Showing 48001 words to 51000 words out of 182697 words

Chapter 17 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22383

sai masifa take yiwa mutane, ni na zaci matar sarki ce ma, yakamata a samu mai kwa?eta ya zata din ga hantarar mutane?"

Hauwwaliya ta daki cinyar ruma ta ce "Ke, ?anwar mamanta cefa"

Yarinyar ta yi murmushin ya?e ta ce "Bari a kawo muku Abinci, sai mu je wurin ki?an ?warya da kilisa"

Ruma ta mi?e ta ce "Hauwwaliya, ni dai zan je wurin da na ga an ?aure dokuna na kallesu, idan an kawo Abincin ki ?ulle mini nawa a ledar da ki ka zo da ita" bu?e baki Hauwwaliya ta yi, da jin hansfreen da ruma ta yi musu.

Kai tsaye ruma ta fito tana cigaba da kallon gidan, da yadda manyan mata ke shiga suna fita, da shiga kala-kala.

"Ke ba kya gani ne, meye haka?" Ruma ta ?aga kai ta kalli wadda ta daka mata tsawar. Matar da take ta hantarar mutane ce.

"Eh bana gani, sandata na fito nema, ke da ki ke gani meya hana ki kauce?" Ruma ta yi maganar tana tsare Samha da ido.

Wata mummunar fa?uwar gaba ta ziyarci Samha, da ta yi tozali da idanun ruma, ga ta ?arama amma wani abu mai kaifi ne a idanun ruma.
Ruma ta ra?ata ta wuce abinta. Da sauri Samha ta bi bayan ruma, amma ta nemeta ta rasa.

Kai tsaye burgar dawakin da suka wuce ta je ta tsaya. Ta tarar da wani dogari yana basu Abinci.
"Sannu da aiki"
Ya kalli ruma ya ce "Yauwwa sannunki"
"Dan Allah ina dokin sarki a nan?" Yayi murmushi ya ce "Nan babu dokin sarki, na 'ya'yan sarki da manyan Hakiman fada ne"
"Dan Allah ka cewa sarki ya bani doki ?aya"
Yayi dariya ya ce "Ke idan aka baki doki ya zaki yi da shi?"
"Hawa zan din ga yi mana" ruma ta din ga yiwa dogarin nan surutu, sai da ya gaji sannan ya ce "To ai Shikenan, yanzu dai fita za ayi da su, za ayi kilisar angwaye"
Ta jinjina masa kai, ta koma gefe ta tsaya, tana kallo aka shirya dawakan, aka yi musu kwalliya sannan aka fita da su.
Hauwwaliya ce ta fito ita da ?awar ta ta tana fa?in "Ke ruma, tun ?azu jira nake ki dawo, amma ki ka ?i komawa"
"Ke ?yaleni, kallon dokuna nake"
?awar hawwaliya wadda suke da Turaki, ta ce "Mu je to, sai mu kalli kilisar"
Suka fita daga cikin gidan gaba ?ayansu, kan barandar wani gida suka je suka tsaya, suna tsumayin a fara kilisar.
Abin yana burge ruma sosai da sosai, duk wanda ya zo wucewa sai ta ?aga masa hannu tana tsalle.Tun da suke wucewa babu wanda ta kira sarki, sai da ya zo wucewa tare da ango.
"Sarki mai koriyar alkyabba, a dawo lafiya, dan Allah ka bani kyautar doki, ko kuma ka ?anani a kan dokinka!!!"
(Wannan 'ya ni kaina tana bani ciwon kai ?? in kun ji ni shiru ku dinga yi mini addu'a, Allah ya ?ara mini lafiya ??)

Mai nema daga farko, ya duba watpad Please ??
Ayshercool
08081012143
[21/07, 10:53 am] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA


Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHE?I TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*




https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban ha?a 1k subscribers a channel ?ina ba, anya akwai amana kuwa??*

Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.



*Ina yiwa 'yan uwa musulmi barka da shigowar, sabuwar shekara musulunci, Ubangiji Allah ya sada mu da alkhairan da yake cikinta, akasin haka kuma Allah ya iya mana*






P 15




Gaba ?aya aka juyo ana kallon ruma, mutanen wurin suka hau dariya.
Shi kansa Jamil da yake ango, da sauri ya ?ara rufe fuksarsa da rawani yana murmushi, dan saura ?iris dariya ta ?wace masa.
Adam kuwa sake tsare gida yayi, kasancewar dama can ba mai yawan fara'a bane ba, jin muryar ruman yake a wani abu daban, anya mutum ce?. Kamar zai juya domin ganin fuskarta, sai kuma ya fasa ya sake rufe fuskarsa da rawaninsa, yayi gaba.

?awar Hauwwaliya kuwa ?an zaro ido ta yi ta ce "Ke kin san waye wannan kuwa?"

Ruma ta ce "Ba shine sarki ba?"

"Ba sarki bane ba ai, ?an gidan marigayi Galadima ne da ya rasu, sunan sarki ne da shi, Takawa ake ce masa, wallahi ki ka bari ya kamo ki, sai kin gayawa mutanen garinku, ba ki san yadda muke jin tsoronsa ko a family ba, hmmm su Ummanmu sun girme shi amma tsoronsa suke ji, ba ya wasa da mutane"

Bayan gama jin jawabin da aka yi mat, ta ta?e baki ta ce "Ta?, na gama yaya umar, ni gani nake kamar na ta?a ganinsa ma, ko a ina oho mini dai na manta, so nake na ga fuskar sa"

Dariya yarinyar ta yi ta ce "Ki zo wataran mu je gidansa, ko gidansu sai ki ga fuskar sa amma daga baya zan la?e ke ki shiga" ruma ta kwashe da dariya ta ce "Ke da wasa nake miki, amma dai zan zo wataran a ?anani a doki"

Yarinyar ta dubi Hauwwaliya ta ce "To yaushe zaku kuma zuwa?"

"Ke, ita fa ruma ba a nan unguwar take ba, zuwa ta yi yau zata koma gida, a ?orayi take fa"

"Haba, idan mun zo hawan salla wataran, sai na zo gidanku"

Ruma ta yi murmushi ta ce "Allah ya kawo ki, amma baki gaya mini sunanki ba"

"Sunana Jannah, ke kuma ruma ko?" Ruma ta jinjina mata kai alamar eh.

Ta mi?owa ruma ledar viba ta ce "Ga sa?onki" ruma ta kar?i ledar ta yiwa Jannah godiya, suka tafi gida.

Allah ya taimaketa, Abdallah bai dawo ba sai bayan salla magariba, sannan ya ?auketa suka tafi gida.

Tun a hanya yake tambayarta meye a ledar hannunta, amma tayi mursisi ta rungume ledarta ta?i nuna masa, har suka je gida.

Mama sai da tayi mita "Abdallah ka ?aukar mini 'ya ka tafi da ita, tun ?azu nake zuba ido in ga ta ina zaku dawo, ka san da wuri take bacci, kun je kun yi dare".

Abdallah ya ce "Mama wai dama kina son yarinyar nan?"

Mama ta bu?e baki, tare da yin murmushi ta ce "Dan ?aniyarka in haifi 'yar a cikina ka ce dama ina son ta, ni duk cikinku waye bana so, ai banda hali irin na ruma son da nake yi mata daban ne, kasancewar ta mace ?aya tilo a cikinku, amma sanin halinta ya sa wasu lokutan nake kamar bana son ta, idan ba haka ta?arar da zata yi sai Allah"

Ruma ta ce "Kai ban ta?a jin kin ce kina sona ba, ashe idan na mutu zaki yi kuka"

Mama ta ce "Ke rabani da shiririta, tashi ki yi sallar isha'i ki zo ki ci Abincin dare ki kwanta, gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta".

Ruma ta tashi ta ce "Ai ni yau ba abincinki zan ci ba, na gidan sarauta zan ci" mama ba ta ?au maganarta da muhimmanci ba, sai da ta idar da salla, ta janyo viva, tana firfito da Abinci.
Mama ta matsata da tambaya, ta bawa mama labarin abin da ya faru.

Abdallah ya ce "Wallahi mama ban ma san ta je ba, na ?arasa na gaisa da abokaina na tsohuwar unguwarmu, shi ne ta samu ta tafi, yanzu da doki ya takaki ki ce me?"

"Doki bai takani ba, sai abin arziki da na samo, kun ga gidan sarautar nan, wai gidan Turaki, gaskiya suna da ku?i, mama kalli kaza guda ta sako mini, kalli kayan gara, ya ma sunan wannan dun?ulellen abun mai kamar kashi?" Ta yi maganar tana nunowa mama Alkaki, gaba ?aya ko a jikinta, dan ita ba ta ji a jikinta ta yi laifi ba.

Mama zurru kawai ta yi da ido ta na kallon ruma, mama ta gaji da fa?a a kan halin ruma, dan haka ta yi shiru ta na fa?in Allah ya shirya.

******

Yanayinsa ne ya nuna wa Ammi cewar ya na cikin damuwa.

"Takawar ka lafiya babban mutum, basarake kuma jinin sarakai, me yake faruwa ne?"

Adam ya yi murmushi ya ce "Bakomai Ammi, gajiyar bikin nan ce ta Jamil, kuma kwana biyu ban hau doki ba yau na hau doki, duk jikina ciwo yake"

Ammi ta yi murmushi, a dole wai sai ya ?oye mata akwai abin da yake damunsa, dan haka ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ka je ka ?an watsa ruwa ka kwanta ka samu ka huta" ya jinjina mata kai, yana shirin tashi ta ce "Yauwwa Takawa, ni ko tun da ka dawo, ka je ka gaida babarka?"

Take ?an ragowar annurin fuskarsa ya ?auke, ya ?an ?ata fuska tare da girgiza kai alamar a'a.

"To ka san dai yakamata ka yi hakan, bana son ?ananan maganganu, tun da yanzu a gajiye ka ke, kuma kana gidan nan yakamata in an jima ko da safe dai, ka je ku gaisa ka ce mata ka dawo"

"To" ya amsa a ta?aice.

*****
Mama sai fama take da ruma a kan shirin makaranta, sai la?ai-la?ai take yi, sai ta fara shiri, sai ta tafi ban?aki yawon kashi, saboda ciye-ciye da ta yi, ya ?ata mata ciki. Mama ta kai matu?ar ?uluwa sai fa?a take yi, ruma kuwa ko a jikinta.

Har ta ?au jaka, sai ga kira a wayar mama.
Mama ta ?aga tare da yin sallama.
"Da ga makarantar su Rumaisa ne, dan Allah idan za ta taho, a ha?ota da wani babba daga gida"

A ?an ru?e mama ta ce "Lafiya, wani abun ta yi?"

"A'a, a dai ha?ota da wani babba, ko babanta ko wakili"

"To shikenan, babu laifi, za ta taho in sha Allah" mama ta ajiye wayar ta kalli ruma. "Ruma, me ki ka yi a makaranta?"

"Ni kuma? Ni babu abin da na yi"

"Ki gaya mini tun kan raina da na ki su ?aci"

"Wallahi mama ni babu abin da na yi"

"Amma aka ce ki je ke da wani babba, anya ruma ke fa ba gaskiya ki ka cika ba"

Ruma ta ce "Ni dai wallahi na san babu abin da na yi"
Mama ya gya?a kai ta ce "Ai shikenan, zamu gani".

Ta ?arasa ?ofar ?akin 'yan mazan, ta ce "Waye ba zai fita ba yau a cikin ku? Wani ya zo ya je mini makarantar su yarinyar nan, an kira ni an ce ta je ita da wani"

Yaya Aliyu ya ce "Mai sunan Baba dai ya tafi makaranta, ni ma ina da lectures ?arfe goma sha biyu, amma bari na zo mu je na ji menene"

Ita kanta ruma tunani take Meyasa ake neman wani a gidansu a makaranta?

Suna tafe a hanya da Aliyu yana mita "Ke, kawai kin sa an katse mini bacci na, Allah ya sa na ji wani rashin jin ki ka yi, na samu abin duka na zane ki"

Ta tura baki ta ce "Ni dai na san ban yi komai ba, wata?ila ma wani abun arzikin na yi ake nemanku, amma kowa ba ya kyautata mini zato"

"Ruma ai ke abin arziki bai kar?e ki ba, sanin halinki ne ya sanya ake tsoron lamarinki"

Suna tafe a hanya, yara da manya mata da maza kusan kowa ya san ruma, suna tafe ana kiranta ta na ?aga wa mutane hannu, har suka isa makarantar.
Ofishin Headmaster suka je, ruma sai rarraba ido take tana 'yan ciye-ciyen ta.
Aliyu suka gaisa da Headmaster, ruma ma ta gaida Headmaster ta koma gefen Aliyu ta tsaya.

Headmaster ya kalli ruma ya ce "Waye ya sallameki jiya ki ka tafi?"

Ruma ta sunkuyar da kai ba tare da ta ce komai ba.

Headmaster ya dubi Aliyu ya ce "To, a gaskiya ?anwarka ce ko 'yar ka ba ta jin magana, sun samu sa?ani da abokiyar karatunta, an yi musu sulhu amma ba ta ji ba, sun kuma fa?a jiya, ta karyata a hannu, kuma ta bita hanya ta din ga jifanta da dutse wai jifan shai?aniya. To uwar yarinyar nan ta ce ba zata yadda ba, yanzu haka tana division ta kai ?ara, suna jiran mu, ka san ?abilu wasu lokutan basu da tawakalli ba su san ?addara ba".

Aliyu ya ce"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke dan ubanki a garin yaya ki ka karya 'yar mutane, kuma baki fa?a ba?"

Ruma ta zare ido ta ce "Kaii Innalillahi, wannan ?an dukan da na yi mata ne ta karye, zagina fa tayi ta zagi mama, ta dakeni shekaranjiya waccan, amma aka bani rashin......."

Cikin tsawa Aliyu ya ce"Rufe wa mutane baki, sai ki tashi mu tafi idan kulle ki za su yi ke ki ka jiyo, tashi mu tafi"
Ai ruma ko a jikinta, ta tur?une fuska.

Haka suka tasa ruma a gaba, zuwa police station. Mama sai kiran waya take ta na tambayar meyafaru, Aliyu ya na ce mata babu komai.

Ko da suka je police station, suka tarar da Asiya, an na?e hannu, ga fuskarta duk a kumbure. Ruma ta kalli babar Asiya, kujera ba ta ?auketa ba, sai wani benci aka saka mata ta zauna, fuskarta ta sha uban tsagu kwaya-kwaya.
Ruma ta sunkuyar da kai ta na so ta yi dariya.

Suka nemi wuri suka zauna, wani ?an sanda ya kalli ruma ya ce "Yanzu wannan ce ta karya ta?"

Cikin gur?atacciyar hausa, babar Asiya ta ce "shi ne ya karya ?ana wannan, ke ni ki ka zana a allo, ban fi babarka kyau ba? Ka zana katuwar mace wai ni ne, kuma ka karya mini ?a, wallahi ba zan yarda ba, yaro ba tarbiyya"

Ruma ta ce "Ni fa mace ce ba namiji ba, kuma ita ta cewa babata tsohuwa, kuma wallahi mama ta fi kyau"

?an sandan ya dakawa ruma tsawa, amma ko gezau ta tsatstsare shi da ido.
Ta tsuke baki, tana cigaba da zazzago madara a hannunta tana sha.

Aliyu ya yi ajiyar zuciya ya yi ?asa da murya ya ce "Wallahi idan ba ki nutsu ba, sai na bar ki a wurin nan, su yi miki duk abin da suka ga dama, kuma wallahi matar nan ta zauna a kan ki sai dai buzunki"

Ta waro ido ta ce "Kai dan Allah ka bata ha?uri, ai sai na mutu idan ta zauna a kaina"

Aliyu ya gyara murya, ya dubi ?an sandan ya ce "Dan Allah Yalla?ai, a yi maganar nan a kasheta a yanzu".

?an sandan ya ce "A'a, case ?in a hannun DPO yake, sai kun jira ya zo"

Aliyu da Headmaster sai bada ha?uri suke, Headmaster sai cewa yake a samu a rufa maganar nan, a rufe case ?in tun da abu ne na yara. Amma babar Asiya ta ce ba ta san zancen ba, sai an biwa 'yar ta hakkinta.

Aliyu suka ?an fara hira da ?an sandan da yake wurin, ruma kuwa da sun ha?a ido da Asiya, sai ruma ta zare mata ido. Aikuwa suka ha?a ido da babar ruma, tana zarewa Asiya ido. Aikuwa ta taso tana tafe da ?yar tana bala'i, ta yo kan ruma.
Ruma ta zabura ta mi?e, ta haye bayan Aliyu ta na ihu.

"Wanna yaron ba shi da mutunci, ba shi da tarbiyya wallahi sai na yi shari'a da baban shi, ya karya mini ?a kuma yana zare masa ido"

Aliyu ya janyo ruma daga bayansa, ya tanka?ata gaban babar Asiya, ya ce "Ga ta nan ci ubanta tun da ba ta da kan gado"

Ruma ta din ga kurma ihu tana "Na shiga uku, dan girman Allah kiyi ha?uri, ki yi mini rai babarmu" babu kunya babar Asiya ta taso tana ?o?arin make ruma.

Ganin rashin dacewar abin da babar Asiya ke shirin yi ne ya sanya, ?an sandan shiga tsakani yana bawa babar Asiya ha?uri.
Ta hau ta din ga bala'i a kan ko sisi ba zata yafe ba, sai an biya ku?in maganin da suka kashe.

Aliyu cewa yake "Dan Allah Yalla?ai ka bari ta jibgeta, yadda gobe ba zata ?ara ba"

"A'a gara dai a bata ha?urin, kar karyayyun su zama biyu"

Ihu ruma take yi tana fa?in "Dan Allah babarmu ki yi ha?uri, wallahi ba zan ?ara ba"

DPO ne ya yi sallama, gaba ?aya hankalinsu ya koma kan sa.

Nan ?an sandan ya ?ame tare da sarawa DPO.

DPO ya ?are musu kallo, sannan ya ce "Sannunku"

Aliyu ya ce "Yauwwa Yalla?ai sannu da zuwa"

Ruma ta dur?usa har ?asa ta ce "Ina kwana"

"Lafiya lau Baby girl, me ki ke yi a nan ba ki tafi school ba, na ganki da uniform?"

?arasowa babar Asiya ta yi, tinkis-tinkis "Yalla?ai, shi ne yaro da ya gaya maka jiya, ya karya mini yaro a school"

Bu?e baki ya yi, ya na kallon ruma ya ce "Ke, ke ki ka karya musu 'ya Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ku shigo daga ciki mu yi magana ".

Suka shiga ofishin DPO, ruma sai ma?alewa Aliyu take yi, tana sunkuyar da kai kar su ha?a ido, da babar Asiya.

Tun da suka shiga babar Asiya take mayar da yadda aka yi tana masifa, DPO mamaki yake yadda aka yi ruma ta iya karya wata, ba da abin duka ba da hannunta. Sai da ta gama banbamin bala'inta, sannan ya dubi ruma ya ce "Yarinyar kirki, zo nan"

"Dan Allah ka yi ha?uri kar ka kai ni prison" Ruma tayi maganar tana tauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login