Showing 132001 words to 135000 words out of 153980 words

Chapter 45 - AUREN WATA TARA COMPLETE HAUSA NOVEL

30 Sep 2024

16349

yayi "Ya wuce Allah yafe Mana Tare "Ameen baba mungode jabir ya fada shiru sukayi kafin Jabir ya ce "Sai magana ta gaba baba yace kuyi hakuri Dan Allah ku mayar Masa da Zahra saboda Yana sonta Kuma ba rabuwa sukayi ba "nannefa baba ya murje ido ya ce "baisan wannan Zancen ba "Magiya Jabir ya dingayi Shima md ji yake kamar zai fashewa baba da kuka cike da magiya ya ce"Dan Allah baba kuyi hakuri ku yafemun wlh tallahi in son matata Dan Allah baba kuyi hakuri ku maidomun ita karku rabamu "Saida MD ya bawa bappa tausayi Kallon baba bappa yayi ya ce "Meyasa zakayi haka Yusufu kaida bansanka Da tsauri ba Kayi hakuri a barwa Allah lamarin Nan Karka shiga lamarin aure tunda kaga Allah shine ya hadasu tun farko dukda Bata shara'a a ba akayi abun to me zai Hana abar Masa sauran yayi ikonsa Dan Allah kayi hakuri ka janye fushin Nan Karka shiga ka zak'e cikin lamarin tunda ba a asan Abunda Allah zaiyi gaba ba"Numfashi baba yaja kafin yayi shiru saikuma ya dago ya ce"Na janye fushi na ka nemu yarda a wajenta idan ta amince ba matsala saiku sasinta Allah ya zab'a Abunda yafi Zama alkhairi"wata irin ajiyar zuciya mD ya sauke kafin ya dago ya dinga jerawa baba addu'oi Sosai ya shiga yiwa baba godiya yanda kasan yayi Masa albishir da gidan Aljanna"Jabir ne ya ce"Tana ciki ne bappa"a a a kanwar mahaifinta ta tafi da ita katsina yanzu Tana katsina ita da yaran"Cikin sauri MD ya dago ya ce "Bappa Dan Allah bamu address din gidan da take Dan Allah"Murmushi bappa yayi ya ce "Kai jikannan nawa ka cika azarbabi to bari Nak'i fad'a maka tunda dai Daman kwacen amaryace zakamun "Dan Murmushi MD yayi Yana Kasa dakai Yana Sosa keya"Shidai baba shiru yayi Jabir ne yayi dariya ya ce "A a a bappa ai kayi mata tsufa"Saida suka danyi barkwanci kafin Baffa ya Basu address din gidan Ba yanda baiyi dasu ba Su tsaya ko fura a Dama musu Amma suka kiya saboda saurin da MD yake su wuce katsina kudade bandir biyu md ya bawa su bappa Amma sukaki amsa ba irin yanda baiyi dasu ba Amma suka ki amsa suka kafe ba yanda ya iya sai maida su yayi a yammar driver ya wuce dasu katsina sai Bayan magrib suka Isa garin katsina salla kawai sukayi suka wuce Unguwar su mama habi dake Bayan high court Basu wani Sha wahala ba Wajen gane gidan almajiri suka tura suka ce ana sallama'bayan fitowar Almajirin ya ce "ance wai wa ake nema"Mamy"MD ya fada jabir yayi sauri ya ce "Kace Zahra ake nema"Kallon md yayi ya ce "waya santa da Mamy in Banda Abunka "Dukna riikicene shysa wlh jabir bakasan irin son da nakeyiwa yarinyar Nan ba shiyasa"Dariyar mugunta jabir yayi ya ce "Au Haba yaushe ka Fara son matar Wata tara Kuma tsaki md yaja yace"Kaga matsalata dakai kenan to wannan dai matar ta Har Abada ce Babu rabuwa "Dariya Jabir yayi fitowa Almajirin yayi ya ce "Ancewai Bazata fito ba "OMG"MD ya fada"Jabir ne ya ce "zasuyi tunanin wasune ko samari kaga Tana da aure bazasu Bari ta fito ba fa"Eh Kuma hakane "MD ya fada kafin ya kalli yaron ya ce "ka ce "Baban su Y'an ukku ne yazo"To Almarin ya fada Yana komawa"Ajiyar zuciya mD ya sauke Dan yaji Dadi koba komai ana tsare Masa igiyar aurensa Fitowa Almajirin yayi ya ce "ance wai ku shiga"Ajiyar zuciya mD ya sauke jabir ya bawa Almajirin 2k kafin su shiga Cikin gidan da a palourn Mai gidan aka saukesu Kafin mama habi ta shigo da hijab dinta dafara'a ta tarbesu suka gaisheta Cikin girmamawa Bayan ta zauna ta ce "Kuyi hakuri an tsaidaku waje bamuganeku ba saidaga baya"Murmushi jabir yayi ya ce "Ba komai mama"Madalla Diyarta ce to shigo ta aje musu ruwa da lemo Bayan ta gaishesu ta juya mama habi ta ce "Ku Sha Mana"Jabir ne yasha MD baisha ba "Shiru sukayi kafin mama rabi ta ce "koba a fada ba nasan ga Baban yaran nan ganin Kama karara Masha Allah"ta fada Tana Kallon md "Murmushi Jabir yayi ya ce "e shine mama. Daman zuwa mukayi mu Kara Baku hakuri"A Haba yaron Nan hakuri Kuma na me ai komai ya wuce anzama d'aya tunda harda zuri'a Allah dai ya Raya Ameen MD ya fada Kasa Kasa kafin jabir ya ce "Mungode Daman daga Chan batsari muke munje mun karaba su Baba hakuri Kuma sun hakura harma sun amince da maganar Komawar Tata suma suka fada Mana Nan inda take.akan muzo Kuma mu nemu amincewarku. Da Tata shine mukazo Mama Dan Allah ayi hakuri ta koma dakinta wlh Yana sonta Kuma insha Allah zai riketa da Amana"shiru mama tayi kafin ta dago ta ce "Ai ba matsala tunda Sun amince muma mun amince Allah zaba Abunda yafi alkhairi saiku nemu yarda a wajenta Bari na shiga na turo muku ita "ta fada Tana mikewa ta shige ciki"MD jinshi yayi Cikin wani irin farinciki Jin abun ya Fara zuwa dasauki Koda mama taje ta fadawa Zahra wadanda ke tafe Saida tayi mamaki mama ce ta ce "tashi ki Mike kuje da yaran ku gaisa ko"Zahra kamar zatayi kuka ta ce "Dan Allah akai mashi yaran ni ba sainaje ba"Dukda Tana da bukatar ganin nasa"Tsaki mama habi taja ta ce "Da Allah tashi kibani waje bansan shiririta kije ku gaisa mutanen su taho tundaga kaduna saboda ke Dan iskanci Kiki zuwa ku gaisa maxa tashi kije kafin ranki ya b'aci"ganin ran mama ya b'aci ya sanyata mikewa da Akhbar a hannunta Ta fito MD suna zaune Yar mama habi ta kawo mishi yaran su biyu Amar da Little Sosai ya yaba yaran sun Kara kyau da wayo har Dariya sunayi sunyi bul_bul gwanin ban sha'awa Duka biyun ya dauka Yana musu Dariya ya ce "oyoyo my kids I really miss you so much please karku sake nesa da daddynku zai shiga wani Hali"Daidai shigowar Zahra Cikin hijab sab'e da Alkhbar tunda ta shigo palourn MD ya kafeta da kallo Bako kiftawa yanajin wata irin kauna da soyayyarta na Kara fusgarsa ji yake kamar yaje ya rungumeta Harta zauna Yana kallonta a sace Zahra ta kellesa idonsa suka sartse Cikin na juna sauri tayi ta kauda Kai gabanta na faduwa nauyayyar Ajiyar zuciya mD ya sauke yanajin wani irin sanyi na ratsa sa shiru Zahra tayi Bata tanka ba jabir ne ya ce "Hajiyarmu ina yini Kodai har yanzu fushin ake damu nidai ina bada hakuri Kuma ina wanke laifi na "Dan Murmushi Zahra tayi ta ce "Ina yini Yaya jabir anzo lfy"lafiya qalau ya triple dinmu "Alhmdulillahi"ta fada Kasa Kasa Tana wasa da zoben hannunta"MD bai daina kallonta ba kamar zai cinye ta Biyun ya aje kan sopa kafin ya koma kujerar da take kamar zai shige jikinta saurin matsawa tayi tare da satar kallonsa suna hada ido ta Galla Masa harara"Mika hannu yayi ya amshi little dake Zillo a hannunta Ajiyar zuciya ya sauke tare da kissing din little ya ce "i Really miss you my All above I love you so much my beloved daughter ina sonki Sosai takwarar Ammy na Kuma Favorite wife d'ina gaki Kuma daughter ta "ya fada Yana mata Dariya kamar tasan me yake cewa tahau Masa Dariya hada Zillo "Tabe Baki Zahra tayi Tana Shirin mikewa ya ruko hannunta juyowa tayi tare da tsatsaresa da Dara daran idanunta tare da juyasu ta ce "ka sakeni meye haka gaban mutane da Allah"ajiyar zuciya ya sauke Yana kallonta ya ce "Please ki dawo ki zauna Dan Allah muyi magana wajenki nazo"Kamar bazatace komai ba saikuma ta ce"Inajinka Amma ka.sakeni"Ai na sakeki nasan tafiya zakiyi Dan Allah ki dawo ki zauna" to ka sakeni Mana ha a saikace wata yarinyar nace ba inda zanifa "sakinta MD yayi ganin Bata tafi ba ya sanyasa sauke ajiyar zuciya Bayan ta zauna Dan nesa dashi Tana wani hade fuska Cikin kakkausar murya ya Fara magana Cikin sigar lallashi da kwantar da Kai ya ce"Dan Allah Dan girman Allah Mamy kiyi hakuri ki janye fushin da kike Dani wlh nayi regrade duk Abunda nayi maki bana daidai ba Ina sonki Mamy son da bazan iya kwatantashi da komai ba son da bantaba yiwa wani mahaluki irinshi ba Mamy shigowarki rayuwata nasan abubuwa da Dama Wanda a chan da ban sanshiba Mamy shigowarki rayuwata nasan meye so inasonki son da ni kaina bazance ga adadinshi ba Ina sonki fiye da yanda nake son kaina Mamy Dan Allah kiyi hakuri ko bazaki Soni ba yanzu Ina neman alfarmar da kidawo gareni mu shimfida sabuwar rayuwa irin ta kowasu ma'aurata mu gyara kuskuren da mukayi a baya mu tarbiyantar da yaranmu sannan mu Basu Kula irin wacce kowasu iyaye ke bawa yaransu Dan Allah Mamy Ina kaskantar da kaina akan kiyi hakuri ki dawo gareni insha Allahu zan koya Miki Sona da kaunata Zan Kula dake Zan soki na kaunaceki na baki duk wace kulawa Dan Allah ki ceci rayuwata please Mamy"Sosai Zahra tayi mamakin Jin furuccin nashi a gareta wai yana sonta tunani tayi bafa ita yake so ba kawai saboda yaranshine da yake mugun so shekara goma bai samu haihuwa ba shine zaiyi mata wayau yace Yana sonta ta koma gareshi Ya wulakantata shida matarshi karshema Kila ya saketa ya kwace Mata yaran tunanin wanannne ya dira tsam a cikin zuciyarta Sosai taji ranta ya b'aci lokaci guda ،mikewa tayi tare da kallonsa ta ce "zamana da Kai ya Kare babushi bazan koma gareka ba ka koma chan Wajen matarka Amma ni Nan da ka gani karka Kara tunanin wai zan koma maka inma mafarki kake. Ka farka kagama tafiyata"Tana game fadar haka tabar palourn Cikin sauri tanajin wani daci da zafi a cikin zuciyarta Jin yaudarar da suka shirya Mata a cewarta"Tashi MD yayi Cikin tsananin tashin hankali ya bita, tuni tabar palourn dafe kanshi da yayi matukar Sara Masa yayi ya ce "Innalillahi wa Inna ilahiraji'un "Ganin Yana Shirin faduwa ya sanya jabir yayi sauri ya tallabeshi ya zaunar dashi Shi kanshi jabir baiji dadin Abunda Zahra tayi ba yarasa wata irin bakar zuciya ce da ita shi har yanzu baiga wani laifin zo a ganin da MD yayi Mata ba take wahalar dashi Haka idan taimakonema ita MD ya Fara taimaka bataji laifin kawarta ba saishi mamakin MD yake Akan wani irin so ne wannan yake yiwa Zahra da har take Masa irin wanna wulakancin Yana shanyewa Wanda tunda yake bai Tana tunanin akwai macen da MD zaizo tayi Masa haka ba matanda rububinshi sure Amma ya like yarinyar karama na Shirin nakasashi "MD. Wani irin zafi yakeji a cikin zuciyarsa kamar zai fashe da kuka ya kalli jabir ya ce...........✍️

*Domin magana da marubuciyar 07026166536*


🇳🇬 *Happy Independence day* 🇳🇬


_*Miss Hajo ce*_🤙
[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy: 🅿️.............*87 & 88*
&
🅿️.............*89 & 90*


Duk Kallon mamaki suke bin Baba dashi shiko nuna zahra kawai yake "MD ne yayi k'arfin halin cewa " Dan Allah Baba kayi mana bayani ina kasan wannan "hawaye na fita daga idon Baba ya ce " y'ata ce d'aya tilo dana mallaka Nina haifeta a tare Nida ita akayi mana harin da har kuka tsinceni tsawon shekaru bansan Inda take ba a tunani ma ta rasu saboda Bansan Inda sukayi da ita ba "cike da mamaki Ammy ta ce Ka nutsu dai Baba wannan ba y'arka bace Mahaifinta Yana Chan Funtua kuma wannan yarinya ce ma bata kai shekarun da kake Tunani ba kadai duba Baba" mik'awa MD yaron Baba yayi ya nufo Inda Zahra take da duk a tsorace ta ke kama hannunta dake d'auke da zoben da awarwaran da tunda Baba ya bata yake hannunta yayi Kallon zoben da awarwaran yake Yana murmushi yana hawaye ya ce "Kece Mamy ashe daman idona zai sake nunamun ke ina raye Mamy na nine Mahaifinki Mai kaunarki ko kin manta ni zahra'u ko kema sun juye miki kwalwar ne Dan karki tona musu asiri kamar yanda suka juyemun tawa Mamy ki tuna mahaifinki Malam Abdussalam sai kuma ya Rungumeta tsam a jikinsa ya ce " Alhmdllh Alhmdllh Allah na gode Maka da ka nuna mun wannan yara y'ata da na shekara da shekaru ina begenta yau gashi Allah ya had'amu ta yanda banyi tsammani ba "ido ido kawai ake tsakanin Ammy da MD har Chuchu zahra ko Itama kuka ta fashe dashi Tabbas wannan din shine kakanta shine mahaifin Mamanta dukta k'are MD ne ya taso yayi kokarin raba su ya ce " ka nutsu Baba kayi mana bayani wannan ba wacce kake tunani bace "Sassauce ruk'on da Baba yayiwa zahra yayi ya juya ya kalli MD ya ce " Haba yaro ya zakamun gardama na haifi y'ata na kasa ganeta"Juyawa yayi yana kallon zahra dake Kuka ya tallabo Fuskarta kallonta ya dingayi yana son yaga banbanci tsakanin ta da mahaifiyar Ta" motsa bakinki "ya fad'a a hankali zahra ta motsa mamaki ya kama Baba ya ce "To ya haka da sanin da nayi mata tun yarinta abun nan d'aya gareta amma yanzu naga biyu " Cikin muryar kuka zahra ta ce "Ba waccen Da kake magana bace y'arta ce " ta fad'a tana hawaye"duk mamaki yagama. Cikasu Ammy ce ta ce "Kamarya y'arta ce kunsanyani cikin duhu fa Dan Allah ku warware mana " Zaunawa Baba yayi jibis yana mamakin jin Abunda ya fito daga bakinta MD ne yaja numfashi ya ce "da Alamun akwai wani Abu a kasa please ku nutsu ku warware mana muna cikin duhu " cikin muryar kuka zahra ta ce "Babana ya bani labarin mahaifiyata yana aikin noma.ya tsinceta a lokacin Bata cikin hayyacinta har aka samu akayi mata magani Dan da ko magana batayi sai daga baya da aka dage da rokon Allah kasancewar gidansu babana duk malamai ne koda ta farka bata iya tuna komai ba sai sunanta ta ce Musu sunanta " Zahra"a haka har Allah ya sasinta kansu da babana sukayi Aure Wanda suka zauna a funtua wajen sana'arsa yace bata tab'a tuna wani nata ba ko ita kanta wacece Sai lokacin da ta haife ni Wanda a nan ta ciro zoben wannan da awarwaro dake hannu na ta basa ta ce idan na girma ta bani zasu taimaka mani wajen gano danginta daga nan bata Kara ce dasu Komai ba game da asalinta Har Allah yayi mata cikawa"Ta k'arasa fad'a cikin kuka "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Ashe karshen saduwata da Zahra'u kenan a rayuwa ,ashe bazan sake ganin y'ata ba d'aya Dana mallaka Allahu akhbar Su mudan basu samu damar kasheta ba kenan Allah mai iko zahra Har saida ta haihu ashe Allah sarki zahra'u Allah ya jikanki yayi miki rahama yasa kina cikin rahama hakika mamy baki mutu da hakkin iyaye ba Kinyimun biyayyar da bakowani d'a zaiyiwa mahaifansa haka ba allah ya jikanki Ashe bazamu kara saduwa ba sai a darussalam Zahra'u ke kika rigani tafiya ashe ba rabon mu sake ganawa yana hawaye ya kamo hannun zahra ya ce " Tabbas ni nan nine kakanki Nina Haifi mahaifiyarki Wannan awarwaron da zoben Tabbas nata ne ko babu su kamanninki da mahaifiyarki kadai sun isa duk wani ahalinmu ya ganki ya shaidaki Allah ya taimaka Mudan bai ganki ba na tabbata da ya ganki tofa da ya zama dole ya kasheki "Mudan " Ammy ta maimaita zahra ko jin abun take tamkar almara wai yau itace gata ga kakanta,yau itace taga jinin mahaifiyarta ,Allah sarki wasu hawayen farinciki ne suka zubo mata tana murmushi ta ce"Kana nufin kaid'in kaka na ne kai ka haifi mahaifiyata daman da rabon zanga dangin Mama a duniya "ta fad'a hawaye na zubo mata saikuma ta Rungume Baba ta ce " Alhmdllh Allah na gode Maka da ka nunamun wannan ranar tamkar almara Baba najima da bakincikin Rashin sanin dangin mahaifiyata bantaba kawowa a raina ba zan hadu dasu Cikin Sauki haka meya kawoka gidan nan har yayi silar haduwata dakai Baba"ta k'arasa fad'a tana hawaye "Rungumeta sosai Baba yayi yanajin kaunarta kamar yanda yakejin k'aunar y'arsa data rasu " sosai su Ammy suka girgiza dajin al'amarin nan Chuchu da Ammy da Hajiya kaka da bata jima da shigowa ba hada hawaye MD ko mamaki ya gama cikasu cewa yayi "mezai hana Baba ka bamu labarin abunda ya raboka da garinku da wadanda sukayi harin rayuwarka da ta iyalanka " Saida suka saki juna daga rungumar da sukayi da zahra kafin ya goge hawayen bak'inciki da takaici ya ce "Yau zan baku labarin asalin waye ni da kuma silar shigarmu cikin wani hali ta dalilin d'an uwa Nida y'ata asalinmu haifaffun Jihar jigawa ne ina da mata d'aya Hajiya Saratu ina da kanne Shida Wanda muka fito ciki d'aya uwa d'aya uba d'aya sai Wanda muke uba d'aya Mudan Wanda shine autanmu shi kadai mahaifiyarsa ta Haifa har Allah yayiwa iyayenmu gaba d'aya a hankali a hankali rasuwa dalilin wannan ya sanya muke matuk'ar sonsa muke jansa a jiki bamu tab'a nuna masa y'an ubanci soyayyar da nake nuna masa ko Wanda muke uwa d'aya uba d'aya bana nuna musu tun ina yaro daman ni natashi mutum ne mai neman na kansa na kasance Dan kasuwa tun ina K'ananan kasuwanci da noma har Allah ya habaka na zama Babban attajiri a garinmu Wanda daidai ne zaka fad'a suna na Alhaji abdussalam Mai fata na samu sunan nan da dalilin Kasuwancinsu fatocin da nayi Mata ta d'aya Hajiya Saratu wadda tsawon shekaru bamu tab'a haihuwa ba sai Bayan shekaru har manyantaka ta fara kamani Allah ya bamu haihuwar y'armu Fatima wacce taci sunan kakarta ne ta wajen uwa hakan yasa Muka fiyan kiranta da "Mamy " Gata da soyayya ba irin Wanda bamawa Zahra'u kasancewarta y'a daya tilo a wajenmu amma dukda gatan da muke bata baihanamu bata ilimin boko da na arabi ba Gabak'i daya Na d'auki yarda na bawa Mudan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login