Showing 93001 words to 96000 words out of 182697 words

Chapter 32 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22426

cikin masifa take.

Muryar wani magidanci suka ji yana ta magiya "Dan girman Allah ku yi mini rai, 'ya ta dan Allah ku rufa mini asiri"

?arar harbi suka ji, daga nan basu sake jin muryar mutumin ba, sai kuka da ihun yarinyar. Wadda ruma sukan yi wasa tare.

Gaba ?aya kururuwar mata da hargowar mutanen ta kara?e ?auyen, ha?i da harbe-harben bindiga.

Kan iya suyi wani yun?uri, wasu irin zaratan maza su kusan hu?u sun afko cikin gidan.

Mijin iya ya tsaya ?yam, babu tsoro a tare da shi ya ce 'Haka muka yi da ku? Kun sa?a al?awari mun yi duk abin da kuke so, amma bamu tsira ba, so kuke lallai sai mun fita mun bar muku garin, idan mun fita ina kuke son mu je?"

Cikin tsawa wani ya ce "Ba tuna mana al?awari muka zo ka yi ba, aiki muka fito yi, kai ku kama shi ku ?aure mana shi" aikuwa suka kama dattijon suka yi masa ?aurin huhun goro, suka rufe masa baki, sannan suka afko cikin ?akin.

Lawisa da zaliha sai kyarma suke yi, ruma kuwa tayi zuruu da ido, tana ganin sarautar Allah, abin da take ji a radion mama yau gashi a zahiri ba labari ba.

Hargitse kayan ?akin suka shiga yi, wasu kuma suka zaga suka kwance garken dabbobin da ake kiwo a gidan, suka yi waje da su.

?aya daga cikin su, ya zo ya dan?i ruma ya fara janta.

Cikin kururuwa iya take fa?in "Ka yi wa Allah da ma'aikinsa ka ?yale yarinyar nan, ba?uwace 'yar amana ce, dan Allah karku cutar da ita".

"Kai wuce da ita" ?ayan yayi umarni cikin tsawa. Iya ta yin?ura zata yi magana, ?ayan ya saka bakin bindiga ya buga mata a ka ta zube a ?asa sumammiya.

Ruma ta zura silifas ?in ta, ?ayan yayi waje da ita yana janta. Ko da suka fita ko waiwayowa ba sa yi, su Zaliha sai kuka suke suna kiran ruma, amma suka ce idan suka kuma magana sai sun harbesu.

Ko da suka fita tuni duk sun tattara wa?anda zasu tafi da su, a cikin daren suka ingiza su zuwa cikin daji, ciki har da ruma.

Tafiya suke tamkar suna ka?a dabbobi, an tattaro mata manya da ?anana sai maza 'yan tsirari.

Tafiya suke a tsananin duhu, ba tare da sun san in da suke sanya ?afafuwansu ba, ruma ganin abin take kamar a mafarki.

Tun suna tafiya ruma tana saka ran tafiya za ta ?are, har ta sare ta fara galabaita ta gaji ti?is, dan haka ta ja ta yi burki ta dur?usa tana hutawa.

Cikin tsawa wani ya ce "Ke! Tashi ki wuce mu tafi"

"Na gaji wallahi, ba zan iya tafiya ba"

"Ba zaki iya tafiya ba? Tashi kan na ?auke kanki da harsashi"

"Wai ya ka ke so na yi, ba ka ga ni yarinya bace ba, wallahi sai dai ku kasheni, nace na gaji ni wallahi ban ta?a ganin bala'i irin wannan ba"

"Dalla kasheta mu wuce, ba zata ?ata mana lokaci ba" cewar ?aya daga cikinsu.

"Tsaya in zauna daga nan, sai ku harbeni, ina zan iya wannan wahalar, Allah yasa idan na mutu na je a sa'a, na san mama za ta mini Addu'a" tayi maganar tana zama.

Wa?anda suke kan babura ne suka iso, wani yayi parking ya ce "Tsayuwar me kuke yi ne?, ku wuce mana".

"Oga wai ta gaji, shine ta samu wuri zauna ta ce mu harbeta"

Hasketa na kan babur ?in ya yi da fitila, ta saka hannu ta kare fuskarta tana mucincina ido, saboda hasken fitilar.

"Ke 'yar gidan waye a garin nan?" Ya tambayeta.

"Nifa ba 'yar garin nan bace, ziyara kawai na zo, gwaggo ta yaudareni aka kawo ni nan, wai sai zamu koma makaranta zata mayar da ni gida "

"Taso ki hau mu ?arasa" yayi maganar yana nuna mata babur ?in da yake kai.

Babu musu ko wani abu ta kama babur ta ?ane, ya ja suka tafi.

Aka cigaba da ka?a sauran a ?afa, tamkar shanu, a iya sanin ruma ita dai kawai sun yi tafiya mai nisan gaske, kafin su ?araso wani ?aton wuri, bayan wani dutse tsakiyar daji sosai da sosai.
Wasu mutanen suka tarar ri?e da manyan makamai, ga wasu mutanen da aka kama duk a zube a ?asa a zazzaune kamar fursunoni.

Ya karkata babur ?in ya ce wa ruma ta saukko.

Ta cimimiye shi sannan ta sauka, tana kallon wurin, sai dai duk da hasken farin watan ba kowa take iya ganewa ba.
?aga kai tayi ta kalli mutumin da ya kawota a babur. Da kayan jikinsa ta gane shi, mutumin ?azu da duka ha?u a kasuwa.
Cikin mamaki ta ce "Kaii, kai ne?"

Ya sanya yatsansa a kan le?ensa ya ce "Shhhhhh, wuce ki nemi wuri ki zauna"

Ta ?arewa wurin kallo, sannan ta kalleshi "Wai a nan zan kwana? Akwai sanyi fa, kuma a wannan filin babu abin rufa ba katifa?"

Wani daga cikinsu ya gyara bindigarsa cikin tsawa ya ce "Zo ki wuce, au ke da?i ma ki ke nema, zaki gane kuskurenki kuwa".

Ba ta motsa ba ta sake duban wanda ya kawota, ya jinjina mata kai ya ce "Wuce ki zauna"

A hankali ta ja ?afarta ta wuce ta zauna a in da aka nuna mata, wani irin sanyi take ji har cikin ?ashinta, ga bishiyoyin wurin sai rausayawa suke yi, ?afafuwanta duk sun yi tsami ga ?aya da ta taka.

Wasu daga mutanen suka koma gefe, suka kunna sigari suna sha.

"Allah mai iko, yau kuma nan Allah ya kawo ni" ta takure jikinta tayi shiru, da yanzu tana gida kusa da mama, mama tana lullu?eta.

***
Da ?yar Adam ya iya kai kansa hotel ?in da yake, bai tsaya ko ina ba sai ?akinsa, ya je ya bu?e ya kwanta a ruf da ciki, yana ta maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un.

Cikin wani abu mai kama da bacci da kuma gizo, yake jin sheshshe?ar kukan ruma, kamar dai kowane lokaci itan dai yake gani tana kuka.

Haka ya wanzu a wannan yanayin, da shi kansa bai iya tantance wane iri bane ba.
Alarm ?in wayarsa ne ya buga, alamar asuba ta yi, hakan ne ya sanya ya farka da kalmar shahada a bakinsa.

Ya tashi zaune ya ?an yi shiru yana tunani, shi dai tun da Allah ya sanya ya taso da ?uruciyarsa bai ta?a cikakkiyar lafiya ba, daga wannan sai wannan, bai ta?a tunanin zai kawo i yanzu ma a raye ba.

Ya yanke shawarar idan ya koma kano, zai kuma neman ruma ya ji meye matsalar sa da ita, da ta hana shi sukuni irin haka.

***
Har gari yayi haske, wa?anda aka ?auko su ruma tare da su ba su ?araso ba, ruma ta kalli wani tsaye da bindiga ta ce masa "Zan yi sallar asuba".

"To waye ya hanaki?"

"Ban gane ba, zan yi fitsari ne in yi alwala, a bani abin salla"

"Duk ciki waye ki ka ga yayi salla a nan, kar in sake jin bakin ki".

Wani dattijo ya ce "Yarinya sai dai ki yi taimama ki juya ki kalli gabasa ki yi salla, amma babu mai baki wani ruwan alwala a nan" tsananin mamaki ya cika ?wa?walwar ruma, ita haryanzu ma ba ta san dalilin da ya sanya a ka kawota nan ba.

Shawarar tsohon ta bi, ita kanta taimamar ba ta iya ba, haka nan ta batsaltsalata, ta yi salla.

Gari yayi haske sosai, sai ga wa?ancan sun ?araso a mugun galabaice, wasu ?afa sai jini take saboda taka ?ayoyi, wasu sai haki suke yi suna kuka, haka suma aka zube su a wurin gaba ?aya.

Matan da suke ciki sai koke-koke suke, wani ?ato ba?i daga cikinsu yayi musu wata razananniyar ?ara "Ku rufe mana baki, ko tarwatsa ?wa?walenku da harsashe".

Ruma tayi zurruu da ido tana kallon mutumin.

"Ke kuma na yi kama da ubanki ne da ki ke kallona?"

Jin maganar ruma tayi a sama ba da?in ji.

"A'a meya kawo zancen ubana kuma, ubana ko da ban san shi ba, yafi ka kyau" tayi maganar cikin ?un?uni.

"Me ki ke cewa?" Yayi maganar yana yo wa kan ruma.

Tayi shiru ta sunkuyar da kai.

Babu wanda ya sake bi ta kansu, aka bar su a wurin nan.

****
Gidan iya kuwa sai da gari ya waye ma?wabta suka shigo, aka yayyafawa iya ruwa, aka tafi da ita Asibiti da ita da mijinta, su lawisa kuwa sai koke-koke suke yi.
Ma?wabtansu kuwa an yi wa yarinyar gidan fyade an kashe babanta an tafi da matar gidan. Nan da nan labari ya cika gari.

Babu shiri gwaggo ta shirya ta sanya lawalli ya goyata a babur ya kaita garin su iya. A nan ta iske cewar an yi garkuwa da rumaisa. A take ita ma ta yanke jiki ta fa?i, ita ma aka yi asibiti da ita.

Iya tuni ta farka, gwaggo kuwa da ?yar ta farfa?o, tunda ta farko take koke-koke tana fa?in "Na shiga uku me zance wa uwar yarinyar nan, da na sani na basu 'yar su, ?aunar yarinyar nan ya sanya na ri?eta, da na san haka zata faru, da na barshi ya tafi da ita. Ni yanzu ina zan saka kaina"

Sai da ma'aikatan wurin suka taru suka yi ta rarrashin gwaggo suna bata ha?uri, amma cewa take "Ni dama tawan suka ?auka suka bar 'yar mutane, bawan Allah ba?uwace 'yar wa na ce, ban san me zasu yi mata da suka tafi da ita, Allah ka fitar da yarinyar nan ni Shafa'atu ina zan saka kaina, ta ina zan yi wa uwar yarinyar nan bayani?"

Likitan ya ce "Ai uwar yarinyar na tabattar musulma ce, kuma tayi imani da ?addara, dan haka ko a gabanta ne za a iya sace yarinyar "

Girgiza kai gwaggo ta yi ta ce "Ba zaka gane ba"

A social media Abubakar ya fara ganin abin da ya faru, kuma ya san da batun an kai ruma katsina, ?auyen da iya take, duk da yana makaranta.
Ba shiri ya kira Aliyu a waya ya sanar masa da a kan lallai ya bincika, su ji ya ruma take, sannan su gaggauta zuwa su ?aukota.

Usman ma ya gani, dan haka a burkice ya ja Aliyu yake nuna masa abinda ya gani.

Aliyu ya ce "Yanzun nan Yaya yayi mini magana a waya, ina son na kirasu a waya amma tsoro nake ji, babban tashin hankalina kar mai sunan Baba ya ji balle mama, dama ya ce gobe in Allah ya kaimu zai je ya ?auko ruma".

Usman ya ce "Ka ga ba wannan ba, ka kiras lawalli a waya ka tambayeshi yaya rumaisa take?"

Aliyu ya girgiza kai ya ce "Usman gabana fa?uwa yake yi fa, ance an karkashe wasu an tafi da wasu, kai dai ka kirasu"

Usman ya kira wayar lawalli, amma ta?i shiga, dan haka ya kira ta ?anlami babban ?an gwaggo, dan tabattar da abin da yake faruwa.

Sai da ta kusa katsewa sannan ?anlami ya ?aga wayar.

Ba tare da sun gaisa ba, cikin za?uwa Usman ya ce "Yaya ?an lami, ya ake ciki ne? Na ji 'yan ta'adda sun kai hari garin su Iya, ya ake ciki ya ya ina ruma?"

Yaya ?anlami ya ce "Wallahi kuwa, dan kaga gwaggo ma tana gadon asibiti, Baba kawai aka sallamo"

Aliyu ya kar?e wayar ya ce "To Allah ya kyauta, ya ya rumaisa, gobe in Allah ya kaimu yaya umar zai zo ya ?auketa ya taho da ita, dan Allah a ?aukota daga garin nan kan ya zo".

"Aliyu sai dai fa mu tsananta addu'a, an samu matsala 'yan bindiga sun tafi da rumaisa!!!"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, me ka ke cewa ne...?"

Usman ya girgiza Aliyu ya ce "Me ya ce maka ne?"

Kan Aliyu yayi magana, suka ga mai sunan Baba a tsaye yana kallonsu, Allah ka?ai ya san iya adadin lokacin da ya shafe a tsaye yana jin su ba tare sun sani ba.

Ayshercool

KANWAR MAZA

BOOK 2 PAGE 5


*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*



Tsuru-tsuru suka yi suna kallon umar, sai dai yanayinsu ya nuna a razane suke, kuma aka rasa wanda zai yi magana.

?arasawa yayi gabansu, ya kar?i wayar daga hannun Aliyu, ya yi dialing lambar ?anlami, yana kira ya ?aga tare da yin sallama. Sai dai ?anlami na jin muryar mai sunan baba cikinsa ya ka?a, dan ba ?aramin tsoron tijarar mai sunan Baba suke ba.

Cikin kakkausar murya Umar ya ce "Me ka gaya musu? Ina ruma take?"

?anlami ya ?an rikice sannan ya ce "Malam umar a saka addu'a, amma Akwai damuwa, ka san shi lamarin ?addarar Ubangiji ba ayi mata shamaki".

Cikin hasala ya kuma cewa"Ba nasiha na ce kayi mini ba, tambayata zaka amsa mini, damuwar me, ka yi mini bayani ina rumaisa take?"

Tamkar an ritsa ?an lami da bindiga ya ce "Umar wallahi 'yan bindiga sun tafi da rumaisa, kuma ba da ita ka?ai suka tafi ba, amma an sanar da jami'an tsaro za su yi ?o?ari a kai, za abi bayansu"

Cikin tashin hankali ya ce "Ya isa haka ?anlami, amma kun san garin nan babu cikakken tsaro kuka tura yarinyar nan? Babu yadda ba ayi ba a kan gwaggo ta bayar da yarinyar nan a dawo da ita gida amma ta?i, ta turata in da ta san babu tsaro, duk yadda ake ciki ku san yadda zaku yi, ni ban san wata magana ba kawai an ha?a baki da ku an yi garkuwa da yarinya ku san yadda zaku yi".
?anlami zai yi magana, mai sunan Baba ya kashe wayar ya cillar ya fice a fusace dan gaba ?aya jijiyoyin kansa sun mi?e saboda ?acin rai da tashin hankali.

Mama ce ta fito tsakar gida ta na fa?in "Wai babana shi da wa yake ?aga murya, me kuka yi masa ne yake ta magana sama-sama?"

Cikin sanyin jiki Usman ya ce "Sa?ani ne aka samu, kin san halinsa da zuciya da saurin fushi"

Mama ta ce "A'a ai kuwa bai fiye yin magana ba, sai an ?ure shi, wani abun dai ku ka yi masa, ko kuma fa?a kuke a tsakanin ku" gani tayi sun jeru basu ce mata komai ba, sai dai fuskokinsu ?auke da damuwa, kamar a firgice suke.

Ta dubi Aliyu da kyau ta ce "Gadanga wai menene, na ganku duk wani iri me yake faruwa ne, ko akwai wata matsala ne?"

Aliyu ya dake ya ce "Babu komai mama, ni bari na fita zan sayo omo na yi wanki".

"Ban da omon da babana ya sayo shekaranjiya ya shigo da shi kaya guda, kusan kayan, wane omon kuma ka ke nema ko ka manta ne?"

Ya dafe kai ya ce "Ohh na manta, aski zani, ai na manta shaf da Oman ne, idan na dawo daga askin sai na yi wankin" yana yin maganar yayi waje, Usman ya rufa masa baya.

Gaba ?aya mama ta kasa gane kansu, kuma ba wanda yayi mata bayanin wani abu. Kawai ta share ta cigaba da sabgoginta.

Duk yadda usman ya so dakewa abu ya gagara, a soro ya dur?usa ya fashe da kuka, shi ya riga ya karaya ya san ubangijin da ya halicci ruma ne kawai zai fitar da ita.

Aliyu ya rungumo shi ya ce "Haba usyy so ka ke sai mama ta gane ne? Dan Allah ka jure kan mu san abin yi, kar mu bari ta gano akwai matsala idam ta gane, ka san tana da hawan jini, yanzu zai iya tashi"

Usman ya ce "Wane abun yi da me zamu kar?ota? Me muke da shi? Mutanen da ba imani ne da su ba, 'ya mace ce fa, Allah ka?ai ya san me zasu yi mata, gara ace mutuwa ta yi ga gawarta da wannan tashin hankalin, wa zai kula da ita?".

Aliyu da tasa zuciyar ma ke daf da karyewa ya ce "Na sani, amma addu'a ba ta bar komai ba Usman ita zamu dagewa, kayi ha?uri tashi ka daina kuka kar mama ta zo ta samemu" haka yayi ta rarrashin Usman.

Mai sunan baba kuwa ji yayi duniyar ta yi masa zafi, ina ma shi aka ?auka aka bar ruma. Yaya mama za ta ji idan ta samu labarin an yi garkuwa da rumaisa?.
Zuciyarsa ta din ga zafi yana jin da zai ga gwaggo sai yayi mata rashin mutuncin da bata ta?a tunani ba, dan yana jin zai iya mangareta dan duk ita ta janyo wannan masifar, duk da tana ?anwar mahaifinsu, cewar da aka yi tana gadon asibiti jininta ya hau bai dameshi ba, dan da jinin tasa uwar ya hau ko wani abu ya samu ruma, gara duk abin da zai faru ya faru.

***
Zuwan takawa a Abuja a wannan karon ya sanya ya samu abubuwa masu muhimmanci da bincikensa bai kai masa ba a baya, sai dai zuciyarsa na ta azalzalarsa a kan lallai ya koma gida, jinsa yake tamkar a kan wuta, idan bai bar garin ba kamar wani mummunan abu zai faru da shi, dan haka babu shiri, ya tattara kayansa ya taho Kano, dama ga Ammi na ta waya dan duk a tsorace take, saboda yanayin jikinsa, Jabir ma duk ya addabeshi a kan nan kano ma akwai aiki, dan haka ya ha?a kayansa ya koma kano.

Sai ka ce a wannan karon ya fara tafiye-tafiye, Ammi sai hamdala take a kan dawowarsa gida lafiya, dan ba ?aramin tashin hankali ta shiga ba, da yayi tafiyar nan dan sam ji ta yi ba ta son tafiyar ta sa.

A gidan Turaki suka ha?u, da takawa, da Jabir da kuma Jamil da ya kasance wa ga Samha kuma cousin ?in sa.
Hira suke yi sosai, suna tattaunawa a kan rayuwa.
Jamil ya zunguri Takawa ya ce "Kai, wai me kake nufi da ni ne, ba fa ka taka gidana ba, ranar da na tare ma ko rakiya ba ka yi mini ba, kuma ba ka zo ba sai harkokinka kawai kake"

?an shiru Adam yayi, tun daga lokacin da ya ji muryar ruma a ranar ya rasa nutsuwarsa, kilisar ma da ?yar aka ?arasata da shi, tunani ya fara yi ko zuwa unguwar su zai yi.
'Ka je ka yi mata me?' wata zuciyar ta tambayeshi.
Tsaki yayi wanda ya fito fili bai sani ba.

"Tsakin me kake kuma?" Adam ya tambaye shi.

Girgiza kai yayi bai ce komai ba.

Jabir ya ce "Yauwwa Takawa, ina mutuniyarka kuwa wannan yarinyar?"

Ha?e rai Adam yayi tare da basarwa, Jamil ya ce "Wace yarinyar, budurwa yayi ne? Kai ka isa ka yi wa ?anwata kishiya?"

Jabir ya ce "To bana ce ba, wata 'yar figigiyar yarinya ce mai kama da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login