Showing 81001 words to 84000 words out of 182697 words

Chapter 28 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22400

yi miki albarka ya rayaki, da 'ya ta na raye da ta yi kamar ke"

"To ta na ina yanzu 'yar ta ka?"

"An kasheta ita da babarta, Allah ya rayaki" ya kalli Aliyu ya ce "A lalla?ata dan Allah, sai wataran 'ya ta" yayi maganar yana ?agawa ruma hannu.

Wata narkekiyar mota ce ta yi parking, mai kyan gaske aka ?ora kayan bindigar a ciki, suka shiga motar aka ja suka tafi.
Ruma ta ?auko wayarta ta fara dannawa.

Aikuwa Aliyu ya dinga zaginta, har da zagin da bai san iya shi ba, dan ruma ta kai shi ma?ura yau, gaba ?aya ruma ba ta da hankali ba ta san ciwon kanta ba, shi tun da suka hau motar, suka yi nisa ya gane bindigogi ne a buhun da ke ?asan kujerarsa, kuma yana fuskantar yaren da suke yi ka?an-ka?an, 'yan ta'adda ne mutanen, amma ruma sai hauka take zubawa da wauta saura ?iris ya kar?i shegiyar wayar nan ya jefa ta ta window. Sai dai yana tsoron yin hakan dan ya ga mutumin nan ya za?e a kan ruma kar yayi masa wani abu idan ya ta?ata.

Direban ya ce "Wallahi bawan Allah Yarinyar nan mai sa'a ce, dan ni na zaci ma da zasu sauka tasa ta zasu yi a gaba su tafi da ita, ko su kasheta surutunta yayi yawa, ba a yi wa wannan mutanen haka"

Aliyu ya ce "Eh kaima ai azzalumin ne, da ka ?auko mu mota ?aya da wannan mutanen".

"Megida ba laifina bane ba fa, kullum akwai irinsu da suke shige da fice zuwa garuruwa, ba su fiye cutarwa ba sai in kun musu rawar kai, mu ma abincinmu da rayukanmu muke karewa".

"Amma jami'an tsaro na garin nan, ga su a tasha, amma ake safarar makamai a tsakanin garuruwa suna gani?"

"Lallai ?an samari zancen ka ke so, lamarin ?asar nan ta mu ai sai dai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, idan ka matsa sai ka kwana a ciki amma manyanmu sun san komai"

Aliyu ya girgiza kai ya ce "Allah ya kyauta".

Sai bayan la'asar sannan suka sauka, Ruma ta sha mita, kamar Aliyu ya ari baki, tayi masa shiru ta ?i kulashi.

Sai da mama ta kira ta ji sun sauka sannan hankalinta ya kwanta.

Gidan da suka je babban gida ne, mak ?auke da part-part, galibi Ruma ta san su, dan suna zuwa gidansu dan haka ba ta ga wani abu na musamman a a wurinsu ba, sai dai yanayin garin yayi mata kyau.
A sashin Gwaggo suka sauka, Gwaggo Atine har da hawayen murna, ta rungume ruma tana yi musu maraba.
'yar autar Gwaggo lawisa, sai kallon ruma take, da yake za su yi sa'anni da ruma, sai kallon ruma take yi.
Ruma kuwa jikinta ne duk ya mutu, saboda uwar tafiyar da suka yi, ba ta ta?a tafiya mai nisan ta yau ba.

Aliyu ya yi alwala, ya ce ita ma ta tashi ta yi salla.
A kan sallayar da ta yi salla, ta nemi wuri ta kwanta, nan da nan jikokin Gwaggo suka fara zuwa ganin ruma.

Ruma a ranta ta ce "Ji bala'i, kamar an ajiye musu buranya, sai kallona suke" ta dun?ule a cikin hijjabinta ta ?oye fuskarta.

Gwaggo tamkar zata goya ruma, su Aliyu su kan zo, shi ma sai a shekara wani daga cikinsu bai je ba.
Nan da nan ta ?orawa ruma.
"Auta taso ki zo ki yi wanka, zaki ji da?in jikinki sosai"
Ruma kamar ta ce ba zata yi ba yamma ta yi, amma ta ga kar ta watsawa gwaggon ?asa a ido, daga zuwanta, ta tashi ta je ta yi wanka da ruwan zafin.
Bayan ta fito ta tarar da lafiyayyiyar alala ta sha manja.
Ruma haryanzu a ?oshe take da kazar da ta ci, dan haka ta ci ka?an ta ce ta ?oshi.

Lawisa kuwa so take ta yi wa ruma magana, amma ruman sai wani basarwa take tana ha?e rai, gaba ?aya jikinta a ciwo yake, saboda wannan wahalalliyar tafiyar da suka yi, ga wani ?acin rai da take ji da ba ta san dalilinsa ba.
Ganin ruma ba zata kulata bane, ya sanya ta fara ?o?arin yin abin da zata burge ruman, sai ?o?arin shishshige mata take yi.

"Ba ki ci alalar da yawa ba, zaki sha fura?"

"Na ?oshi" ruma ta bata amsa a ta?aice.

Lawisa ta yi murmushi ta ce "To rama fa"

"Baiwar Allah cikina ne a cike fa, na ?oshi, ko ha?ama ki ke so in yi?"

"A'a, ko in ?auko miki fulo ki kwanta".

Ruma ta ce "Eh, dama na gaji sosai"

Lawisa ta je ta ?auko fulo, ta kawo wa ruma, ruma ta kwanta babu jimawa ta hau bacci.

***
Nema yake ya fita daga hayyacinsa, duk Addu'a da ta zo bakinsa yi yake yi, amma kansa kamar ana buga masa wani abu, ga wayarsa na ta ringing amma ba zai iya ?agawa ba, ya lumshe idanunsa, ya jin yadda cikin naman jikinsa ke wani irin zafi, idanunsa kamar za su fito saboda ciwon kai, ya dafe kan yana karanta al?ur'ani a fili, a hankali wani mawuyacin bacci ya kwashe shi.

Rumaisa ya gani a kan wani dutse a zaune tana kuka. Haya?i na ta tashi a wurin, amma yana iya gane fuskarta.

*Wallahi sai ka yi dana sanin abin da ka yi mini, daga yau ba zaka sake yi wa wani abun da kayi mini ba, ba dai ta?amarka ku?i ba, to ni nan Rumaisa kai da ku?in naka da sarautar ta ka sai ka dur?usa mini a kan gwiwoyinka, kuma ka saka a ranka nice nan abokiyar gabarka* kamar yadda ta gaya masa a ha?uwarsu ta ?arshe, haka ma a yanzu take sake maimaita masa, ya bu?e idonsa a hankali a cikin dodon kunnensa yake cigaba da jin sautin muryarta.

Ruma ma da bacci ya kwasheta, a razane ta yi wata 'yar ?aramar ?ara ta farka, tana haki kamar wadda ta sha gudu, a lokacin duhun magariba ya rufa! Gaba daya suka yo kanta suna tambayar ta ko lafiya?.

Ayshercool
[8/22, 11:41 PM] Maman Aslam: *Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*


Tamkar wadda aka tsamo da ga kwata haka ruma ta juya ta koma gida tana kuka, mutane a hanya wasu na tambayarta ko lafiya? wasu kuma suna mata dariya, yara sa'aninta kuma suna dariya ta kamo kifi soyayye, saboda yadda ta yi tsumu-tsumu da ta?o.

Takawa kuwa tafiya yayi yana jinjina taurin kai da tsagwaron tsageranci gami da rashin tsoro irin na Rumaisa.
Ya da?e bai ga abin da ya bashi mamaki kamar rumaisa ba, amma babu mamaki kamar yadda ya sanya aka masa bincike an tabattar masa da a cikin maza bakwai ta tashi, har halinta na rashin ji sai da aka gaya masa, tare da makarantar da take zuwa, a nan ya tabattar da muryarta da yake ji tabbas ta ta ce, tun da gidan gonarsu a unguwar su yake. Amma ya aka yi ta san gidansu har ta bishi can.

Ya tsaya da mamakin ne a lokacin da ya tuna ?arawo da ta la?anta masa, a take ransa ya ?aci, ya sake ?udurar aniyar sai ya ladabtar da ruma ta hanyar da ta dace.

Idan ya tuna sharrin da ta sake li?a masa, wai ya ta?a mata nono, sai ya rasa me ma zai yi, mamaki ko dariya?.

Mama ce ta kalli ruma ta ce "Meye haka, meya same ki?"

Cikin kuka ruma ta ce "Wani bugagge ne ya wanke ni da ruwan kwata, wallahi ba zan yafe masa Allah ya tattaro masifar duniya da ta gabasa da yamma kudu da arewa....

"Rufe mini baki? Ban hana ki yi wa mutum irin wannan addu'a ba? Wata?ila bai sani ba"

"Mama kalli jikina fa, ya na sane yayi mini, wallahi ba zan yafe ba, kuma in Allah ya yarda sai an sace motar, sai na yi masa tijarar da bai ta?a ganinta ba idan na kuma ha?uwa da shi, kuma sai an sace motar na ga ta tsiya"

"Wane mahaukacin ne yayi miki haka? Makaho ne shi?" Usman ya fa?a yana ?arewa uniform ?in ruma kallo, da suka jagalgale da ta?o.

Mama ta ce "A'a, kar ka zigata dan Allah, wuce ki je ji cire kayan, tsautsayi ne, kuma Allah yana tare da masu ha?uri"

Usman cikin takaici ya ce "Haba mama, kalli jikinta fa wallahi wannan da iskanci yayi mata, waye shi a ina yake? Kin gane shi? A nan unguwar yake?" Ya jero mata tambayoyin.

?an shiru tayi ta tuna furucin takawa, na zai kama yayyenta ya rufe su, ya saka a rushe musu gida. Nan da nan ta ce ni ban san shi ba, zuwa ya yi wucewa, yayi mini haka, to wallahi Allah ya isa na"

Huzaifa ya ce "?araso na tayaki ki wanke jikinki" ta ?arasa, Huzaifa ya ?ebo ruwa a rijiya ya hau she?awa ruma, sai da ta kusa shi?ewa, mama ta din ga yi masa fa?a, ?arshe dai ruma ba ta je makarantar ba ranar, ba ta yi jarrabawar ba, wunin ranar kuka ta din ga yi, tare da janyo wa takawa jafa'i iri-iri.

A daren da yakamata washegari su ruma su tafi katsina, ta fara ciwon kai da ciwon ciki, har zuwa wayewar gari, dan haka mama ta ce sai dai a ?aga tafiyar zuwa kwanaki biyu idan ruma ta warke.
Har zuwa azahar ruma tana kwance tana fama da ciwon ciki, Yasir ya ce "Shegen ciye-ciyenki na masifa ne yake janyo miki ciwon ciki, kece ci wannan ci wancan a islamiyya kullum cikin tauna kamar tunkiya" ruma ba ta yasir take ba, ta kanta take yi dan haka bata kula shi ba. Aka kai ruma chemist aka sayo mata magunguna.

Mama aka yi wa waya daga cikin gari, babur ya buge Hauwwaliya ta karye a ?afa, dan haka babu shiri mama ta shirya cikin tashin hankali ta tafi.

Ruma sai kuka take, ga karayar hauwwaliya, ga zafin ciwo kuma wai mama ba zata tafi ta barta ba. Mama ba ta saurareta ba, ta shirya ta yi ficewarta.

Burgima ta din ga yi a tsakar falon mama tana kuka, kamar wata yarinyar goye, sai gunji take "Wayyo cikina"

"Ke!" Ta ji tsawar mai sunan Baba daga ?ofar ?akin. Take ta nutsu ta yi shiru.

"Mara hankalin ina ce ke? Dan baki da lafiya sai ki ishi mutane, ba zaki yi addu'a ba?"

Shiru ta yi tana kuka ?asa-?asa dan ita ka?ai ta san abin da take ji.

Aka jima kuma sai amai, ga jikinta ya ?au zafi sosai. In da ta yi aman a nan ta zauna ta kasa tashi. Sai Aliyu ne ya wanke mata baki ya ?agata ya mayar da ita ?aki, ya wanke wurin.

Har bayan azahar mama ba ta dawo ba, ga ruma jiki ya?i da?i, Aliyu ya ce zai samo abin hawa ya kaita asibiti. Usman ya ce a fara ba ta abinci ta ci tukuna.

Cikin ruma ya sake ?ullewa, har cikin ?afafuwan ta, ta tashi da ?yar, ta tafi toilet yin fitsari.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku dan Allah ku taimake ni " suka jiyo ihun ruma a toilet.

Mai sunan Baba ne ya tafi da gudu ya bu?e ban?akin a razane, dan duba meya sameta, suma sauran suka rufa masa baya, amma suka tsaya a waje saboda ya na bakin ?ofar.

Ruma ce a tsaye, ta gama fitsarin ta mi?e tsaye tana kallon yadda fitsarin na ta ya gauraya da jini, duk da ba wani mai yawa bane ba.

"Meye haka?"

Cikin rawar jiki ta nuna masa ta ce "Mai sunan baba ka ga, fitsarin jini nake, mutuwa zan yi" tayi maganar idonta na cika da hawaye.

"Yaushe ki ka fara irin wannan fitsarin?"

"Yanzu kawai na gani" tayi maganar tana dafa bango, saboda jirin da take ji.

Ya waiwayo ya kalli Yasir ya ce "?auko mata zanin mama" Yasir shima jiki na rawa ya tafi ?akin mama, dan hankalinsa ya tashi sosai.

Ya sake duban Usman ya ce "?an ?ora mata ruwa ya yi zafi, ta yi wanka" cikin damuwa Usman ya ce "To meya sameta?"

Ya ?an ?age kafa?a ya ce "May be is her fisrt period"

A razane Aliyu ya ce "What! Rumaisan? How old is she? Yarinya ce fa sosai"

Usman ya ce "Ikon Allah"

Mai sunan Baba ya mi?a mata zani ya ce ta ?aura ta fito. Ta ?aura ta fito ya bata kujera ta zauna, Usman ya zuba ruwa ya wanke ban?akin. Ruma kuwa jikinta sai rawa yake yi tana tunanin ?arshenta ne ya zo.

Usman ne ya fita sayo pad, sai dai babu wanda ya san ya ake amfani da ita.

Gaba ?ayansu suka diririce, musamman ganin yadda ruma ke kuka, Huzaifa kamar ya tayata kukan, ita sam ba ta san menene ya sameta ba, mai sunan Baba ne kawai yake ta wani basarwa.

Aka kai mata ruwa tayi wanka, usman ya tattare kayan da ta cire, ya zuba a bokiti ya zuba musu ruwa.

Gaba ?aya mai sunan Baba ya rasa ta ina ma zai fara, gaba ?aya baya manta lokacin da aka haifi ruma, kamar jiya aka haifeta haka yake gani, wai ita ce yau period ya zo, yarinyar da ko ciwon kanta ba ta sani ba, ban da tarin rashin hankali da rashin kunya ba abin da ta sani, duk wani abu da ya shafi rayuwa ba saninsa ta yi ba.

Sai da yayi browsing, sannan ya ga yadda ake amfani da pad, ya nuna mata, har zuwa yadda ake discarding ?in ta, ta kar?a ta saka, sannan ta saka kaya.

Ya kalli su Usman ya ce "Su basu wuri, za su yi magana" ba musu duk suka fita.

Ya kalli ruma ya ce "Kalleni nan" ta ?aga kai ta kalleshi.

"Ko akwai wani abu da ya ha?aki da wani?"

Ta ce "Eh" gabansa yayi wata irin mummunar fa?uwa ya ce "Menene?kuma waye shi?"

"Wani mutumi ne, ruwan kwata ya watsa mini da motarsa jiya da safe".

"Ba wannan nake nufi ba, ko akwai wani wanda yayi miki abin da bai dace ba, ko wasan banza ko ya kai hannunsa jikinki?"

Tunowa ta yi da takawa, yadda ya cakumota, amma tayaya za ta fara yi wa mai sunan Baba wannan bayanin, ai kan a kai ga takawa, ita zai fara tattakawa, a karon farko da ta yi masa ?arya ta ce "Babu kowa"

"To idan ma akwai ki ka ?i fa?a, idan na gano sai na yankaki na zuba a rijiya, kuma wannan yanayi da ki ka shiga, duk wanda ki ka bari ya ta?aki ko yayi miki wasan banza, ciki zaki yi kuma mutuwa zaki yi" gaban ruma ne yayi mummunan fa?uwa, meye makomar ta?ata da takawa yayi? Ta yi ciki kenan?.

Haka suka shimfi?a tabarma a tsakar gida, suka kewaye ruma, yau har masu zuwa ball ba wanda ya fita, suna ta jera mata sannu, ban da masu fifita da masu ba ta abinci.

A haka mama ta dawo ta tarar da su, cikin mamaki ta dube su ta ce "Wai har yanzu jikin ne?"

Usman ya ce "Tun da ki ka fita a haka take"

Mama ta ce "To Allah ya ?ara afuwa, wallahi ina can muna fama, da ?yar aka samu aka ?ora yarinyar nan, tana jin jiki, sannu 'yar auta" ruma dai ba ta amsawa mama ba, ta sake lafewa a cinyar Aliyu.

Mai sunan Baba kuma yana gefe kamar mai gadi, yana kallonsu.

Mama ta kalli kayan ruma da suke shanye, gidan ko ina tsaf, amma ko girkin dare ba su ?ora ba.

Mama ta ce "Yasir, tashi ka ?ora mana ko taliya ce a ci da daddare" gaba ?aya basu da walwala kamar wadda aka ce musu ruman mutuwa ta yi.

Cikin damuwa mama ta ce "Wai me yake faruwa ne duk na ga kun yi jugum-jugum? Duk dan ba ta da lafiya ne ku ka zo ku ka tare a wuri ?aya haka, ba an sayo mata magunguna ba?"

Duk shiru suka yi, suna sunkuyar da kai aka rasa mai iya yi wa mama bayani.

"Mama fitsarin jini fa nake yi " Ruma ta yi maganar daga kwance.

"Wane irin fitsarin jini kuma? A garin yaya?" Mama ta yi maganar a tsorace.

Usman ya ?an yi gyaran murya ya ce "Wato ainihin, muna tunanin, wato ko.. abin nan na mata da suke duk wata, wato haila shi ta fara" waro ido waje mama ta yi ta ce "Ban gane ba"

Mai sunan Baba ne ya kar?a yayi wa mama cikakken bayanin abin da yake faruwa.

Mama ta yi salati tare da tafa hannu ta ce "Ruma haila, iko sai Allah girma ya riga hankali zuwa, a yanayin jikinta ban ta?a kawo zuwan wannan abun yanzun ba, ikon Allah"

"Mama wai menene ya sameni?"

"Girma ki ka yi" mama ta bata amsa.

Mama ta sake kallon igiya da kayanta a kan igiya, ta jinjina kai ta ce "Lallai ?anwar maza, yanzu har ?an kamfan ma ku kuka wanke mata? Iko sai Allah to Allah ya shiga lamarin, amma akwai bada?ala".

"Mama wai mutuwa zan yi?"

"Ba mutuwa zaki yi ba, abin da yake hana 'yan makarantar ku salla shi ne ya zo kanki". A gaban su Yasir mama ta zauna tana yi mata bayanin komai, sai a yanzu ta gane wasu daga cikin karatun da aka yi musu a Islamiyya in da suka dosa.

Gaba ?aya jikin ruma yayi sanyi, babu babban abin da ya tsorata ruma, sai cewa da mama ta yi ita ma yanzu za a din ga rubuta mata zunubi idan ta yi sa?o.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku, dan Allah kar a rubuta mini zunubi".

Aliyu da ta kwanta a kan cinyarsa ya ce "Wallahi sai an rubuta miki, gara tun wuri ki nutsu ki shiga hankalinki"

"Astagfirullah, dan Allah mama kar a rubuta mini zunubi, ba na jin magana, dan Allah mama kar a din ga rubuta mini zunubi bana son na mutu yanzu. Wayyo Allahna"

Mama ta ce "Iko sai Allah, na ga yadda za ayi wannan lamari da wannan yarinyar mara kan gado".

Har zuwa washegari aka samu zazza?i ya sauka, amma jikinta babu ?wari, mama da kanta ta kaita ban?aki za ta yi mata wanka, sai dai pad ?in jikinta ba ta ?aci ba, mama tana yi mata wanka ruma tana ?oye ?irjinta.
Mama kawai ta yi dariya ta cigaba da silleta.

Da ta fito da ita kuwa, tuni sun ha?a mata tea, Yasir ya ?auko mata kayan sawa, har da pad ?in da zata saka.

Mama kawai girgiza kai ta yi, gaba ?aya sun wani nutsu sun damu, duk saboda ?anwarsu.

Ruma ta yamutsa fuska ta ce "Ni ba zan saka wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login