Showing 141001 words to 144000 words out of 182697 words

Chapter 48 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22425

yaron, zuwa yanzu babu abun da yake damunsa, kuma gwaje-gwaje sun nuna malaria ke damunsa, sai kuma pneumonia, amma ba wata mai damuwa ba.
Mama ta ce "To masha Allah, Ubangiji Allah ya ?ara afuwa".

Mama ta tafi da shi ?akin da rumaisa take, ta kar?o pack ?in da Bashir ya sayo na jaririn, da madararsa da komai.

Ta ha?a ruwa ta yi wa yaron wanka, ta shirya shi, ta ha?a madara ta bashi, ta mi?awa rumaisa shi. Ruma har da ajiyar zuciya ta zubawa yaron ido, sai ta fara hawaye.

Mama ta ce "To kukan na menene?"

"Mama tausayin yaron nan nake ji, mun sha wahala sosai da tuni an kashemu, ko shi an kashe shi, wasu mutane ne suka ce dole a kashe shi, kar ya rayu fa".

Mama ta ce "Wasu mutane ne?"

"Nima ban san su ba, Allah ya baka lafiya yarona" tayi maganar tana shafa kan jaririn, tana murmushi shi kuma sai cin hannunsa yake yi, yana kallon ruma yana lumshe ido.

Mai sunan Baba ne yayi sallama, shi da Usman, hannunsu ?auke da kayan abinci.

Duk suka gaida mama ta amsa musu, ruma ta ce "Mai sunan baba ina kwananku?"

"Lafiya lau ya jikin naku?".

"Da sau?i Alhamdilillah"

Umar ya ce "Allah ya ?ara afuwa, kai Abdallah tashi ka ha?a mata abun karyawa"

Abdallah ya ha?awa rumaisa shayi da uban ?wai, ya bata da ?yar ta sha shayin, ta ce ita bata son cin komai.

Mai sunan Baba ya sanya mama a gaba, a kan lallai sai ta tashi sun tafi gida, sai ta je ta huta ya kaita ganin likita, da ?yar mama ta amince, ya sakata a gaba ya ce Abdallah ma ya tashi ya je gida ya huta ya dawo da yamma. Aka bar ta da ita da Usman, sai jaririnta da take ta shafa kansa tana murmushi.

Adam kuwa kwanan zaune yayi, yayi kuka kamar ya fita a hayyacinsa haka ya wayi gari, Ammi ma kusan a haka ta kwana, tunani kawai take yi a kan ina zasu samu mafita, ta ina za su fara.

Wajen ?arfe goma na safe, Bashir ya je gidan su takawa, ya sa aka yi masa iso wurin Ammi, ta bayar da damar a shiga da shi, cikin girmamawa suka gaisa ya ce "Ammi dama na zo ne mu koma asibiti da Adam, muje mu ji ko akwai wani bayani da zamu samu daga bakinta yarinyar, tun da naga jikinta da sau?i, amma na kira wayoyinsa a kashe na je can gidansa an ce bai kwana a can ba".

Ammi ta ?an dube shi ta ce "Malam bashir ban ji da?in ?oye mini abun da ke faruwa da ku ka yi ba, gaba ?aya kun jagwalgwala al'amura, amma shikenan na san ba laifinka bane, shi ya fi kamata ya sanar da ni, bari na duba ko a gidan nan ya kwana ma"

Ko da Ammi ta je ?akin Adam a zaune ta tarar da shi, babu alamar ya runtsa, idanunsa sun yi jawur sun kumbura.

Ammi ta ce "Ka yi sallar asuba kuwa?"

Ya jinjina mata kai alamar eh.

"Tashi ka yi wanka, ka karya ga Bashir can yana jiranka"

"Ammi dan Allah ya ?yaleni, bana son jin komai, ka?aici nake so".

"Shi ka?aicin me zai maganta maka bayan mai faruwa ta riga ta faru, so kake jama'a su fuskanci wani abu kafin mu kai ga samun mafita? Ka tashi ya ce so yake ku je ko akwai bayanan da zaku samu a bakin yarinyar"

Adam bai kums cewa komai ba ya tashi ya shiga ban?aki, bai san a yaya yayi wankan ba ma, ya fito, Ammi ta saka shi a gaba, ya ?an zu?i shayi ka?an ya fita. A falo ya tarar da Bashir, su Iman suna gaishe shi, amma babu wadda ya amsawa haka ma barorin da suke wurin, ya ce wa bashir tashi mu tafi.

Ammi ta bi bayansu tana yi musu magana ?asa-?asa.

Nusaiba ta yi wa iman kallon meyake faruwa ne, iman ta ?an ?age kafa?a alamar ita ma ba ta sani ba.

A harabar gidan suna shirin hawa mota, sai ga motar Jabir ya shigo gidan, takawa bai tsaya ba ya shiga motar bashir, saboda baya son magana da kowa a halin yanzu, kuma ya san jabir ritsa shi zai yi da tanbayoyi masu ma'ana da marasa ma'ana.

Takawa suna tafe a hanya shi da bashir, babu mai cewa komai, can bashir ya ce 'Adam ka kwantar da hankalinka, komai zai tafi dai-dai ina kyautata zaton zamu samu duk wani information da zai iya taimaka mana a kan binciken mu".

"Bashir, komai ya hargitse mini, ban san ta ina zan kuma sake fuskantar matsalolina ba, jiya kwana na yi ina tunani, yaya aka yi yarinyar nan ta ku?uta da jariri ina Aisha take, wani irin tashin hankali da tozarci ne haka ace matarka ta haihu a hannun 'yan ta'adda?" Yayi maganar cikin tsananin damuwa da zafin rai.

Bashir ya dafa shi ya ce "Calm down, ka bi komai a hankali, komai zai dai-dai ta in sha Allah".


Baba uwani ta kasa zaune ta kas tsayez babban burinta shine ganin yadda za ta yi ta san meyake faruwa, ta samu ta kaiwa Mummy labari, domin a kan idonta Ammi da takawa suka shigo a daren jiya, haka zalika yanayin yadda ta ga fuskokinsu a wayewar garin yau ta sake tabattar da akwai wani abu da yake faruwa kuma da alama babban al'amari ne, amma babu wata hanya ko kafa aka bari balle ta ji labarin.


Bashir sai da ya tsaya a hanya ya sai carton carton na ruwa da maltina, suka ?arasa Asibitin da rumaisa take.

Bashir ya sanya masinja ya ?auko kayan da suka zo da su, ya biyo su.

Da sallama suka shiga ?akin da rumaisa take, ba dan ?arancin shekarunta ba, kai ka ce mai jego ce, saboda yadda take rungume da jariri a hannunta, usman ya amsa musu sallamar ruma kuma ta ?ago ta kallesu.
Bashir ya sallami masinjan nan, sannan suka zauna, suka gaisa da usman, suka tambaye shi mas jiki ya ce da sau?i, wanda duk bashir ne yake yi, Adam ba ya iya magana.

"Rumaisa ba magana, ina kwana ya baby?".

"Lafiya lau" ta fa?a tana satar kallon takawa da yayi zuru-zuru ta ta?e baki.

Mu ga babyn yayi maganar yana kar?ar jaririn yayi murmushi ya ce "Alhamdilillah, kin ga babyn zai warke ya barki, gaskiya ki daina langwai" ita dai ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Bashir ya mi?awa adam yaron, ya kuma kallonta ya ce "To ya jikin naki?"

"Ba sau?i" ta fa?a kai tsaye.

Usman ya ce "Ke fa da?ina da ke ?arancin tunani, ba zaki godewa Allah ba ki ce da sau?i, zaki ce ba sau?i?"

Sai ta fara kuka ta ce "To ina sau?i? Mama ta aske mini gashi, bana iya taka ?afata ?eyata ma ciwukan zafi suke yi mini, ga ha?ar?arina ciwo yake mini".

Bashir ya ce "Ya salam, kin gayawa likita? Ko kin fa?i da wurin ne?"

Ta ce "A'a wani sule ne ?ato ya dinga takani da ?afarsa a wurin, tun daga nan yake mini ciwo"

Bashir ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Adam ba shi jaririn a mayar da shi nursery dan Allah, dan na ji yana atishawa ko sanyin nan yayi masa yawa".

Adam bai motsa ba, ya zubawa yaron ido yana jin wani irin tausayinsa da ?aunsrsa na shiga ransa, ya kar?i jaririn ya bawa usman, usman ya fita mayar da shi ya rage daga takawa sai bashir da ruma a ?akin.

Bashir ya kalli rumaisa ya ce "Rumaisa, kamar yadda dai na yi miki bayani da fari, Adam abokina ne, dukkaninmu jami'an tsaro ne na farin kaya, zai yi miki wasu tambayoyi ne dan Allah ki bamu ha?in kai"
Rumaisa ta kawar da kanta gefe, ta?i ko kallon in da Adam yake.

Adam ya numfasa ya ce "Ta yaya zaki tabattar mini wannan ?an na Aisha ne, ita ta haife shi"

Rumaisa jin tambayar ta yi kamar da rainin hankali a ciki "To ai ba sai ka tabattar ba, tun da dai ni na san ?anta ne, shiyasa na ce ba kaine babansa ba".

Bashir ya ce "A'a ruma yi ha?uri, kin san komai a hankali muke bi tun daga tushe, ki bamu amsa Please".

Ta ?aga filon da take kai, ta janyo ?ankwalin aisha, da yake a ninke, ta wurgawa adam cinyarsa "Ni banda wannan ban san me zance maka ba".

Ya saka hannu ya ?au ?an kwalin yana jujjuya shi, yana tuna wasu abubuwa da suka faru, tabbas ?an kwalin aisha ne.

Ya ?aga kai ya kalli Ruma ya ce "Ina aisha take yanzu? Ya aka yi ki ka ku?ita da jaririn? Ita tana ina?"

Tayi masa banza, dan ranar ?arshe da ya wanketa da ruwan kwata ne ya fa?o mata.

"Ruma amsa mana, ina aishan take? Kar ki damu, adam ?an sanda ne na farin kaya, ki yi masa bayanin komai"

Cikin tura baki ta ce "Saura na korayen kaya, ni ban san in da take ba"

"Kamar ya baki san in da take ba, ya ina magana kina shareni, ina Aisha take ina matata"

Ruma ta za?al?ale ta ce "Ka bita dajin ka ?aukota, ka san kana sonta ka bari aka sace ta, ka ?i zuwa ka fitar da ita, da ku ba gawara babu ba, ba da jami'an tsaro ake ha?a baki ba, haka aka ce da bakin su 'yan bindigar suka fa?a, in so kuke ku ganta sai ku tafi dajin ai, kuma wallahi idan kuma kun sani aka sace mu kuka ?i taimaka mana a fito da mu, sai Allah ya saka mana, dukan da na sha a wurin mutanen nan ma ya isheni, ka zo zaka dameni"
Gaba ?aya ido suka zubawa rumaisa, tana kuka tana tsiwa.

Adam ya ce "Ni kike gayawa haka?"

"Tsoronka zan ji ne, wallahi bana tsoron kowa sai Allah subhanahu wata'ala, kuma wallahi tun da Allah ya sa na fito sai ka gane ba ka da wayo, sai na rama abun da kayi mini"

Kallon tuhuma Bashir ya shiga yi wa rumaisa da Adam, kenan sun san juna, akwai wani ?oyayyen abu kenan a tsakaninsu.

Usman ne yayi sallama, ya tarar da rumaisa tana kuka, su kuma sun zuba mata ido.

Ya ce "Lafiya kuwa?"

"Ba wannan ne ya sakani a gaba yana zare mini ido ba, wai sai na gaya masa in da matarsa take, kuma ni ban san komai ba, likita ma fa ya ce kar a din ga takura mini amm yake hantarata"

Adam ya dafe goshinsa yana tunanin meya dawo da wannan jarababbyar yarinyar rayuwarsa, meyasa take li?e da ?addararsa ne.
Shi kuwa bashir mamaki ne ya ishe shi, maganganun ta sun girmi shekrunta, ya kalli usman ya ce "Tambayoyi kawai muke mata, so muke mu yi ?o?arin ceto uwar yaron ita ma, ba wani abun aka yi mata ba".

Usman ya kalleta ya ce "Ke ki gaya musu abin da ki ka sani mana"

"Ni ban san komai ba"

"Kamar yaya, ya aka yi ki ka kar?o jariri ki ka gudo, ina babarsa take?"

"Tana can" tayi maganar tana share hawaye.

"Ke ya aka yi ki ka fito?"

Sake ?are baki tayi tana kuka ta ce "Wallahi likita ya ce a daina takura mini, da me zan ji kai baka san wahalar da na sha ba, kun ha?u kuna hantarata"

Usman ya ce "Ke fa rumaisa makira ce wasu lokutan, uba waye ya hantarekin?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ya kalli su Bashir ya ce "Tun da ba zata fa?a abubuwan da ake bu?ata ba, ku ?auke ?anku ku tafi, kar ta sake ganinsa ma"

Ihu ta fara yi "Ni kar ku ?aukar mini ?ana".

"To ki yi musu bayanin abun da suka tambayeki*

"Ni ban san komai ba, ba 'yan sanda bane su, su je dajin mana su duba, ni nace ba abun da na sani, ni duk na manta wasu abubuwan ma".

Sarautar Allah bashir ya zubawa ido, bai ta?a zaton tana da baki haka ba, saboda yadda ya tsinto ta a galabaice.

Bu?e ?ofar ?akin aka yi da ?arfi, da duk sai da suka waiwaya domin ganin waye.


*?500 ne, via 0009450228 Aisha Adam, jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*
Ayshercool





*KANWAR MAZA*

*20*


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

?? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Abubakar ne ya shigo, yana dira daga tasha ya wuto asibitin ba tare da ko gida yaje ba, da gudu ya ?araso ya rungume rumaisa, ko sauran mutanen da ke ?akin bai kalla ba, ya rungume rumaisa yana zubar da hawaye.

"Yaya Sadik ?ina" rumaisa ta yi maganar tana ?an?ame shi tana kuka"

Bashir ya kalli Usman ya ce "Abokina, wai har ku nawa ne yayyen nata ne?"

Usman ya yi murmushi ya ce "Mu bakwai ne, ita ce autar mu"

"Masha Allah, ba wanda zai ce mamanku ce ta haifeku, sam ba ta tsufa ba" yayi maganar yana murmushi.

Abubakar ya kalli Usman ya ce "Meyasa ba a gaya mini tun a jiya ba, sai yau da asuba Aliyu ya gaya mini".

"Mama ce ta ce kar a gaya maka, kar ka ce zaka taho a jiya, ga wanda ya tsinto ta a katsina nan" yayi maganar yana nuna masa bashir.

Abubakar ya nufe shi ya mi?a masa hannu yana fa?in "?an uwa, mu gode mun gode Allah ya saka maka da alkhairi, tun da aka ?auki rumaisa muka rasa nutsuwa mun gode sosai Allah ya biya" ya sake komawa wurin ruma yana dubata ya ce "Allah sarki autarmu, haka ki ka koma duk kin rame ruma, kullum tunaninki muke yi"

"Nima kullum sai na yi tunaninku, sai na ganku a mafarkina" tayi maganar tana sheshshe?ar kuka.

Bashir ya dubi Adam ya ce "Akwai bu?atar mu tafi, na san masu zuwa dubiya zasu yi ta zarya, mu ?yaleta ta ke?e da 'yan uwanta" takawa bai iya cewa komai ba, Bashir ya ja hannunsa suka fita.

Suna tafe a hanya Adam ya ce "Ka wuce da ni gidana, bana son komawa gida yanzu".

Bashir ya ce "Shikenan, amma dan Allah kar ka je ka damu kanka, ko ka yi ta tunani, hakan ba wani amfani da zai yi maka" still dai Adam bai ce masa komai ba.

Can bashir ya kuma cewa "Amma it seems you know each other before kai da yarinyar nan, a ina ka santa?"

"Bashir, dan Allah ka ?yaleni, ina cikin tsaka mai wuya, dole yarinyar nan ta yi magana, kan al'aamrin nan ya ?ara kwa?ewa" yayi ya a hasale.

Bashir ya ?an gya?a kai ya ce "Haka ne, amma dole ka rage zafin zuciyar nan mu bi a hankali, dan yarinyar nan da alama gardamammiya ce ta fika taurin kai" ya cigaba da tu?i, ba wanda ya kuma cewa komai.

Can gidansu Adam kuwa, su Iman suka ?ara shiga damuwa, ganin ammi ba ta fito karyawa ba, kuma sun je wurinta hadimarta ta tabattar musu da cewa ta ce kar wanda ya je wurinta, tana bu?atar ka?aici.

Cikin damuwa Nusaiba ta ce "Iman, ko ke kin san wani abu ne da yake faruwa, why are they behaving like this? They all look strange today"

Cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login