Showing 69001 words to 72000 words out of 182697 words

Chapter 24 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22418

maganarmu ne dai da muka fara"

Samha ta ja tsaki ta ce "Wai kai baka ganewa ne? Ba mun gama wannan maganar da kai bane ba?"

Ya ?an yi shiru sannan ya ce "Ina ?ara baki lokaci ne, gudun kar ki dawo kina cizon yatsa daga baya, kin fi kowa sanin halin sa da taurin kai, ke a tunaninki ta ina burinki zai cika, kina daga zaune kina shashashanci lokaci na ?ure miki? Kiyi abin da ya dace ki samu burinki ya cika, ganin bayan Adam baya na nufin yi masa illar da ba zai amfanu a gareki bane ba, amma ganin bayan nasa shi ne samun damarki na biyan taki bu?atar. Idan so nake na kawar da Adam, abu ne mai sau?i a gareni, amma ni ba hakan nake bu?ata ba, ha?in kanki kawai kiyi tunani amma".
Bai tsaya jin amsarta ba, ya katse wayar, Samha ta bi wayar da kallo, tamkar za ta ga Khalifa a ciki. A hankali ta ajiye wayar ta yi shiru tana jujjuya maganar sa, sai dai ta kasa gano cikakkiyar mafita a kan lamarin.

"Samha, me ki ke tunani ne?"

Samha ta kalli mai maganar ta girgiza kai ta ce "Babu komai"

"Ki yi sauri ki je ki duba kayan nan, bana son sai an fitar mutane sun gama za?a tukuna"

Samha ta ce "Shikenan" sai dai hankalinta da nutsuwarta sam ba sa tare da ita.

***
Sam ruma ta rasa sukuni, gaba ?aya sallolinta addu'a take a kan Allah ya sa mai sunan baba ya huce, idan bai huce ba bata san in da zata samo ?ari biyun nan ba, gashi ya ce kar ta sake ta tambayi kowa a gidan.
Gashi har wayewar garin yau ba ta samu ku?in ba, wunin ranar bai kulata ba, bai kuma ce ta bashi ku?in ba, sai da dare yayi, ta rasa dalilin da ya sanya yake son hukunta ta da daddare ya hanata bacci.
Tana zaune zuruu ta takure, tana zancen zuci ta ga ?afafuwan sa, tana ?aga ido suka yi ido hu?u.
Take ta rikice ya fara "Wallahi yaya ban samo ku?in nan ba, ban san a in da zan samo su ba, kayi mini rai dan Allah".

"Kin san ba ki da inda zaki samo ku?in kika arar mata ku?i, da uban wa zaki biyata da? Wato sata ki ke kenan"

Cikin kururuwa ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wallahi ban ta?a ?aukar kayan wani ba. Wallahi dama niyyata na tara mata, sai na biyata amma wallahi bani da ku?in da zan biyaka dan Allah kayi ha?uri"

Cikin kaushin murya ya ce "Sai fa kin nemo ku?ina kin biyani, ko a ina ne"

"Wallahi sai dai in kayana za a sayar a biyaka, amma wallahi bani da su"

"Wallahi da kin samo ku?in nan kin bani, sai na taka kanki, ta tabatta sata ki ke yi, ko a gida ko a waje, amma sai Allah ya ?wace ki, kin yi sa'a da kin gane shayi ruwa ne, sai na sakaki a mari na kulle, kuma ki cigaba da abin da ki ke yi kar ki fasa, idan ki ka kaini bango sai dai ki ji an ?aura auranki da malam Ladan, ko na sakaki a mari" jikin Ruma har ?ari yake, saboda wannan taratsin da yake yi mata kamar ta yi fitsari haka take ji. Ba ta samu damar sha?ar isashiyar iska ba, sai da ya bar ?akin ta dinga ajiyar zuciya.
Mama kuwa sam ba ta tanka musu ba, dan a yanzu kowane hukunci mai sunan Baba zai ?auka a kan ruma, ba zata nema mata sassauci ba, saboda ruma babu alamar shiriya a tare da ita.

Sai da wannan ?urar ta lafa, sannan ruma ta samu nutsuwa, ta cigaba da harkokinta.

Kamar mai ?aukar karatu, haka ta nutsu a kan waya, tana kallo a Instagram wani abun ta yi dariya wani tayi tsaki.

Kan wani hoto taje, wani kyakkyawan mutum, ya sha kayan graduation, yanayinsa bai yi yanayin fara'a ba, amma ya ?an ge?are baki yayi murmushi, har za ta yi liking saboda a rayuwarta tana son ta ga mutanen da suka yi nasara, musamman ta kammala karatu.
Kawai sai ta sake wurgawa, ta ga wani hoton nasa a cikin turawa, ta dinga dubawa, sauran hotunan duk a cikin turawa, da kuma aji na karatu, ajin tamkar ofishin wani shugaban ?asar.
Haushi ne ya kama ruma da tuno yadda ajinsu yake, sheranjiya da aka yi ruwan sama, suka je suka tarar ruwa ya cika ajinsu, murfin kwano ya yaye, sai ha?esu suka yi a wani ajin.
Ai babu tunani ta shiga comment section ta ce An ?ibi haramun an je karatu, Allah ya isa ku?in talakawa, ?arayin ku?in mutane, bamu yafe ba muna fama ajinmu ko rufi babu. daga haka ta ?ara gaba, ta cigaba da kallonta.

Ta gama abin da take, ta ajiye waya ta shiga nata shagali.

Sai da daddare ta dawo, ta sake ?aukar waya, ta ga an yi mata reply a message, ta yi ta murna yau an kulata a Instagram, dan ganin mutanen Instagram ?in take wasu mutane daban.

Sai dai tana dubawa ta ga wani yayi mata replying da 'Ya aka yi ki ka san da ku?in talakawa ya yi karatun'

Cikin zafin rai ta rubuta 'Idan gaskiya ne meyasa ya tafi ?asar waje karatun, su yi a Nigeria mana" ta rufe datar ta ajiye tana huci, tare da ?an jin releif a ranta, dan ta da?e tana son samun damar da zata isarwa irin wannan mutanen abin da yake ranta.
Yanzu take jin kallon waya yayi mata rana, da ta ?i yin zuciya har ta iya yadda ake amfani da irin wannan abubuwan.

***
Takawa ne ri?e da waya a hannunsa, Jabir sai surutu yake yi masa, amma kasancewar suna da banbancin hali shi da Jabir, ya sanya Jabir bai damu da rashin amsawar Takawa ba, saboda shi mutum ne ba mai yawan magana ba.

Can Adam ya ?ago rai a ha?e ya ce "Kai, wai ban hanaka ?ora hotuna na a social media ba?"

Jabir ya yi dariya ya ce "Tuna baya ne, ya sanya na ?ora gashi ka yi kasuwa 'yan mata sai comment suke yi, wa?anda kuma suka sanka, suna yabawa tare da jinjina maka"

Adam ya yi guntun tsaki ya ce "Kana da matsala" har ya wuce account ?in Jabir, kawai ya koma ya shiga comment section yana dudduba abin da aka ce.

Sai dai lokaci ?aya annurin fuskarsa ya ?auke, har wata zufar ?acin rai ta fara tsatstsafo masa a goshinsa, duk kusan ko yaushe a cikin damuwa yake, amma ya da?e bai ci karo da abin da ya daki zuciyarsa kamar wannan ba.
Ya ?aga ido yana kallon Jabir, Jabir ya ce "Ya dai, ya na ga kana kallona?"

Ri?e wayar yayi, ya cigaba da kallon Jabir, Jabir ya mi?e ya duba wayar, ya yi tozali da abin da ya sanya Adam ?acin rai.
Jikinsa ne yayi sanyi, dan sam bai san an yi wannan comment ?in ba. Yana ?o?arin yin magana takawa ya ce "Kira mini Sidi a waya, ayi mini tracking ?in account ?in nan"



(Mun kusa kammala book1 in sha Allah, mai bu?ata yana iya yin payment na book 2.
500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank. Sai a turo mini evidence of payment ta 08081012143, zan ?an bada time kan na cigaba da book2, sai an gama payment, hajiyata idan har kina iya sayen data ki saka a wayar ki, to ki tara ku?i ki sai book ?in ?anwar maza, you will never regeret tafiyar akwai ?aruwa a cikinta. Ina alfahari da ku masoya)

Ayshercool
08081012143
?ANWAR MAZA


Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

P21


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE, KO INFECTION? KO KUMA SO KI KE FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI,
SANNAN YAN UWA KUSANI DUK SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO*

Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu.

?? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin* su.
*1 Supplements na gyaran jiki*

*2 Supplements na gyaran gashi*

*3 Supplements mai da* *tsohuwa yarinya anti aging*

*4 Supplements na karawa* *fata kyau da sheki glowing skin*

*5 Supplements na masu ciwon jiki da stress

*6 Supplements na masu ciki, da masu shayarwa*

*7 Supplements na masu shayarwa*

*8 Supplements na tsofaffi*

*9 Supplements na karin ni'ima da tighteningn*

*10 Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11 Supplements na gyaran* *nono da mazaunai breast/hips*

*12 Supplements na gyaran* *HQ ciki da waje*

*13 Supplements na rage* *tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14Supplement na whitening/glowing skin*

*15 Supplement for Acne, dark spots remover*

Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158



https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban ha?a 1k subscribers a channel ?ina ba, anya akwai amana kuwa??*

Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.






Jabir ya ?an yi gyaran murya ya ce "Ka ga dan Allah ka kwantar da hankalinka, ka san ba a rasa irin wa?an nan a social media yaran talakawa ne kawai marasa tarbiyya amma dan Allah kawai ka share"

Takawa ya kalli Jabir ya ce "Ka kira mini Sidi na ce"

Jabir ya girgiza kai, wasu lokutan takawa akwai kafiya da gardama, da ga ganin comment ?in mace ce, kuma koma menene ba zai huce ba tun da ta riga ta yi.

Ya lalubo lambar sidi, ya kira masa shi, ya bashi wayar.

Cikin zafin zuciya ya kar?i wayar, ya yi wa sidi bayanin abin da yake son ayi masa.
Yana gama wayar, ya jefa wa Jabir wayar, ya fice daga ?akin gaba ?aya.


Sosai samha ta ?ata lokaci wurin yin kwalliya, kasancewarta 'yar ?walisa, sai dai babbar matsalarta ta ?ware a iya shigar banza, tun da garin Allah ya waye, bayan sun kammala waya da khalifa ta ji ta na son ganin takawa, dan haka da la'asar ta shirya ta tafi gidan, domin ganinsa.

Sai dai cikin sa'a, da ta shigo kan ta kai sashin Ammi, ta ga takawa ya taho fiuuu. Yanayinsa na rashin walwala bai sanya ta damu ba, balle ta saurara da abin da ta yi niyya.

Kai tsaye ta tunkari in da yake, ta fara yi masa magana, ko kallon in da take bai yi ba, yayi gaba abin sa, mamaki ne ya cikata, amma ba ta ha?ura ba ta bi bayansa zuwa sashin Ammi, sai dai a sashin Ammi ma bai tsaya a falo ba, ya wuce ciki. Gaba ?aya zuciyarsa a cunkushe take, an da?e ba a gaya masa abin da ya ?ona masa rai kamar wannan comment ?in ba, danganta shi da sata ba.
Samha kuwa gani tayi da kunya ta bi bayan takawa.
Nusaiba ce ta fito cikin shiri, da alama fita za ta yi, tayi arba da Samha a falo a tsaye.

"Ya dai na ganki a nan a tsaye, ko zama baki yi ba?" 'yan kame-kame Samha ta hau yi "Amm, dama takawa yana nan ne?"

"Ban sani ba, amma meyasa ki ke nemansa?"

Tsuke fuska Samha ta yi ta ce "Ina ruwanki da dalilin da ya sanya nake nemansa, ba abin da ya shafe ki bane"

"Haka ne, amma kamar yayi banbarakwai da yawa, ko kin manta waye shi a wurinki, Anty Samha ai ana barin halak dan kunya"

"Shut up! Na ce miki akwai wani abu ne a tsakaninmu, kin san bana son raini ko? Kuma ko ba komai ai takawa ?an uwana ne" Nusaiba ta ce "Haka ne, Allah ya taimaka" ta wuce ta bar Samha a falon.

Samha ta damu ta ga Adam sosai da sosai, domin samun ?warin gwiwar yanke hukunci a kan abin da Khalifa ya zo mata da shi.

Fitar Nusaiba babu da?ewa, Samha na tsaye na ta tunani, ma'aikatan sashin Ammi babu wanda ya tanka mata tun bayan gaisuwa, saboda sun san halinta na dizgi da wula?anta mutane da cin zarafi.

Iman ce tayi sallama a cikin falon, kamar kullum tana ganin Samha gabanta ya fa?i.
Salo-salo kamar mara lafiya iman ta ?araso cikin falon, ta kalli Samha ta ce "Anty Samha ina wuni?"

Samha ta ?ago kai ta kalli iman, ta yamutsa fuska, ta tsani iman fiye da yadda ta tsani 'yar uwatta. Ta ko ina iman kyakywar ce, ko da kwalliya babu, ko a wani yanayi yarinyar kyau ne da ita, ko kuka ko dariya, ko fushi ko fara'a komai kyau yake mata, ga tsananin kusanci da yake tsakaninta da takawa, bayan ?aya katangar da ta yi mata shamaki da cimma burinta da take ta ?o?arin rusheta, iman ma wata babbar matsala ce a gare ta, dan duk tsanani akwai aure a tsakanin ta da takawa. Ba ta sake tabattar da Iman matsala ce a gare ta ba, sai da samarin 'yan matan gidan suke zamewa su ce suna son iman, sai da su Fauziyya suka yi da gaske, wurin dam?ara mata mummunan fenti, da yayi mugun taka rawa wurin rusa farincikin rayuwar iman sannan suka samu sau?i, ga yarinyar sumi-sumi kamar munafuka, tana da sanyin hali, nutsuwa da kuma girmama mutane, shiya sanya kowa yake sonta, ban da yanzu ma da ake janye jiki daga gare ta.

"Anty Samha, wai ya na ga kina ta kallona? Me na yi kuma?"

Wani mugun kallo ta yiwa iman ta ce "Zan yi maganinki ne, magani na har abada, idan har baki bar sabgar takawa ba" iman na shirin magana, Ammi ta fito da sauri daga sashenta tana ?walawa iman kira.

Ganin Ammi a ru?e ya sanya iman bin Ammi da sauri, ba tare da tunnin komai ba, Samha ma ta rufa musu baya.

A ?akin Ammi suka tarar da takawa a sheme a ?asa.

Cikin ru?u Ammi ta ce "Iman ina maganin sa"

Cikin rawar jiki iman ta ce "Ammi me aka yi masa kuma ciwon ya tashi?"

"Ban sani ba, kawai yana shigowa ya fa?i yi sauri ki ?auko".

"Kin san ya da?e ciwon bai tashi ba, sai na binciko shi a in da na ?oye, bari na ?auko"

Samha ta ce "Ammi meya same shi ne?"

"Bashi da lafiya ne" Ammi ta bata amsa a ta?aice.

Iman ta ?an jima sannan ta kawo maganin, wani mai ne a doguwar kwalba ta zo da shi, ta bu?e tana shafawa takawa a goshinsa, jikinsa sai wani irin rawa yake yana ?amewa kamar mai farfa?iya.

Iman ta dinga shafa masa tana karanto adduoi daban-daban, kusan mintuna goma sannan ya daina abin da yake yi, da kansa ya tashi ba tare da ya cewa kowa komai ba, ya je ya hau kan gadon Ammi ya kwanta ya rufe idonsa.

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ammi bari na tafi, dama mama ce ta aiko ni wurin Mummy, na biyo na gaishe ki, bari na tafi Allah ya ?ara lafiya".

Har samha zata fita, Ammi ta kirata, Samha ta dawo gaban Ammi.
Ammi ta ri?o hannun Samha ta ce "Dan Allah Samha kar ki gayawa kowa takawa bashi da lafiya, wa?anda suka san yana da wannan rashin lafiyar sun zata tuni ya warke, dan Allah ki rufa mini asiri, ki yi shiru da bakinki" Ammi tayi maganar kamar zata yi kuka.

Cikin kulawa Samha ta ce "Ammina, kar ki damu, babu wanda zan gayawa in sha Allah, rufin asirinki ai namu ne, ba wanda zai ji in sha Allah "

Ammi ta jinjina kai, ta yiwa Samha godiya, iman kuwa tausayin Ammi yakamata, ammi haryanzu ba ta san halin samha ba, ko da yake ba wanda zai yadda da samha fuska biyu ce da ita.

Jiki a sanyaye Samha ta wuce sashin Mummy, sai dai sashin na ta shiru babu kowa. Kai tsaye ta nufi ?akin Mummy.
Ta tarar da mummyn na waya, ta samu wuri ta zauna tana jiran ta kammala wayar.
Mummy ta kammala wayar ta dubi Samha ta ce "Samha 'yar ?walisa, ya aka yi ne, na ga duk jikinki a sanyaye?"

Samha ta dubeta ta ce "Mummy, wai dan Allah baki da masaniya a kan rashin lafiyar Adam?"

"Wace rashin lafiya kuma?"

"Rashin lafiyar da ake cewa yana da ita, yau na gani da idona"

Mummy ta waro ido waje ta ce "Ki na nufin bai warke ba dama?"

"Eh, mahaifiyarsa ta nemi na yi shiru da bakina, amma na kasa jurewa, sai da na ga iman tana ta shafa masa wani abu a fuska, sannan ya tashi, anya Mummy babu hannunki a ciki?"

Mummy ta yi wani murmushi sannan ta ce "Samha kenan, ke idan da hannuna a ciki zan kasa gaya miki ne, ai da ko a wurin mahaifiyarku zaki ji, babu ruwana a cikin lamarin nan, ni ban ma san haryanzu yana da wannan ciwon ba, a zatona tuni ya warke"

Samha ta rausayar da kai, sannan ta mi?e tsaye ta ce "Na tafi, dama sauri nake" bayanta mummy ta bi da kallo, sannan tayi wani irin murmushi ta ce
"Yarinya man kaza, wannan labari yayi mini da?i da ki ka zo mini da shi, dama na da?e ban ji labari mai da?in wannan ba. Zan cigaba da amfani da wawancinki ina ruftaki, dole in je

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login