Showing 180001 words to 182697 words out of 182697 words
wanke adam.
Ayshercool.
*Paid book ne, ?500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*
Masifa mummy take kamar ta ari baki, duk ?o?arin da ta yi, amma turaki lokaci ?aya ya watsa komai.
Takawa ma mamaki ne ya kama shi, da ganin abun da turaki ya ce, ya wanke shi ya ?au laifin, bai jira komai ba ya tafi gidan turaki.
Bayan an yi masa iso ya shiga sun gaisa da turaki, ya dubi turaki ya ce "Allah ya baka yawan rai, na ga abun da ka gayawa manema labarai, amma ni yakamata na ?au wannan laifin na magantu ba kai ba".
Turaki ya murmusa ya ce "A'a mu ?in ne dai yakamata, wambai ya zo nan ya nemi mu sanya ka fito duniya ka bayar da ha?uri, a kan abun da ya faru, wai sunan masarauta na neman ?aci saboda kai, hakan ya sanya ni na bayar da ha?urin, kar ka ji komai"
"Amma Allah ya taimake ka..."
Turaki ya girgiza wa adam kai ya ce "An rufe wannan babin, ina ?a ta?"
Adam ya ce "Wace ?ar ta ka?"
Turaki yayi murmushi ya ce "?a ta yarinyar da ta kawo jikana, rumaisa"
Adam ya ?an tsuke fuska ya ce "Tana gidansu"
"Allah sarki, duk lokacin da aka ganta, ace muna gaisuwa, Allah ya ?ara mata lafiya" turaki yayi maganar yana murmushi, yana tuna lokacin da rumaisa ta zauna a gabansa tana ta zuba shirme son ranta.
Haka adam ya tashi ya tafi, yana ta tunani kala-kala a ran sa. Idan har turaki zai fito duniya ya kareshi, zai iya fuskantar duniya ya ce duk mai cigaba da zarginsa idan yana da hujja. Kansa na kashe aisha ya je ya nema mata hakkinta a kotu.
'kar dai shawarar wannan yarinyar mara kan gado zaka ?auka, ta kai ka ta baro' wata zuciyar ta garga?e shi, tsaki ya ja ya kawar da wannan tunanin a ransa.
Maganar da turaki ya fito ya yi, ta ?ara yamutsa hazo, kowa da abun da yake fa?a, yayin da hakan ya ?ara tunzura wambai, turaki ya ?ara zubar musu da mutunci ta hanyar kare adam.
Yau kwanaki kusan bakwai rabon rumasa da jaririnta, dan haka ta shiga damuwa ba ka?an ba, tana ta tunani daban-daban a zuciyarta. Wata irin ?ishirwar son ganin yaron ke damunta.
Ta gama shirinta tsaf za ta tafi makaranta, ta fito daga gida har ta nufi hanyar makaranta, ta kalli ku?in makarantarta a hannunta, kawai ta canza hanya, ta nufi titi.
Ta san ku?in hannunta ba zai kai ta gidansu takawa ba, dan haka ta sa?i hanya da ?afafuwanta ta dinga tafiya kamar mara hankali.
Tun da sanyin safiya, har rana ta ?aga ta fara jin zafinta sosai a jikinta. Idan ta gaji ta zauna ta huta, idan ta huta ta tashi ta cigaba. Sai da ta ci fiye da rabin tafiyar sannan ta samu napep ta yi masa magiya ya ?auke ta, shi ma in da ya ajiyeta da sauran tafiya, ta sauka ta cigaba.
Sai dai da ta ?arasa, tana zuwa ?ofar gidan, security suka tare ta.
Ta kalli wanda ya sha gabanta ta ce "Wucewa zan yi"
"Ki je ina?" Ya tambayeta.
"Ciki mana wurin ?ana, ko ba ka gane ni ba ne?".
Ya ce "Na gane ki, sai dai an ce kar mu sake barinki ki shiga idan ki ka zo?"
Cikin mamaki ta kalli securityn ta ce "Waye ya ce kar a sake barina na shiga?"
"Takawa, shi ya ce kar ki sake shiga idan kin zo in ba shi ya ce ba"
"Kam bala'i, wai wannan wane irin mutum ne, shi wane irin azzalumi ne, idan har ba zan din ga shiga ba, ya bani ?ana mana, ai dai ya san ba maula ce take kawo ni ba ko?"
"Ke da shi ne wannan, matsa daga nan"
Wata irin zuciya ta turnu?o rumaisa ta ce "Wallahi ba in da zani sai an bani ?a na, wallahi yau sai na shiga gidan nan, wane irin mugun mutum ne shi, ba shi da imani ba shi da tausayi, wallahi sai na shiga sai dai ku kasheni" ta yi maganar tana tunkarar gate ?in.
Tare gate ?in ?aya yayi, cikin tsawa wani ya ce mata "Ki ka motsa daga nan sai na harbeki"
"To ka harbenin mana, sai me? Allah sai na shiga"
Gaba ?aya ta rasa abun da za ta yi, ta fashe da kuka, saboda uwar wahalar da ta shawo, kan ta samu ta zo, amma ta tarar wai an hanata shiga.
Ta fi mintuna talatin a tsaye a rana tana kuka, ?aya daga cikin masu gadin ya ce "Wannan wace irin jarababbiyar yarinya ce haka?"
"Kai ne baka santa ba, kwanakin baya ta ta?a zuwa gidan nan, zata aikata fiye da abun da ta yi yanzu"
Kamar daga sama, ta hango shi yana tunkaro ?ofar gidan, sanye da ?anan kaya, kunnensa ?aya da Bluetooth, fuskar nan tasa fayau ya yi ?iba abunsa, kan ya ?arasa gate ?in rumaisa ta tashi da gudu, ta je ta ri?e rigarsa tana kuka.
Sororo yayi yana kallonta, "Shi ne kace idan na zo kar a sake barina na shiga, ka san da haka ka kar?e mini yarona? To ka shiga ka ?auko mini sabir ba zan sake zuwar muku gida ba"
?aya daga cikin security zai yi magana, ya ?aga masa hannu ya dakatar da shi, ya kalli rumaisa ya ce "Wane jaririn ki ke magana a kai?"
Waro ido rumaisa ta yi ta ce "Ni zaka rainawa hankali ka mayar mahaukaciya, wato ma baka san wane jaririn nake magana a kai ba, wallahi sai na ?ebo maka ?an sanda, ko kuma tun da kai ma ?an sanda ne, na san ha?a baki zaku yi, al?ali zam je na gaya wa, kuma ka bani ?ana ba zan sake zuwar muku gida ba"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, mu shiga ki ga ?an na ki, sakar mini rigata".
"Wallahi ba zan cika ka ba, ka gudu su hanani shiga" ta ?ara ri?e masa riga, suka nufi gate ?in.
"Ranka ya da?e, Yalla?ai ya ce kar a sake bari ta shiga".
"Ni kuma na ce sai ta shiga, ko nima an hana ni shiga ne?"
Ya girgiza kai, suka bu?e gate ?in, suka shiga, sai da suka zo ?ofar shiga sashen ammi, sannan ta saki rigarsa ta shiga ciki da sauri.
Sai dai tana shiga babban falon ammi, abun da ta gani ya razanata.
Turus! Ta yi ta tsaya, Adam ta gani a zaune sanye cikin suit farare, da shi da ammi a falon, sabir a kan kujera yana barci.
Ta waiwaya ta kalli hanyar da ta shigo, sannan ta kalli in da Adam yake.
Ammi ta ce "Rumaisa daga ina haka?"
Ta ?arasa ta zauna, safarta tayi futu-futu saboda tafiyar ?afa, ta zauna ta ce "Tun safe nake tahowa, da ?yar na zo gidan nan, dan na ga sabir, amma da na zo aka hanani shigowa, wai ya ce idan na zo kar a sake barina na shigo, sai kuma na ganshi ya zo wucewa zai shigo gidan nan, tare muka shigo na bar shi a waje, amma kuma da na shigo na ganshi a nan a zaune, a waje da ?anan kaya na ganshi, amma kuma a nan na ganshi da wasu kayan". Tayi maganar tana kallonsa.
Adam bin rumaisa ya yi da kallo, yana mamakin anya kanta ?aya, jin ta ce da ?afa ta taho, kuma yanayinta ya tabattar da hakan.
Ammi ta ce "Ohh Mahmud ya shigo gari kenan?"
"Waye Mahmoud? Ba shi na gani a waje ba kenan?".
"Ba shi ki ka gani ba" Ammi ta bata amsa.
Rumaisa ta gyara zamantaz tana shafan kan Sabir, sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce "Allah sarki, Allah ya sa idan na fita na ganshi na bashi ha?uri ban san ba shi bane ba, na yi ta masa masifa*.
"Amma rumaisa ba makaranta zaki je ba na ganki da uniform?".
"Makaranta zani, amma na kasa jurewa, ba bu abun da nake so sai in ga sabir, amma na zo wai an hanani shigowa, ban da dalilin sabir ma ni mai zai kawoni gidan nan, ina ga ma alhakin yaran mutane da nake cin zali ne ya kamani, Allah ya jarrabeni da son yaron da ake wula?anta ni a kansa, bakomai wataran sai labari"
Maimakonsa ammi ta ji maganganun rumaisa sun yi tsauri, sai ma wani irin tausayinta da ya kamata, lallai rumaisa tana cikin jarrabawa ta gaske saboda sabir.
Ammi ta ri?e hannunta ta ce "Rumaisa, babu mai wula?antaki a kan sabir, sabir ?anki ne, ki yi ha?uri zan ?au hukuncin da ya dace a kan Adam, amma daga yanzu duk lokacin da ki ke son ganinsa, akwai lambata a wayar mamanki, ki kirani ni kuma zan saka a kawo miki shi, ko na kawo miki shi da kaina, kin ga yanzu kin yi missing school, bari ya mayar da ke gida, tun da dama wurin aiki zai koma"
Rumaisa ta girgiza kai ta share hawaye ta ce "A'a, zan koma gida da kaina, kuma ba zan sake zuwa gidan ba, balle masu gadi su ci mutuncina a waje kamar yadda aka yi mini yau kamar ?ar maula" tayi maganar tana sake fashewa da matsanancin kuka.
"Kiyi ha?uri, in sha Allah hakan ba zata sake kasancewa ba, babu mai sake wula?anki a kan sabir, ko shigowa gidan nan, tun da gidanku ne, bari a kawo miki ruwa ki sha, ki ci abinci sai ya mayar da ke gida".
Ta girgiza kai ta ce "A'a na gode, dama sabir kawai nake son na gani, ban ci wani abun ba balle yayi tunanin ina fakewa da son ganin sabir ina zuwa kwa?ayi".
Kalaman rumaisa ya tabattarwa da ammi rumaisa ba wauta da ?uruciya kawai ta iya ba, ta san mutuncin kanta, kuma tana girmama kanta.
Ta ce "Ai na baki ha?uri, kuma na gaya miki zan ?au mataki a kansa, kuma ko me zai ce ki rabu da shi, abun da ki ka yi masa a rayuwa bai isa ya biyaki ba, ladanki yana wurin Allah, tashi mu je ki sha ruwa ki sake karyawa, wannan tafiyar da ki ka yi na san kin gaji sosai" da ?yar rumaisa ta amince ta tashi ta bi ammi, dan tana ganin mutuncinta da darajarta, amma ba dan haka ba, sai ta ce ko iskar gidan ba zata sha?a ba balle ruwa, saboda cin mutuncin da aka yi mata.
Ammi ta kai rumaisa falonta, ta saka a ka kai mata abinci, ta fita ta bata wuri dan ta ci, ta dawo ta tarar da Adam a falo.
Rai a ?ace Ammi ta ce "Ban ji da?in abun da ka yi ba ?warai da gaske, muzanta yarinyar nan da aka yi a waje, a kan me zaka ce kar a sake barinta ta shigo?"
Cikin ladabi Adam ya ce "Tuba nake, ba na yi haka ne domin ?ata miki rai ba, amma yawan zuwanta gidan nan akwai matsala, bana son ta shiga cikin wani hatsari saboda ni ko ayi amfani da ita wurin cutar da waninmu"
Ammi ta ?an yi shiru ta ce "Ban ?i ta taka ba, amma a ?uruciya irin ta ta, da irin ?aunar da take nunawa gudan jininka bai kamata a ?auki wannan matakin kai tsaye a kanta ba, ba tare da bin wasu hanyoyi da ba zata ga an wula?antata ko cutar da ita ba. Tana da matu?ar wayo da kaifin basira, dan haka abun da ka yi mata dole ta kirashi da wula?anci da tozarci, kar ka sake yanke makamancin wannan hukuncin ba tare da izinina ba".
Ya risuna ya ce "In sha Allah"
"Ka biya ka fara ajiyeta a gida, ka sanar musu halin da ake ciki, don a saka ido sosai a kan ta ta daina missing makaranta, kuma kar ta sake yin wannan doguwar tafiya haka a ?afa ita ka?ai"
Ya jinjinawa ammi kai.
Rumaisa ta fito, idanun nan sun yi ja ta ce "Ammi zan tafi".
"Maman Sabir har kin gama, bari ya mayar da ke gida" rumaisa ta kalli Adam sannan ta kalli ammi za ta yi magana, ammi ta girgiza mata kai ta ce "Ba'a jayayya da umarnin giwar galadima" Ammi ta yi mata maganar cikin garga?i, haka ya tilastawa rumaisa yin shiru.
Adam ya mi?e yayi gaba, rumaisa ta dur?usa ta sumbaci goshin sabir, sannan ta bi bayan Adam.
Kamar yadda ransa yake a ha?e, haka ita ma ta tsuke ta ta fuskar, babu alamar wasa da yarinta.
"Laa ka ga, bawan Allah" Adam ya ji maganar rumaisa, tsayawa yayi ya waiwaya bayansa, da gudu ya ga ta nufi jikin bishiyar dabinon da ke tsakiyar harabar gidan. Mahmud ne a tsaye yake waya, amma ya katse wayar ya zubawa rumaisa ido yana jiran ta ?araso.
Ta ?arasa tana ?an haki ta yi murmushi ta ce "Ashe ba kai ne shi ba?"
Mahmud ya ce "Shi wa?"
Rumaisa ta nuna masa in da Adam yake.
"Na zata shine da na ganka ?azu, idona ya rufe sosai da ?acin rai, ga gajiya kuma kuna kama sosai da sosai, dan Allah ka yafe mini na yi maka rashin kunya a gaban mutane"
Yayi murmushi ya ce "Kin ga jaririn naki?"
"Na ganshi, Allah ya saka maka da alkhairi da ban ganshi ba yau, da ina ga mutuwa zan yi. ?a na ne fa anty aisha ta bar mini shi, amma ya ?wace shi kuma wai ya hana ni shigowa gidan nan"
"Wace aishar?"
"Kai baka san ta ba? Kai ba ?an nan gidan bane?".
"Eh ?an nan gidan ne, amma bana ?asar jiya da daddare na dawo".
"Au ho, to in gaya maka sace ni aka yi a katsina, sai aka sato anty aisha matarsa, ta haihu ta rasu ta bar mini jaririn na ku?uto da ?yar, bayan na yi kwanaki ina wahala, amma ya ?wace ?an kuma wai idan na zo kar a sake barina na shigo, dan Allah wannan ba mugunta ba ce ba?"
Mahmud ya yi murmushi ya ce "Bai kyauta miki ba gaskiya"
"To kai baka ta?a zuwa sashin ammi ka ga jaririn ba, au ashe fa ka ce jiya ka dawo, ba ka ga ?an nawa ba, mai kyau tubarkallah, ai na san ammi zata nuna maka shi ma, tunda a gidan nan ka ke"
"Eh a gidan nan nake, amma ni ba a sashinsu nake ba, ni ?an Mummy ne".
"Wacece kuma hakan?" Ta tambayeshi tana ?an gyatsine fuska.
"Babata ce, ko baki san mata biyu ne a gidan nan ba? Anyway na ga kamar jiranki yake yi, ki je kar ya zo nan wurin ya karairayaki, shi yafi masa komai sau?i"
Cikin fitsara rumaisa ta ce "Wallahi wuce nan, na gode sosai ba zan ta?a manta taimakon da ka yi mini ba yau, kuma ka na da kirki fiye da wancan mutumin, dan Allah ka je ka ga ?ana a wurin ammi, sunanshi Mahmud ana ce masa sabir" tana maganar ta yi gaba tana murmushi.
Turus Mahmud yayi ya bi rumaisa da kallo, Adam ya sanyawa ?an sa sunan Mahmud? Ya tambayi kansa, dan abun da mamaki.
Wurin motar adam ta nufa, da tuni ya kunnata, ya fito ya saka ana karka?ewa motar ?ura.
Ya ?arewa rumaisa kallo ya ce "Bawanki ne ni da zaki shanya ni ki tafi yawon surut?".
Ta kalleshi ta ce "Ba yawon surutu na tafi ba, godiya na je yi masa na bashi ha?uri. Ya nuna mini karamci saboda ni ?an adam ce bai koreni ba ?azu da na rasa nutsuwa ta ina kuka ba, ya taimaka mini na samu abun da nake so". Ta yi maganar irin ko maganar ta yi masa da?i ko kar ta yi masa bai shafeta ba.
"Tun daga lokacin da ki ka sake shigowa rayuwata, ki ke ta wasu irin halayya da son nuna lallai akwai wani abu a tsakanina da ke, ina ?aga miki ?afa albarkacin yaron nan da kuma ?uruciyarki, idan ki ka cigaba da wannan abubuwan ki ka shiga trap ?i na zaki sha wahala na gaya miki, and as from today kar ki sake zuwar mana gida, abun da ki ka yi Allah ya baki lada, bana bu?atar sake ganinki a cikin gidan nan da sunan kin zo ganin yaron nan, idan kuma ki ka cigaba da zuwa zan nesanta shi da ke, nisantawa mai tazarar gaske da ba zaki iya cimm masa ba, dan haka idan ma wani abun ne a ranki ya sanya ki ke bibiyarsa, ki saka abun da na gaya miki a ranki. Idan har zaki cigaba da bibiyar yaron nan, za'a iya amfani da ke a cutar da shi, dan haka bana bu?atar sake ganinki a kusa da shi" yayi maganar cikin kashedi.
Cak ta tsaya ko ?wa?w?waran motsi ba ta yi, sai wasu irin hawaye da suke zubowa daga idonta.
Ayshercool