Showing 9001 words to 12000 words out of 182697 words
son zumunci kai ni ne ba ayi" Gaba ?aya sai ta manta da damuwarta, ta shantake suna hira.
Sai da aka jima sannan ta shiga ?aki ta ajiye allonta.
Sabgoginta ta shiga yi, ta zage ta ce ita zata yi wa su Babban Yaya girki, abincinta zasu ci.
Aikuwa fa?a ya kaure, Huzaifa ya ce ba zasu ci jagwalgwalonta ba su zasu yi girkinsu, ?arshe Yaya Sadik ya ce na Rumaisa zai ci.
Zuwa Azahar gida ya ?inke kowa ya hallara a falon Mama suna cin Abincin rana, Sadik sai jinjinawa ?o?arin Rumaisa yake ta yadda ta iya girki mai yawa haka, Huzaifa da Yasir kuwa sai kushewa suke yi.
Zaratan maza ne su bakwai sai Rumaisa, Mama a hankali take binsu ?aya bayan ?aya da kallo, tana tuna baya.
Hadiza shine sunan Mama na gaskiya, haifaffiyar garin Kano ce, unguwar mandawari. A nan ta taso tayi karatun boko da islamiyya, sai dai tana aji uku na Sakandire, ta ha?u da mahaifinsu Rumaisa, Muhammad Aminu a nan unguwar sabon sara, amma asalinsa ?an garin Katsina ne, yana zuwa gidan wan mahaifinsa ne a Kano yana koyan harkar kasuwanci, a nan suka ha?u suka yi aure, kan Hadiza ta gama makarantar sakandare.
Haihuwar fari Mama ta haifi tagwaye Abubakar Sadik da Umar faruk sune 'ya'yanta na fari, Sai ta kuma haihuwar Usman, sai Aliyu, Abdallah da Huzaifa, Yasir ne kawai ba ?an ta ba, ?an ?anwar mahaifinsu Rumaisa ne, ta haife shi da kwana ka?an Allah ya yi mata rasuwa, a lokacin Mama tana shayar da Huzaifa sai ta ha?a su ta shayar da su tare, ba zaka ta?a cewa ba 'yan biyu bane ba, ko ba ita ce ta haifesu ba.
Mama gaba ?aya tayi tunanin ta daina haihuwa, saboda galibi bai fin shekara biyu uku a tsakanin yaran take haihuwa, amma bayan haihuwar Huzaifa sai da ya shekara takwas, kawai ta daina ganin al'ada, sai ga cikin Rumaisa.
Tun da Allah ya sa ta haifi Rumaisa, kowa ya ?auki soyayya ya ?ora mata, kasancewarta kallabi a tsakanin rawuna, kowa babban burinsa ya faranta mata.
Mahaifinsu Rumaisa, mutum ne mai matu?ar kulawa da son iyalinsa, kasancewar Ruma ce ka?ai 'yar sa mace yafi kowa ji da ita, ba shi da magana sai ta Rumaisa, Akwai tsananin ?auna da sha?uwa a tsakanin Ruma da mahaifinsu, dan kusan tafi son sa a kan Mama, saboda Mama akwai fa?a, Abba kuwa lalla?ata yake. kwatsam Allah ya yi masa rasuwa tana da shekaru uku kacal a duniya, bayan yayi gajeriyar rashin lafiya.
Bayan rasuwar sa sai da Rumaisa tayi cuta kamar ba zata rayu ba, saboda alhini. Dangin mahaifin su Rumaisa suna da zumunci sosai, sun so a rarraba musu yaran su ri?e su, amma Mama ta ce ba ta son a raba nata kan yaranta, dan haka ta ce su ?yale mata su.
Haka tayi ta ?awainiya, 'yan uwa da abokan arziki suna taimaka mata da abin da zasu iya
Tasowar Rumaisa a cikin 'yan mazan nan, wannan ya ?auka wannan ya sauke ya sanya ta taso tamkar namijin ita ma. Ba ta jin magana ga rashin tsoro, ga tsiwa da ?an karen surutu da iyayi, gashi lokacin da take tasowa girma ya fara kama Mama duk tayi sanyi, dan haka ta mayar da Mama kamar wata kakarta ba uwa ba.
Mutum ?aya take tsoro shi ne Baban Mama, Yaya umar mai sunan baban Mama, Allah yayi masa kwarjini shi ko irin wasan nan na yarinta baya yi, ba shi da abokai, ga tsare gida ba shi da fara'a ko walwala baya son shiga mutane sam, idan kaga an taka masa burki kai tsaye to Yaya Sadik ne. Mama tana matukar girmama shi saboda sunan mahaifinta da yake da shi.
Yanzu Rumaisa tana aji hu?u na Firamare, Abubakar yana Dutse yana karatu, babu wanda yake da cikakken ?arfin ?aukar ?awainiyar gidan gaba ?aya, amma kowa babban burinsa ya nemo ya kai gida, komai suka samu mahaifiyarsu da ?anwarsu kawai suke tunani.
"Hajiya Mama, ya naga kina ta kallonmu ne kamar da ba?o a cikinmu".
Mama tayi murmushi ta ce "Allah nake yiwa godiya, da ya sanya duk ku ?in nan nawa ne, Allah ya dafa muku ya ?ara ha?a mini kanku"
Suka amsa da "Amin"
Yasir ya ce "Mamanmu, maganin kukanmu Allah ya ?ara hore mana, mu gantataki fiye da kowace irin uwa a duniya"
Huzaifa ya ce "Hmm kamar gaske, nan fa kake zuwa da abin duniyarka ka hanata, ka hana kowa ka bawa waccan yarinyar mai kama da Akushin"
Murgu?a baki tayi tana fari da ido ta ce "Tubarkallah zu?ul-zu?ul maye ya ci kansa da kansa, wallahi ni bana kama da Akushi, son kowa ?in wanda ya rasa"
"Ke dalla ware, meye son kowa ?in wanda ya rasa, aba Kamar gurguwar akuya" Yasir yayi maganar yana dariya.
Haushi ne ya kamata ta bu?e baki za tayi rashin mutunci, ta sanya idonta a cikin na Umar, ta ha?a maganar da zata yi, da lomar abincin ta ha?iye.
Suka gama cin abincin, Yasir ya kwashe kwanuka, ya fara ?o?arin wankewa, Huzaifa ya shigo da tsintsiya zai share ?akin, Umar ya ce ya ajiye tsintsiyar ya bawa Rumaisa ta share.
Haushi ne Yakamata ta lura tun da aka kawo ?ararta ya tsaneta, dama can ba wani shiga shirginta yake yi ba.
Bayan ta kammala sharar ta nemi wuri za ta kwanta Mama ta kalli kan Rumaisa, da ta fara tsifa, tayi rabi ta bar rabi ta ce "Fita ki bar mini ?aki, karki sake shigowa sai kin gama wannan tsifar.
Fitowa ta yi ta na tura baki, tana nema ta yi kuka.
"Autar Mama, meya ?ata miki rai ne?" Cewar Yaya Abubakar da yake ?o?arin shiga ?aki.
Dama ?iris ta ke jira, dan haka ta fara kuka "Ba mama ce ta koreni daga ?akinta ba, wai sai na gama tsefe kaina ba, ni mama ta tsaneni".
Girgiza kai ya yi ya ce "Yi ha?uri ki daina kukan, bari na zo na tayaki tsifar"
Haka suka zauna ya samu kibiya ya tsefe mata kan tsaf, suka wanke gashin, ya ce da safe zai bata ku?in kitso.
Mama ta na kallonsu ba ta kula su ba, ta cigaba da sabgoginta.
Abdallah yana ta dube-dube a kitchen, ya ci karo da allon Rumaisa, duk gefensa ya karye, ga rubutun jiki yayi ba?i ?irin, ba ta sake wani ba.
Ya fito da allon a hannunsa ya ce "Ruma, wannan allon naki yaushe zaki yi wani rubutun?" Ta ha?e rai ta ce "To ban iya ba, sai na iya zan wanke".
"Haka dai, ba kya ja a ko ina, daga arabin har bokon, Allah ya sa su zaneki idan ki ka je sati mai zuwa, baki wanke allon kin yi wani rubutun ba, gandamemiya da ke amma haryanzu a izifi biyu ki ke"
Sai da yayi wannan maganar ta tuna yadda malam Babba ya dinga ?wala mata kira amma ta gudo gida, yanzu sati mai zuwa ta yaya zata je makarantar allon? Kuma muddin abin da ta yiwa malam ya zo gidan nan, ta san ta ka?e".
"Astagfrillah, ni 'ya su meyasa haka ne, garin in gujewa wani hukuncin sai na fa?a wani tarkon, ya zan yi da raina?.
Ayshercool
08081012143
Kar a manta ayi subscribing YouTube channel ?ina na Cool hausa tv
[18/06, 2:35 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Ku yi subscribing YouTube channel ?in mu, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Arewabooks @ ayshercool7724
Watpad@ ayshercool7724
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
p 4
Ko da sati ya zagayo, Mama tana sa ran ta ga Ruma ta shirya ta tafi makarantar allo, amma ta ga bata da niyyar yin hakan.
Sai ma aiki take a tsakar gida, wanda ba ta saba ba, tana na?e yayyenta je komai.
Aliyu ne ya fito daga ban?aki, hannunsa ri?e da buta ya kalli Ruma ya ce "Ke ina makarantar allon?"
Ta ?an ?ata fuska ta ce "Ni na cire kaina na daina zuwa".
"Saboda ke ki ka saka kanki, shine sama ta ka ki ka cire kan ki ko? Da alama baki da gaskiya"
Mama ta fito tsakar gida ta ce "Ali ajiye butar nan ka je mini makarantar allon ka ji me ta aikata, dan ban yadda da ita ba" dan jikinta ya bata Ruma wani laifin tayi.
"Wallahi Mama ba abin da na yi, ba sai ya je makarantar ba, idan ya je ma sharri za su yi mini, ba sa sona malaman"
Mama ta ce "Au malaman ne suke miki ?arya Rumaisa, ai ko me za ace mini kin aikata ba zan musa ba"
Huzaifa daga cikin ?aki ya ce "Dama saboda ?awayenta ya sa ta ce ita ma a sakata a makarantar, ba dan Allah take zuwa makarantar ba ".
Aliyu ya saka jallabiyarsa ya tafi makarantar allon.
Bayan fitarsa rantse-rantse take ta yiwa Mama, akan ita fa ba abin da ta aikata a makarantar nan, amma Mama ta shareta.
"Ruma!"
"Na'am Yaya Sadik "
"Zo ki sayo mana ?wai ki soya mana mu karya"
Kasancewar Ruma akwai kwa?ayi, ya sanya ta daina fargabar zuwan Aliyu makarantar su, ta kar?i ku?i ta tafi aiken da Abubakar ya yi mata.
**********
A kashingi?e take a kan kujera, ta ?ora ?afa ?aya kan ?aya, ta tattara dukkan wata nutsuwarta a kan ?atuwar wayar hannunta, da alama ko me take kallo mai muhimmanci ne.
"Samha me ki ke wa wannan kallon ?urillar ne?"
Wadda aka kira da Samhan ba ta motsa ba, balle ta daina abin da take yi.
Hannu ?ayar ta saka, ta zare wayar daga hannun Samhan, tana dubawa.
Har a wannan karon, Samha ba ta yi motsi ba, balle ta kar?i wayarta ta ba.
"Samha kina da hankali kuwa? Wai dan Allah da gaske ki ke dama?"
Samha ta ja ajiyar zuciya ta ce "Nusaiba, ke da kin ?auka da wasa nake yi dama?"
Nusaiba ta jinjina kai ta ce "Eh, ni ban san abin da ki ke fa?a har zuciyarki ba"
Samha ta gyara zamanta ta kalli Nusaiba, cike da son tabattar mata abin da take fa?a ta ce "Nusaiba, ban fara dan na daina ba, ko zan tafi tsirara zan mallaki abin da zuciyata take muradi"
Nusaiba ta ?an jinjina kai ta ce "Amma ya batun ala?a fa, ko kin manta?".
"Ala?a bata gabana, na san a yadda zan yi wasana. Kar ki manta anjima akwai walima a gidan Shamaki"
"Hmmm Allah ya kaimu, Allah ya sa ba wani banzan abun zaki yi ba".
Wani ?an guntun murmushi Samha tayi, ta ce "Koma dai menene, we should see"
********
Ko da Runaisa ta dawo gida daga aiken Yaya Sadik, tana daga tsakar 6 tarar da Yaya Aliyu a falo yana wassafawa Mama abin da aka gaya masa a makarantar allonsu, ga Yaya Umar a zaune.
"Wallahi mama ba ki ji yadda ake complain a kan yarinyar nan ba, malaminsu ya ce dama ko ta dawo korarta za su yi, ba karatun take yi ba, sai tsokana da fitsara, da damben da yaran mutane, wai sam ba ta da nutsuwa da ?a'a, malam Babba ya tara su zai hukunta su sun yi laifi ta ?au allonta ta gudu, yana kiranta amma tayi masa banza".
Cike da fushi Umar ya ce "Ba kune kuke goya mata baya take wani rashin mutuncin ba, tun da ta san ko me ta ?auko zaku tare mata ba, ku bari ta tsokano wa?anda zasu nakasata yadda gobe ba zata ?ara ba. Babu wanda yake fa?ar alkhairi a kan ta sai sharri" ya ?arasa maganar yana fitowa tsakar gida cike da fushi.suna yin ido hu?u da Rumaisa ta saki ?wan hannunta a ?asa ta na ja da baya, saboda tsoro da fargaba.
Taku biyu ya yi ya dan?ota, ya sanya hannunsa ya ri?e kunnenta ?aya da ?arfi.
Wani irin ihu ta kurma tana ri?e hannunsa, saboda ji tayi kamar zata ?aga kai ta ga kunnen a hannunsa, saboda azabar zafi.
"Dan ubanki idan har ba zaki canza hali ba, makarantar kwana zan kai ki, tunda ba ki in da yake miki ciwo ba, ko mu mayar da ke can ?auye, su miki aure"
Usman ya ce 'Ai Rumaisa sai ka ce wadda ta sha nonon aljana, hatsabibancin ta yayi yawa, ba ta jin magana sam"
Abubakar ne ya fito daga ?akinsu a fusace, ya ?araso ya ri?e hannun Rumaisa, ya kalli Yaya Umar ya ce "Sakar mata kunne" Umar ya ?an yi turus yana kallon Sadik.
"Baka ji bane?"
Sadik ya maimaita masa. Yaya Faruk ya saki kunnen Rumaisa, da idanunta tuni suka yi ja saboda kuka.
Ya janyota ya zaunar da ita a kan tabarma, ya dinga share mata hawayen fuskarta.
Cikin ?acin rai ya ce "Yakamata ku dinga yiwa kan ku adalci a kan yarinyar nan, ita ka?ai ta tashi a cikinmu mace, tayaya zaku ce sai kun tan?warata yadda ku ke so? Tayi laifi kowa yayo kanta, ba mai yi mata nasiha, daga mai ce mata munafuka sai me ce mata aljana haka ake rayuwa?"
Yasir ya ce "Wallahi Yaya Sadik, duk ranar da yarinyar nan ta kwaikwaya maka rashin mutuncin da take aikatawa zaka gane ba tsanarta aka yi ba"
"Koma dai yane, a dinga barin yarinya ta huta a daina takura mata haka "
Guntun tsaki Umar ya ja, ya fice daga gidan gaba daya, suna zaman zamansu Mama ta haifo wannan 'yar kalen hanjin da ta gallabi rayuwarsu.
Yau cikin dare, Mama ta tashi tana ibada, kamar yadda ta saba domin a cewarta wanda duk ya tara zuriya yake neman kuma dacewa, bai ga ta bacci ba.
Fitilar ?akinta ta kunna, haske ya gauraye ko ina, Rumaisa tayi rashe-rashe a kan katifa, zaninta daban ita daban daga ita sai wando, kanta ko ?an kwali babu.
Mama ta girgiza kai, ta janyo zanin ta ?aura mata, ta saka mata hula ta lullu?eta, sannan ta fice ta ?auro alwala ta zo ta tayar da salla. Sai dai sam Ruma ba ta san an yi bama, tana ta fama da bacci.
Can Mama ta kuma juyawa, amma ta ga Rumisa ta kuma yada zanin, ?afafuwanta duk suna ?asan katifar, ta kuma tum?ur tana bacci.
Haushi ne ya kama Mama, ta ?arasa in da take, ta ?ala mata duka a cinya. Amma maimakon ta tashi, sai ta sake dun?ulewa tana bacci.
"Ke Ruma, ba zaki tashi ba sai na saka miki bulala?" Da ?yar ta tashi tana murza ido tana kalle-kalle.
'tashi ki ?auki rigarki ki saka, ki ?aure kanki ki je ki yo alwala ki salla".
"Wai har asubar ta yi ne?"
Mama ta ce "Wato ke idan ba sallar farilla ba, baki san ki yi nafila ba, sai dai ki saki le?e kina bacci. Ki je kiyi alwala ki zo ki yi salla ki ro?i Allah ya yaye miki wannan wautar da rashin hankali da kike fama da shi" kafin Mama ta gama maganar, Rumaisa ta sake ?ingirewa ta kwanta.
Aikuwa mama ta ?ule, ta janyo mafici ta shiga rafka mata a cinyoyinta, a razane ta mi?e tana sosh-soshe.
Mama ta bata riga da ?an kwali ta ?aura, ta korata tayo alwala.
Mama ta koma kan tata sallayar ta cigaba da salla.
Kusan mintuna arba'in, Mama ta manta ta tura Rumaisa tayi alwala, ta kalli shimfi?arta taga bata wurin.
Da sauri ta tashi ta fita tsakar gida tana dubawa, sai dai babu Rumaisa babu dalilinta.
Lelle?awa Mama ta hau yi, tana nemanta a cikin gidan amma bata nan.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ina yarinyar nan ta shiga ne haka?" Tayi maganar lokacin da ta ?arasa soro tana haska fitila, amma taga ?ofar gidan a rufe.
?ofar ?akin samarin gidan ta tsaya tana bubbugawa da ?an ?arfi.
Usman ne ya taso cikin yanayi ya bacci, ya kalli Mama ya ce 'Mama lafiya kuwa?".
Cikin tashin hankali ta ce "Ruma na tasa tayi sallar dare, daga ta fito tayi alwala, na nemeta na rasa".
?walalo ido waje yayi, ya ce "Ruman? To ina ta tafi?"
Mama ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, na duba ?ofar gida tana rufe da sakata ba a bu?e ba"
Mamaki duk ya cika Usman ya ce "To in ta shiga a tsohon daren nan, bari na sako rigata a bu?e gidan a dudduba".
Ya shiga cikin ?akin, ya kunna wutar lantarkin ?akinsu, sai ga Ruma a tsakiyar su Yasir tana bacci.
Kunna fitilar ne ya sanya Huzaifa ?o?arin yin juyi, amma ya ji mutum a kusa da shi, yayi zaton Yasir ne, dan haka ya dage ya hanka?a Rumaisa, ta kifa kan Yasir amma ba ta farka ba.
Usman Ya ce "mama le?o kiga"
Jiki na rawa mama ta shiga ?akin, daidai lokacin da Yasir ya ji nauyi a kansa shi ma ya dage ya hanka?ata gefe guda.
Mama ta shiga tafa hannuwa tana salati, a irin magagin bacci, da shirme na Rumaisa tsaf za a saceta tana wannan baccin na asara.
A ?ufule Huzaifa ya tashi yana zage-zage ya zata Yasir ne yake damne shi, amma ya ga Ruma a tsakiyar su, ga su Mama a tsaye.
"Ke uban me ki ke yi a ?akinmu, mama meyafaru?"
Jin hayaniya ya sanya Sadik ma farkawa, ya dinga kallonsu ?aya bayan ?aya 'mama lafiya kuwa'.
'lafiya lau, kai Huzaifa taso mini ita'
Abubakar ya kalli in da Rumaisa ke ta more laushin katifa tana barci.
"Wai me ya kawo yarinyar nan ?akin nan?"
Usman yayu masa bayani kamar yadda Mama tayi masa.
Sadik ya ce "Kai Huzaifa, kai da Yasir ku sauko ku bar mata katifar dan Allah, wannan ba tashi zata yi ba"
Yasir ya ce "Kaii, Yaya haryanzu fa yarinyar nan tana fitsarin kwance, kawai a tasheta ta fita, kar ta tsula mana fitsari dan katifar nan wuyar bushewa za ta yi".
Yaya Umar kuwa tun shigowar Rumaisa yana kallonta, lokacin bai da?e da kwanciya ba, ya ganta ta shigo tana tangal tangal, ta nemi wuri ta kwanta, tun da ta shigo yana kallonta.
Mama ta ce "Ba zata kwana a nan ba, taso mini ita ta wuce mu tafi".
Yasir ya daddaki Rumaisa a kafa?a, amma ta hau surutai da irin fa?ace-fa?acen da suke yi da yara a makaranta.
?arshe haushi ya ?ule, Umar ya tashi dan?o Ruma ya hanka?owa Mama ita tsakar gida, ya rufe musu ?ofa.
Mama har mamakin wannan magagi da kuma suratan baccin da Rumaisa take yi, ita duk wani da mutane suke yi, nata ya zarta ?a'ida.
Har mama ta kama hannunta zuwa ?aki, magagin bacci take yi.
******
Sassanyar iskar da bishiyoyin ke bayarwa ne ya ha?u da ?amshin furanni, tare da samar wani kyakkyawan yanayi mai sanyawa zukata nutsuwa da annashuwa.
Duk da wannan tarin ni'ima, gaba ?aya Samha ba ta jin dadin yanayin sam.
Wayar hannunta ce ta fara ringing, wadda ta katse mata dogon tunanin da take yi, ?agawa tayi ta kara wayar a kunneta ba tare da ta ce komai