Showing 96001 words to 99000 words out of 182697 words
bainu, ban ta?a ganin yarinya mara mutunci da rashin tsoro irinta ba".
Adam a ransa ya ce "Ai ba ka san mara mutunci ba, sai ka ga wasi?ar da ta rubuta mini' amma a zahiri yayi shiru kamar ba da shi suke hirar ba.
***
"Ina sonka Adam, so bana wasa ba, so mai tsananin gaske son da nake jin zan iya komai domin na mallake ka, duk da na rasa dalilin da ya sanya bana gabanka, ko da yake ba rasa dalili na yi ba, nafi kowa sanin dalilin da yasa bana gabanka, kuma ina daf da magance komai domin in samu mi?a??iyar hanya ?o?ar ta cimma muradina na rayuwa da kai, ko baka aureni ba ina son kasancewa da kai na rayu ?ar?ashin kulawarka. Ban sani ba ko zuwa nan gaba asirina ya tonu duk da bana tunanin faruwar hakan, amma idan ma ya farun ka yi mini uzuri soyayyar ka ce ta janyo mini hakan" tamkar ta?a??iya haka samha ta saka hoton Adam a gaba ta na surutu, hoton yana sanye da kaya ne na sarauta, ya ?an sauke rawaninsa yana murmushi, wanda aka ?auka da hawan wata salla.
Sai da ta gama soki burutsunta, ta mayar da hoton ma'ajiyarsa, ta tashi ta ?arasa shirinta ta fice.
Mummy ce tare da aminiyarta zaune a ?uryar ?akin Mummy suna tattaunawa.
"Wai hajiya Lubabatu babu wani zazzafan malami ne, abubuwa kamar sun tsaya mini, sun ?i cigaba kamar yadda nake so".
"Haba Jamila, ke kin san an da?e muna ha?a rijiya, rijiyar da muke saka ran samun ruwa a kowane lokaci, mun shirin da idan balli ya tashi akwai rikici, ke dai mu cigaba da ha?uri".
Mummy ta girgiza kai ta ce "Ya ci ace burina ya gama cika, nifa da dai da mintuna biyar bana son ruhin Binta ya kasance cikin kwanciyar hankali da farinciki, so nake ta dauwwama a ba?in ciki har ?arshen rayuwarta".
Dariya Hajiya Lubabatu ta yi ta ce "Haba Jamila, ai ko a haka kika barta wallahi ta yabawa aya za?inta, kuma ta ?an?ana ku?arta, amma ki cigaba da ha?uri ai mun ?ana tarko daban-daban".
Mummy ta jinjina kai ta ce "Shikenan, bari mu ga zuwa yaushe, na cigaba da sanya musu ido, duk wani motsinsu uwani na gaya mini, kuma na ce lallai ta kawo mini maganin da waccan 'yar tsintuwar ke shafa masa".
"To shikenan, to bari mu ga yadda abubuwa zasu kaya".
***
Har azahar babu wanda ya kula su ruma, masu kuka na yi masu addu'a na yi, ga yunwa ta addabeta a gida wataran ?arfe bakwai ta karya, amma har bayan azahar babu wanda ya kulasu balle ya basu wani abu.
Tashi ruma ta yi ta samu ?aya daga cikin 'yan bindigar ta ce "Bawan Allah yunwa nake ji, ku bani abinci na ci"
Wani mugun kallo ya yi wa ruma ya ce "Zo ki cinyeni, an gaya miki nan wurin hutu ne da jin da?i?".
"Ai ni ba mayya bace da zan cinyeka, idan ma cin ne ban ga abin ci a nan ba, idan ba za a bamu abinci ba meyasa zaku kawo mu nan?" Ta na rufe baki yana hanka?eta sai dai fa?i ?asa ya saita ta da bindiga "Idan ki ka yi mini hauka, yanzu na lahira zasu yi maraba da ke".
Ruma ta kalli yadda ta fa?i ?asa, wata irin zuciya ta harzi?ota ta mi?e tsaye ta sake kallonsa ta ce "Na fa?a a bani abinci yunwa nake ji, ai da?inta idan ka kasheni ba a wuta zaka sakani ko aljanna ba, hisabi na Allah ne, to na fa?a a bani abinci yunwa nake ji, harbeni maza kai kuma a ?ara maka kwanakinka a duniya"
Babu alamar tsoro ko shakka a tare da ruma, kowa sai da ya Zubo mata ido, saboda ?arfin halinta.
A fusace ya tashi yayi kan ruma, amma wani ya ri?e shi, ya ce kar ka kuskura, ?yaleta idan ka yi mata wani abun za'a iya samun matsala, ka bari oga ya zo ya fa?i ya za ayi".
Huci ya din ga yi yaso ya tattaka ruma, ko ya keta mata haddi a gaban mutanen wurin, ya kawo ?arshen harshenta.
"Ni baka kyauta mini ba da baka bari ya kasheni na huta ba"
"Wato ke dai bakinki ba zai mutu ba ko?"
"Idan har so ku ke na yi shiru, to ku kasheni ko ku mayar da ni gidanmu, wannan ai zalunci ne ni yunwa nake ji" tayi maganar tana share hawaye.
Dattijon nan ne dai na jiya ya ce "Yarinya ki yi shiru da bakinki, kar su citar da ke, wannan mutanen ba ayi musu haka".
"To ni yunwa nake ji" tayi maganar har cikin zuciyarta.
Duk wani kurari da zare ido ruma ta?i yin shiru, kamar ma da gayya take yi dan ta tunzurasu su yi mata abin da za su yi mata.
***
Har dare mama ba ta san abin da ya faru ba, kuma an rasa wanda zai gaya mata, sai mita take musu cewar ita fa ta kasa ha?uri ta kira gwaggo idan an dawo da ruma ta ha?ata da ita, amma wayar gwaggon ba ta shiga. Sun yi mamaki da duk jin rediyon mama ba ta ji batun kai harin ba.
Ganin tana ta surutu ita ka?ai ba wanda ya tanka mata, ya sanya ta magantu "Wai ba zaku gaya mini meke faruwa ba ne? Duk cikinku fa yau babu wanda ya ci abinci, kun ?i walwala kun ?i magana, kuma kun ?i gaya mini menene?"
Usman ne ya tashi ya ce "Mama sai da safe, ni dai bana jin da?i ne".
Babu wanda ya bawa mama amsa, a hankali duk suka watse daga tsakar gidan, mama ta sha jinin jikinta ta fara tunanin menene ya faru haka, da basa son gaya mata?.
Babu wanda ya saurari su ruma sai bayan la'asar, aka zo da wasu kuloli a kan babur, aka rarraba musu wata busashshiyar gurasa, gaya guda ?ai-?ai, sai pure water ?aya tamkar mabarata.
Ruma ta kalli gurasar nan, duk uwar yunwar da take ji, amma a rasa me za a bata sai wannan takurarriyar abar a bushe, babu mai babu komai a jiki.
Gashi duk ta bushe kamar ?anzo.
Ruma ta gasta ta fara ?o?arin ha?iya, amma ta kasa ha?iyewa, da ?yar ta dannata da ruwa, daga gutsura ?ayar nan ba ta ?ara ba ta shanye ruwanta ta yar da ledar, sauran kuwa tuni kowa ya kama gurasar nan suka cinye.
***
Duk wata tattaunawa su Usman da sauran 'yan uwansa sun yi, amma sun rasa ta ina zasu ?ullowa lamarin, duk in da zasu buga sun yi, amma babu wani labari game da in da su ruma suke, gashi da wani ya ce zai je katsinan mama za ta gano akwai abin da yake faruwa, dan a yanzu haka ma duk ta tsargu, mussaman yadda suka daina walwala ga kuma ta fara shiga damuwa rashin shigar wayar gwaggo.
Su huzaifa ma sun gano abin da yake faruwa, sai dai yanayin ru?ewa da Huzaifa da Yasir suka yi, ya sanya mama cigaba da jefa musu zargi da kuma kokwanto.
Yau ?arfe tara na safe taga duk sun fito daga ?akinsu sun jeru a tsakar gida, kamae kullum babu wanda yake walwala a cikinsu, kuma babu mai sunan Baba a cikinsu.
Mama ta girgiza kai ta ce "Koma menene Allah yayi muku maganinss, tunda ni dai ina tsakaninku ba zaku gaya mini ba".
Ta fito daga ban?aki kenan, Abubakar yayi sallama ya shigo da jakarsa ta makaranta, sai dai kallo ?aya tayi masa shima ta ga tsananin tashin hankali a fuskarsa.
Mama tayi saroro tana kallonsa, cikin ?arfin hali ta ce masa "Kai kuma me ya dawo da kai yanzu?"
Suka ha?a ido da Aliyu, Aliyu ya sunkuyar da kai, Yasir kuma ya hau goge hawaye.
"Saddi?u, dan Allah kai ka gaya mini menene? Ku daina ?oye mini koma menene, na kasa nutsuwa sun ?i su gaya mini abin da yake faruwa, na rasa gane kansu, dama har akwai abin da ban cancanci in sani ba?"
Abubakar ya ajiye jakarsa ya kamo hannun mama ya ce "Mu je ?aki mama sai mu yi magana"
Mama ta buge hannunsa ta ce "Ba in da zani, ku yi ta ri?e abin ku a cikinku nima bana son ji, idan abin da bana ?auna a rayuwata bai wuce ganin fuskokin da ba sa son damuwata in gansu cikin damuwa ba, ko ba zan maganta muku ba ai na yi addu'a" ta juya za ta wuce ?akinta.
"Mama ruma ce" ya furta a hankali, cak mama ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya, ta ji maganar ta sa kamar bai fa?eta dai-dai ba.
Ba tare da ta waiwayo ba ta ce "Mutuwa ta yi?"
"An yi garkuwa da ita, a garin su Iya, a cikin harin da aka kai ?auyen har da ita aka ?auka".
Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mama za ta iya cewa ko mutuwar iyayenta ba ta girgizata kamar wannan abu da ta ji yanzu ba, ji ta yi kamar ba a hayyacinta ta ji maganar ba, tamkar an mata yayyafin wuta, Rumaisa a hannun 'yan biniga, gara ace kashe mata ita suka yi, ta tura a ?auko mata gawarta, amma ruma 'ya mace ?arama a hannunsu a tsakiyar dajin Allah, Allah ka?ai ya san me za su yi mata, ga halin ruma da ta sani na rashin kunya da surutun tsiya, tsaf za su illata ta.
Jikin mama ne ya hau rawa, ta sake ?are musu kallo, Huzaifa da Yasir suna ta kuka, Aliyu kuma ya sunkuyar da kai, haka Abdallah, Usmsn kuwa barin tsakar gidan ya yi, babu mai sunan Baba ko ba a gaya mata ba ya tafi katsinan ne.
Ta yin?ura da niyyar ?aga ?afarta, ta tafi luuu gaba ?aya suka yi kanta suna kiran sunanta
Ayshercool
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Sosai suke girgiza mama, amma ko motsi ba ta yi, a gigice Abdallah ya ?ebo ruwa ya din ga shafa mata a fuskarta Usman ya ?auko mafici yana yi mata fifita.
Aliyu ya kalli Usman ya c "Usman wani ya je ya samo napep mu kaita asibiti da sauri".
Usman ya ce "Ko nan da zaure ba zan iya fita gani nake komai zai iya faruwa kan na dawo, sai dai ko su Yasir".
Yasir da yake ri?e da hannun mama ya ?ara ?an?ame hannun, ya ?i tashi yana kuka.
A hankali mama ta yi tari, ta fara motsawa tana Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Babban fatanta Allah ya sa idan ta bu?e idanunta ace mata mafarki take yi.
Sai dai tana bu?e ido ta kalli fuskokin su Huzaifa, hakan ya tabbatar mata a zahiri ne, ruma an yi garkuwa da ita.
Sannu suka din ga jerwa mama, amma ta kasa amsa musu, a hankali ta ce "Ku kira babana, dan Allah ya juyo gida kar ya je, mu bar wa Allah komai".
"Amma mama meyasa?"
"Kar yaje ya tayar musu da hankali ko shi ma wani abun ya same shi, zuwan nasa babu abin da zai ?ara ku kira mini shi a waya, ya dawo gida dan Allah".
Jiki a sanyaye Abubakar ya janyo wayarsa a aljihunsa ya kira lambar Umar.
Mai sunan Baba na ?agawa Abubakar ya ce "Akhi mama ta ce ka dawo gida, bata yarda ka je ba?"
A hasale Umar ya ce "A kan me zaku gaya mata, kun san ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba dan me za a gaya mata? Wannan ai ba yi ba ne, idan wani abu ya sameta fa?"
Shima Abubakar da zuciyarsa ke a kusa ya hayayy?o masa "Kai saurara ni ka ke wa shouting? Da wanne zan ji ne? Har zuwa yaushe zamu cigaba da ?oye mata. zamu dawo mata da rumaisa ne idan bamu gaya mata ba? zaka din ga yi mini hayaniya kai ka?ai kake cikin damuwar ne? Duk ta shiga damuwa ba mai cin abinci kowa baya walwala kuma an ?i sanar mata abin da ke faruwa, zuwa yaushe za a cigaba da ?oye mata, idan ka ga dama ka dawo idan ba ka ga dama ka je ka yi abin da ka ga dama"
Umar yayi wa ?an uwansa uzuri, damuwa ce ta sanya ya sauke masa, dan Sadik ba dai ha?uri ba. Suna gama wayar Abubakar yayi cilli da wayar zai tashi mama ta ri?e shi.
Cikin tawakalli da ?arfin hali ta ce "Yi ha?uri, kar ka yi fushi dan Allah, ka lalla?o mini shi ya dawo ka san halinsa"
Abubakar yayi ajiyar zuciya zai yi magana wayar mama ta fara ringing a ?aki, Yasir ya je ya ?auko, mai sunan Baba ne yake kira.
Mama ta kar?a da sauri ta kara a kunnenta ta ce "Babana dan Allah ka dawo gida" tayi maganar muryarta na rawa.
"Ki yi ha?uri mama, daga sallar asuba na wuce, ina Katsina yanzu haka na kusa ?arasawa ki yi ha?uri ba abin da za zan aikata, zan je wurin jami'an tsaro ne, ki kwantar da hankalinki in sha Allah za ta dawo lafiya ".
"To" kawai mama ta ce ta saki wayar, tana wata irin ajiyar zuciya, zuciyarta sai wani irin zafi take yi mata, amma idonta ya bushe babu hawaye.
Su ruma kuwa yau kwana na hu?u kenan suna hannun 'yan bindiga, ba wanka ba wanki, ga azabar yunwa ruma ba ta iya cin abin da ake bata, ruwan nan ?aya idan an basu da shi take sha idan tana jin fitsari ta yi. Duk azabar kashi irin na ruma, ta matse abin ta ba ta yi.
Tun da ruma take ba ta ta?a kawo tsintar kanta a irin wannan halin ba.
Ga duka da wasu lokutan ake yi wa wasu, duk da ita babu wanda ya ta?a dukanta, amma ana dukan wasu ciki har da mata, 'yan bindiga su dake su su taka su da ?afa.
Wani tarihi ruma ta tuna da aka ta?a basu a islamiyya, a rayuwarta tana son malaman da suke basu tarihi, dan duk abin da take zata nutsu ta saurara.
Akwai ranar da malamin yayi musu tarihin Annabi yunus da kifi ya ha?iye shi, ya karanta *La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*
Har ruma ta ce "Kai malam amma kifin da ya ha?iye annabi yunus, dai yayi girman duniyar nan?"
Malamin ya yi murmushi ya ce "Meyasa ki ka ce haka? Kin san girman duniya kuwa?"
"To ai malam kifin da inuwa mai kifi yake sayarwa, da wanda ake talla ko ?an tsako ba zasu iya ha?iya ba, amma na ji ka ce kifi ya ha?iye mutum"
"Kifi ne dai babba ruma, amma ba kamar girman duniya ba, kuma ba a gaya mana girman kifin ba a Alqur'ani, abin da nake son ki ri?e yanzu shi ne, falalar wannan addu'a da annabi yunus Alaihissalam ya karanta, a duk lokacin da kika shiga wani mawuyacin hali, ko ki ka shiga hannun wasu azzalumai to kema ki karanta Addu'ar da Annabi yunus Alaihissalam ya karanta *La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*"
"To malam, in Allah ya yarda zan din ga yi, to wace addu'a zan yi idan na yi wa mama laifi kar ta yi mini fa?a ko ta saka mai sunan Baba ya sakani kama kunne?" Jik tambayar da ta yi, ya sanya 'yan ajin suka kwashe da dariya.
"A'a ai dole idan ki ka yi laifi ayi miki fa?a ko a hukunta ki, amma a duk lokacin da kike fargabar ha?uwa da wani, mugu ko ma?iyi sai ki karanta *Allahumma inni as'aluka min nuhurihim, wa'auzubika min shuriruhim*"
Ko da ruma ta tuna da wannan tarihin da malaminsu ya yi musu sai ta fara nanata "*La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*"
Ihun wata mata ne ya sanya ruma waiwayawa taga ko dukan na ta ake, amma taga ?aya daga cikin mutanen yana jan ta tana ihu, tana a taimaka mata. Babu wanda ya tanka mata mutumin yayi cikin dajin da ita.
?aya daga cikin 'yan bindigar ya ce "Ai gara hakan, tun da 'yar matsiyata ce ba za su biyan ku?in da aka ce su kar?eta ba".
Kusan awa biyu mutumin ya dawo ba tare da ita ba.
Ta ji wasu a kusa da ita suna magana ?asa-?asa "Innalillahi, ita ma sun mata fya?e sun kasheta" Ruma ji tayi kamar ta tambayesu meye fya?e, tunowa tayi lokacin da take tambayar mama meye fya?e su Aliyu suka din ga hantararta.
A take ta fashe da kuka, saboda yadda take kewar gida, duk suka juyo suka kalleta.
"Ke meye haka?"
"Mama" ta fa?a cikin kuka.
"Yi mana shiru ko in taka ruwan cikinki"
"Wallahi ba zan yi shiru ba, wayyo Allah mama yaya Aliyu yaya usy dan Allah ku zo ku ?aukeni zan mutu, wayyo Allahna" kuka take sosai kamar wadda wani iftila'in ya afkawa.
Wata mata ce ta din ga rarrashin ruma tana bata ha?uri da ?yar ta yi shiru, ta cigaba da nanata addu'ar nan.
Mai sunan Baba kuwa yadda yaje ya tarar da gwaggo ne ya sanya jikinsa yin sanyi, ya tarar iya ma tana asibitin ita da mijinta, gwaggo sai kuka take ba ta ko cin abinci, likitoci na ta fama jininta ya sauka abu ya gagara, saboda yadda ta addabi kanta.
Tana ganin mai sunan Baba ta sake rushewa da kuka, "Dan girman Allah ku yi ha?uri, ku yafe mini umaru ban zaci abin zai kasance a haka ba, tsananin ?aunar da nake yi wa ?an uwana ce na mayar kanku, ban yi hakan dan ba?anta muku ba, son da nake wa ruma ya sanya na hanata, da na san haka za ta faru da ba zan ce ma azo da ita ba, ku yafe mini dan Allah" gaba ?aya suka fashe da kuka, har su iya da su Lawisa da aka sace ruma a gabansu.
Ganin yadda dattijuwar ke cikin tashin hankali ita da iyalanta ya sanya ya ji duk jikinsa yayi sanyi, idan ya ce zai ?aga musu hankali bai yi musu adalci ba, tun da suma ba da son ransu hakan ya faru ba.
Ya ?arasa ya zauna a gefen gadon gwaggo sannan ya ce "Ki daina kuka, ko dan saboda a samu jininki ya sauka, yanzu ya ake ciki an sanar da jami'an tsaro ne ko kuwa ya ake ciki?"
Dagaci ya ce "Ka san garin namu, jami'an tsaro ba su fiye bamu agaji ba, mu da su mutanen muke yin sulhu, duk abin da muka saka jami'an tsaro wata ?arnar suke yi mana, amma dai saboda ita rumaisan mun sanar da jami'an tsaro, amma sun