Showing 72001 words to 75000 words out of 182697 words
gidan Galadima, sai Hajiya Luba ta ji wannan zancen"
****
Ruma kuwa tuni ta manta abin da ta yi, dan ba ta ?auki abin da tayin wani abu mai muhimmanci ba, sabgoginta ta cigaba da yi, sai dai tana iya ?o?arinta yanzu a kan kar ta yi wani abun da zai kuma ha?ata da mai sunan Baba, dan karonsu babu da?i sam.
***
Kamar ko yaushe, haka yanzu ma muryarta ta yake ji a kunnuwansa, a hankali ya bu?e idonsa, yana son tabattar da a ina yake, abin da ya iya tunawa shine ya shigo cikin gidan sashin Ammi, amma daga haka bai iya tuna komai ba.
A hankali kunnuwansa suka jiyo masa muryar Ammi tana karatun Alqur'ani.
Ya juya, ya kalli Ammi, ta na sanye da hijjabi, iman kuma ta ziro masa ido tana kallonsa.
Da sauri iman ta ce "Ammi ya farka"
Cikin kulawa Ammi ta dube shi, ta ?ora hannunta a goshinsa tana yi masa sannu.
Ya jinjina kai, Iman ma ta shiga jero masa sannu yana jinjina kai.
"Takawa, duk da na san ba ka so, amma ya zama dole ka yi ha?uri mu cigaba da neman magani, a baya abu ya lafa amma Kwatsam yau sai gashi ka fa?i, dole mu yi wani abu a kai kafin a farga a samu abin fa?a.
Shiruu Adam ya yi yana sauraron Ammi, ba tare da ya iya cewa komai ba.
Ammi ta kalli iman ta ce "Auta, duk da bani da matsala da ke, amma ke ma ki yi shiru, ko waccan ru?a??iyar Nusaiba kar ki gayawa"
Iman ta ce "In sha Allah Ammi, bari na je na mayar da maganin".
Zuwa washegari takawa ya ware, kamar ba shi ba, ya cigaba da azalzala a kan a nemo masa mamallakin account ?in nan da aka ce masa ?arawo da shi.
A washegari Mummy ta shirya ta tafi gidan Galadima mai ci a yanzu, wato gidan su Jabir.
Hajiya Lubabatu na ganinta suka yi wata shewa, tare da gaisawa da junansu.
Hajiya Lubabatu ta ce "Ya akwai labari ne?"
"Da ?umi-?uminsa ma kuwa, mu shiga daga bedroom.
Cikin ?aki suka shiga, Mummy ta ce "Ya jikin Galadima ne?"
Hajiya Lubabatu ta ce "To ni me ma zance miki ne, a ?arshen watan nan dai nake son ko ni ko jabir wani ya je, ance dai da sau?i"
"To Allah ya ?ara afuwa, amma gaskiya Yakamata ki mi?e ki ?ata ala?ar da ke tsakanin Adam da Jabir, kin san idan babansu ya rasu sarauta gidanmu za ta dawo, ke sai ki zuba ido shikenan babu makoma, idan sarauta ta dawo hannun Adam waya san lokacin da zai mutu balle Jabir ?in ma yayi sarautar, duk da ina ta ?o?arin ?ara rura wutar gaba tsakaninsa da Mahmud, sai dai Mahmud wawa ne, ya ?i mayar da hankali a kan Sarautar, ba ta gabansa ".
Hajiya Lubabatu ta yi murmushi ta ce "Jamila kenan, ai kema kin san ba a zaune nake ba, kuma da sannu dukkaninmu zamu yi nasara, ai ke dama ba kya burin sarautar ta dawo gidanku"
"?warai kuwa, shiyasa nake ta son komai ya ?aci, ko kin san ashe Adam bai warke daga wannan larurar da yayi ba yana yaro, mai kamar farfa?iyae nan ba?"
"Haba dai, ya aka yi ki ka sani?"
"Samha ce ta zo ta titsiyeni, wai ta gani a sashin su, wai ko ina da hannu a rashin lafiyar ta sa, na ce mata ni babu ruwana, da ciwonsa na ganshi"
Hajiya Lubabatu ta ce "Kai samha ma akwai bin ?wa?w?wafi, shareta kawai ai aiki yana kyau sosai"
"Haaa ke dai bari, idan har ina raye ko zan tafi tsirara sai Binta ta ?an?ana ku?arta in Allah ya yarda sai ciwon nan ya zame masa hauka tuburan, na ka?a sauran yaran nata tare da wannan shegiyar yarinyar mai kama da larabawa"
Hajiya Lubabatu ta yi dariya ta ce "Shi dai wannan ?a abu ya zame masa goma da ashirin, da hauka ko in ce farfa?iya, ga kuma maita duk shika?ai"
"Hmm ke dai bari, ina jiran lokacin da zan kwatsa zancen nan a cikin masarautar Kano, ?an da suke ji da shi maye ne, da ya sha a nonon uwarsa, ta ta ba ta baiyyana ba sai ta shi"
Cike da rashin imani suke ?ya?yace dariya, kamar ba za su bar duniya ba.
Cikin dare da misalin ?arfe biyu da rabi, Baba uwani ce ke san?a kamar 'yar fashi, ta bu?e babbar ?ofar sashen Ammi ta fita, kai tsaye ta nufi sashen Mummy, tana tura ?ofar sashin ta bu?e, ta kutsa tana waige-waige.
Hanyar kitchen ta bi, ta tarar da Mummy a wani ?aki a zaune tana jiranta.
Baba uwani ta du?a ta gaida Mummy, Bata amsa ba ta dubeta ta ce "Kin san dalilin da ya sanya na nemekk?"
Ta girgiza kai alamar a'a.
"An ce mini ?an uwar ?akinki Adam, haryanzu bai warke ba, ciwon nan da yayi da yarinta yana nan yana fama, jiya ma ya tashi haka ne?"
Baba uwani ta ce "Wallahi ban sani ba uwar ?akina, jiya ta aikeni, kuma ina tunanin babu wanda ya sani, saboda da na dawo ban ji labari ba".
"Ba tambayarki nake dogon labari ba, ance mini akwai wani abu da aka shafa masa, ya tashi da wuri, wannan abin nake son ki sanya ido ki ?auko mini"
"Ranki ya da?e, ai ban san a in sa suke ajiyewa ba, ba ta sanya ni a sabgar neman maganin sa ba"
"Bai shafeni ba uwani, ki aikata abin da na ce kawai, tashi ki bani wuri"
Haka baba uwani ta taso, tana tunanin ta in da zata fara aiwatar da wannan aiki mai mugun hatsari.
****
Yau ruma fakar idon Yasir ta yi, ta ?auki wayar nan ta jefa a jakar makarantar ta, ta yiwa mama sallama ta tafi makaranta. Sai dai da ta je makarantar babu wanda ta iya nunawa wayar, gudun kar yaran su tona mata asiri a ?wace wayar, sai dai ta na jin kanta ri?e wayar nan da take yi, duk da ba wayar kirki ba ce ba.
Yau mama ba ta nan, ta je cikin gari za su kai wani kayan lefe na wani ?ansu, dan haka ruma sai lissafi take a kan ba zata islamiyya ba, ?ulewa za ta yi a ?aki ta yi kallo a waya, kuma ta sha baccinta.
Ta tsaya ta sai gya?a a hanya, tana tafe tana ci, kamar ba ?iya mace ba, dan ruma duk wani abu na jan aji na mata ruma ba ta iya ba, haka nan take rayuwarta kamar namiji.
?arar mota ta ji a bayanta, sai dai kan ta kauce, ta ga an sha gabanta da motar, wasu ?arti ne suka fito suka ce "Shiga mota"
"In shiga aje ina kamar a film ?in indiya"
Cikin tsawa ?ayan ya ce "Ki shiga mota na ce"
Ruma ta cake ta ri?e ?ugu ta ce "Wai saboda me, in shiga ka kai ni ina?"
"Kai dalla dannota kawai, za ta ?ata mana lokaci" sau ?aya ya tanka?a ?eyar ruma, ta hantsila cikin motar.
Aikuwa ta din ga kurma ihu "Al'ummar ?orayi an saceni, dan Allah ku kawo mini agaji" rufe motar suka yi, suka ja dama motar tint ce, sai dai ruma ta cika musu kunne da kururuwa.
"Ke, kin ishemu, zamu yanka ki da da wu?a a motar nan"
"Wallahi ba zan yi shiru ba, kun satoni kun sakani a tsakiyarku bayan ku ba muharramaina bane ba".
Wanda yake tu?a motar, ya dubi na kusa da shi, cikin harshen turanci ya ce "Anya kana ganin wannan yarinyar ce kuwa?"
"Oho, mu kai masa ita dai, shi zai tantance ".
"To ai gani na yi yarinya ce sosai, yaushe wannan zata iya wannan abu?"
"Kai wannan sai ta aikata, ji yadda take wa mutane ihu, dan ya ce ban da cin zarafi da sai na sakata a silent yanzun nan".
"Wallahi idan baku bu?e mini motar nan na fita ba, sai na tara muku jama'a, ashe ma ku ?ananan 'yan kidnapping ne, da kuka sace ni, to wallahi ni ?anwar maza ce, idan yayyena suka gano ku, sai kun raina kanku" babu wanda ya kulata cikinsu, har suka isa in da zasu je, ba ta yi shiru ba ko na mintuna. Haka zalika idan za a kasheta ba ta san ta in da aka bi ba, saboda ba?in glass ne a motar.
Ita dai ta ji an tsaya, aka bu?e mota aka ce ta fito. Fitowa ta yi tana kallon harabar da aka paker motar.
Ingiza ruma suka yi, ta ?an?ame jakarta tana kalle-kalle.
Wani falo aka shiga da ita, suna shiga wani irin sanyi ya daketa, ta ce "Wayyo sanyi" duk sai da suka kalleta kamar wata 'yar ?auye.
Ita ba kawotan ne ya dameta ba, tsaruwar gidan da yadda aka narka masa dukiya ne ya burgeta take ta kallo.
Sanyin Ac ne ya fara damunta, saboda haryanzu babu wanda ya ce mata komai, tunani ta fara yi, idan mama ta dawo ta tarar bata nan fa, gaba ?aya hankalinta ya tashi yayi gida, a yadda take jin labarin kidnapping dai ba haka ake yin sa ba, ko da yake dai ai babu maraba.
Mi?ewa tayi ta dubi mutumin da yake zaune a bakin ?ofa ta ce "Bawan Allah dan Allah ku zo ku sallameni, kar babata ta dawo ta ga bana gida"
"Wuce ki zauna, kafin na fasa kanki da harsashi"
"A'a da bom zaka fasa mini kai, ni me na yi muku ne?"
"Wallahi ki ka cigaba da yi mana hayaniya, sai na saka igiya na ?aureki"
"Kamar ya ya ka ?aureni da igiya, sai ka ce ragon layya? Dan Allah ku zo ku mayar da ni"
Cikin tsawa ya ce "Ki koma ki zauna na ce".
Tsaki ta ja ta koma ta zauna, bin ruma ya yi da kallo jin yadda ta yi masa tsaki.
Zama ta yi ta ?auko gya?arta ta cigaba da ci, tana ?ata wurin, mai gadin na ta kallonta yake, ita kamar ma ba ta damu da ?aukotan nan da suka yi ba, gaba ?aya ba ta da wata damuwa.
Ta gama cin gy?arta, ta bu?e jakarta ta ?auko rake. Duk ta ?ata wurin, ta gama ta gaji tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.
Surutan mutane suka ji, alamar za a shigo. A cikin mutanen da suka shigo su uku, tana yiwa ?aya kallon sani, sai dai ta manta a ina ma ta sanshi.
"Tana ina?" Ya fa?a a ta?aice.
"Gata nan a gabanka sir, ita muka samo, kuma ta fa?i wasu abubuwa da ya sake tabattar da ita ce" cewar ?aya daga cikin wanda suka kawo ruma.
Mamaki ne ya kama shi, ta ina ?aramar yarinya kamar wannan, ta samu waya, har ta iya yi masa wannan comment ?in.
Ya zauna ya na ?are mata kallo, sai wani ha?e rai take tana basarwa, tana harare-harare ta gefen ido.
Jabir ya ce "ka bi komai a sannu Please, ka ga ?arshen abin ma ashe yarinya ce, dama ha?ura kai kamar yadda na gaya maka da farko".
"Me na yi miki ki ka kirani da ?arawo?" Yayi maganar yana tsareta da ido.
Mamaki ne ya kama ruma, ita a ina ta sanshi da zata kira shi da ?arawo. Ya sake maimaita maganar amma tayi banza ta?i magana.
Jabir ya ?auko wayarsa, ya shiga account ?in da ruma tayi comment da shi ya nuna mata, ya ce "ke ki ka yi wannan comment ?in?" Ta zubawa Jabir ido, shima ta ?i kulashi, sai dai a yanzu ta gane in da ta ta?a ganin Adam, a Instagram taga hotonsa tayi comment.
"Wai kurma ce ne?"
"Sir wallahi ba kurma bace, yanzu ta gama magana iskanci ne, ka bari a casata kawai".
"Am talking to you, me na yi miki ki ka ci mutuncina, wai na saci ku?in talakawa, ance miki ni ?an siyasa ne?"
Jabir ya ce "Easy Adam, yarinya ce ?arama, ki na ji ki san abin da zaki din ga rubutawa a social media, wanda ya baki waya ma shi ne babban mai laifi, da ya bawa under age waya. Babban mutum ne sannane, ?an gidan marigayi Galadiman Kano ne, bashi da ala?a da siyasa, amma kin yi masa ?azafi shi mahaifinsa basarake ne, kuma ?an kasuwa ba ku?in tal.....
"Shut up Jabir, na meye zaka din ga yi mata wani bayani"
"A'a ka yi ha?uri, kin ga bashi ha?uri komai ya wuce" wani kallon zaka bushe ruma tayi masa, ta ?ara gyara jakarta ta ?auke kanta gefe guda.
Mamaki ne ya cika Adam, shi da yake dodo ko a cikin manyan mutane, amma shi wannan 'yar shilar ke rainawa hankali, yana yi mata magana amma ta mayar da shi ?an iska.
Jabir ya jinjina kai ya ce "Lallai gaba da gabanta, anya wannan yarinyar ba mahaukaciya bace ba?"
Kallon Jabir tayi ta galla masa harara, haka kawai tana ganinsa ta ji ta tsaneshi, wani mugun haushinsa ya kamata, ya fiye shishshigi.
Adam rasa abin yi ma yayi, dama wata babbace he knows how to deals with her, amma wannan ya hukunta ta ya ce ya yiwa wa?.
Ruma ta mi?e tsaye da jakarta, tana kallon wanda suka kawota, jinjina kai kawai suke, da ganin namijin ?o?arin da ubangidansu yayi.
Cikin ?un?uni ta ce "Ni a mayar da ni in da aka ?auko ni" tayi maganar tana nufar ?ofar fita.
"Ku kamata ku ?aure mini ita, sannan a nemo mini waye ubanta, in nuna wa babanta banbancin arziki da tsiya, shine dai-dai yi na, dan na fuskanci bayan talauci har da rashin tarbiyya a tare da ita.
Ba tare da ta waiwayo ba ta tsaya, dan ma kar ta kalleshi ya yi mata kwarjini ta ce "Shi baban nawa sai ka bishi kabari ka nuna masa ka fishi ku?i, kuma Alhamdilillah ni dai an yi mini tarbiyya dai-dai gwargwado, kuma wallahi sai na saka yayyena sun yi maka bugun sakwara, har DPO na unguwarmu sai na gaya masa, ba sunanka Adam ba ?an galadima ko wambai to wallahi sai na fa?a ka saceni ka kawoni cikin maza" tuni ya daskare a wurin, jikinsa ya hau tsuma, ga zafin maganganu da fitsarar Ruma, ga razani na jin muryar da take ta addabar kunnuwansa.
Cikin azama ya fizgota, ya juyo da ita gabansa, ya ri?e hijjabinta tare da rigar uniform ?in ta. Kallon hannun takawa tayi, da ya sanya wani agogo mai kyawun gaske, amma babban abin da ya razana ruma, yadda ya ri?ota ta wuya hannun ?aton namiji a jikinta kan ?irjinta, abin da aka ce ta ?oye ta tattala, kar wani ya kai hannu wurin, idan ba haka ba za tayi ciki, amma hannun wani ?ato a wurin !!!
(Saura page ?aya mu kammala book1, wanda za su sai book 2, an fara payment 500 ne, in sai an gama document 800.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz bank.
Sai a turo shedar biya ta 08081012143)
Ayshercool
08081012143
?ANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
P22
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE, KO INFECTION? KO KUMA SO KI KE FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI,
SANNAN YAN UWA KUSANI DUK SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO*
Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu.
?? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin* su.
*1 Supplements na gyaran jiki*
*2 Supplements na gyaran gashi*
*3 Supplements mai da* *tsohuwa yarinya anti aging*
*4 Supplements na karawa* *fata kyau da sheki glowing skin*
*5 Supplements na masu ciwon jiki da stress
*6 Supplements na masu ciki, da masu shayarwa*
*7 Supplements na masu shayarwa*
*8 Supplements na tsofaffi*
*9 Supplements na karin ni'ima da tighteningn*
*10 Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11 Supplements na gyaran* *nono da mazaunai breast/hips*
*12 Supplements na gyaran* *HQ ciki da waje*
*13 Supplements na rage* *tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14Supplement na whitening/glowing skin*
*15 Supplement for Acne, dark spots remover*
Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban ha?a 1k subscribers a channel ?ina ba, anya akwai amana kuwa??*
Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.
Wani mugun ?acin rai ne ya kama ruma, kamar za ta yi kuka ta ce "Malam meye haka? Meyasa zaka ta?ani ka cikani"
Cikin tsananin mamaki, da rashin abin yi yake sake sauraren muryar ruma "Da..d...dama kece, meyasa ki ke bibiyata mai na yi miki ne?"
"Ni yaushe na sanka ma? Ka cikani kafin na yi maka hauka da tijarar da zaka yi dana sani, ka sakar mini hijjabi"
Tsananta ri?on da yayi wa ruma ya yi, yana sake bin ta da kallo, yana jin tamkar ba shi bane ba, anya mutum ce yarinyar nan, ko kuma dai muryar ce ke cigaba da yi masa gizo.
Ganin yadda duk ya gigice kamar zai fita hayyacinsa, ya sanya Jabir ?o?arin cire hannun takawa daga jikin ruma.
"Takawa, dan Allah ka kula mana, yarinya ce fa ?arama ba sa'arka ba, dan Allah ka saketa, sannan kamar yaya tana bibiyarka?"
Hanka?e ruma yayi, ya koma gefe ya zauna, yana dafe goshinsa.
Kuka ruma take wiwi, ta ?auki jakarta.
Jabir ya kalli wanda suka kawo ruma ya ce "Sidi ku mayar da ita".
Suka tasa ruma a gaba, ta waiwayo