Showing 87001 words to 90000 words out of 182697 words

Chapter 30 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22394

uwatta ce. Abin yayi ta bawa ruma mamaki, ita a gida unguwarsu wa ma ya damu da wani, da za a din ga tambayarka waye wannan.

Ko da suka dawo gida ma, ruma a hankali take sakin jiki da lawisa, suka fara aiki tare suna ?an ta?a hira.

Wajen sha ?aya na safe, lawalli ya ?auki Aliyu a babur ?in sa suka tafi can wani ?auye, in da a nan wasu daga cikin gonakin nasu suke, wurin gidan wani kawunsu da suke kira da baba Habu.

Ruma ta zazzage kayan da ta zo da su tana sake ninkewa, bayan ta gama ta ?auko wayar nan ta ta, ta fara kallon hotunan ta.
Lawisa ta zauna a kusa da ita tana le?awa. Gwaggo ce ta kira lawisa, ta tashi ita kuma ruma ta cigaba da kallon wayar.

Hotuna ne da videos da ta din ga yi ciki har da wani sashe na wannan jakar ta bullet da ?aya daga cikin mutanen nan ya rataya, sannan a hotunan akwai in da gefen fuskar ?aya daga cikinsu ta fito.
Ruma ya ajiye wayar tana tunin wasu abubuwa da suka dabai baye mata kai ta kasa gane kansu.
Bindiga dai jami'an tsaro ne suke ta'amalli da ita, amma ta yaya za ayi ace da saninsu ana shiga da fita da su ba tare da sun tsawatar ba?' ajiye wayar ta yi, tana son ?ara nutsawa cikin tunani, amma kwanyarta ta gaza bata komai.

"Ruma zaki je rafi, muje ki ga ruwa da duwatsu".

Gwaggo ta ce "Ke kar ki kaita ki wahalar da ita mana"

Ruma ta ce "A'a gwaggo zan je" tayi maganar tana mi?ewa tsaye, ta saka hijjabi suka sake fita.

Wani ?an madaidaicin rafi suka je, 'yan mata wasu na wanki a gefe, wasu kuma suna ?iban ruwa. Ruma ta samu na yi, ta din ga ?aukar hoto, ta din ga tsalle-tsalle a wurin, yanayin ya burgeta.

Kan wani ?an dutse ta hau, can nesa ta hango wani wuri ba?i?irin kamar an yi gobara. Ta kalli lawisa ta ce "Lawisa, can gobara suka yi ne?"

Lawisa ta ce "Wallahi wasu fulani ne suka kafa sansani a wurin, cikin dare aka kawo hari, aka ?ona musu shanunsu, suka ce manoma ne suka yi musu ake ta rigima, da ?yar abin ya lafa"

"Kaii aka ?ona musu shanunsu, kuma da gaske manoman ne suka yi musu?"

Lawisa ta kai bakinta kunnen Ruma ta ce "Ke 'yan ta'adda ne fa suka yi musu, amma aka ce fa?an fulani da manoma ne, amma kar ki ?aga hankalinki fa, mu nan haka lafiya lau muke zaune, an fi tashin hankalin a wuraren su Baba habu".

Ruma ta yi ajiyar zuciya ta ce "To kuma ba a gayawa 'yan sanda ba?"

Lawisa ta ?walo ido ta ce "'yan sanda, a ina zamu ga 'yan sandan ko sun zo me zasu yi, wataran dai sojoji na zuwa ayi ta harbe-harbe abin tsoro"

"Zo mu je wurin, in ga wurin sosai da sosai "

"Ke, Aikuwa tsaf fulanin nan zasu illata mu, yadda suke a ?ule zo mu tafi gida, na cewa Gwaggo ba zamu da?e ba"

"Ke ki tafi, ni ba yanzu zan taho ba".

"To ai baki san hanya ba"

Ruma ta ce "Idan na ?ata na tambayi hanyar, ni wurin can nake son zuwa " tsoro ne ya kuma kama Lawisa ta cewa ruma "Ki zo yanzu mu koma gida, akwai hanya mai sau?i da zan bi da ke muje wurin ".

Ruma ta ?an rausayar da kai ta ce "Ina fatan ba ?arya ki ke yi mini ba, ina son in ?auki hotunan wurin in ?au komai, yadda zan ji da?in bayar da labari, kuma idan na bayar a yadda tunda ina da hoto".

Lawisa ta yi murmushi ta ce"Haka ne, karki damu" ta lalla?a ruma suka koma gida.

Sai dai a washegari ruma ta faki idon mutanen gidan ta fice, kai tsaye wurin da aka yi wa fulanin nan ?one-?one ta je. Sai dai tafiyar da nisa sosai, wurin shiru ba kowa sai ragowar abubuwan da aka ?ona, da tsirarun bukkoki a can gaba ka?an, wurin kamar an yi wata annoba.

"Ke wace wannan me ki ke yi a wurin nan?" A hankali ta waiwaya taga wani dattijo a tsaye s bayanta, hannunsa ri?e jallon ruwa.

"Sannu baba" ya amsa da yauwwa.

Yana cigaba da ?arewa ruma kallo.

"Baba gidan 'yan uwanmu mu ka zo, na hau wani dutse na hango nan shine na ce bari na zo na gani, Allah ya mayar da alkhairi amma kun gayawa 'yan sanda abin da ya faru?"

Kallon ruma yake, yadda take magana fiye da shekarunta.

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Gidan wa ki ka zo a garin nan?"

"Gidan dagaci ne, ?an uwan babanmu ne" ya jinjina mata kai ya ce "To mun gode da jajen da ki ka yi mana, amma maza ki tafi kar sauran mutanen rigar nan su ganki".

"To in sun ganni mai zai faru me na yi musu?"

"Kasheki za su yi, dan haka muje na raka ki hanya" babu musu ya saka ruma a gaba har zuwa cikin gari, suna tafe suna hira ruma tana addaba masa da tambayoyinta da ba sa ?arewa"

A hanya suka yi sallama, ya koma ita kuma ta ?arasa gida.

Gwaggo duk ta tashi hankalinta rashin ganin ruma, ita kuwa ko a jikinta ta ce kallon gari ta fita yi.

Sai dai a tattaunawar ta da dattijon nan ya gaya mata wasu abubuwa da suka sake ?aure tunaninta.

****
Hajiya Lubabatu ce ta tsaya a tsakiyar ?akinta, tana kallon hoton Galadima mai ci a yanzu, wands ya kasance mijinta da yake can ?asar Germany yana jinya, ta ?an lan?wasa yatsan hannunta ?aya sannan ta furta "Ka yi ha?uri ranka ya da?e, bani da isasshen lokacin da zan cigaba da ?atawa a kan ka, goben ?ana ita ce a gabana yanzu " ta yi maganar tamkar na cikin hoton yana jinta.


Khalifa ne zaune a kan kujerar da take kallon wadda mahaifinsa yake, mahaifinsa sai murmushi yake sannan ya nisa ya ce "Ina jinka Khalifa".

"Yauwwa daddy, kamar yadda nayi maka bayani, na tsara komai kuma ina da ya?inin komai zai tafi dai-dai da yardar Allah".

"Haka ne, ban?i ta taka ba, na kuma yabawa ?o?arin da kake yi, amma gani nake komai zamu yi wa yaron nan ba zamu huce ba, yanzu haka bayanai sun zo mini yana garin Abuja, sai dai ban san wurin wa yaje ba, idan har ya cigaba da abin nan EFCC zata bincike ni, kuma daga haka ya ?ata siyasata, ya ci mutuncina kuma ya ?ata gobenka".

Khalifa ya gyara zama ya ce "Daddy, ai shiyasa nake ta ?o?arin aikin nan ya tabatta, ta yadda zan kau da hankalinsa a kan komai, ya tattarashi a wuri ?aya, ka harda dani, abin nan zai yiwu daddy, kuma akwai nasara a ciki".

Senator wakili ya yi murmushi ya ce "To shikenan, ina saurarenka, sannan duk abin da kake bu?ata, i will make sure that I provide it".

"To Shikenan Daddy, godiya nake "

Yayi murmushi tare da jinjina masa.

***
Kwanakin su ruma uku, ta saki jikinta, duk da kullum sai sun yi waya da mama, yawo kuwa kamar ta ci ?afar kare, har gona suke zuwa ita da Lawisa, har ta saba da sirikan gwaggo da yaran ma?wabta.
Sai dai gona ?aya aka samu aka sayar, a gonakin baban nasu, kuma shima dubu ?ari bakwai kawai aka samu, saboda yanayin in da gonar take babu tsaro sosai.
Ana i gobe zasu dawo kano, Gwaggo ta shirya ruma, ta ha?ata da lawisa lawalli ya kai su can wani ?auye, gidan wani ?anin mahaifinsu, wai su gaishe su.
Aliyu sai mita yake yana tambarat gwaggo yaushe su ruma za su dawo, saboda da sassafe yake son su kama hanya, gwaggo ta ce kar ya damu, gobe da safe zasu dawo.

Har washegari da safe su ruma ba su dawo ba, Aliyu ya ce "Gwaggo, wai haryanzu su ruma ba zasu dawo ba, tafiya fa zamu yi, bana son rana tayi mana".

Gwaggo ta ce "Gadanga, sai dai kayi tafiyarka kai ka?ai, ina sane na tura ruma can, sai za a koma makaranta zan dawo da ita da kaina, yanayi ya nuna mini babu isasshen tsari a jikinta, kuma akwai bu?atar ta zaga ta san dangin mahaifinta suma su santa"

Aliyu ya ce "Amma gwaggo ba mu yi haka da mama ba, dan Allah kar ki yi mini haka".

Gwaggo ta ce "Mhmm, sai kuma ka yi, na gama magana"

Saroro Aliyu ya yi ya ma rasa mai zaice, ya ciro wayarsa ya kira mama a waya.

Yana kira mama ta ?aga ta yi sallama.

"Mama, gwaggo fa ta tura ruma wani ?auye, wai ba zamu taho tare ba sai an koma makaranta zata da wo da ita".

Gwaggo ta ?an ?aga murya ta ce"Eh, ni na ce ba zata dawo yanzu ba, sai na gama nema mata tsarin jiki, sannan kuma ta san dangin mahaifinta, tunda ba zuwa take ba"

Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Aliyu ka taho kawai, idan ka tsaya zai zama abin magana, ?yaleta taho"

"Amma mama...

"Kar ka ce komai, in dai ruma ce, da kansu za su tattaro su dawo da ita, ka taho ka barsu".



Ayshercool.


*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*






Abin da gwaggo ta yi ba ?aramin ?atawa Aliyu rai yayi ba, da ya san haka ne da ba zai ta?a bari ta saka a kai ruma ko ina ba, daga zuwa ziyara kawai ta ri?e 'ya wai sai wani lokaci.

Ya sake duban gwaggo ya ce "Gwaggo, ruma fa ba zata yarda ta zauna a garin nan ba, rigima za ta yi miki idan ta dawo ta tarar na tafi na barta".

Gwaggo ta ce "Babu komai, na san yadda zan shawo kan kayata, amma a yanzu dai ba in da zata".

Takaici ya ishi Aliyu, ya bi gwaggo da kallo.

"Gadanga ko dukana zaka yi ne? Na gama yanke hukunci, idan kuma kaima zaka zauna ne ni haka nake so, sai mu zauna idan lokacin yayi sai ku tafi duka".

Tabbas ba dan gobe yana da test mai muhimmanci a makaranta ba zama zai yi, ya saka lawalli a gaba sai ya kai shi ya ?auko ruma, amma ba yadda iya ya ?auki jakarsa ya fice.

****
Har Adam yayi kwanakinsa uku a birnin tarayya, bai iya aikata komai ba, saboda da ya fita da niyyar zuwa wani wuri, sai jiki ya hau rawa kai ya hau ciwo, ga ruma da ta addabawa rayuwarsa ya kasa mantawa da ita, komai yake yi sai ya din ga ganinta.
Bayan ya cika kwanaki hu?u, ya kira Ammi yayi mata ?aryar bai gama abin da yake yi bane, sai dai tattaunawar haka aka yi ta babu shi, duk da halartarsa tattaunawar na da matu?ar muhimmanci.
A kwana na biyar ya kira direbansa a waya, ya ce ya zo da mota ya same shi a hotel ?in da yake.
?arfe biyu direban ya sameshi, sai dai a wannan karon cikin ikon Allah tun da ya fito sau ?aya kan ya sara, jiri ya ?an ?ebe shi, amma ya tattara nutsuwartsa, yana addu'a, ya nufi motar.
Suka gaisa da direban nasa, yayi masa ya hanya, daga nan ya ce ya gaya masa in da zai kai shi.
Mintuna ashirin ce ta kaisu, a harabar wata plaza suka yi parking, Adam ya bu?e motar ya fita.

Wani matashi ne zaune wanda zai yi sa'an Adam, yana danna computer, yana ganin Adam ya mi?e cikin girmamawa yana murmushi ya ce "Barka da zuwa"

Adam ya ?arasa yana murmushi, ya mi?a masa hannu suka gaisa, sannan ya zauna.

Matashin ya kalli Adam ya ce "Adam, ya aka yi an shirya zama da kai, amma ba ka yi attending ba?, na din ga kiran wayarka ba ka ?agawa, har wayar ma ta daina shiga gaba ?aya?"

Adam ya ?an taune lips ?insa na ?asa ya ce "Am sorry Habib, wata matsala aka samu, amma komai normal yanzu in sha Allah".

Cikin kulawa Habib ya ce "Are you safe?"

Adam ya jinjina kai sannan ya ce "Me aka tattauna, wace matsaya aka cimma?"

Habib ya ?an rausayar da kai ya ce "To, mun tattauna yadda yakamata, amma dai kamar yadda na yi maka bayani da farko, ko da ka fito ?arara ka bayyana lamarin nan, ko an je kotu za a sake su, saboda haryanzu baka da wata cikakkiyar hujja ta zahiri da zaka kafa, yanzu ko kun yi wani abu a kai, ya riga ya gama shiri, da tattaunawa da lawyoyinsa, ya shirya tsaf da ka yi attacking zai yi depending, yanzu abin da yafi shine ka sake mayar da hankali sosai da kai da abokan aikinka, ku samo hujja ta gaske, ta zahiri da za ayi amfani da ita, nima zan shirya tsaf domin cimma nasara ni da tawagarmu"

Adam yayi ajiyar zuciya tare da dafe goshinsa, ya sake ?agowa ya kalli Habib ya ce "Duk wata hanya da zan bi domin neman hujjar kama mutumin nan an tosheta, kuma kullum kallon mutunci ake masa, ana sake bashi girma tare da shigar da shi cikin al'amuran ?asar nan, bayan su ne babbar matsalar mu"

"Adam, tun da ka ga haka, ba shi ka?ai bane, ko dai an san me yake yi ake rufa masa asiri, ko kuma akwai wasu manyan da suke aikin tare "

"Haka ne, abin da nake tunani kenan nima, amma babu komai in sha Allah zamu yi nasara, zan cigaba da ?o?ari, ina son magana da saifu ma, zan zauna a garin nan sai Allah ya kaimu monday zan koma kano".

Habib ya ce "To shikenan, Allah ya yi jagora, gashi ko shayi ban baka ba"

Adam ya girgiza kai ya ce "Kar ka damu"

Daga haka Adam ya tashi ya fita, ya saka direbansa ya mayar da shi masauki. Sam ya ?i yadda yaje gidan sa, saboda wani Dalili nasa.

***

?auye ne sosai in da aka kai ruma, sai dai mutane masu matu?ar karamci da girmama ?an Adam, tamkar za su goya ruma, dan wasunsu duk basu santa ba, sai dai sun san mahaifinta sosai tunda ?a ne a wurinsu.
Garin sun yi noma sosai, sai dai an girbe an tare shi a cikin gonaki, ba a kwashe an kai gida ba, ga yanayin garin kamar yanayin garin da aka yi wata annoba.
Wani wurin a ?one, wani wurin dai gashi nan.
Tun da safe ruma ta fara cewa ita azo a mayar da ita gidan gwaggo, yau zasu koma gida ita da yaya Aliyu, amma dattijon da ya kasance ?anin kakanta ne ya ce "Ai jikata ba ke ba tafiya, sai hutun makarantar bokonku ya ?are, kina nan tare da mu"

A ?an razane ruma ta ce "Saboda me?"

"Haka gwaggonki ta ce"

"Ni gaskiya ba zan iya zama a garin nan ba, gida nake so na koma na ga mama, na gaji, ni ku mayar da ni gida" ta yi maganar tana kuka.

Matarsa da ake kira da iya ta ce "Haba rumaisa, muma fa duk iyayenki ne, muna ?aunarki sosai, ki kwantar da hankalinki kin ji, za a mayar da ke, idan ki ka matsa zasu iya ?waceki gaba ?aya, 'yan kwanaki zaki yi a mayar da ke"

"Ni mama nake son na gani".

"Ki yi ha?uri, za a mayar da ke in dai wurin mama ne" An kai ruwa rana sosai da ruma, kan ta daina koke-koke, sai dai ita ma ta ha?a musu aiki, ba komai take ci ba, tsirfar yau daban ta gobe daban.

In da ta ?an ?ara samun sassauci, shine tana tare da lawisa, kuma a gidan akwai wata sa'ar tata zaliha, dan haka sukan ?ebe mata kewa.

***
Ba ?aramin ?acin rai 'yan mazan mama suka shiga ba, tun bayan da Aliyu ya dawo musu babu ruma, tare da sanar da su hukuncin da gwaggo ta yanke ba.
Abdallah ya ce "Wallahi gwaggon nan tana da matsala, tsabar mugunta ta yi garkuwa da yarinya dan son zuciya daga kai mata ita a sada zumunci".

Sai da suka yi dariya jin abin da ya ce, wai tayi garkuwa da ita.

Usman ya ce "Wane irin garkuwa kuma?".

"To idan ba garkuwa ba, ta yaya zata saka a kai yarinya wani ?auye a ?oyeta, wai ba zata dawo yanzu ba, amma idan ta cika musu ciki da rashin ji, ai sa dawo da ita da kansu"

Suna cikin tattaunawar mai sunan Baba ya dawo, suka gaisa da Aliyu, ya tambaye shi ina ruma? Ya sanar masa da yadda suka yi da gwaggo.

Tsuke fuska yayi ya ce "Wane irin abu ne haka? Idan na gama exams ranar lahadi zan je na taho da ita, akan me zasu ri?e ta?"

Mama ta ce "A'a babana, tun da na ha?ura dan Allah kuma ku yi ha?uri ku ?yalesu, yanzu sai ace zigaku nake yi, su je su ?arata, sati biyu ai kamar yau ne"

"Duk da haka, bai kamata ruma ta zauna a wurin nan ba, babu tsaro gaba ?aya dole zan je na taho da ita, dan ba ta zuwa makarantar boko yanzu, islamiyya fa?" Sosai ya ?au zafi, mama dai ta ce ba ta yadda wani yaje ya ce zai taho da ruma ba.

***
Gaba daya ta tattara hankalinta da nutsuwarta a kan litattafanta, gefe kuma ga calculator tana dannawa, tayi ?ai ?ai a ?asan carfet, ta saki dogwayen kalbar da aka yi mata, ta zubo har kafa?arta, duk da kalbar ta tsufa amma ta yi kyau sosai.
Nusaiba ta turo ?ofar ?akin ta shigo da sallama.
Iman ta amsa mata, ta zuba mata ido tana kallonta.

"Sarkin littafi, me kuma ake yi?" Iman ta kalli litattafan ta yi murmushi ta ce "Boko nake ci masoyiyya, ta samu ne?"

Nusaiba ta zaune ta ce "Eh to, ba nace ba, uncle J ne ya zo, kuma da alama ke yake son gani, sai tmbayata yake kina ina?"
Tsaki iman tayi, ta gyara zamanta tana ?o?arin mayar da kanta kan litattafanta.

"Kai, uncle J ?in ki ke yi wa tsaki, ya zo ya sakani a gaba sai tambayata yake kina ina?"

"Anty Nusaiba dan Allah ki ?yaleni da sabgar mutumin nan, wai me zan yi masa ne dan Allah?"

"Nifa na kasa gane abin da kuke ?oyewa, anya ba sonki yake yi ba?"

Da sauri iman ta girgiza kai ta ce "Dan Allah Anty Nusaiba kar ki ?aga maganar nan, idan har Ammi ta ji za ta bayar goyon bayan hakan, ni kuma ba zan watsa mata ?asa a ido ba, amma ni bana sha'awar duk wani wanda ya fito daga masarautar na, ke kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login