" tasowa tayi ta ce "Kalli Chan ta fad'a tana nuna mata wani waje" wajen zahra ta Kalla bata fahimci komai ba saboda wani haske daga gani guda biyu hannunsu rike da juna ta juya ta kalli maman tata ta ce "Mama Haske ne na gani" Murmushi ta kuma ta ce "Kinsan meye hasken can" a a a "" To hasken Chan kece Tare da abokin rayuwarki kudin haskene mai maganin duhu "Da mamaki ta ce " bangane ba Mama"Zaki gane nan gaba kawo hannunki"Mik'a mata hannun tayi "Wasu irin kwandalolin kudi ne taga ta fiddo sai Haske suke guda Ukku kamar zinare har wani Wal_Wal suke ta damk'a mata a hannunta Tare da rufewa ta ce " Ki bawa jikokina kowa d'aya idan sunzo kice ina gaishesu kuma ina sonsu sannan ta bata fuska ta ce "Bazanji dadi ba muddin kika asarar da alkhairi nan dake cikinki zahra ina son kiyi rayuwa Me kyau ki Tara zuri'a mai albarka da zakiyi alfahari da ita ko Bayan ranki sudinga maki addua y'ay'a da kike gani dukiya ce mai daraja Wacce ya kamata mu darajasu mu martaba su sannan inayi miki murna da samun abokin rayuwa na gari kuma Haske a cikin rayuwarki dama ta all'umma Zan Tafi Y'ata sai wata Rana " Cikin kuka Zahra ta ce "Dan Allah Mama karki k'ara tafiya ki dawo ina sonki ina tsananin bukatarki cikin rayuwata " Hawaye na zuba daga Idanun Matar ta na murmushi ta ce "Kalli Chan hasken chan dake rike da hannunki shine mamayina a wajenki zaibaki farinciki insha Allahu tamkar Wanda zan baki " zahra na kallar wajen ta kuma ganin hasken dazu kafin ta juya taga babu Matar babu alamar ta a wajen "Kara sosai ta fashe dashi cikin kuka ta ce " Mama Mama Mama "A matuk'ar firgice da gigicewa ta farka tana Kiran " Mama Mama Mama da karfi"A rude md ya farka yana kallon yanda ta firgice tana ihu tana Mama "Rik'eta MD yayi sosai tare da Fara tofa mata adduo'i a Amma bata fasa kuka ba Tana kiran Mama Wanda MD dukya shiga kogin tunani Har aka kira asuba yana tofa mata adduo'i karatun qur'ani ya shiga rera mata cikin zazzak'ar muryarsa A haka ya samu tana sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali ta fara dawowa hankalinta har tagama nutsuwa tana shirin barin jikinsa ya ce Ina kuma zaki" a sanyaye ta ce "Salla zanyi" Ajiyar zuciya ya sauke tare suka Mike Bayan tashiga toilet tayo alwala Shima sai sannan ya samu damar zuwa yayi shiya jasu salla suna gamawa zahra ta hade kai da gwuiwa ta shiga rera kuka sosai mafarkinma dayazo mata a abun al'ajabi ya tsaye mata a rai tsawon rayuwarta koda wasa bata tab'a mafarkin mahaifiyarta ba sai wannan Karin sosai tashiga kuka tana tunwoa da Abubuwan da suka faru a mafarkin gani take kamar gaske ji take kamar gaske ne gata ga mahaifiyarta ji tayi inama bata farka ba Sosai take kuka tanajin wata irin soyayyar mahaifiyarta na ratsa kowani sassa na jikinta MD lure yake da ita yasan kukan take kuma yasan irin yanda ta tashi Tabbas tayi wani mafarki ne ganin kukan nata yayi yawa ne ya sanyashi cewa"Me ya sanyaki firgita lokacin tashinki a bacci da kuma wannan kukan da kike ko kinyi wani mugun mafarkin ne"fuskartat jab'e jab'e da hawaye ta ce "Nayi mafarkin Mama na ne bantab'ayi ba Sai yau ina son na sake mata magana saita tafi" ta k'arasa fad'a cikin kuka sosai"Lokaci guda Jikin MD yayi sanyi a sanyaye ya ce"Bata raye ne?kanta sadde ta daga masa kai"Sosai MD yaji wani irin tausayinta ya kara tsarguwa a ransa Tabbas yasan Rashin uwa Babban gibi ne su kansu mahaifine suka rasa suna damuwa duk sanda suka tunashi bare ita data rasa Mahaifiya Sosai yakejin tausayin yarinyar na ratsa duk wani sassa na jikinsa "Shi mamaci har kullum Addua yake buk'ata ba kuka ba Addua da Sadaka itace kawai take buk'ata wajenki a halin yanzu shine Babban gatan da zaki mata tayi alfahari dake Na Haihuwarki da tayi kuma taji dad'in barin baya da tayi ki daina zubar mata da hawaye har kullum mamaci baya son kuka addua kawai yake bukata " Kasa tsaida kukan zahra tayi ta ce "wannan shine karo na farko dana tab'a ganinta Shima kuma a mafarki ba zahiri ba zanso kullum ta dinga zuwamun koda a mafarkin ne" ta k'arasa fad'a cikin kuka"Janyota jikinsa MD yayi ya fara Lallashinta a hankali ya ce"Kina nufin bakisan mahaifiyarki ba?Gyada masa kai tayi tana Hawaye "Ko baki da wayau ta mutu" muryarta na rawa ta ce "a haihuwa ta ta mutu wai" Allahsrk Allah ya jikanta yasa ta huta yasanya tana cikin Rahama ki daina mata kuka please Addua take buk'ata "Gyada masa kai tayi har lokacin hawaye take lokaci guda kuma Ta firgita tare da mik'ewa " ta wara hannunta ta ce "Ina Kudin da ta bani " ta fad'a tana dube dube Zanin gadon ta zazzaga amma bataga komai ba nanfa tahau sabon kuka ta ce "Dan Allah bakaga wasu kudade ba Masu kamar zinare A fa hannuna ta damk'a mun banyarda na sakesu ba kaga kuma yanzu babu su" Ganin Tana neman zaucewa ya sanya MD Zuwa Inda take ya zaunar da ita ya ce "Ki nutsu Mamy mafarki fa ba Gaskiya bane Dan Kinga Abu ko anbaki Abu a mafarki bashi ke nuna cewa zaki tashi kiga abunba a a wani mafarkin yana mana nuni ne da wani alkhairin ko kuma akasin haka Dan haka bazakiga abunda ta bakiba ki daukesa matsayin Alkhairi" Tana Goge hawayenta ta ce "Kuma fa cewa tayi na bawa jikokinta kowa d'aya guda Ukku ne ta bani Amma banga ko d'aya ba" Nazari MD ya fara Tabbas akwai isharar da mahaifiyar ta takeson yi mata a mafarkin nan amma Kuma dole ne ya samu ya nutsar da ita kar mafarkin ya gigitata yinin ranar haka dai zahra tayini sukuku MD shi yayi kokari wajen ganin ta cire mafarkin nan a ranta Tundaga ranar zahra bata Kara yunkurin Zubar da Cikin ba sannan duk lokacin data tuna da mafarkin da tayi saitayi hawaye sosai ta k'ara duk'ufa wajen yiwa mamanta Addua MD ko gidan marayu dake Abuja da yake tainakawa da kayan abinci yakai da niyyar Allah ya kaiwa mahaifiyar zahra ladar sosai tausayinta ya nunku a cikin zuciyarsa sanin cewar marainiyace da yayi kulawa ta musamman yake bata ita da abunda ke cikinta hankalinsa ya kwanta sosai Ganin bata Kara masa yunkurin Zubar da Cikin ba Bangaren zahra koda ta warware daga mafarkin nanfa ta k'ara tuburewa akan ta gaji da zaman gidan ya maida ita gaban iyayenta ta shirya yi musu bayanin koma meye MD ji yake bazai iya barinta ta tafi ba matukar ba haihuwa tayi ba Bangaren Ammy sosai ta shiga kogin tunani jin muryar mace da tayi a wayar MD Wanda ta tabbatar da ba Amira bace sosai hankalinta ya tashi karfa Dan nata ya halaka ya fara neman mata tunda tasan daman Chan hakuri yake da Amera sunan suna da Aure ne hankalin Ammy inyayi dubu ya tashi Tsoranta kar MD mace ya Aje a abujar ta d'auke masa hankali har baya zuwa kd Duka ina kd ina Abuja kullum adduarta akan Allah ya tsare mata d'an nata daga sharrin zina Bayan wata biyu Wanda cikin watanninan zahra kamar a k'aya tayisu dukda kulawar da MD ke bata duk kwana biyu likita yakan zuwa har gida ya duba ta saboda taki yarda suje asibitin a haka dai MD yana Daurewa yanzu cikin watansa Bakwai ba yan kwanaki amma zakuyi mamakin irin girman da yayi kamar yanzu ne.Lokacin haihuwar sosai zahra ta fara tsorata da irin nauyin da Cikin yayi mata da kuma irin motsin da takeji Bangaren Asmy kullum cikin fargaba da tashin hankali take na Rashin zahra wata Ukku sai yanzu taga Rashin kyautawarta na barin MD ya tafi da zahra da tayi a halin yanzu tanason fad'ar abunda ya faru Dan tagaji da boye boye amma tana tsoron halin da Baba zai shiga baigama warkewa ba Kuma yaji wannan sabon labarin na Auren zahra bada masaniyarsu ba Yau suna waya da Chuchu daga bangaren Chuchu ta ce"a Gaskiya Asmy baikamata mu zuba ido akan al'amarin nan ba sai daga baya nayi tunanin kwata_kwata kinyi hauka na barin mutumin nan d'aya tafi da zahra Bakisan mutum ba,bakisan garinsu ba ,bakisan sana'arsa ba wata kila d'an yankan Kaine ma ko d'an sayar da mutane Ki barshi ya tafi ita Wanda ke kanki bakisan Inda zai kaita ba haba asmy Haba ya kamata mu bincika al'amarin nan mu gano Inda y'ar uwarmuce take karta kuma shiga wani halin data shiga a baya "Asmy na hawaye ta ce " Wlh Chuchu duk banyi wannan tunanin ba sai yanzu da kika fada hankalina ya k'ara tashi innalillahi wa inna ilaihiraji'un wlh chuchu ki yarda kwalwata bata aiki yanda ya kamata wani gamin innayi Abu kamar mahaukaciya Bayan Babban kuskuren da muka tafka a baya yanzu ma na sake wani a Gaskiya banyiwa zahra adalci ba wlh Chuchu saboda banason ta shiga wani hali yakesanya nake aikata irin wannan abubuwan yanzu Dan Allah meye mafita ta ina zamu ganosu"Numfashi Chuchu taja ta ce "hanyar farko na wajenki ina shi abokin nasa da kuka had'a abun tare kuna waya dashi"? bama waya yayi bloack Dina tun lokacin da muka nemu saki"turkashi Chuchu ta fad'a kafin ta ce 'Kina da number sa to har yanzu"Cikin Sauri ta ce "Eh Eh" Ayawwa to yanzu kinsan yanda za ayi ke kika kirasa ganewa zaiyi zamu shirya masa plane idan yasan wata ai basu san wata ba turoman number tasa a message yanzu zanyi masa plane d'in dazan gano address dinsa Kinga daga nan munkamasa shi zai fad'a mana dole inda abokin nasa yakai zahra"cikin farinciki Asmy ta mik'e ta ce "Alhmdllh Gaskiya Chuchu kina da kwalwa me kyau wlh bantaba tunanin wannan ba bari namaza na turo maki" tana katsewa Chuchu taji shigowar message Number ta d'auka ta fara kwafewa a wayarta harta gama kwafa zaro idanu tayi ganin Fitowar number jaber baro b'aro a jiki kara sanyawa tayi taga again number tasa ce gabanta na fad'uwa ta kira Asmy ta ce "Sis inaga fa wrong number kika turo mun ki duba please" A a a banturo maki whrong ba daidaice wlh saboda copy dinta nayi na sender maki Kinga Ko ai daidaice kuma saida na duba sosai "Cikin tsananin firgice Asmy ta ce " ya sunansa"Jabir"Asmy ta bata amsa kai tsaye"jabir"Chuchu ta maimaita da karfi"Eh sis Jabir lafiya?Cikin Sauri ta ce "Ya sunan abokin nasa da ya auri zahra?Mustapha sunansa na mance sunan Baban nasa amma akwai a videon d'aurin Auren" Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Chuchu ta shiga nanatawa cikin zuciyarta kardai ace Yayanta ne ya auri zahra?danson tabbatarwa ta ce "Ki turoman da video din d'aurin Auren yanzunnan a what's app Dan Allah" Sosai Asmy tayi mamaki rudewar na Chuchu dukda a waya ne Ta ce "to bari na tura maki" Tuni zufa harta karyowa Chuchu What's apo tahau tashiga Asmy tayi ta jiran taji shigowar sako VA ayi minti biyu ba taga shigowar video hannunta har karkarwa yake tayi saurin budewa ta fara Duba d'aurin Auren Ga MD a zaune har zuwa Inda Liman ya daura Auren zahra yusuf da Mustapha dikkko" abun saiyazowa Chuchu tamkar almara Tabbas Yayanta ne Daman Yaya shine Wanda ya auri zahra kenan?Shine uban cikin dake jikinta,Shine ya gudu da ita kenan"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un ta shiga furtawa da karfi lokaci guda ta firgice batasan lokacin da kuka yaci karfinta na ta ce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un shikenan Dara taci gida Kamar wacce aka zabura haka ta mik'e tare da rugawa da gudu bata zarce ko ina ba sai d'akin Ammy Inda ta sameta kan prayer mat tana lazumi cikin kuka da rud'u Chuchu ta mik'awa Ammy wayar tace " Ammy amsa ki Kalla abun Al'ajabi da mamakin Dana gani Ammy "Lafiya Auta meye zangani karki dagamun hankali" Ammy ta fad'a"Ammy ki fara Kalla ki gani kafin nayi miki bayani "Hankalin Ammy dukba kwance ba haka ga amsa ta fara Kallon videon har takai karshe zuciyarta chunkushe kanta gaba daya ya kulle Da ganin wannan rikitaccen al'amarin Kallon Chuchu tayi hankali tashe ta ce " me hakan ke nufi Chuchu yaushe babana yayi Aure bamu sani ba "cikin kuka Chuchu ta kwashe labarin komai da Asmy ta fad'a mata da abunda ya faru gidansu zahra na zargin cikin da komai bata boye wa Ammy ba " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un kawai Ammy ke maimaitawa sosai Abun yazo mata tamkar saukar aradu a ka Jin abun take tamkar almara batasan lokacin data fara hawaye ba ta ce "Babana yabani mamaki bantaba tsammanin haka daga garesa ba dukda Aure ne amma baikamata suyi Aure ta wannan hanyar ba a Gaskiya ba a kyautawa Yarinyar nan ba kawarta da Babana da Jabir sun cuceta " Cikin kuka Chuchu ta ce"Ammy ita Asmy ba laifin ta bane Allah duk laifin su yaya ne Kinga su Suka tsoratata akan zata rasa ta shysa tayi haka"Goge hawayenta Ammy tayi ta ce "Hakane Maza kiramun Jabir kice duk Inda Yake inason ganinsa saiyayimun bayanin dalilinsu na na yin haka wlh zasu fuskanci b'acin raina da basu tab'a gani ba Dan iskanci idan aure yake so ba har lokaci Hajiya ta basa yayi ba Dan Raini da wulakanci Shine zaije yayi Aure a b'oye su wulakanta yarinya maza kiramunshi" Chuchu na laluben number Jabir harta samesa ta kira yana d'auka Ammy ta amshe wayar cikin fushin da baisanta dashi ba ta ce "Na baka nan da minti Talatin kome.kake ka sameni a gida" hankali tashe ya ce "Lafiya Ammy?Inkazo zakaji koma.meye minti Talatin na baka" tana gama fad'ar haka ta katse wayar tana huci minti Talatin bai cika ba Jabir ya iso gidan yakira Chuchu ya shaida mata yana palour baki daya suka fita palourn Wanda kallo d'aya zakayiwa Ammy kasan ranta a matuk'ar b'ace yake "har kasa Jabir ya gaisheta ya ce " Ammy Lafiya wannan kiran gaggawar"tana binsa da harara ta ce "ba lafiya ba munafukai watau daman da munafurci da kuka k'ulla k0 to asirinku ya tonu munji komai Abu d'aya nakeso ka fad'amun gaskiyar magana yanda take kuma wlh ka sake kamun karya zaku fuskanci Karin wulakancin da zan muku daga kai har babana fad'amun Gaskiya Had'in baki kukayi da Dr wajen Auren zahra sannan dalilinku nayin hakan wannan amsar biyu kawai nake buk'ata" Hankali tashe Jabir ya d'ago yana Kallon Ammy tuni harya fara zufa cikin muryar Rashin Gaskiya ya ce "Ammy wa ya fad'a maki maganar nan" ya fad'a a rarrabe "Ammy nabinsa da harara ta ce " a tunaninki bazamuji ba ko To asirinku ya tonu Daman ance rana d'aya ta barawo rana d'aya tame kaya ba bani amsar tambayar da nayi maka fak'ad"Ammy ta fad'a cikin d'aga murya"Innalillahi Jabir ya shiga nanatawa a ranshi Tabbas dole ne ya fad'awa ammy Gaskiya Dagowa yayi kallo d'aya zakayi masa kasan ba Gaskiya ya ce "Ammy zanyi miki bayanin komai Amma Dan Allah kiyi hakuri sannan karkiyi fushi" Inajinka oya ka fad'amun karka dinga b'atamun lokaci"numfashi yaja kafin ya labartawa Ammy komai d'aya faru bai boye mata komai ba saboda daman yasan da irin wannan ranar dukda yayi mamakin yanda akai Ammy tasan da maganar Salati Ammy tayi ta tafa hannu ta ce "Naga ta kaina ni Fatima daman a saboda Amera ne kuka aikata wannan Abun kunji kunya kun rako maza wlh Babana yaban mamaki bantaba tunanin zaiyi irin wannan Rashin imaninba Ya sanya yarinya a cikin wani hali kawai saboda shegiyar amera kayan bannza kawai a saboda banzar biyan bukatarku kuje ku auri yarinya ba sanin iyayenta Kuyi mata wayau ku tsoratasu kuga mugaye azzalumai wlh babana sai yayi nadamar abunnan d'aya aikata zaisan mu yayiwa haka zaisan zahra ba a banza take ba wlh tallahi saina kwatar mata hakkinta zan mance cewa ni na haifeshi na kwatawa zahra hakkinta tamkar Nina haifeta bana zalinci sannan bana goyon zalinci Kenan so kukayi ku cuceta ta haihu ku kaiwa waccen y'ar Iskar d'an da ita kanta tarbiya bata isheta ba bare harta tarbiyar da wani mu kuma ayi mana lullubi ko to ai dayake a cikin abun ba Allah gashinan asirinku ya tonu hada had'o karyar Amera ta samu ciki toni bansan wannan wani irin so da tsoro ne babana yake yiwa amerarnan ba Abu saikace an asircesa A baka damar kayi Aure kawai saboda gudun b'acin ranta kaje ka yi Aure a b'oye ka zalinci yarinyar mutane wlh Duka a cikin abunnan banga laifin Zahra da Kawarta ba ko Kad'an kune manyan mugayen da kuka tilastasu suka amince muku macuta mayaudara Tsaffin munafukai Ka tashi kaban wuri wlh saikunyi mamaki na Akan Lamarin nan daga kai har shi Babban munafikin sannan Ka fad'amun gidan da yake idan ka fita saika kirasa ka fad'a masa ga yanda mukayi kace ya gudu da ita kaga abunda zai faru"Jabir dukya tsure ya ce "Dan girman Allah Ammy kiyi hakuri wlh nikaina nayi Nadama tsaki Ammy taja tace" ai nadama baku fara ba ma ka fad'amun gidan da yake da ita " kasa yayi da kansa yace "buzu quarters "Mikewa Ammy tayi ta ce