Showing 12001 words to 15000 words out of 182697 words
ba.
"Ki fito mu tafi, ina haraba".
"Ok, ya maganar mu? Kun yi magana da ita, zasu zo ne".
Nusaiba ta ce "Hmm, Samha kenan ke meya hana ki tambayeta?"
"Nusaiba bana son wasa, am serious about it".
Nusaiba ta ?an ta?e baki ta ce "Eh, za su zo" Ta sauke wayar daga kunnenta, ta nufi hanyar fita daga lambun.
***
Mama tana yawan yin istigfari da nemawa Rumaisa shiriya, musamman yadda bakin mutane yayi yawa a kanta, duk wani rashin ji irin na ?a namiji shi take yi, bama irin na mata sa'aninta ba, duk sa'aninta ta kere su a rashin ji. Babu yadda Mama ba tayi ba a kan aje a bawa malaman makarantar allon su ha?uri, ta koma amma mirsisi Yaya Umar ya ce sai dai a sauya mata makaranta, in da zata fi mayar da hankali, amma a ?asan zuciyarsa zafin maganganun da malaman suka yi a kan Rumaisa ne ya fi ?ata masa rai har ya sanya ya ce ba zata koma ba.
Ita kuwa Rumaisa ganin Yaya Umar ya hana a mayar da ita makarantar allon Malam Babba, tayi ta murna a ganinta ta huta da zuwa makarantar nan mai cike da takurar tsiya, Allah ya sa makarantar bokon ma a cireta, ta dawo gida Mama ta bata jari ta dinga sayar da wainar fulawa a ?ofar gida. Murmushi ta yi bayan wannan tunanin ya zo ranta.
Ta dubi Abdallah da yake ninke kayan da ya wanke ta ce "Yaya Abdallah, dan zaka gayawa abokananka zan fara sayar da wainar fulawa, naga kai ne me abokai masu ku?i, ka talatta musu su zo su dinga saya, ba irin abokan su Huzaifa ba gayyar ?olawa da tsamaye ba"
Saroro ya kalleta ya ce "wace irin wainar fulawa kuma?"
"Eh tun da na daina zuwa makarantar allon, sai Mama ta bani jari na diga sayar da wainar fulawa a ?ofar gida".
Huzaifa ya ce "Eh dama kin yi kalar sayar da wainar fulawar ai, ai ni da kai na zan din ga yi miki ciniki, ai suyar wainar ce ta dace da le delu"
Murgu?a baki tayi ta ce "Da dai ban san halinka bane, ci ka tsere ka rusa mini jari, kama kar ka sake ce mini wata deluna gaya maka.
Ta mayar da hankalinta kan Abdallah ta ce "Dan Allah Yaya Abdallah ka yi magana mana".
"To ai Ruma na rasa me zance miki ne, wace irin wainar fulawa ana zaman lafiya".
"To Yaya ba gara ace ina sana'a ba, kuma ku huta ba, ana ta shelar mata su kama sana'a, Mama ai zaki bani jari ki saka mini albarka ko?"
Mama ta ce "kada Allah ya nuna mini wannan rana, kuma kar ki sake sakoni a cikin shirmenki, idan kuma ki ka sake sai na ci ubanki ke da soya wainar fulawa a ?ofar gidan, tun da ke dai Allah bai sa an raba hankali kin samu ba" ?ata fuska tayi a ranta ta ce 'sai na tambayi Yaya Abubakar, na san shi ba zai hana ni ba ai, tun tuni ake cewa mata su kama sana'a ni kuma zan yi ana hanani'.
Umar yana ?aki yana jin shirmen da Ruma take, ji yake kamar ya ?auketa ya kai ta boarding kowa ya huta, amma ya san Mama ba zata ta?a amincewa ba.
Wayewar garin Allah, wurin ?arfe sha ?aya na safe, mama na shirin fita, telar da take yiwa Mama ?inki ta aiko da ?inkin da Mama ta kai mata, bayan mama ta kar?i ?inkin ta sallami yaron, ta kalli Ruma ta mi?a mata ledar ta ce "gashi nan kayanki ne".
Da murna ta kar?i ledar ta bu?e, cike da son ganin menene a ciki.
Tana bu?ewa tayi karo da wata atamfa koriya da yellow, ta kalli Mama ta kalli atamfar sannan ta ce "Wallahi Mama wannan Salamatu mai kayan ba ta kyauta mini ba, sai da nace ba na son atamfar nan, amma dan taga ba na nan shine ta li?a miki, ki ka saya amma shikenan na gode, amma dai ba dan an ?inka ba sai na mayar mata" ba ta gama rufe baki ba, ta bu?e kayan taga riga da zani jaka a tsaye, da wata uwar bunjumemiyar riga kamar zata tashi sama.
"Ta kalli mama ta ce "Mama wai wannan kayan nawa ne ko kuma naki?" Ruma tayi maganar a rikice.
Mama ta ce "Ni ce zan saka wannan kayan? Naki ne mana"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu mama wannan ne kayan salla na, dan Allah kalli rigar tsaf sai an saka irina sittin a ciki, mama ko gwada ni fa ba ayi ba aka ?inka kayan"
A fusace Mama ta ce "Naji na gode, ki ajiye mini kayana tunda ba ayi miki gwaninta".
Yasir ne ya dubi Ruma ya ce "Amma Ruma baki da kirki, yanzu mama ta sai miki kaya ta bayar a ?inka miki, amma ?iri-?iri ki nuna ba kya so".
Mama ta ce "Rabu da ita, ta je ta ?arata".
"Mama kiyi ha?uri, ba cewa nayi bana so ba, amma dan Allah kalli rigar nan, ni ba tattabara ba ina zani da wannan rigar kalli hannun kamar fuka fukai, ba irin wannan rigar na gani a jikinku a wannan tsohon hoton naku ba?"
Yasir ya kar?i rigar yana dubawa, ?unshe dariyarsa yayi ya ce "To dan ubanki maje gaba aka yi miki, tun kina yarinyarki da ke, wato kin fi son matsatsun kaya ko, to baki isa ba, wannan rigar da ita zaki yi wankan idi mu je masallaci, maje gaba ce "
Haushi ne ya gama cika Ruma, ta tura baki tana jin kamar ta yi ihu.
"Wace irin maje gaba, ai sai a bari nayi gaban tukuna, sai a ?in ka mini daidai ni, idan ban je gaban ba fa?"
Mama ta ce "Rabu da ita, ta gama rashin mutuncinta tun da abin nata haka ne, daga wannan ba zan ?inka mata wasu ba, da su zata yi sallar, dama ba jin maganata take yi ba, nima an zo wurin da zan fanshe, bana ba kayan salla sai kala ?aya".
Yasir ya ce "Wallahi mama hakan ma ta gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ya ?ara bu?i, ai kin yi ?o?ari, ke Ruma wannan rigar idan ki ka sakata ai ba sai kin ?aura zanin ba, ka?an ya rage ta zama doguwar riga, idan kuwa zaki ?aura zanin sai ki ?aura shi a kam rigar, ki yi ?aurin barmana coge wallahi kyau zaki yi"
Gaba daya ta fuskanci Yasir rashin mutunci kawai yake yi mata, kamar zata fashe haka ta tattare kayan ta kai ?aki ta zubewa Mama a kan kujera, ta barwa ranta cewa gara tayi zamanta a gida da salla, da ta saka wannan zulumbuwar rigar a matsayin kayanta na salla ta fita ayi mata dariya.
Mama ta fita yin barka a ma?wabta, hakan ya bawa Yasir damar zama ya sanya Ruma a gaba ya dinga tuntsira mata dariya, duk wanda ya shigo sai ya ?auko masa kayan ya nuna masa, daga atamfar har ?inkin irin na zamanin su Mama ne.
Huzaifa ya fi kowa ?ya?yatawa, ya ce "Lallai mama ta iya punishment, ai ni ta biyani da aka miki wannan ?inki, kamar yadda Yasir ya fa?a, idan ki ka saka kayan nan, ki ka kafa ?auri irin na barmana mu samo ?orrai, da sallar nan mu baza ki?an ?warya a cikin unguwa, wallahi ku?i zamu samu, dan dama mutane duk sun watsar da al'ada".
Abdallah har da yi mata magiya a kan ta gwada kayan yanzu, ya ga yadda za su yi mata. Tayi musu banza ta koma gefe ta ci magani.
Yaya Usman ne ya zare mata ido, wai sai ta gwada kayan sun ga yadda za suyi mata, kasancewar tana shakkarsa shima, haka ta je ta saka kayan ta fito tana danne kukan da yake ?o?arin ?wace mata.
Tana fitowa tsakar gidan Huazaifa ya bushe da dariya ya ce "Waya ga babba da jaka".
Abdallah ya ce "Allah ya bar mana Delun mu, wallahi dama delun aka saka miki, kin yi kyau".
Usman Ya ce "Abdallah, yi mata ?aurin barmana cogen, mu gani, zan mata video"
Duk yadda ta so ha?iye kukan sai ta kasa, sun kewayeta sai dariya suke kamar sun ga mahaukaciya, ga Usman yana yi mata video da wayarsa suna dariya.
Huzaifa sai kifawa yake, kamar wanda ya zare, yana cewa Usman"Ka yi mata hoton da Black and white mu ce ga kakar su Mama 1940"
Babu tsammani Umar ya shigo, ya tarar da Rumaisa a tsaye kamar an dasa ta, ga uban ?auri a ka, ta ?aura zani a kan riga, tana tsaye tana kuka su kuma sun kewayeta suna dariya.
"Meye haka?" Yayi maganar a kausashe.
Usman ya ce "kayan sallarata ne, aka kawo take ta rashin mutunci wai bata son kayan, shine nake punishing ?inta, nan gaba ta koyi godiya ga Allah a kan duk abin da ya bata, sannan ta godewa wanda ya batan".
Shi kansa Yaya Umar ji yayi kamar ya yi dariya, saboda yadda Ruman tayi a kayan, kai da gani ka san sun yi mata yawa, sai tayi kamar wadda ta kawo tallan kalwa birni.
Gimtse dariyarsa yayi ya wuce ?akinsu, suka gama yi mata rashin mutunci sannan suka sallameta.
Da ta koma ?akin ma, sai da ta sha uban kukanta, ta cire kayan ta ajiye tana jin yadda ranta yayi mugun ?aci a kan abinda suka yi mata.
Kasancewar yau ba tuwo mama tayi da daddare ba, ya sanya ruma zaman cin abincin dare ba tare da mita ko ?un?uni ba, ga kuma uwa uba a ?ule take da rashin mutuncin da su Yaya Abdallah suka yi mata. Tana ta lissafa yadda zata rama abin da suka yi matan ta huce.
Duk da yadda yau tayi shiru, babu wanda ya kula da shirun nata, dama mama na jin haushin tayi mata abu ta kushe, mama ta mayar da hankalinta kan 'yan mazanta suna ta hira.
"Mama ina da tambaya" duk suka waiwayo suka kalleta.
mama ta ce "To ina jinki, Allah ya sa na sani"
"Wallahi na san ?arshenta banzayen tambayoyinta ne marasa kan gado, dan Allah mama kar ki saurareta" Huzaifa yayi maganar yana kallon Ruma.
Cikin tsiwa ta ce "Ban kasa da kai ba, dan haka babu ruwanka da ni".
Mama ta ce "Yi tambayarki ina jin ki"
"Yauwa, dan Allah kar na tambayeki kuma kice mini sai an kwana biyu, menene Janaba, kuma meye fya?e!!!"
Ayshercool
08081012143
Kar a manta ayi subscribing YouTube channel ?ina domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
[20/06, 6:52 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following ?ina a arewabooks a kan account ?ina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.
P5
Sak suka yi gaba ?ayansu, lomar da Yaya umar ya ha?iya ya ji ta?i wucewa tana kai komo a wuyansa kamar zata dawo. Amma ya basar kamar bai san me suke fa?a ba.
Huzaifa kuwa tsam ya mi?e yana fa?in "Ai sai da na ce kar ki saurareta ki ka ?i, sai ku san abin da zaku gaya mata" yana maganar ya bar tsakar gidan.
Mama ta rasa mai zata cewa Ruma da hankalinta zai ?auka, sam yarinyar bata tunani dai-dai da shekarunta.
"Wai ya na ji kin yi shiru? Me kuma nayi?" Ta yi maganar cikin ta?ara.
Cikin ?arfin hali mama ta ce "Ke a ina ki ka ji wannan kalmomin da ki ka tambayeni?"
"Mama ya kuma ki ke tambayata bayan nima tambayarki nayi"
"Ki amsa mini dan ubanki" mama tayi maganar a hasale.
Ta ?an cuna baki sannan ta ce "Ba wani ne ya gaya mini ba, kece ki ke jin radiyo ranar, na ji ana cewa ayi wankan janaba idan aka yi ko me? Oho na manta shi ne nake son na san meye janaban, kuma meye wankan. Shi kuma fay?e idan aka fa?a a radiyo sai na ga hankalinki ya tashi kina girgiza kai kina Allah ya tsare zuriyar musulmi baki ?aya, shine nake son na san menene?"
"Tir?ashi, aiki ga mai ?areka mama Allah ya bamu alkhairi " Yaya Aliyu ya fa?a yana ?o?arin shigewa ?aki.
Yaya Usman ya ce "Kuma duk abin da ake fa?a a radion babu wanda ki ka ri?e sai wannan?"
Ruma ta ce "To ai akwai wasu ma, mantawa nake yi ne sai yanzu na tuna"
Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Kina jina ko Ruma?"
"Eh ina jinki"
"Yauwwa, zan gaya miki zan miki bayani, amma ba yanzu ba sai an kwana biyu, yanzu ko na yi miki bayani ba zaki gane ba, kuma nan gaba ko ba a gaya miki ba ma, zaki gane da kan ki".
Cike da yarinta ta ce "Nan da kwana biyu ranar asabar kenan, in Allah ya yarda zan tuna miki ki gaya mini"
"Ba wanna kwana biyun nake nufi ba hansai, sai kin ?ara girma da hankali"
Cikin mamaki Ruma ta ce "Yaushe kuma zan ?ara girman da hankali, wancan karon ma fa na ta?a tambayarki menene MATA MAZA, ki ka ce mini sai na girma, na tambayeki menene haila ki ka ce mini ba yanzu ba, amma da zan yi wani abun sai ki ce ina girma amma bana hankali wane irin girma ki ke son nayi to?"
"Ke tashi ki wuce ki kwanta dan uwarki, kawai kin saka mutane a gaba da tambayoyinki na shirme, ko a gidan uban wa ki ke jiyo wannan manyan maganganun oho miki, wuce kan na karya ki biyu, ba zaki tambayi abu daidai da hankalinki ba sai wanda ya fi ?arfin kanki" sai da ta kalli in da Yake zaune yana bata umarni, bayan da fari yayi kamar bai san me suke yi ba.
A hankali ta tashi ta nufi ?aki, tana tunanin menene aibun tambayarta?.
Tafiya ta yi ?aki, ta gyara shimfi?arta ta kwanta, tana tunanin meyasa kullum tayi tambaya sai ace mata ba yanzu ba sai an kwana biyu, ko ace wai tana tambayoyin da suka fi ?arfin ?wa?walwarta me hakan yake nufi kenan?. Da wannan tunane-tunanen bacci yayi awon gaba da ita.
Da safe tana kwance tana baccinta, duk samarin gidan sun gama komai, har abin karyawa, Kasancewar Asabar ce Ruma tana ta baccin asara, ba aikin fari balle na ba?i, har ?asan ranta tana matu?ar jin da?in rashin zuwa makarantar allo da ba ta yi, saboda tana samun isasshen lokacin bacci.
Ji take ina ma ace bokon ma ta daina zuwa, idan tayi baccinta ta ?oshi da yamma ta kfa suyar wainar fulawa a ?ofar gida ta tara 'yan ku?a?enta.
Baccin yayi mata da?i, tayi nisa sosai a duniyar mafarkai kala-kala, ta ji kamar daga sama ana taka mata ?afa.
Bu?e ido tayi a hankali, amma ta?i motsawa, tana son ta tabbatar da a zahiri ne ko duk cikin mafarkin ne.
Ji tayi an kuma zungurarta da ?afa, ba tare da ta waiwayo ba ta ce "Wallahi Huzaifa zan maka rashin mutuncin da baka ta?a tunani ba, kar ka sake takani"
Bai ji kashedin ba, ya sake haurinta da ?afa, "Allah ya isa wallahi, kuma ba zan tashi ba" tayi maganar tana sake dun?ulewa a wuri guda.
?ashin bayanta ya kuma daka da ?afarsa, ta yin?uro a matu?ar zafafe, da nufin ta kafa masa ha?ora ko a ina ne, amma me tayi tozali da Umar a tsaye a kanta.
Jikinta ne ya hau tsuma, ta ma rasa me za ta yi, ko ta ce.
Shiru yayi yana nazartarta, daga bisani ya ce "Ki tashi ki je ki ki yi wanka ki karya ina jiranki, kuma idan ki ka ?ata mini lokaci kin san sauran"
Saroro tayi tana kallonsa, da ba ta gama fahimtar me yake nufi ba.
"Za ki tashi ko sai na yi ball dake?" Cikin hanzari ta tashi, ta ?auke katifarta ta nufi ban?aki tana mamakin to ina zasu je, kar dai boarding ?in zai kaita kamar yadda ya ce. Gabanta ne ya fa?i ta fara tunanin ko ta gudu.
Kai tsaye ta nufi ban?aki, tana shiga ta tarrar da an ha?a ruwan wanka, ba tayi tunanin ko ruwan waye ba, ta rufe ?ofa ta hau wanka da shi.
Yasir ne ya nufo ban?akin da sauri, wuyansa ?auke da soson wankansa, zai shiga ban?aki saboda ya kai ruwan wankansa, amma yana zuwa ya ga ?ofar a rufe.
Iya ?arfinsa ya hau dukan ?ofar yana fa?in "wani ?an rainin hankalin ne ya shiga bayan na kai ruwa?"
Gyran murya tayi masa, tsaki ya ja ya ce "Ki hanzarta zan yi wanka na fita na kusa makara.
Tun yana saka ran zata fito har ya tashi ya fara zaginta yana bugun ?ofar.
Ba ta da tabbacin wankan da tayi ta fita, ta bu?e ?ofar ban?akin, zagi ya dinga surfa mata, bai kai ga rufe baki ba, idonsa ya sauke a kan bokitin da ya ha?a ruwa, Ruma ta zubar da komai.
A hasale ya zura hannu ya janyota tsakar gida ya ce "Wallahi yau mai ?watarki sai Allah, na zuba ruwa na kai zan fita makaranta kina can kina bacci, amma ki zubar mini".
Babu alamar nadama ta tsuke fuska ta ce "To ba Yaya Umar ne ya ce nayi wanka ba"
Wani ran?washi ya yi mata a tsakiyar ka, da azabar zafinsa ya sanya ta dur?usa a kan gwiwoyinta, tana sakin wani irin kuka mai sauti.
Yaya Umar ya ?aga labulen taga ya le?o ya ce "?yaleta tun da ka daketa" ba ?aramin ?aci ran Yasir yayi ba, dan niyyarsa sai ya yiwa Ruma dukan da duk taurin kanta sai ta bashi ha?uri.
Kasa karyawa tayi saboda kuka, tana tsaye tana duru-durunta, Umar ya shigo hannunsa ri?e da leda ya mi?a mata ya ce "Maza ki shirya ki wuce mu tafi"
Kar?ar ledar tayi tana duddubawa, uniform ne na islamiyyar su Huzaifa, makarantar da ta ce ko aljanna ake rabawa a cikinta ba zata yi ta ba, saboda azabar tsaurinsu, asabar da lahadi tun tara sai biyar ake tashi, ba a fashi balle makara, ga haddar Alqur'ani ake yi da gaske ba wasa ba.
Saroro tayi tana kallon Yaya Umar, cike da rashin fahimta amma ta kasa yi masa Magana.
Wata uwar harara da ya yi mata ne, ya sanya ta shiga ?akin Mama, ta saka uniform ?in jikinta sai tsuma yake yi, ita ta san har ga Allah ba zata iya zaman makarantar nan ba.
Mama dai ba ta ce musu kanzil ba, ya tasa ta a gaba suka tafi.
A zuciyarta tana