Showing 21001 words to 24000 words out of 182697 words

Chapter 8 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22407

idona, wallahi mama idan kin ji me yake gaya musu sai kin ri?e baki, duk da wani abun bana ganewa, duk basu san daga waje ina jiyowa ba, kuma maimakon Yasir ya fito daga ajin nan, amma ina yana zaune ana koya musu abin da bai kamata ba.

Saroro yasir ya yi, ya ji me aka koya musu da bai kamata ba, suna ha?a ido da ruma, ya tuna karatun da aka yi musu, kan ya kai ga ?aukar mataki ta ce "Ina ji ai yana ce muku, wai ko idan mutum ya rungume mace alwalarsa ba ta karye ba, ko kiss, dan Allah wannan mama ba iskanci bane da ?ata tarbiyya, nan idan muna kallo aka nuno kiss ?auke tashar ake yi, amma wai malaminsu yake gaya musu.
Kuma naga ai turawa ne kawai suke rungume-rungume da kiss, mu wannan ba ?abi'ar mu ba ce amma yake gaya musu, wallahi makarantar nan ?ata tarbiyya ake yi".

"DAN?ARI!!"


GODIYA GA TARIN MASOYA MASU BIBIYAR LITTAFIN ?ANWAR MAZA, COMMENT ?IN KU NA SANYA NI NISHA?I, KAR A MANTA DA SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ?IN MU DOMIN SAMUN DA?A?AN LITATTFAN HAUSA NA SAURARO.

AYSHERCOOL
08081012143
[25/06, 4:11 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA


Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES


https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.



P7


Dafe goshi Yasir ya yi yana murzawa a hankali, ruma 'yar bala'i ce, ba zata tashi yi maka hansfree ba a cikin jama'a sai kowa ya hallara kamar mai sanar da wani abu mai muhimmanci, in da ya gode wa Allah da ya kasance, a makaranta ta ji ana koya musu, da bai san da wasu kalaman zai amfani wurin kare kansa ba.
Ita kuwa ta za?al?ale tana ta jawabi, babu wanda ya tanka mata, karo da idanun Umar ne ya sanya mata aya a jawaban da take kwarowa babu ?a??autawa.
"Zo nan" yayi maganar cikin bada umarni.

Kamar mara gaskiya haka ta tashi ta je gabansa ta dur?usa.
"Je ki ?auko mini jakarki ta makarantar boko da ta islamiyya"

"Dummm ta ji gabanta ya fa?i, har gara jakar islamiyyar ta ma, tun da ba a da?e da sakata ba litattafan da mutuncinsu, amma ta makarantar boko dai kam sai dai Allah ya kyauta.
Jiki babu ?wari ta je ta kwaso jakunkunan, ta zo gabansa ta ajiye su.
Ya kalli jakarta ta makarantar boko, duk ta ci ubanta da jagwalgwalon biro, har da zanen 'yan aljanu a jiki da su ABCD a jikin jakar, sunan 'yan gidan nan kuwa babu wanda ba ta rubuta a jiki bs. Tun daga nan ya san cikin jakar ma ba za ayi abin arziki ba.
"Oyaa zazzage litattafan na gani"

Babu musu ta janyo jakar ta zazzage, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, litattafan nan sun ga duniya, tamkar ?era ya ci rage mata. Kaf litattafan babu bango a jikinsu, sun yi kaca-kaca, wasu ma nanna?e su tayi, wasu ta ninka su biyu, a ta?aice kai ka ce bolar wani office ?in ce. Sai uban fensura sun kai biyar a cikin jakar, ga su ulu da farar ?asa da sauran goriba duk a ciki.
Umar ya kalli ruma, ya kalli bolar dake gabansa, dan ba zai ce litattafai ba.
"Yanzu wannan sharar ce litattafan karatun naki?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.
Ya sanya hannu ya ?au littafi ?aya yana dubawa, ba uwar da take yi a ciki, littafi ?aya sai ta yi duk subject ?in da ta ga dama a ciki.
A hankali ya cigaba da duba litattafan nata, ga class work da tarin assignment, wasu tayi ta ci zero wasu makin da take ci ma gwanin ban haushi, subject ?aya ya ga ta mayar da hankali tana yi yadda yakamata, kuma ba ta fa?uwa shine maths.

Yayi ajiyar zuciya ya ?aga kai ya kalleta ya ce "Ashe asarar ku?in tara kawai ake a banza ko? A biya miki ku?in makaranta idan zaki tafi sai an baki abin tafiya makaranta, amma ki je kina wannan jakancin, kalli wai wannan ne litattafan ki na karatu, kalli wannan wai 4\20 ki ka ci, ba zaki iya kawo abin da baki iya ba gida a koya miki, wasa da surutun banza fa?i ba a tambaye ki ba shi ki ka saka a gaba ko?"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"?arya na yi miki kenan? To bari ki ji na gaya miki, ina nan zan zuba ido a kan result ?in da zaki kawo wannan karon, wallahi idan bai yi mini ba sai an miki repeating "
Ras! Gaban ruma ya fa?i "Na shiga uku, dan Allah ka yi ha?uri, zan daina surutun in dinga karatu".

"Kar ma ki yi, wallahi primary 1 zan saka a mayar da ke, ki cigaba da da?i?anci, kuma ina samun information a kan abin da ki ke a islamiyya, ke kin zama jan wuya zaman ajinku ma ba kya yi, ke kin sakawa kan ki ba zaki iya karatu ba ko? Oya bu?e Alqur'ani nuna mini a surar da ku ke"
Ai nan ma badan-badan tayi ta yi, domin kuwa ba ta san a ina suke ?in ba.
Carbi ya bata, ya biya mata aya biyu, ya ce tayi ta maimaitawa sai tayi ?afa dubu.
Da haka yaya umar ya ?waci yasir, ta zauna ta dinga nanata karatu har barci ya fara ?aukar ta, da ta fara bacci yake zuba mata carbi a ?afa, ta tashi a gigice ta cigaba da karatun, da haka sai da ta haddace rabin shafi, bai ?yaleta ta kwanta ba sai wurin ?arfe ?aya na dare, da kuka haka ta kai karatun nan, ya sa ta kwashe bolar litattafan ta ya sallame ta.

Washegari, har makarantar boko, yaya umar ya je ya iske ta, ya kai mata sababbin litattafai, ya sanya aka kirawo ta ofishin shugaban makaranta, nan ma ba abin da suke yi, sai wassafawa yaya Umar halin ta na rashin ji.
Ya bata litattafan, yayi mata kashedi tare da jadadda mata, idan har ta cigaba da da?i?anci, sai ya sa an yi mata repeating.

*********
Zaune take a kan makeken gadonta, ?akin cike da kayan alatu kai da gani ka sam mai ?akin 'yar gata ce.
Ta dun?ule wuri guda a kan gadon, idanunta sun yi jawurr alamar ta sha kuka.
Daga ita sai doguwar riga 'yar kanti, kanta babu ?an kwali, kallo ?aya zaka yi mata ka san tana cikin matsananciyar damuwa.
Turo ?ofar ?akin aka yi, wata babbar mace ce ta shigo ?akin, idonta sanye da farin gilashi, hannunta ri?e da tray da cup.
Cikin tausayawa ta kalli yarinyar, ta ?an girgiza kai, ta ?arasa ta ajiye trayn, ta rungumota tana fa?in "Haba Iman ?ina, shikenan rayuwa bawa ba zai jurewa ?addara ba? So ki ke ciwona nima ya tashi?"
Iman ta girgiza kai, hawaye na cika idanunta.
"To Meyasa zaki takura kan ki, haka Allah ya so dama, ai dama tun farko biyayya ce zaki yi mini, kuma Allah bai yi yiwuwar abun ba, amma ki yi ha?uri kin ji babyna"
Ta jinjina kai lokacin da take sake kwantar da kanta a jikin matar.

Ta ?akko tea a kofa tana bawa Iman a baki, tana sha tana share hawaye, kai da gani ka san akwai tsantsar soyayya da ?auna a tsakanin su. Ta gama bata tea a baki, ta dinga shafa gashin ta, tana yi mata nasiha.

**********
Mama ta mayar da hankali sosai a kan ibada, mutane na ta shirin zuwan watan ramadan, mama tana ta azumi ita da su yayyen ruma, amma ban da hajiya ruma da cin abincinta ne kawai ya dameta.
Yanzu haka ta cinye taliya, ba ta ?oshi ba, ta kwa?a garin kwaki ta zauna tana ci.
Yasir sai masifa yake mata, wai shegen ci ne da ita kamar akuyar ?auye, ko saurarensa ba ta yi ba ta cigaba da tura abincinta.
Mama ta kalleta ta ce "Wai ke ruma, ko zuciya ba zaki yi ba, azumin nan da kowa yake yi na neman lada ko guda ?aya ki gwada ba?"

?an ?ata fuska tayi ta ce "Mama ni sai Allah ya kaimu watan ramadan, idan na fara azumi tun yanzu, ai ramewa zan yi kan salla"

"Ke ta ramewa ki ke, dan ubanki ina nuna miki ibada amma ke ba kya so"
Shiru ta yiwa mama tana cigaba da dan?arar garin kwakinta, dan ba ta ji za ta iya wannan azumin ba, idan na du gari ya zo dai ta jarraba.

Bisa ga jajircewar yaya Umar, aka samu ruma take ?an ta?uka abin arziki a makarantar islamiyya, shima ba wani sosai ba, dan sam ba ta bayar da hadda, tana iya ?o?arin ta ko ba duka ba, ta ?an iya karatun da aka biya musu, saboda idan yaya umar ya titsiyeya ta ?an samu abin karanta masa dan ya bari ta yi barci, idan kuwa ba baka ba ta san sauran.

Yau ana can ana sallar la'asar, ruma tana zaune tana shan mangwaron ta, tuni ta yi sallarta a cewarta ba za ta iya bin jam'in nan ba, tun tana tsayuwa sai jiri ya fara kwasarta ba za ayi a idar ba.
Ta gama shan mangwaronta, ta tafi wurin alwala wanke hannu.
A wurin alwalar akwai yaran da suma ba sa sallar, suke ta wasan su.
Babu tsammani, ruma ta ji an zuba mata bulala. Tamkar wadda ta fita hayyacinta, haka ta tashi a gigice, tana duba wanda yayi mata wannan ?anyen aiki haka.
Wani prefect ta hango, bayan ya zuba mata bulalar ya tafi kora sauran yaran da bulala.
Cikin ki?imewa, ta ?auki ?atuwar buta guda ?aya, ta bishi a guje tana ihu, ta dinga watsa masa ruwan. Ya waiwayo ya tsaya yana kallonta, ta ga hakan bai mata ba ta dinga ?wala masa butar, daga ?arshe ta dur?usa ta ?ibi ?asa tana watsa masa tana kuka.

Tamkar soko, haka ya tsaya yana kallonta, ko ?wa?w?waran motsi ya kasa, balle ya kare kansa.
An idar da salla kenan, hankali ya fara dawowa kan in da kukan rumaisa ke tashi, bayan ta gama ?ata masa jiki da ruwa da ?asa a gogaggen uniform ?in sa, ta ha?a hannayenta biyu tana yakushinsa gami da kai masa duka.

Da ?yar wani malami ya ?an?areta daga jikin matashin yaron, wanda ba dan ya girmeta ba, kuma babu dutse to babu abin da zai hana ta fasa masa kai da dutse, dan ba ta ga laifin da ta aikata zai zuba mata wannan bulalar ba.
Malamin ya dubi ruma ya ce "Meyasa ki ka yi masa haka? Meye haka ki ka yi?"

Cikin kuka ta ce "Dukana ya yi babu abin da na yi masa, wanke hannuna kawai nake yi shine ya dake ni, kuma wallahi ban yafe ba". Har ta gama maganar kuka take yi, jikinta yana rawa.
Yayin da hankalin ?aliban duk ya dawo kan su ruma, da jikin Auwal da ruma ta du?un?una masa kamar ya fa?a ta?o.

Ha?uri malamin ya bashi, ya ce ya je ya wanke jikinsa.
Kuka ne kawai auwal bai yi ba, amma ya ji zafin abin da ruma ta yi masa ba ka?an ba.
Auwal ?an ajin su Yasir ne, ya san ?anwar yasir ce, sai dai sam bai ta?a shiga sabgar ruma ba, kuma shi bai ma san ita ce a dur?ushe a wurin ba, yayi mamakin ?arfin hali da kuma tsaurin ido irin na ruma.

Ko da labarin abin da ruma ta aikata ya kai kunnen yasir, ha?uri yayi ta bashi, auwal ya nuna ba komai, amma a cikin ransa yana jin ba zai iya ?yale ruma ba sai ya ?au mataki a kanta.

Babu yadda Yasir bai yi da ita a kan ta ba wa auwal ha?uri, amma mursisi ta ce sai dai ya mutu idan har sai ta bashi ha?uri.
Tun da ruma ta yiwa auwal wannan haukan, sauran prefect ?in ma tsoron ta?ata suke yi, dan sun fi yadda da aljanu ne da ita, saboda tsaurin idonta yayi yawa sosai.

*********
Gaba ?aya ruma ba ta wani ?okin zuwan salla, saboda ta san ba ta da kayan salla, mama da gaske ba zata ?ara mata komai na kayan salla ba, ko kayan ado da ake saya mama ta?i sai mata, a cewar mama wannan shine hukuncinta na ?in jin magana. Ta ji haushi sosai amma ta danne ta cigaba da zuba ido, dan kuwa sallar akwai sauran lokaci.
Yau ta shigo gida daga makarantar boko, da wata takarda a hannunta sai yashe baki take yi.

"Deluwa, murmushin me ki ke yi ne haka, takardar meye a hannunki?"

Kallon banza ta yiwa Huzaifa ta ce "Na gaya maka bana son sunan amma ka ?i daina gaya mini, sai na maka rashin kunya ace bana ji"

Huzaifa ya ce "Yi mini rashin kunyar, ki gani idan ba ?arar da ke ba".

"Hmm ha?uri halin abin ?aunar mu Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, shi ya sa ba zan kula ka ba" girgiza kai yayi yana murmushi, ta cire takalmanta ta shiga ?akin mama.

Mama ce da Abdallah a zaune a falonta suna hira, yana guga.

Mama ta dubi ruma ta ce "Murmushin me ki ke yi ne?"

Ruma ta ?agowa mama takarda ta ce "Presentation zan yi a makarantar mu, kowa aka bashi, ni ba a bani ba, na dinga kuka da ?arfi nace idan ba a bani ba, na daina zuwa makarantar, shi ne fa Headmaster ya ce nima sai an bani, spelling b ne zamu haddace words ?in nan ?ari biyu da hamsin, zamu yi mu da 'yan wata makaranta"

"Ai fa kai ba hankali, wai ki ka dinga kuka da ?arfi ko kunya ba ki ji ba" Abdallah ya fa?a a hasale.

"To ai da ban yi hakan ba, ba zasu bani ba" tayi maganar cikin ta?ara.

Mama ta ce "amma dai ba su san ta nawa ki ke zuwa ba ko da suka baki?"

Ruma ta tsuke fuska ta ce "Wato mama ke ma dai da?i?iyar zaki ce mini ko?"

Abdallah ya ce "To mecece idan ba da?i?iyar ba" gaba ?aya haushi ya kamata, ba ta kuma kulasu ba ta shiga sabgoginta. Duk wanda ya shigo ta ce masa an bata spelling b sai su ce ai ba ci za ta yi ba, kada makarantar za ta yi.
Babu wanda ya bata ?warin gwiwa, ga yaya Abubakar ya koma makaranta, dama dai yana nan ne shine zai biye mata.

Zaune yake a cikin chemist ?in, yana jiran mai chemist ya sallame shi, kamar daga sama ta shigo chemist ?in ta ce "Gashi ka bawa mama maganin ciwon kai" na zai manta wannan muryar ba, ko a mafarki ya ji ta, yana ?aga kai suka ha?a ido.
Murmushi ta yi masa ta ce "Yaya auwal ina wuni" juyawa ya yi ko da wani take ba da shi ba.

"Baka da lafiya ne?" Tayi maganar tana kallon allurar da mai chemist ?in yake zu?ewa.

A hankali ya ce "lafiya lau, ya su yasir?"

"Suna nan lafiya, ya jiki?"
Da sau?i ya bata amsa, yana tuna yadda ta damalmala masa kaya a islamiyya, da yadda yayanta ya rutsata ta bashi ha?uri amma ta ce sai dai ya mutu, ba zata bayar ba, idan suka ha?u a makaranta, sai ta tsaya ta harare shi, har da murgu?a baki, amma wai yau take gaishe shi, har da su yaya bayan ko yayan nata yasir ba ta ce masa yaya.

"Deluwa wannan hamsin ?in taki za ta kar?uwa kuwa?" Cewar mai chemist.

"Awaisu mai chemist, duk ranar da na tashi jajjaga maka rashin mutunci, a kan kirana da deluwa, sai ka yi kuka" ta fa?a very serious.

Dariya ya yi ya ce "Ke, ai ko ban kai sa'an 'yan biyun gidanku ba, na san na girmi Aliyu, amma ni zaki saka kuka?"

"To shikenan, ka cigaba zaka gani, bani maganina na tafi"

Bayan ya bata maganin ta kalli auwal ta ce "Yaya auwal, Allah ya ?ara lafiya" tana gama maganar ya fita tana tsalle kamar kwa?uwa.
Tun da ga ranar da suka ha?u da auwal a chemist, kullum ta ganshi a makaranta sai ta gaishe shi, duk da baya sakar mata fuska idan zai amsa, amma bai sanya ta daina ba.

****
?aya ga watan ramadan, bayan gari ya ?auka an ga wata, mutane na ta shirin ?aukar azumi, da asuba mama ta tashi kowa sahur, amma da ?yar ruma ta tashi ta yi sahur, saboda nauyin bacci.
Ranar ?aya ga azumin ya kama asabar ce, ruma ta ce gaskiya ba zata iya zuwa islamiyya ba, tun ?arfe goma take jin kamar zata mutu.
Wajen ?arfe sha biyu na rana, ta dinga yiwa mama kuka tana burgima wai hanjinta na gutsutstsurewa ita fa mutuwa zata yi.

Aliyu ya ce 'mama dan Allah ki ?yake yarinyar nan, tun da ba zata yi ba ta je ta ?arata".

"Aikuwa sai ta yi, idan ya wajaba a kan ta wa zai mata?"

"Mama ki bari ua wajaban sai ta yi, kalli fa kamar zata rasu"

Mama ta ce ruma ba zata karya azumi ba, mama tana can tana salla, ya kandamowa ruma ruwa ta sha ta karya azumi.
Sai da mama tayi kamar ta zane Aliyu dan takaici, a ganinta sangartar ruma ta yi yawa.

Abu kamar wasa, ruma ta?i yin azumi, idan ma ta ?auka ta ji wuya, sai ta karya abin ta, idan aka sha ruwa kuwa tafi uban kowa za?ewa, da?yar ska samu ta yi shida, shima Usman ya ce bai yarda da ingancinsu ba. idan aka ce ta je sallar asham kuwa sai ta ce ita wallahi gajiya taje yi da tsaiwa, ?afafuwanta sai sun fara su?ewa ake ruku'u, nan ma sai bayanta ya kusa karyewa ake ?agowa ba zata iya ba. mama kuwa ta gaji ta kamata ta zaneta da mafici.

Idan kuwa aka matsa ta je sallar asham, wataran a can cikin yara ake tsintowa mama ruma tana tsalle -tsalle ko dambe a maimakon salla, tilas mama ta hanata zuwa take titsiyeta su yi a gida.

Sai da salla ta gabato, ruma ta sake da tabattar da mama ba zata yi mata wani ?inkin ba, ta dinga yi wa mama magiya, a kan ta yi mata wasu kayan, amma mama ta ce ba zata yi ba, lokaci ne da zata rama rashin jin da ruman take yi mata.
Gaba daya ?okin sallar ya fita daga kanta, saboda ba ta son kayan da aka sai mata, gashi sallar bana ko arzikin takalmi da jaka bata samu ba, dan haka ta ce ba zata yi ko kitson salla ba.

Mama ta bata ku?i ta ce taje ayi mata lalle, dan ba zata yi salla haka ba.
Ruma ta tafi ?unshi tun safe, sai bayan la'asar ta dawo.
Mama ta kalli lallen nan babu kyan gani, kamar ana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login