Showing 3001 words to 6000 words out of 182697 words
Mama ?akin ta huta, saboda Mama mitarta ba ta ?arewa sam, gefe guda tana yiwa Allah godiya da Dodonta bai yi magana ba.
Wani irin bacci ne mai da?in gaske yayi awon gaba da ita. A cikin baccin nata babu zato babu tsammani sai ji tayi an yi sama da ita da hannu ?aya.
"Wayyo Allana, Innalillahi wa innalillahi raji'un, warin hannuna na hagu zai karye Mama!" Sai da ya dungurar da ita a tsakar gida, suka yi ido hu?u, ta ga wanda yayi mata wannan aikin.
Jikinta ne ya hau kyarma, dan idonsa kawai idan ransa a ?ace yake abin tsoro ne.
A ?asan zuciyarta ta ce 'Shikenan tawa ta ?are, Allah ya sa na cika da kyau da imani!.
Ayshercool
08081012243
[16/06, 9:00 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Ku yi subscribing YouTube channel ?in mu, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Arewabooks @ ayshercool7724
Watpad@ ayshercool7724
P2
Kasa ?auke idanunta tayi daga kallonsa, saboda azabar firgici da razanar da ta yi.
Ya janyo kujera ya zauna a gabanta, ya ?an ?ura mata ido, sannan cikin kaushin murya ya ce "Gidan uban wa kika tafi da ta aikeki, tun la'asar ba ki dawo ba sai magariba?" Yayi Maganar yana tsareta da ido.
Kasancewar akwai wutar lantarki, ya sanya fes take kallon fuskarsa da idonsa.
"Ba magana nake yi miki ba, ki ka tsare ni da ido?" Ya daka mata tsawa.
Zabura tayi ta yin?ura za ta yi magana,amma ya sake cewa "Kuma wallahi kika yi mini ?arya sai na ci ubanki a daren nan"
Jiki na rawa ta fara zayyane masa yadda aka yi tun bayan fitarta.
Huzaifa tun da yaga Yaya Umar ya shiga ?akin Mama ya jiyo kukan Rumaisa, ya sha jinin jikinsa, dan ya san yau sai yadda Allah ya yi.
Mama kuwa girgiza kai kawai ta yi, jin Yadda Ruma take fa?ar gaskiya sa?anin ?azu da ta yi mata ?arya.
Umar ya ce "Namiji ce ke da zaki tafi aron taya?" Ta sunkuyar da kai tayi shiru.
"Kuma me nace miki a kan dambe a hanya, karya ce ke?"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
Ya ?ora da cewa "Wato ke duk wani abu da za'a gaya miki sai dai ya shiga ta kunnenki na dama, ya fita ta hagu ko?"
Ita dai tayi shiru tana rarraba ido.
"Kyaci ubanki, tashi ki kama kunnenki tun da ba zaki yi hankali ba".
Maraicewa tayi zata fara yi masa magiya, amma da yayi mata wani mugun kallo, ba shiri ta mi?e ta dur?usa ta hau kamun kunne.
Gaba ?aya Huzaifa ji yayi bai ji da?i ba, maimakon a hukuntata tun a lokacin amma sai da aka bari ta fara bacci, za a sakata kamun kunne, ya tsaya ta ?ofa yana le?en tsakar gidan ya san yanzu zata galabaita, gashi babu wanda ya isa ya hana Yaya Umar abin da yayi niyya sai Hassan ?in sa wato Abubakar Sadik, shi kuma baya nan.
Umar ya nutsu yana duba litattafansa, Rumaisa kuwa sai tanga?i take tana neman ta fa?i, amma yayi banza da ita, dan ta san idan ta fa?i ko ta tashi ba zata iya ?aukar wani hukuncin ba.
Tun tana kuka ?asa-?asa har ta fara yi da ?arfi, saboda azabar gajiyar da ta yi.
"Tashi" ya fa?a ba tare da ya kalleta ba. Ta ?ago duk ta ha?a uban gumi, ga hawaye da majina duk a fuskarta.
"Kukan uban me kike yi?"
Cikin kuka ta ce 'Yaya na gaji ne, dan Allah kayi ha?uri ba zan sake ba, na tuba"
"Da alama haryanzu baki yi laushi ba, yi zaman babur tun da kin gaji da kamun kunne"
Babu kalar izayar da Yaya Umar bai yi mata ba a daren, har Sai da Mama ta ji babu da?i a ranta, amma tuna cewar yarinyar ba 'yar goyo bace ba, ya sanya tayi banza ta cigaba da laziminta.
Aliyu ne ya fito daga ?akinsu, cikin damuwa ya ce "Dan Allah Yaya kayi ha?uri ka ?yaleta haka ta je ta kwanta dare yayi, wallahi ta horu, kuma ga gobe in Allah ya kaimu da makaranta".
A fusace Umar ya kalleshi ya ce "Ka ?ace mini daga gabana ko sai na ha?a da kai?" Ran Aliyu ba ?aramin ?aci yayi ba, kawai ya girgiza kai ya shiga ban?aki.
Sai da ya tabbatar da ta galabaita sannan ya ce ta zauna ta huta, shi kuma ya tashi ya fita.
Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, saboda jin cinyoyinta take kamar babu nama a cikinsu sai rodi, saboda azabar sagewa da suka yi, ?ashin bayanta ma ban da azabar ciwo babu abin da yake yi mata.
Yaya Umar na fita, Huzaifa ya ?araso in da take yana mata sannu cikin tausayawa kamar ba shi ne ya gama bawa Mama shawarar ta ha?ata da Yaya Umar ba.
Ya je ya ?ebo ruwa ya bata, ta kar?a ta kafa kai tana sha tana kuka. Ta gama sha, ya kar?i kofin ya ajiye yana goge mata hawayen fuskarta.
"Uban me kake a nan wurin?" Basu ji dawowar Yaya Umar ba, sai maganarsa kawai suka ji, suka yi tsuru-tsuru.
"Zaka tashi ko sai na ha?a da kai?" Jiki na rawa Huzaifa ya tashi, ya koma ?akinsu.
Ya kalli Ruma da ke ta ajiyar zuciya, ya tabbatar ta galabaita, ya san yanzu haka jikinta na ciwo, ya jefa mata leda a jikinta ya ce "Maza ?auki ki shanye"
Jiki na rawa ta ?au ledar, doguwar jarka ce cike da youghurt mai sanyi a ciki, ta ?aga kai ta sha rabi, yana tsaye yana kallonta, ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Na ?oshi".
Jin bai ce komai ba ne ya sanya ta ?ago ta kalleshi, ganin yana mata wani irin kallo ne, ya sanya ta cigaba da sha tana yamutsa fuska, da ?yar ta shanye, ta ajiye robar tana jiran umarni na gaba.
"wuce ki je ki kwanta"
Da ?yar da yin?ura ta tashi, ?afafuwanta na ta rawa saboda ciwo, ta shiga ?aki.
Tana shiga ta tarar da Mama na salla, ta fa?a kan katifa tana kuka.
Mama har ta idar da sallar ba tace mata komai ba, ta cigaba da kukanta har bacci ya ?auke ta.
Cikin bacci ta ji Mama na ?ala mata duka a cinyarta "Tashi" duk da yadda ta ji zafin dukan, amma ta bu?e idonta a hankali ta kalli Mama, ba tare da ta ce komai ba.
"Saboda tsabar rashin hankali, ki kwanta ki yi fitsari a kwance, ke ba jaririya ba ba 'yar yaye ba" jin abin da Mama ta fa?a ne ya sanya ta mi?e zumbur, ta ganta luntsum a cikin fitsari.
Waro ido ta yi ta ce "Na shiga uku, wallahi na zata a mafarki ne, dan Allah kiyi ha?uri"
Mama cikin ?acin rai ta girgiza kai ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, zaki tashi ki fita kije ki gyara jikinki ko kuwa?"
Sannu a hankali ta sauka daga kan katifar, saboda yadda jikinta ko ina yake yi mata ciwo, saboda punishment ?in da Yaya Umar ya sanya ta.
Da ta fita tsakar gida da rarrafe ta ?arasa ban?aki, ta wanke jikinta ta dawo ta canza kaya, ta jingine katifar tayi kwanciyarta a ?asa.
Har ga Allah, tana jin yadda fitsarin ya matseta, amma ta ji gandar tashi, saboda bacci take ji sosai, ga kuma ciwo da jikinta yake yi, dan haka ta cigaba da baccinta, da ta ganta a ban?aki ta zaci a gaskene ta saki fitsarinta.
Tana jin yadda Mama ke ta mita, amma ita ko a jikinta, wani nannauyan baccin ne ma yayi awon gaba da ita.
Da Asuba ma an kai ruwa rana kan Mama ta samu Rumaisa ta tashi ta yi salla, dan sai da ta yi i?irarin ha?ata da Yaya Umar sannan ta tashi ta yi sallar.
Ta idar da salla Mama tayi mata maganar shirin makaranta, amma ta tura baki ta ce "Ai kina gani jiya mai sunan Baba yana azabtar da ni baki hana shi, ni bani da lafiya, ba zani ba cinyata kamar an mini ?orin karaya haka nake ji na"
Mama ta yi mata shiru ta cigaba da laziminta, Huzaifa ne ya fara shigowa ?akin Mama ya gaisheta, suka gaisa ya tambayi Mama mai za'a ?ora na karin kumallo?.
Mama ta ce "Bari gari yayi haske, sai a sayo gasara, ka cewa Yasir ya feraye maka dankali, sai a soya"
Huzaifa ya jinjina kai ya mi?e, har zai fita idonsa ya sauka a kan katifar Rumaisa, ya ?an yi turus ya dubi Mama ya ce "Mama ba dai fitsarin kwance yarinyar nan tayi ba?"
"Gashi kuwa kana gani, ai Yarinyar nan sai addu'a kawai".
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, su Balama an yi asarar kunnuwa, ba sai ki saka ta fitar miki da ita daga ?aki ba, sai ?akin ya fara wari tukuna, abinka da fitsarin gardiya bana jariri ba, tashi shashasha" ya ?arasa maganar yana zuba wa Rumaisa duka a ?afa.
A gigice ta tashi zaune ta raba ido, tayi zaton Mama ce ta daketa, amma taga Huzaifa a kanta.
"Me nayi maka zaka dakeni?" Tayi maganar a ?ule.
"An dake ki ?in, tashi ki fitar mata da wannan katifar daga ?aki, mai abin kunya ?atuwa da ke kina fitsarin kwance"
"Ba zan fita da ita ?in ba, uban shishshigi ko ina ruwanka, tun da ba a kan ka nayi ba, kuma ruwa ne ya zube ba fitsari nayi ba".
"Au Mama ?arya take yi miki kenan, ba zaki tashi ba?"
Cikin tsiwa ta ce "Ba zan tashi ba"
mi?a hannu yayi, ya janyota ya ?agata, ya ce "Wallahi sai kin fita da katifar nan kin wanke kayan da kika yi tsiyar a kan su". Idan da sabo Mama ta saba da wannan halin nasu na fa?ace-fa?ace, gashi Huzaifa ya bawa Rumaisa kusan shekaru shida, amma fa?a kamar suna ganin hanjin junansu.
Mama ta sharesu ta ?i ko kallon in da suke, Rumaisa ta dinga turjewa tana kwarara ihu.
Basu yi aune ba suka ga Yaya Umar a tsakiyar ?akin, take suka yi cirko-cirko suna kallonsa.
Cikin kaushin murya ya ce "Meye haka karnuka ne ku?"
Suka girgiza kai a tare.
"Me kai mata take wannan ihun, da idon Mama bai sanya kun daina ba?".
"Fitsari ta yi a kwance, shi ne nace ta fita da kayan"
Cikin mamaki Umar ya kalleta ya ce "Fitsarin kwance kuma? Kina me kika yi fitsari?"
Cikin rauni ta ce "Wallahi Yaya tsautsayi ne, kasa tashi nayi"
"Tsautsayin uban wa? Kwashe kayan ki fita ki wanke ?azamar banza kawai".
Haka ta ja katifar ta fita da ita tsakar gida, ta kwaso kayan da ta yi wa fitsari ta hau wanki.
Huzaifa ya faki idon Yaya Umar ya dinga yi mata dariya.
Duk wanda ya fito tsakar gida ya ga katifar Rumaisa sai ya ce me ya fito da katifar, Huzaifa sai yayi farat ya gaya musu ai fitsarin kwance ta yi.
Tausayinta ne ya kama Usman, ganin yadda take kuka, kuma ba ta saba yin fitsarin kwance ba, ya je ya kar?i kayan ya tayata.
Kowa da abin da yake fa?a a kan Ruma, wasu na mata Addu'a shiriya wasu kuma na yi mata fa?a har da zagi.
Tamkar gidan 'yan mata, haka zaratan samarin nan suka kama aikin gida, wasu na wanke-wanke, wasu shara da Abin karyawa, kan gari ya ?arasa haske, hatta ruwan da Rumaisa zata yi wanka, an dafa ta ha?a ta yi wanka.
Haka suka jeru a tsakar gida, tare da Mama suna karyawa, Rumaisa kuwa sai shan kunun take da ?yar tana yamutsa fuska.
Can ta kalli Mama ta ce "Mama Kununa bai ji suga ba, yayi tsami da yawa".
Haushi ya kama Mama ta ce "Amma a gabanki aka zazzage sugan kowa ya ?iba ko? Kuma kin san ya ?are"
Ta ture kofin kunun ta ce "Nifa dama kunun nan gudawa yake sani, gashi bai ji suga ba, ni cikina ma har ya fara ciwo"
Umar kawai ya girgiza kai, Rumaisa ba zata ta?a zaman mintuna goma lafiya ba, ba tare da tayi abin da za a yi mata magana ba.
Haidar ya kalleta, ya zura hannu a Aljihunsa ya ?auko ?ari biyu ya bata ya ce "Jeki wurin Mamuda ya baki buredi da suga, akwai ruwan zafi sai ki ha?a shayi ki sha"
Washe baki tayi, ta ce "Allah dai ya biya da aljanna, gadanga na Mama" ta ?au kofin kununta ta turawa Mama kunun ta ce "Mama ki shanye kunun na bar miki" tayi waje.
***
Da ?yar ta ?arasa makaranta yau, saboda ciwon cinyoyi da take yi, sakamakon horon da Yaya Umar ya bata a daren jiya.
"Ruma hatsari kika yi ne?" Cewar wata matashiyar yarinya sa'ar Ruman, gannin yadda take tafiya da ?yar.
Ta ha?e rai ta ce "Me kika gani?"
"Gani nayi kina tafiya da ?yar, kamar wadda ta warke daga karaya"
Cikin gatse Ruma ta ce "Eh, tirela ce tabi ta kaina, da ta wuce na taso na taho"
"A'a Allah ya baki ha?uri"
Duk da yadda jikinta babu da?i, hakan bai hanata fa?ace-fa?ace da neman rigima ba, dan idan ba tayi hakan ba ace lafiyarta ?alau ba.
Bayan an tashi ba ta tsaya ko ina ba ta tafi gida, tana zuwa ta tarar da katifarta a tsakar gida kamar yadda ta barta.
"Mama yanzu dan Allah a nan aka bar mini katifata, sai anyi ba?i sun tambayi ba'asi ace fitsarin kwance nayi?"
"Au ba ke kika yi ba, ni nayi kenan?"
Ta ?arasa ta zauna a kusa da Mama ta ce "Haba Mama, kema fa kin san tsautsayi ne, rabona da fitsarin kwance tun ina jairiya, tun ban fi wata hu?u ba na daina fitsarin kwance" wani irin kallo Mama tayi mata, jin uwar ?aryar da ta saki.
Mama ta ce "Tashi ki cire Uniform, kiyi wanka ki zo kiyi salla, ki tsefe wannan kan naki, ?azamar banza da yake ban yi magana ba, baki ga dama kin mayar da kai kin tsefe ba, kuma wallahi ya kai gobe in Allah ya kaimu baki gama tsifar nan ba, sai na zaneki".
Hannu ta saka ta shafa kanta, ?anann kitso ne a kanta, a ?alla guda arba'in da ?oriya, Mama ta bata ku?i ta je ayi mata kitson hannu guda biyar, saboda ba ta son tsifa, amma ta kar?i ku?i a wurin Yaya Usman ta je aka yi mata ?anana.
Ta san yau ko Mama zata kwa?anta ta ta cinye ba zata iya gama wannan tsifar ba, haka nan ta tashi ta je ta yi wanka, ta yi alwala ta saka wasu kayan. Ganin Mama ta tada salla, ta le?a Window ta ga Usman da sallaya a hannu zai tafi masallacin juma'a, ta ?au hijjabinta ta bi bayansa.
Sai da ta fito ?ofar gida sannan ya kalleta ya ce "Ina zaki?"
"Masallaci mana" ta bashi amsa.
"Kin tambayi Mama?"
Ta gya?a masa kai alamar eh.
Ya ce "Shikenan muje" ya sanyata a gaba suka tafi masallaci.
Mama ta da?e tana yiwa Rumaisa Addu'a bayan ta idar da salla, kullum cikin Addu'a take yi mata, amma tana girma tamkar ana sake turata, ko alamar hankali babu a tare da Rumaisa.
Da suka dawo daga masallaci tana kallon Rumaisa, ba ta ce mata uffan ba, Rumaisa sai raragefe take yi, tana sauraron ko Mama zata yi mata magana amma taga ta shareta.
Ba tare da ta yi tsifar ba, ta ci Abincin ranarta tare da Yaya Aliyu, ya siyo kifi ?auri biyu, ya bawa Mama ?aya ya ce gashi nan duka gidan, ?auri ?aya kuma suka ci shi da Rumaisa.
Bayan sallar la'asar, ta ?au allonta ta tafi makarantar allo.
Tana zuwa Habiba ta tare ta da harara, tare da sheda mata cewar Sani ya ce sai ya yi mata dukan tsiya, idan ba ta biya shi tayarsa ba.
Tsaki Rumaisa tayi ta ce "To, ya kasheni ya huta mana, tayar banza da ta wofi, shi bai san tsautsayi ba"
A ?ufule Habiba ta ce "Au hakama zaki ce? Ki zo girma da arziki na ara miki tayar, amma ki je ki ?atar ko a jikinki?"
"To tayar da ku?i ya saya? Idan da ku?i ya saya ya fa?i ku?inta, yayyena su biya shi"
Habiba da ta gama fusata ta ce "Dalla can, uwar meye a gidan naku, banda gayyar maza da tsiya, sai ka ce wata uwar kuka ajiye, har kike a fa?i ku?in tayar a biya"
"Ku kun ajiye wata uwar ?in ne, da kuna da wani abun ai babarku ba zata sayar da fanke da safe ba" Tayi maganar tana murgu?a baki.
Cikin rawar murya Habiba ta ce "Kar ki sake ki zagar mana uwa"
"Ni ban zagi babarku ba, ni dai na san fanke take sayarwa, fanken naku ma mai Shegiyar tsada, ?anana kamar ?uli-?uli, dan ranar Yasir ya ce har kiyashi ya gani a cikin fanken" kan Rumaisa ta rufe bakinta, tuni Habiba ta sha?o hijjabinta, zata rufeta da duka.
Abinka dai mai nema a duhu, balle ya samu a sarari, nan Rumaisa ta zage ?wanji ta tabattarwa da Habiba ita ?in ?ANWAR MAZA ce.
Abin takaici da malami a gefe yana biyawa wasu allo suka har?e da dambe.
A fusace ya mi?e ya saka bulala ya zane musu jiki, musamman Rumaisa, tsabar masifarta ya sanya baya son ta a ajinsa, kullum cikin rigima take, ga allonta sai yayi wata ba tayi wani rubutun ba, ga da?i?anci da surutu.
Idan da abin da Rumaisa ta tsana bai wuce duka ba, ta ji zafin dukan bulalar da Malam Ashiru yayi mata ba ka?an ba, dan haka ta koma gefe tayi shiru tana kuka. Ta rasa meya sanya ya tsaneta haka.
Habiba kuwa da ?awayenta, suka ?udiri aniyar idan aka tashi sai sun na?awa Rumaisa duka saboda suna jin haushinta suma, a kan damben da aka yi a ?ofar gidan mai marka?e ranar Alhamis, gashi ta zagi fanken babar ?awarsu.
Ana tashi cike da takaicin dukan da Malam yayi musu, Rumaisa ta ?au allonta ta nufi gida, sai share hawaye take. Sai dai yau babu tsokana a hanya, babu neman magana saboda bayanta sai ra?a?i yake na dukan da malam yayi mata, gashi ba ta warke daga ciwon jikin punishment ?in Yaya Umar ba.
Babu tsammani ta tarar da su Habiba a wani lungu suna jiran isowarta.
Turus tayi tana binsu da kallo kamar ba ta sansu ba.
Babu ko ?ar ta cigaba da tafiya tana yin?urin ratse su ta wuce.
Shan gabanta Habiba ta yi ta ce "Ke kin isa ki tafi, ba dai ni kika zaga ba, kika kuma zagi babarmu ba, wallahi yau sai kin gane kuskurenki, kuma wallahi Sani ma ya ce sai kin biya shi tayarsa.
?aya daga cikin yaran ta ce "Ai wallahi yau sai kin daku, haka nima ranar kika zubar mini da marka?e, zaki gane