Showing 153001 words to 156000 words out of 182697 words

Chapter 52 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22451

Allah ya kaimu, sannan ya duba idan da yiwuwar a sallameta"

Adam ya ?ago ya kalleshi ya ce "Babu in da za a sallameta sai ta fa?i in da matata take, ko na sanya a tsareta"

Bashir ya girgiza kai ya ce "No, Adams, a hankali zamu bi ta, duk da muna cigaba da ?ata lokaci, kuma can katsinan ma, babu wani cikakken bayani, dan haka na yanke shawarar zamu je da police, kai tun da ban san meye a tsakaninku ba, kamar wasu ma?iyan juna kai da ita, za mu je da masu uniform, wata?ila su ta yi musu bayani, yadda ake ciki sai mu san abun yi".

"Zuwa yaushe kenan?"

'Zan yi magana da Hassan, sai muje ko zuwa gobe in Allah ya kaimu da safe ne".

"Wannan shi ne chance na ?arshe, idan har ba ta yi magana ba, zan saka ta yi ta ?arfin tsiya!".

Ayshercool.



*Littafin ku?i ne, ?500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*

*Paid book ne, ?500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, masu bu?atar special kuma, suna iya zuwa arewabooks su yi searching.*



Bashir ya ce "A'a, ba sai an kai ga amfani da ?arfin tsiya ba, zata yi magana a hankali, ?uriciya ke damunta, amma duk da haka kamar akwai wata 'yar tsama tsakaninka da ita, yanayin abubuwan da take yi maka, kamar da gayyya take yi maka".

Adam ya ?an yi guntun tsaki ya ce "Manta da ita kawai, sai gobe in Allah ya kaimu, X-ray ?in na ta babu wata matsala?"

Bashir ya ce "Ai na gaya maka sai gobe in Allah ya kaimu likitan zai duba".

"Allah ya kaimu"

Bashir ya amsa da "Amin".

**
Nusaiba tun da ta ji abun da yake faruwa, ta rasa nutsuwarta, ko abincin kirki ba ta iya ci. Yanzu haka tana tsaka da tunanin da ta saba ta ji Iman ta dafata "Anty Nusaiba" Nusaiba ta ?an zabura sannan ta sauke numfashi ba tare da ta ce komai ba.

"Anty Nusaiba tunanin me ki ke yi haka ne?"

"Bari kawai Iman, tun da Ammi ta gaya mana zancen nan, na kasa nutsuwa ina tausaya mana idan zancen nan ya fita, kin san yadda aka samu a gaba da ma a masarautar nan, ?iris ake jira wani abu ya faru, to ga wannan babbar magana gaba ?aya na kasa nutsuwa, idan har ba Anty Aisha aka gano ba, wallahi muna cikin tashin hankali".

"Haka ne, amma babu abun da ya gagari addu'a anty nusaiba, kuma babu ta yadda muka isa mu kaucewa ?addara, in sha Allah babu abun da zai faru".

"Iman, na san kina dakewa ne kina ?o?arin kwantar mini da hankali, amma kar ki manta abun da aka gaya wa mutane a kan barinta ?asar nan, kin san yadda aka sako yaya Adam a gaba, yanzu idan maganar nan ta fasu, babu irin sharrin da ba za ayi masa ba ba shi ba har Ammi da mu baki ?aya. Shiyasa ni tun farko ban so hukuncin da ammi ta yanke ba, tun da komai mu?addari ne" ta ?arasa maganar tana kuka.

Iman ta rungumeta ita ma tana zubar da hawaye ta ce "Na sani Anty Nusaiba, amma Ammi uwa ce, duk abun da zata yi, tana yi ne dan bamu kariya da wanzuwar farincikinmu, kuma in sha Allah ?o?arin ta ba zai tafi a banza ba, komai zai zo ?arshe da yardar Allah, ki daina damuwa, komai zsi zo da sau?i, ai babu abun da ya gagari Allah" suka cigaba da kuka iman na rarrashin Nusaiba.

Baba uwani ce ta shigo tana sallama, tare da zuro kai. Da sauri suka gyara iman ta amsa mata.

Ta dubi iman ta ce "Uwar ?akina lafiya kuwa?".

Iman ta ?a?alo murmushi ta ce "Lafiya lau baba uwani, akwai wani abu ne?"

"Ni fa na kasa gane muku gaba ?aya, giwa ta daina walwala, mai gida ma haka, kuma gashi na tarar kuna kuka, dan Allah me kuke ?oyewa ne meyake faruwa haka? Gaba daya gidan babu da?i, babu wata walwala saboda yanayin nan da ku ke ciki" Ta yi maganar tana neman fashewa da kuka.

Nusaiba ta ce "Baba Uwani babu wani abu kar ki damu".

Cikin damuwa iman ta ce 'Dan Allah kar ki yi kuka baba uwani, komai zai daidaita ba wani abun bane ba, Ammi jikinta ne ya ?an tashi shiyasa bata walwala, kuma kin san walwalarta ce ta mu, kar ki yi kuka Please" baba Uwani ta matse ?walla ta ce "To shikenan, Allah ya bata lafiya, ya sanya komai lafiya, ya jishe mu alkhairi" tana gama maganar ta juya ta fice.

Iman ta ce "Allah sarki baba uwani, tana sonmu da yawa, bana son in ga masu shiga damuwar nan suna ?ara yawa, Allah ya bamu mafita, ina shirin gaya miki wani abu, wannan maganar ta kunno kai".

Nusaiba ta dubeta ta ce "Wane abun?"

"Ki bari wannan matter ta yi settling, zan gaya miki".

"No, kin san ba zan jure ba, ba zan iya jira ba, ki gaya mini yanzu kawai".

Iman ta ja numfashi ta ce "Kin san me uncle J ya ce mini?"

Nusaiba ta girgiza kai ta ce "Sai kin fa?a".

"Wai so na yake yi, kuma ko ban amince ba zai bi ta in da ya san za a bashi ni"

Nusaiba ta yi murmushi ta ce "Ni na san a rina ai, take-takensa duk ya gama nunawa, amma ke mai ya sa na ga kamar ba kya son shi ne? Mai uncle J ?in ya yi?"

Iman ta ?an murza zoben hannunta ta yi shiru.

"Do you still loves him?" Nusaiba ta yi maganar tana kallon fuskar Iman.

Iman ta ?an waro ido ta ce "Who?".

"Your recent ex, ?an......"

"Shhhhh" iman ta katseta.

"Kar mu kai ga nan Please, mu bar maganar ma kawai"

Baba uwani kuwa da ke la?e a ?ofar ?akin, jin sun sauya hira ya sanya ta tafi tana tsaki "Aikin banza jarababbu, sun ?i yin maganar gaba ?aya, zancen da suka yi kuma, idan na kai mata ba so take yi ba, aikin kawai".

***
Adam yana kwance ya ?ura wa roofing ido, sai ya tuna Jabir, abun da yayi masa ?azu ya tuna, sai ya ji bai kyauta ba, jabir a komai yana tsaye a kan lamuransa, bai kamata ya yi masa haka ba, kuma jabir mutum ne mai kaifin tunani da hangen nesa, sanin ko ya so ko bai so ba zancen zai fit6, ya yanke shawarar ya yi wa jabir zancen, mussaman da suna tare Ruma ta yi masa abun da ta yi masa da farko, tare da saka ran Jabir zai iya samo masa mafita.
Da sauri ya tashi ya fita, ya ?au mota ya tafi gidan Galadima mai ci.

Sai dai tun a hanya yake kiran wayar Jabir ya ?i ?agawa, ya je gida ya tarar Jabir baya nan, sarai ya san in da zai same shi, dan haka bai tsaya ko ina ba sai can.

Ko da Jabir ya ga Adam, ?o?arin share Adam ?in ya yi amma ya kasa.

"Wurinka na zo" Adam yayi maganar yana duban idon Jabir.

"Ina jin ka" jabir yayi maganar yana basarwa.

Adam ya sanya hannu ya ?ago Jabir da kwalar rigarsa, ya ja shi suka fita waje.

"Wai meye haka ka ke yi?".

Adam ya tsuke fuska ya ce "Yaya na zo wurinka in ce wurinka na zo, ka shareni ba ka fini mulki da jin kai ba, na san ka sani".

Jabir ya kalli Adam ya ce "Har ka manta few hours ago abun da ka yi mini?".

"Forget about it, just feel like to share it you"

"Ka ri?e sirrinka, tun da bai kamata na sani ba".

Adam ya dafa kafa?ar Jabir ya ce "Kar ka yi mini yawa mana, yakamata ka saurareni".

"Ina jin ka"

Adam ya ?an yi shiru, sannan ya gaya wa Jabir abun da yake faruwa.
Sak jabir yayi, gaba ?aya jikinsa yayi sanyi, wani irin gumi ya shiga tsatsfo masa ya ce "Takawa, wannan fa ba ?aramar magana ba ce, case ne mai girman gaske, ni gaba ?aya sar?a?iyar nan ta yi yawa, na kasa ganewa gaba ?aya, an ce Aisha zata tafi ?aro karatu, kuma tana Saudiyya rainon ciki, ta dawo ba wanda ya sani an yi garkuwa da ita, ta haihu jariri ya ku?uta ita ba a san in da take ba, wannan zancen kamar film ko almara ni ban gane ba".

Cikin matsananciyar damuwa Adam ya ce "Bar shi a baka gane ?in ba, ka san wacece ta zo da yaron?"

Jabir ya girgiza kai, Adam ya ce "Wannan yarinyar da ta zageni a social media, da na yi niyyar hukuntawa ka hanani".

Jabir ya waro ido kamar su fa?o ya ce "Again? Ita a ina ta samu jaririn naka?"

"Wai kai Jabir anya ka ci waec kuwa? Duk bayanin da nake baka ganewa, amma ni babban mamakina bai wuce yadda yarinyar nan take manne da ?addarata ba, ita ma an yi garkuwa da ita watannin baya, Bashir ne ya tsinceta a Katsina, a hanyar kai ku?in fansar aisha, ta zo da ?ankwalin aisha wanda ya ?ara tabattar mini ba ?arya take yi ba, sai dai duk yadda muka ka?a muka raya ta?i fa?ar komai a kak aisha, kamar tana amfani da hakan ta rama abun da na yi mata ne".

Zamewa jabir yayi ya tsuguna yana maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Adam kuma yana tsaye yana murza yatsunsa ya na jin yadda hawaye ke cika masa ido.

Sai da Jabir ya gama salallaminsa, sannan ya tashi tsaye, ya dubi Adam ya ce "Yanzu ba lokacin tattauna wata magana ba ce, babu isasshen lokaci, dole a nemo in da aisha take kan kowa ya ji wannan zancen, gashi ka ce sun daina kiranka a kan ku?in fansarta".

Adam ya jinjina masa kai alamar eh.

"Ka ga, maza mu je mota, muje Asibitin".

Haka Adam ya ?auki Jabir suka tafi wurin rumaisa.

A can unguwa kuwa, mama na nan suna ta fama da jinyar rumaisa, amma maganar jaririn nan ta cika gari, kasancewar mama babu wanda suka yi wa bayanin in da rumaisa ta samo jariri, ko a 'yan uwa ba kowane ya sani ba.
Wasu suka din ga cewa ciki rumaisa ta yi, shi ne aka kaita wani wurin ta haihu, dama wannan shegiyar fitinarta ta da rawar kai ta yi yawa, tsaf zata aikata, ba su yi la'akari da irin raunukan da suke jikinta ba, wasu ma cewa suke yi, ba wani saceta da aka yi, rainon ciki ta yi. Ya yin da wani sashen suke cewa gaba ?aya rumaisa ba ta yi kama da wadda ta ?au ciki ta haihu ba, dan a yadda take ?in nan, idan ma cikin ne, abu ne mai wahalar gaske ace ta iya haihuwa da kanta, haka unguwa ta ?auka, wasu suna sukarta, wasu suna bata kariya, sai dai su mama sam basu sani ba, dan ko a gari babu wanda ya iya tarar zaratan samarin nan ya yi musu zancen.

Yanzu ma mama na ta shirin su kwanta, ruma ta sha magungunan ta, tana ta shafa dogon gashin jaririnta, tana kallon dogon hancinsa.

"Meyasa ka yi kama da babanka, dama babarka ka yi kama, da ka fi haka kyau boy na" ta yi maganar tana kissing ?in sa a goshinsa, tana murmushi da jin soyayyar Sabir na shiga zuciyarta.

Yaya Abubakar ya dubeta ya ce "Mama boy, zan tafi gida, gobe in Allah ya kaimu zan biyo mu yi sallama, zan koma school zamu fara exams".

Ruma ta ?ata fuska ta ce "Dan Allah kar ka tafi, bana son ka tafi".

"Ki hi ha?uri, exams ?in nan ce zata saka na koma, ba dan haka ba a kusa da ke zan kasance in ta kallonki gudan jinina"
Ta yi murmushi ta ce "Allah ya bayar da sa'a"

Mama ta ce "Ka zo ka tafi kar ka yi dare"

"To mama, ban gaji da ganinku bane" kan mama ta yi magana Adam suka shigo.

Ruma ta kawar da kai tana fa?in "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" domin ta gaji da ganin takawa, da kullum sai ya zo sau biyu, kuma duk zuwa sai ya ?aga mata hankali a kan ta gaya masa in da Aisha take.
Ba ta ?ara ha?e rai ba sai da ta ga Jabir, sarai ta gane shi, da shi aka ha?a baki Adam ya ?aukota yayi mata wula?anci.

Cikin girmamawa suka gaisa da ammi, yayin da jabir ya ?urawa rumaisa ido, da ta ha?e rai.

Suka gaisa da Abubakar ma, da yake tsaye yana shirin tafiya.

Mama ta ce "Ana ta ?awainiya da rumaisa fa, mun gode sosai Allah ya yi albarka, ya shiga lamarin ka ya kareka da ga sharrin ma?iya".

Adam ya ce "Bakomai mama, yi wa kai ne, ki daina godiya ma, addu'a muka fi bu?ata"

Rumaisa a ranta ta ce "Ji shi, wai mama sai ka ce babarsu, dan tsabar kuturun iyayi, wallahi mamanmu ce kawai" ta yi maganar a zuciyarta.

Abubakar ya ce "Ruma baki iya gaisuwa bane?"

Ta ?ago ta ce 'Au wai ba?i mama ta yi, sannunku"

"Ya jiki kuwa?" Jabir yayi maganar yana kallon ruma.

"Da sau?i".

"Ai da yake ban san meyafaru ba, sai yau, shiyasa bamu zo da shi na dubaki ba, mu ga jaririn"

Maimakon ta mi?o shi, sai saka hannu ta dafe shi, tana harare-harare.

Abubakar ya matsa ya ?auko masa jaririn, ya bashi sannan ya fara yi wa ruma mita "Wai ke wace irin yarinya ce ne? Ke shikenan ba wanda zai ta?a yaron nan sai ke, ke da kece uwassa ban san yadda za'ayi ba".

"To ai nice mamansa, ai dai bar mini shi ta yi".

Ya ce "Ke tafi can, ke ma ?in ai Haryanzu rainonki ake yi, mama bari na wuce na je gida na ha?a kayana"

"Yaya Sadik, sai da safe ka gaishe da su"

"Ba yanzu duk suka tafi ba, duk kuna tare sai da safe, ban da yi wa mama rigima dan Allah, a bari sai mun zo mu ayi mana" murmushi ta yi Abubakar ya kama hanya ya fita.

Jabir ya zubawa yaron ido, Adam da ke zaune a gefensa ma, ya zuba masa ido yana sa?a abubuwa daban daban a ransa.

Mama ta juya tana amsa waya, ruma ta lalla?a a hankali ta sauko daga kan gadonta, ta saka hannu ta ?auke jaririn daga hannun jabir, a gabansa ta ce "A'uzubi kalaimatillahi tammat" ta ?arasa gadonta ta kwantar da jaririnta, ta hau gadon tana ta ha?e fuska.

Adam ya ?an kalli jabir, kallon irin ka gani ko?.

Jabir ya girgiza kai ya ce "Rumaisa, na ji duk abun da ya faru, ina fatan Allah ya tsare gaba, amma yakamata ki bayar da ha?in kai wurin ku?utar da maman yaron nan in dai kina ?aunar ?an ta da gaske, da haka zaki tabattar mana son gaskiya ki ke wa ?an ta".

A wula?ance rumaisa ta kalli Jabir ta ce "An gaya maka ina abu dan na burge mutane ne? To kar Allah ya sa ku yadda ?in mana ina ruwana, wata?ila shi sai in gaya masa kai ban gaya maka ba, mugwaye kawai, kuma ni ba dan ta bar mini jaririn nan ba, ba abun da zan yi da ?an ku, dan ni bana ko ?aukar yara, idan aka bani ri?on ?a ma, mintsini yake sha da cizo, wannan kuwa ?ana ne, ba wanda ya isa ya ?wace mini shi ehe" ta yi maganar tana fari da murgu?a baki".

Jabir ya ce "Kan uba, haka ki ke?"

"Ai na fi haka ma, idan kun gama zaman kwa tafi, ko ku cigaba da zaman jirana in gaya muku in da take, tun da ni na saceta" tana gama maganar ta juya ta kwanta.

Jabir ya ri?e ha?a yana jinjina kai, Adam kuwa tuni ya fusata ya tashi fuuuu ya bar ?akin, a waje ya tarar da mama yayi mata sallama suka wuce.

A mota Jabir yake cewa Adam "Ban ta?a zaton azabar taurin kan yarinyar nan ya kai haka ba, ji yarinya ?arama da iya shege".

"Shawarar da bashir ya bayar, ita ce last option ?ina, idan ta?i ba da ha?in kai, zan yi abun da ba ta zato" a haka suka tafi gida suna tattaunawa.

Washegari da safe Ammi ta shirya, zata asibiti Nusaiba da Iman sun so bin ta, amma ta ce a'a su yi ha?uri ba yanzu ba, ta saka aka she?a girki, ta saka a mota, tana shirin shiga motar su tafi, ta ji yo muryar Mummy "Giwa, waye Babu lafiya ne na ganki da kulolin abinci da safiyar nan? Ko wani ne a cikin yaran amma ki ke ?oye mini?"

Ammi mamaki ne ma yakamata, ya aka yi ta fito da sassafe haka, har ta ganta.

'Ba ?aya yara duk suna lafiya, wani abu ne mai muhimmanci" daga haka Ammi ta shige motar, ba tare da sake tanka Mummy ba.
Mummy ta ri?e ?ugu ta jinjina kai ta ce "Lallai ta tabbata akwai abun da ki ke ?oyewa giwa, kuma da alama yana da muhimmanci a wurinki, bari mu ga idan na banka?o ko menene in da zaki saka kanki, zan saka a bi bayanki, domin ganin in da ki ke zuwa"

Rumaisa tana jin zuwan Ammi, suna ta hira ita da mama, amma ta yi bakam kamar bacci take yi, alhalin idonta biyu maganar ce kawai ba ta son yi.
Sai da likita ya shigo, sannan ta tashi suka gaisa da Ammi, likita ya duba X-ray ?in ta ya ce babu wata matsala, ha?ararin nata ma buguwa ce kawai, zai rubuta mata magani.

Mai sunan baba ma tuni sun zo, tare da Abubakar ya biyo yayi musu sallama zai koma makaranta.
Ammi take tambayar mama ko 'yan biyu ne saboda kamanin da suke yi, ba ta gane su, kawai dai ta lura da ?aya yana da fara'a ?aya baya yi.
Mama ta ce "Eh 'yan biyu ne, Abubakar da mai sunan babana, shi ne sa, ba ka dariya sai hamma".

Ammi ta yi murmushi ta ce "Tubarkallah Allah ya ray miki, familynki sun burgeni sosai da sosai, rumaisa a yayyen nan naki ki bani biyu mana, na je na ?ara da nawa yaran mana, ni nawa duk rasuwa suke yi, saura uku a raye"

Mama ta ce "Allah sarki, Allah ya raya wanda suka rage, ya ji?an wanda suka rasu".

Ammi ta amsa da Amin.

Aka zubawa ruma abinci, Abubakar yana bata a baki, tana ta shagwa?a.

Bashir yayi sallama, da shi da 'yan sanda hu?u cikin uniform.

Ruma ta tsaya cak tana bin su da ido, nan suka gaggaisa da kowa, Ammi ta bi bashir da kallon ko lafiya.

"Maman Boy, ya jiki? Yau zaki ganni da police, su ne case ?in binciken

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login