Showing 135001 words to 138000 words out of 153980 words

Chapter 46 - AUREN WATA TARA COMPLETE HAUSA NOVEL

30 Sep 2024

16369

Wanda Duka huldar kasuwanci na Shi na sanya a ragamar abun kasancewar girma ya fara kamani shi kuma lokacin yana tashen yarinta duk wasu garuruwa da nake huld'a dasu shi yake zuwa ya wakilceni sosai na dorasa akan dukiya ta saboda yarda Wanda a ido ya nunamun yafi kowa kaunata tare da iyalina ina son mudan har cikin raina Wanda har sauran y'an uwana sukance Nafi kaunarsa akansu Nayiwa mudan duk wani gata na Gina masa Gida Tafkeke na saya masa mota sannan koda ya tashi neman Aure Nina tsaye masa Akan hidimar komai duk wani gata da Dan uwa ke yiwa Dan uwa nayiwa mudan da gangan nake sakar masa kofar dazai samu alheri ina sane saboda ina son Shima yazama wani Abu ko Bayan raina ya zama shine zai kula da iyalina da dukiya ta hakan yasa bana boye masa komai yasan duk wani sirrina yana kanena amma bani da abokin shawara sama dashi ashe bansaniba soyayyar ido mudan yakemun bansani ba ashe mudan Makasar rayuwata yake nema k'watsam wata rana da bazan tab'a mantawaba ranar bak'inciki,ranar da ta kasa goguwa a cikin tarihin rayuwata muna kwance tare da iyalina a lokacin Zahra'u ta zama budurwa Har anfara shirye_Shiryen Aurenta Dan mutane da dama bama jigawa kadaiba har sauran jahohi sukan fito su nuna.suna son zahra Saboda yarinyace mai matuk'ar nutsuwa da hankali Ga kyau uwa uba tarbiya Dan zahra bata tab'a b'atamun raiba ita da mahaifiyar ta mariganyiya Muna cikin bacci mukaji barayi sun duro mana sosai hankalinmu yayi tsananin tashi ba wacce muka tunano sai y'armu Duk mun rikice mun dunkule waje guda a haka mukaga Shigowar garda_gardan samari Wanda bazan iya cewa ga yawansu ba saboda tashin hankalin da muka shiga gabak'i d'ayansu suka zagayemu da bindiga gaba d'aya fuskokinsu a rufe Na tsakiyarsu ne ya bud'e fuskar Wanda saida na kusanyi sumar tsaye ganin Mudan ne tsaye da bindinga ya saitani dak'yal na iya D'aga baki cikin tashin hankali na ce "Mudan ,mudan" Kecewa yayi da wata mahaukaciyar Dariya ya ce "Kana mamakin gani na a nan ko to ka daina mamaki nidinnan da kake gani makashinka ne da hannuna zan kasheka yau na kashe iyalanka gabak'i d'aya zan mallaka gabak'i daga dukiyarka Tun Asali daman ni ba Kaunarka nake ba dukiyarka kawai nake So kuma Alhmdllh lokacin amsarta yayi saboda Nasan Duka gaba d'aya ilahirin adadin dukiyarka da kadarorinka ina son Ka daukomun duk wasu takkadun kadarorinka da baka bani ajiyarsu ba ka mik'omun da hannunka kafin na kasheka" sosai hankalina yayi tsananin tashi Dan uwana Ace akan dukiya zai iya kasheni nashiga tashin hankali da rudun da bantaba shiga ba ranar ina hawaye na ce "Mudan zan mallaka maka Duka dukiyar daka buk'ata amma ka sani Amana Bazata barka ba mudan ka mance cewar ni jininka ne ka zab'i da ka kasheni Akan dukiya daudar duniya Tabbas yau na yarda da cewar d'an Adam bashi da Tabbas" wata irin Tsawa ya dakamun ya ce "Bana buk'atar jin wani Wa'azi daga gareka ka bani abunda na fad'a" Suna tisamun bindiga aka naje na D'auko masa gabak'i d'aya takaddun kadarorina sannan nasa masa hannu a wasu takaddun da tashin hankali baisa na tuna takaddun menene Matata cikin tashin hankali da bak'inciki ta ce "Amma kaidai mudan anyi butulu mugu azzalumi macuci insha Allahu karshenka bazaiyi kyau ba saikayi mutuwar wulakanci makaskanci " Harbin da yayiwa Matata ne A kirji ya k'ara rud'ar dani da shigar dani cikin tashin hankali daidai lokacin da naga shigowar zahra D'akin tana shirin shigowa Na ce "Ki gudu zahra karki shigo ki gudu karki yarda mugayen nan su kamaki zahra ina son ki tsira juyawar da zasuyi Su bita tana ji tana gani ta Ruga a guje inaga lokacin da wasu daga cikinsu suka mara mata baya kafin kuma Naji Jiniyar y'an sanda cikin tashin hankali Suka rude mudan yace mu maza mu tafi Harbin nan da nayi ne ya janyo hankalin jami" an tsaro d'aya daga cikinsu ya ce "To shikuma wannan yazamuyi dashi" mu tafi dashi mun kasesa a.hanya suka fad,a suna sungumata kamar wani yaro Cikin boot din mota suka jefani sosai nasha azaba kamar zan rasa rayuwata Kafin bansan Inda suka tsaya ba saigani nayi sun fiddo ni sun jefani cikin daji suna saita ni da bindiga daga lokacin bankara sanin abunda ke faruwa ba duk halin da na shiga na shige shi ne sanadiyar d'an uwa ya kashe mun mata a kan ido na yaso hallaka rayuwata inbanda Allah yasa ina da sauran kwana a gaba "ya k'arasa fad'a cikin hawaye " Kowa dake palourn saida ya girgiza dajin wannan labarin wai Dan uwanka ne yayi maka haka musamman zahra da yau ta had'u da kakanta sannan taji Tarihin mahaifiyarta sosai su Ammy da MD suka jajintawa Baba sannan sukayi Allah wadarai da wannan D'an uwan nasa ranar Baba jinshi yayi cikin wani irin farinciki ganin jinin y'artasa harda jikokinta md ko yasha alwashin saiya kwatowa baba hakkinshi a wajen Dan uwanshi duk inda yake bayan komai ya lafa Baba ta kalli ammy ya ce "Hajiya naji kince Zahra ce maman yaran Nan ko kina nufin ki cemun matar jikana ce "Murmushi dauke da fuskar ammy ta ce "Eh baba matarsa ce Allah ya kawoka a daidai lokacin da muke da bukatarka Kallonsu Zahra tayi har md ta ce "ku bamu waje zamuyi magana"A tare suka tashi Zahra jinta take cikin farinciki marar musaltuwa bayan ammy tayiwa baba tsoho bayanin yanda asalin aurensu Zahra ya kasance saidai ta boye musu na dalilin auren akan matarsa saboda batason Zahra ko danginta suji abunnan abun kunyarta ne Sosai baba yayi mamakin al'amarin ta wani bangaren Kuma yaji Dadi Sosai da ammy ta fada Masa yanzu md yanason Zahra Sosai itace dai take tunanin ko Bata sonshi bazata amince da koma Masa ba sannan batasan ta yanda zasu tunkari iyayenta ba sun tattauna Sosai tsakanin Ammy da Baba har Kaka kafin su tsaida magana akan jibi idan Allah ya kaisu za a tafi garinsu baba ayi masu bayani sannan a Basu hakuri haka ko akayi ranar suka shirya gabaki dayansu Ammy,kakan Zahra,Chuchu,Zahra,da triple dinta sai Hajiya Kaka ,md ne kadai ba a je dashi ba bayan isarsu batsari Kai tsaye gidan bappa suka wuce Wanda Zahra itace ta gwada musu hanya Banda faduwa babu abundan gabanta yake Sosai Aka karramasu Dukda zarha Bata yarda ta had a Ido da kowaba gabanta kawai ke faduwa A sace take Kallon baba da Shima tunda ya shigo ita yake kallo fuskarshi ba alamar walwala ganin da Zahra a tafiyar bappa yasan maganace Mai mahimmanci hakan yasa ya Kira Yan uwa baba su mama habi kowa duk ya hallara a dakin bayan an gaggaisa cikin mutunci Nan ammy tayi musu bayanin komai game da auren Zahra da sukayi da d'anta a boye har ciki ya Samu har zuwa haihuwarta suma dai Bata fada musu dalilin auren na md ba ta ce dai shirme ne irin na Yara sannan ta Kara kafa musu hujja da nuna musu video din daurin Auren sunyi mamaki matuka da gaske Jin wanna chakwakiyar su mama habi kuwa ajiyar zuciya suka sauke dukda sunji zafin aurar da kanta da Zahra tayi Amma Kuma sunji Dadi da diyan suka kasance y'an halak baba ko cikin bacin Rai ya ce"Kin bani mamaki Zahra ina tarbiyarki,ina iliminki,har ki aurar da kanki ba tare da izinin iyayenki ba kenanma bani da wani amfani a wajenki Dan haka. Ki tashi kibani guri tunda bani da wata daraja a wajenki har Kika iya aurar da kanki ba izininmu ki tashi ki tafi bana bukatar ganinki"Baba ya fada cike da takaici,"Kuka sosai Zahra ta fashe dashi ta ce "Dan Allah Baba kayi hakuri ka yafemun.."Saikuma ta Kara fashewa da wani sabon kukan sosai baba ya nuna bacin ransa matuka.inda su ammy dasu baba har Hajiya Kaka hakuri kawai suke bashi kowa yayi mamakin irin yanda baba ya nuna bacin ranshi kasancewarsa mutum.mai hakuri dakyal da jibin goshi aka samu aka shawo kan baba Amma Kuma saiya gindaya sharadi akan Zahra bazata koma ba zata zauna a wajenshi har lokacin da zata yaye yaran ta mayar musu da Su "Nanfa hankali ya Kara tashi musamman na ammy da Chuchu "Hakuri ammy ta dinga bashi ta ce "Dan Allah malam kayi hakuri munsan mu masu laifi ne a gareka Amma ka sassauta a dauki abunnan matsayin kaddara Dan Allah malam kuyi hakuri a sasinta wlh yaron yayi matukar nadama kuma.yanzu haka Yana son Zahra Yana son idan kun amince ta koma a matsayin matarsa tahar abada Dan Allah malam kuyi hakuri kodan arzikin yaran Nan har ukku dake tsakaninsu"Ammy ta fada hankali tashe "Nanfa baba yace baisan wanna zancen ba Indai Zai yafawa Zahra abunda tayi mashi to zata zauna ne a wajenshi sannan ya Aiko mata takardarta tunda ba aure ne akayi na mutunci ba idan ba haka ba ta tashi ta bisu ya bar musu ita har abada"Sosai hankalinsu ya Kara tashi Banda Zahra ta taji sassauci gwara ta zauna a Nan din kawai "Baba tsoho ne ya saka Baki yacewa "Ammy 'kiyi hakuri Hajiya a barmata sudin Yana cikin fushi ne a Bari su huce kawai"Badan Ammy taso ba dole ta amince musu chuchu ko hada kukan Dan batason tayi kewar Zahra daidai da second yanda takejin zey a ranta haka takejin Zahra tamkar ciki daya suka fito Nan Hajiya Kaka ta gabatar musu da Baba matsayin kakan Zahra Sosai kowa yayi al'ajabi dajin wanna al'amarin baba ko yayi farinciki matuka na ganin mahaifin tsohuwar matar tasa Kuma kakan y'arsa Sosai yaji dadin bayyanuwar ahalin na Zahra dukda sunyi al'ajabi dajin wannan labarin na baba Mai rikitarwa Bayan sunci abinci an karramasu Wajen la'asr suka fito domin tafiya an cika musu ledoji da kindirmo Sosai Ammy da chuchu sukayi sanyi na barin Zahra mama habi da matar bappa suka rike triple chuchu ko ta garkame little Sosai sai kuka take ganin haka ya Sanya Zahra kasa da kanta Tana hawaye sai yanzu takejin kewar su da zatayo ga Kuma baba tsoho da ko sabawa basuyiba Shima tare zasu koma har mota suka rakosu Wanda chuchu dakyal ta Mika little ta ruga da gudu mota Tana kuka Ammy ko dauriya kawai tayi Tana rike da hannun Zahra ta ce "To takwara mun wuce saimun dawo ganinku"Zahra batasan lokacin da ta fashe da kuka jikin Ammy ba duk kallonta suke Sosai ta dinga kuka Ammy da itama zuciyarta ta kusa karyewa dakyal ta lallasheta ta shige mota da gudu Zahra ta koma ciki Tana kuka girgiza Kai kawai baba tsoho yayi Bayan sun Kara bankwana suka wuce cike da kewa da jimamin barin Zahra chuchu ko har suka Isa gida Tana kuka Dan ba Zahra kadai zatayi kuka ba hada triple da tayi muguwar shakuwa dasu kwana tare tashi tare kullum suna hannunta Ammy ma hakan ta kasance baba tsoho ko Shi kadai yake sake sake a ransa bazaiso abunda mahaifin Zahra ya fada ya faru ba watau na rabuwar Zahra da md yasan muddin Zahra ta rasa yaron Nan to fa tayi babban Rashin miji na gari Dan Shi kanshi yasan yaron mutumin kirki ne tashin hankalin da md ya shiga Najin labarin baro Zahra da da yaran baya musaltuwa Sosai ya burkucewa Ammy kamar Zai musu hauka su kansu mamakinshi suka dingayi yanda yake magana kasan Yana cikin tashin hankali ya ce "Ammy me yasa zaku baromun mata meyasa Ammy na fada maki ina son matata meyasa Zaki maida ita Gashinan kin lalata komai Ammy Ana neman rabani da matata wallahi bazan saketa ba kome zakuyi kuyi haba Ammy saikace Ba d'anki ba kinsan Sarai ina cikin tashin hankali shine saida kikayi yanda kikayi Kika rabani da mamy na Baki hakuri ba iyaka Ammy nayi regrade duk abunda nayi Ammy Amma kikaki hakura saida Kika rabani da matata why Ammy me nayi maki"Ya fada kamar Zai fashe da kuka"Ba Ammy ba hattababa tsoho saida ya tausaya Masa "Cikin kwantar da murya Ammy ta ce "Babu Wanda yafini sonka da Zahra babana nafi kowa kaunarka da Zahra saboda bazanso rabuwarka da itaba duk abunda nayi make nayine saboda tayi daraja da martaba wajenka ka gane amfaninta Amma bawai Dan karabu da ita ba ni zanfi kowa shiga bakin ciki ace ka rabu da Zahra In son Zahra tamkar yanda nakeson su chuchu "To Ammy meyasa Zaki Baro musu ita meyasa Zaki kaita wajensu Ammy yanzu kina gani sun amshe mun mata Ammy duk laifinki ne meyasa tun farko Baki sasintani da matata ta ba Kika dinga jamun Rai ni mamy tun ranar Dana fara haduwa da ita nasan darajarta da mahimmanci ta da amfaninta a cikin rayuwata.."Kasa karasa magana yayi saboda wani daci dayakeji a cikin zuciyarsa "Ammy ce ta ce "ka nutsu baba na dole ne a kaita Wajen iyayenta ayi musu bayani Susan halin da ake ciki saboda su sukafi kowa hakki a kanta kaga ko Baba da kagani shiya haifi mahaifiyarta to baikai dangin mahaifinta da mahaifinta hakki a kanta ba kayi hakuri harsu huce " bai tankawa Ammy ba saboda baima San abunda zaice mata ba Kuma, fuuuu yabar dakin kamar Zai tashi sama cikin tsananin bacin Rai "Chuchu ma Tana kuka ta Mike ta ce "Daman Ammy duk laifinki ne tun lokacin da yace yanason momcy kikakiya yanzu Gashinan kinja iyayenta sun amshe Mana ita"ta fada Tana tashi da gudu ta Ruga"Tagumi Ammy tayi ta ce "Oh ni !Fatima yanzu Kuma laifin Nan duka sun maidoshi kaina.........✍️⁩

*07026166536 domin magana da marubuciyar*

⁦🇳🇬⁩*Happy Independence*⁦🇳🇬⁩


*_Miss Hajo ce*_ 🤙


[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy: 🅿️............*95 & 96*
&
🅿️............*97 & 98*


_*SEMI FINAL*_ ⁩💃💃💃



"Why jabir me nayi Mata da zata nunamun irin wannan tsanar wlh jabir Ina son matata bazan iya rabuwa da ita ba please me yasa ta Kasa fahimtata "Kayi hakuri bloody Dan Allah komai yayi farko Yana da karshe kamar Wanda aka zabura haka MD ya aje little yabar palourn ya fita daga gidan y'ar mama Habi tazo ta dauki yaran jabir ya fita ya bishi MD dafe kanshi yayi da yakejin kamar zai rabe biyu ranar hotel suka kwana Dan MD ya dauki alwashin bazai koma Kaduna ba harsai Zahra ta amince Masa Tundaga ranar MD.basu koma kd ba hotel suke kwana kullum saisunje gidan mama habi Saida Yaga yaran Amma Zahra taki bashi hadin Kai ta fitoma su gaisa kiyawa take mama habi ko Sosai ta dinga Mata fada akan wulakancin da take yiwa bawan Allahn Nan yayi yawa Yauma Bayan sun tafi Bata yarda ta fita ba kwance tayi Tana hawaye ita. Kanta yanzu karya take ta ce "Batason Musty Saidai Kuma batajin zata koma Masa ya wulakantata"MD Saida sukayi sati biyu a katsina suna zarya jabir harya Fara gajiya a lakacin ne Kuma MD ya Fara wani irin ciwo Zazzabi da azababban Ciwon kai yau tunda safe Jabir Yana lekawa dakin ya samesa durkushe Yana Numfashi sama.sama hankali tashe Jabir ya dinga kiransa Amma baya iya mayar Masa sai Numfashi yakeja Cikin kidimewa da taimakon ma'aikatan Wajen aka Kai MD asibiti Kai tsaye medical center aka wuce dashi da isarsuma emergency akayi dashi Ammy jabir ya Kira ya fada Mata suna katsina MD ba lafiya "Cikin tsananin tashin hankali Ammy ta ce "Katsina Kuma jabir Me ya kaiku katsina meya samesa"Hankali tashe ya labarta Mata akan Zahra ne satinsu biyu garin"Salati Ammy tayi ta salamce ta ce gamunan yanzu"Hankali tashe Ammy da chuchu suka Wuto katsina kasancewar ta fly suka hau yasa sukayi saurin zuwa Sosai hankalinsu yayi matukar tashi ganin halin da md ke ciki Cikin kuka chuchu ta ce "Ya Jabir Ina Take fadamun wani gida ne take "Ki Bari chuchu a Fara sanin halin da yake ciki tukwana ayi wata magana daga baya "Cikin kuka ta ce "Yaya jabir Dan Allah ka fadamun please ka kaini gidan da take Dan Allah "Ganin irin yanda chuchu ke kuka Ya Sanya jabir daukarta a mota ya dinga lallashinta har suka iso gidan da Zahra take Cikin kuka ta shige Gidan a palourn ta samu Zahra itama dukta rame Tana bawa Amar Madara Cikin tashin hankali da kuka chuchu ta ce "Shikenan momcy Kin kashe Yaya Kin sakashi Cikin wani Hali saboda soyayyarta da yake maki meye laifinshi Dan yace kawai Yana sonki Momcy Yaya Yana halin mutuwa ko rayuwa saboda ke.."ta karasa fada Cikin wani irin kuka Mai cin rai"Hankali tashe Zahra ta Mike kadan ya Hana Bata saki Amar ba cikin tsananin tashin tashin hankali ta Dora hannu aka saikuma ta fashe da kuka ta ce "Na shiga ukku chuchu Yana wani asibitin "Medical center ta fada cikin kuka ai Zahra Bata kuma sauraransu ba hijab dinta kawai dake kusa da ita ta sanya ba Shiri tayi waje a guje kamar wata mahaukaciya Tana fita ta tsaida napep ta fada Masa asibitin dazai kaita hankalinta matukar tashe suna Isa asibitin bama ta saurari Mai napep dinba Dan bama ta fito da kudi ba hango Ammy da tayi jikin wani ward ya sanyata rugawa a guje ba Abunda take in Banda kuka Tana zuwa ta fashe da kuka ta fada jikin Ammy Tana kuka ta ce Dan Allah Ammy karya mutu Ammy wlh Ina son mijina dan Allah Ammy ki taimakamun"ta fada Tana fashewa da wani irin kuka saikuma ta zabura ta ce "Ina ne inda yake Ammy Dan Allah"Ammy na hawaye ta nuna Mata dakin"Ai Bata saurara kowa ba ta Ruga a guje Tana hangoshi doctors biyu akanshi batasan sanda ta Ruga ta fad'a jikinshi ba Tare da fashewa da wani irin sabon kuka ta garkamesa ta ce "Dan Allah ya musty ka tashi karka tafi ka barni wlh Ina sonka please ka tashi Dan Allah"sosai ta rumgumesa doctors din duk kallonta suka tsayayi MD kamar cikin bacci yakejin kamar Zahra daukarsa mafarkine Saida ya bude idanunsa da sukayi Masa nauyi ya sauke a kanta data Haye kirjinsa Tana kuka"numfashin da taking yayi ne ya sanyata sauri tashi tare da saurin Kama hannunshi ta cikin Ido suke kallon juna yunkurawa MD yay ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login