Showing 162001 words to 165000 words out of 182697 words
ita?"
"Allah ya baka yawan rai, ha?i?a ni mai laifi ne, kuma a shirye nake da kar?ar hukuncin da duk ka zartar a kaina. Wannan jaririn ?an wurin aisha ne matata, kamar yadda aka kai ruwa rana da surutu a kan karatu da nace zata tafi. Duk ba wannan ba ma, maganar da nake maka, yanzu haka fulani ba ta duniya, ya rasu" Adam yayi maganar kansa a ?asa hawaye na gangaro masa.
Ayshercool.
paid book ne, ?500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu bu?atar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*
Haka suka cigaba da ?ulla mugunta kala-kala suna dariya.
Wunin yau Samha ba ta bi ta kan wayoyinta ba, sai yanzu ta nutsu, ta ?au wayoyinta ta kunna, ta ajiye su a kan gado, ta shiga wanka. Daga shigarta wanka zuwa fitowar ta missed calls sun fi goma sha.
Mamaki ne ya kamata, tana shirin duba missed calls ?in, kiran Fauziyya ya shigo wayarta. ?an ?ata fuska ta yi ta ce "Wai lafiya ake yi mini wannan kiran kamar mara gaskiya?".
Fauziyya ta ce "Ke dalla can, idan ma wani rabon ne har ya wuce ki baki ?aga waya ba, kawai kin wani kashe wayoyi".
"Ke karki ?aga mini hankali, hutu na zo yi dan me za a dameni? Ina jin ki"
Fauziyya ta ce "To, ai ni zancen ne ma ban san ta ina zan yi miki shi ba, abun farinciki zan ce miki, ko kuma tashin hankali da jimami, ko kuma abun ?aure kai?"
Samha ta ?an juya idonta ta ce "Fauzi, zan kashe wayata fa".
"Katangar da ta da?e da tsaye miki, ta hanaki cikar burinki ta rushe".
"Kamar yaya kenan?".
"?anwarki ce ta mutu"
Mi?ewa Samha ta yi, ji ta yi kamar ba ta ji dai-dai ba, wai ?anwarta ta mutu.
"?anwata wacce? Wace ?anwar tawa?"
"Ahh, wacece ta sha gabanki ta hana cikar burinki na auren yayanmu, aisha ?azu aka ce wai ta rasu a wurin haihuwa, a garin da ta je karatu, amma an dawo da jaririnta, amma dai kamar akwai wani abu da ake ?oyewa ba a son a sani".
Wata iska samha ta fesar ta ce "I hope ba ?arya ki ke yi mini ba?".
Samha ta ce "Ana ?arya da mutuwa ne? Ki tambayi wanda ba sa yi miki ?arya sai ki tabattar".
"Am sorry, ba haka nake nufi ba, zan kiraki" ta kashe wayar ta cillata kan gadonta, ta hau sintiri a ?akin.
To murna za ta yi ko kuwa jimami, wata zuciyar ta ce "Ke ina ki ka gata jimami, damar da ki ka da?e ki na jira, Allah ya kawota a sama ki tsaya wani jimami? Yanzu hanya ta mi?e miki fetal, aiki ka?an ya rage miki".
Wayarta ta rarumo, sai dai ta rasa wa za ta kira ma, jefar da wayar ta yi, ta janyo akwatinta ta hau shirya kayanta, ko ba ta samu jirgi ba a mota zata koma gida gobe.
A daren ranar babu wanda ya runtsa a iyalin ammi, mussaman ita, da a kunnenta kishiyarta da facalolinta ke jifanta da miyagun maganganu.
Sabir kuwa tuni mama ta aike da shi gidan wata 'yar garinsu da take aure a kano, matar kamar ?anwa ce a wurin ammi, dan haka aka kai sabir can, duk surutun da aka din ga yi ba ta fa?i in da sabir yake ba.
Washegari ma haka aka ?ora zaman makokin aisha, samha kuwa tun da sassafe ta taho kano, sai dai ta rasa wani mood yakamata ta shiga, na farinciki ko akasin haka? Duk yadda ta so ta ji lamarin ya ratsata ta kasa, babban fatanta Allah yasa da gaske Aisha ba ta raye.
Sai da ta isa gida ta tarar da tarin mutane, sannan ta tabattar da gaske aisha ta mutu, tun daga waje ta fashe da kukan ?arya, dan kar a fuskanci wani abu, kai tsaye ta nufi cikin gidan tana kuka kamar gaske.
Nan yan makoki suka din ga rarrahinta suna yi mata nasiha a kan aisha addu'a take bu?ata ba wannan kukan da take yi ba.
Abu kamar gaske, Samha ta din ga kuka tana tumami, ana rarrashinta da ?yar ta yi shiru, ta tafi ?akin mamanta ta kwanta ta samu bacci.
Sai bayan la'asar sannan Hajiya Asama'u ta shiga ?akin ta tashi Samha.
Ta dubi Samha ta ce "Ke yanzu Samha dan aishar ta mutu ki ka zauna kina wannan uban kukan kamar ni na muty? Yarinyar da ta hanaku rawar gaban hantsi a wurin mahaifinku, har wani kukan mutuwarta zaki yi?".
Samha ta ?an duba bayan mama, ta ji babu almar wani zai shigo, sannan ta dubi mama ta ce "Mama na dole ne, ko ba kowa ba wasu san da cewa ina son Adam, idan har na nuna ban damu ba, wasu ma ai sai su ce ina murna da rasuwarta ne, nima na dole ne kukan, amma mama ya aka yi ta mutu wai? Sannan ina ?an da ta haifa ?in?"
Mama ta kwa?e baki ta ce "Mhmm, su suka san me suka yi mata dai, wai can in da ta tafi karatun a can ta zo haihuwa ta rasu, jiya nan suka zo da jaririn, ammma sun ?i fito da shi yanzu, tun jiya ake fama amma Giwa ta?i fa?ar in da yaron yake sai ?oye shi take sai ka ce ciwo".
Samha ta jinjina kai ta ce "Ta? a nan aka yi mata sutura kenan?".
"To waye ya ga gawarta, wai a can london ?in ta mutu aka binneta, haka suka ce fa, ni ko yaushe ta yi cikinma oho, na ga dai tana can tana karatu, to can ya bita yayi mata cikin? Ko kuwa da cikin ta tafi Allah masani, saboda wata lalacewa ma, ita ya turata karatu ?asar waje, ya zo yana nema ya haikewa iman".
Samha ta girgiza kai ta ce "Mama ba haka aka yi ba, batun iman wannan wani abu ne da Mummy ta shirya shi, amma yadda abubuwan ne suke wakana, akwai wani abu a ?asa, amma dai bari na yi wanka na sauya kaya".
Ta tashi ta ?au wayarta ta shiga ban?aki, lambar Khalifa ta nemo, ta kira shi, sai da ta kusa katsewa sannan ya ?auka.
Ba sallama ba komai ya ce "Ya akwai labari ne?"
"Eh kusan haka, Allah ya yi wa matar adam rasuwa ne".
"Na ji labari" ya katseta.
"A ina ka ji?".
"Kin manta fitacce ne shi? Labarin duk ya kara?e dandanlin sada zumunta".
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Haka ne, sai dai an ce a can london wai aka binneta, ba a kawo gawarta ba, sai jaririnta kawai".
Da sauri khalifa ya ce "What? Jariri kuma? How a wace ma?abartar aka binneta a London ?in? Suwaye suka halarci jana'izar ta a can?"
"I don't know, nima abun da na zo na tarar kenan" ta bashi amsa.
Khalifa ya yi dariya ya ce "Shikenan, kin zo mini da labari mai da?i, wannan ma wani abu ne na ya?ar adam".
"Amma dai ina fatan ba cutar da shi zaku yi ba, sannan ina son cire hannuna a contract ?in nan, tun da ma dai wadda ta hanani rawar gaban hantsin ta mutu, ina ga na samu chance"
Khalifa ya ce "Haka ki ke gani?"
"Eh mana, babu abun da yayi saura ai"
"Ba zai yiwu ki sa?a yarjejeniyar mu haka kanki tsaye ba, dole ki kammala mini aikina".
A fusace samha ta ce "Kai saurara, ba fa 'yar ka ba ce ni, ka daina yi mini magana da isa kana bani umarni, ka kiyayeni" da haka ta kashe wayarta tana tsaki.
Kwanaki uku aka yi aka watse daga makokin aisha, sai dai adam sam baya hayyacinsa, kana kallonsa ka san a tashin hankali yake, ko abinci baya iya ci, haka yake tafiya gidansa, ya zauna ya saka kayan aisha a gaba yana kallonsu.
Ranar da suka rabu ya tuna, da zai yi tafiya, lokacin kwananta biyu da dawowa tana yi masa magiyar ya barta ta yi tafiya, ya din ga jan kumatunta yana yi mata dariya ya ce "Cikin nan naki ya sanya kumatunki ?ara cika, kuma sun fi da?in wasa a haka" kwa?e fuska ta yi za tayi masa kuka ta ce "Dan Allah ka mayar da maganata serious please ka bari na je".
"Ki bari idan na dawo da kaina zan kai ki, kin ji fulanina".
Kamar ?aramar yarinya ta shiga turza ?afarta za ta yi kuka ta ce "Dan Allah kar ta mutu ban je na dubata ba".
Ya ?an tsuke fuska ya ce "Bana son rigima fa, ke ba ki ga yadda cikinki ya tsufa ba, kin san hatsarine ki fita a san kin dawo, a sirri fa na bari ki ka dawo, tun da kin kasa ri?e kanki, sai kin dawo wurin mijinki"
Bu?e baki ta yi ta ce "Ni haka nace maka?"
Dariya yayi mata ya ce "Idan ma baki ce ba, yanayinki ya nuna ai, tun da ki ka dawo ko waje ban le?a ba, soyayya kala-kala kawai nake sha, ki yi ha?uri jibi zan dawo in sha Allah sai na kai ki"
Idonta ne ya cika da hawaye, amam ya mayar da abun jokes, ya cigaba da ja mata kumatu yana kashe mata ido.
Da ya zo nan a tunaninsa ya dur?ushe a kan gwiwoyinsa, yana kallon kujerar dressing mirror da ta zauna, suka yi wannan abu, da washegari ya ga message ?in ta na ban ha?uri, a kan ba zata iya jiran dawowoarsa ba jikin kakarta ya tsananta da yawa.
Ya dinga zubar da hawaye yana surutai a hankali, wata irin kewarta tana ratsa shi.
Wani abu ne mai kama da bacci ya ?auke shi, kawai sai ganin rumaisa ya yi a kan kujerar, tana zaune tana ta yi masa dariya, 'Sarki mai koriyar alkyabba, ka ?ananiba dokinka" tayi masa maganar tana murmushi, daga bisani ta taso ta nufo shi, tare da mi?a masa hannu, ya mi?a hannunsa zai ri?o nata, kawai yayi firgigit ya farka yana kalle-kalle. ?an tsuke fuska ya yi, ya tuna yadda ya din ga fama rumaisa tana yi masa gizo a baya, da ?yar ya daina ganinta, kwatsam yanzu ma ta cigaba da yi masa gizon, ba dan ya ganta tare da 'yan gidansu ba, to da babu shakka zai gazgata cewar aljana ce ita.
Kusan kwanaki ukun nan, rumaisa ta ?i sakin jikinta, kusan kullum cikin kuka take a kan a dawo mata da jaririnta, tun mama tana ta tata har ta gaji ta ?yaleta, abinci ma sai an yi kamar za a zaneta sannan take ci. 'yan islamiyyarsu tawaga guda suka yo, har da malamansu suka sake zuwa dubata, amma mirsisi ta?i kulasu, ta?i magana.
Kwanaki hu?u da sallamar su, mama ta ce wa usman yakamata su je gida su yi wa ammi gaisuwar rasuwar aisha.
Mai sunan baba na jin jaka ya ce bai yadda ba, kar su zata wani abun suke nema a wurnsu, tun da sun yi musu gaisuwar a asibiti ya isa.
Mama ta ce "Kai ka san ba zamu je wurinsu domin neman wani abu ba, amma dai-dai gwargwado sun yi ?awainiya da ?anwarku, kuma babu laifi dan an bisu gida an kuma yi musu gaisuwa, shi ne abun da yakamata ai, tun da rashi suka yi. Shi dai mai sunan baba ba haka ya so ba, amma babu yadda ya iya haka ya ha?ura ya ?yalesu.
Mama ya shirya ya saka rumaisa ta shirya, ta ce usman da Aliyu suka raka su, ruma sai murna take ko ba komai, zata ga Sabir, sai jin da?i take yi, ta shirya cikin riga da hijjabi, sannan ta kawo face mask ta saka.
Usman ya ce "Meye kuma na rufe fuska?".
"Bana son a din ga kallona duk in da na je"
Ya ce "Ko kuma baki da gaskiya ba, ko kin yi wa wani laifi"
"Haba yaya usy, yaushe na dawo da zan nemi maganar ma".
Yayi murmushi ya ce "Ashe kina sane ki ke neman maganar"
Gyara zaman hijjabinta ta yi, ba tare da ta sake magana ba suka tafi.
Gidan galadima kuwa, ammi ta kar?o sabir, su iman sun kewayeshi suna kallonsa, yaron ha?urinsa har yayi yawa, ba ya kuka sai ya ga dama, sai dai yayi ta bacci.
Babu in da ya bar adam, kamarsa ?aya sak da adam, an yi masa wanka an shirya shi, nusaiba tana bashi madara a feeder.
Iman ta ce "Allah sarki rayuwa, Allah ya yi wa anty aisha rahama, mun ci buri sosai a kan haihuwar nan, duk da yadda ake ?oyewa ba a son a san da cikin, amma tayi buri a kan cikin, kusan kullum sai ta turo mini hoton siyayyar da ta yi wa baby".
Ammi ta ce "Rayuwar duniyar kenan, amma ba zan ta?a manta yadda aisha ta mutu ba, Allah ka kawo mana tsaro a ?asarmu, ka ?ara kiyaye al'ummar musulmi" suka amsa da amin.
Adam ne ya yi sallama, suka amsa gaba ?aya, su iman suka shiga gaishe shi, bai iya amsa musu ba sai jinjina musu kai kawai da yake yi.
Ya dur?usa ya gaida ammi. Ammi ta amsa masa tare da tambayarsa ya ha?uri.
Muryarsa a raunane ya ce "Alhamdilillah"
"Allah ya yi mata rahama, Sannan a cigaba da ha?uri duk mai rai mamaci ne". Ya jinjinawa ammi kai, tare da zura hannunsa a aljihunsa, Saboda vibrating da wayarsa ta fara.
Bai san mai lambar ba, amma ya ?aga tare da yin sallama.
Aliyu amsa sannan ya ce "Aliyu ne yayan rumaisa, mun zo mu yi maka gaisuwa ne, mun shigo cikin gidan bamu san ina zamu bi ba, a wurin bashir na kar?i lambarka".
Adam ya ce "Ok babu damuwa, bari na zo gani nan" ya mi?e ya ce "Ammi ina zuwa".
Rumaisa kuwa ri?e ?ugu tayi tana ?arewa harabar gidan su takawa kallo, ga motoci gefe guda kuma ga burgar dawakai, ko ina sai manyan bishiyu da ?anana, sai kalle-kalle take kamar 'yar ?auye, ga dogarai suna ta shiga suna fita, suna kaiwa da komowa a harabar.
Rumaisa ce ta fara hango adam ya nufo su, ya rame sai uban wuya, da dogon hanci, idon nan nasa jawur ya ?araso in da suke yana yi musu sannu da zuwa.
Risunawa ya yi ya ce "Mama sannu da zuwa, ya gida?".
Cikin kulawa mama ta ce "Lafiya lau, ya ?arin ha?uri?"
"Alhamdilillah"
Haka ya bi su usman duk suka gaisa, amma bai kula ruma ba, ita ma ba ya kula shi ba.
Ya ce "mu shiga daga ciki"
Rumaisa dama tun da ya zo yana fara magana, ta wani juya ?eya, irin ba ta ma san yana wurin ba, sai dai kamar yadda ta ga ya rame, haka shima ya ga tayi rama, ta fi cikowa kwanaki uku baya da aka sallameta daga asibiti.
Yayi musu jagora zuwa ciki, rumaisa ta gwalala ido, ganin kayan alatun da ke falon ammi, ya wuce da su babban falon, ya ratsa da su zuwa falon ammi, wanda bai kai wanda suka baro ba.
Yayi musu iznin su zauna, ya kira ?aya daga cikin barorin ammi, ya ce a kar?i su rumaisa. Ya ce "Bari na yi wa ammin magana".
"To ina ?ana yake?" Ta yi maganar ba tare da ita kanta ta yi niyyar maganar ba.
Banza yayi mata bai kulata ba, sai da ya juya zai bar falon, sannan ya ce "Na kai shi koyo yadda ake gaida mutane"
Aliyu ya ce "Ai da abun duka ka samu ka zaneta wallahi, mara kunya kawai".
Adam yana barin falon, rumaisa ta mi?e tsaye, ta sake zama a kan kujerar ta ce "Wayyo laushi, Innalillahi kujerar nan ta ji katifa yasin, kujerar masu ku?i daban take, har na tuna wata kujera da na gani a gidansu wata 'yar ajinmu, kujerar nan duk ?ashi, sai soso duk a waje, na ?usa ta kusa tsarge mini mazaunai"
Usman ne ya talle mata ?eya ya ce "Gaisuwa fa muka zo, ki ke yi mana surtu, shashasha" shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ?asa kamar ta Allah.
Mama ta ce "Rumaisa yaushe ki canza halaye zuwa na banza ne? Dama haka na koya miki rashin gaida mutane ko?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a ki yi ha?uri"
Aka zo aka din ga jere musu kayan abinci kala-kala, da na sha, ita dai rumaisa burinta ta ga Sabir.
Adam ya je ya tarar da ammi ta aiki su Nusaiba, daga ita sai sabir a ?akin, ya ce "Ammi kin yi ba?i".
Ammi ta ce "Suwaye, na ce duk wanda yayi gaisuwa ya tafi ina son hutawa ne".
Rasa mai zai cewa ammi yayi, dan ko sunan rumaisa ba ya son kamawa, ya ce "Yarinyar nan ce, da mamanta da yayyenta suka zo yi mana gaisuwa".
Cikin rashin fahimta ammi ta ce "Wace yarinyar kenan?"
"Wannan yarinyar da ta zo da Sabir" Sabir ?in ma da ya fa?a ji yake kamar ya kwafsa, kasancewar rumaisa ce ta sanya masa sunan.
Cikin fara'a ammi ta mi?e tana fa?in Allah sarki.
Adam ya kar?i Sabir a hannun ammi, da niyyar ya gwanyawa rumaisa, suka fito falon.
Ko ammi ba ta kalla ba, ta mi?e tsaye tana jiran Adam ya ?araso ta kar?i Sabir, amma ya canza hanya ya yi wani wurin. Ai ba su ankara ba rumaisa ta bi bayansa da gudu tana "Ka tsaya in ?auke shi, ka zo ka bani ?ana".
Ayshercool.
paid book ne, ?500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu bu?atar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*
Da fari bayan bayyanar rumaisa, mama ta zaci ruman nutsuwa ta ?an ratsata, amma ina sai ta ga akasin abun da ta yi tsammani, halinta yana nan yadda yake, Aliyu na ?wala mata kira amma ta rufawa takawa baya.
Murmushi ammi ta yi ta ce "?yaleta, shi ma dai neman magana ne ya sanya ya ?auke shi zai fice, da na san haka zai yi da ban bashi sabir ?in ba".
Usman ya ce "Ai gara da ya hanata, ?in gaishe shi ta yi, sai tambayarsa ina ?an ta dan ba ta da kunya"
Mama ta girgiza kai ta ce "Rumaisa ai sai fatan Allah ya shirya. Hajiya ina wuni ina gajiya?" Ta yi maganar tana mayar da kallonta ga Ammi
Ammi ta ce "Lafiya lau Alhamdilillah, ya gida ya iyali?".
"Kowa lafiya ?alau, ya kuma ?arin ha?urinmu".
"Ha?uri mun gode Allah"
Mama ta ce "To Allah ya sa ta huta, Allah ya rahamsheta"
Ammi ta amsa da "amin ya rabb, ya jikin rumaisa kuwa ina fatan ta wartsake gaba ?aya"
Mama ta ce "Jikinta dai da sau?i, amma ta?i sakin jiki kullum kuka ita sabir, yau ne ma ta ?an saki jiki har da hira da ta ji an ce za