Showing 63001 words to 66000 words out of 182697 words

Chapter 22 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22397

?ANWAR MAZA


*Na Aisha Adam (Ayshercool)*

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES




P19

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE, KO INFECTION? KO KUMA SO KI KE FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI,
SANNAN YAN UWA KUSANI DUK SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu.*

?? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin* su.
*1 Supplements na gyaran jiki*

*2 Supplements na gyaran gashi*

*3 Supplements mai da* *tsohuwa yarinya anti aging*

*4 Supplements na karawa* *fata kyau da sheki glowing skin*

*5 Supplements na masu ciwon jiki da stress

*6 Supplements na masu ciki, da masu shayarwa*

*7 Supplements na masu shayarwa*

*8 Supplements na tsofaffi*

*9 Supplements na karin ni'ima da tighteningn*

*10 Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11 Supplements na gyaran* *nono da mazaunai breast/hips*

*12 Supplements na gyaran* *HQ ciki da waje*

*13 Supplements na rage* *tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14Supplement na whitening/glowing skin*

*15 Supplement for Acne, dark spots remover*

Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158


https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban ha?a 1k subscribers a channel ?ina ba, anya akwai amana kuwa??*

Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.



P 19



"Wai ke duk yadda mutum ya so ya kwa?eki ya nuna miki rayuwa ruma ba kya ganewa, sai ka ce rainon daji, yanzu usman ?in zaki gayawa kin fara ?irgar dangi, abin da ake ?oyewa a tattala?, kai wannan yarinya kune yaran ?arshen zamani"

"To mama ai gani na yi yayana ne, kuma bana ?oye musu komai"

"Eh ba kya ?oye musu komai, kuma aka ce miki ciki har da tsairaicin ki ko? ?auki kaya ki saka ni ki fice ki bani wuri, kan na taso kanki."

Ruma ta dur?usa ta ?au kayanta ta saka, dama mama ce za ta aiketa.

Mama ta kalleta ta ce "Ruma wai ke komai naki butsu-butsu babu kintsi, haka ake ?aura zanin ma, dama a dama ake ?aura zani, kalli ?waurinki duk a waje kamar zaki tsallaka wuta"

Kamar ruma za ta yi kuka ta ce "Mama ni ya zan yi, ni wallahi bana son zanin nan, idan ina tafiya a hanya ji nake yi, kamar na kwance shi na ri?e a hannu, har?e mini ?afa yake, ni nafi son wando ko doguwar riga"

"Aikuwa kin daina saka su, dole ki koyi ?aurin zani ki na 'ya mace, matsonan na ?aura miki"

Ruma ta ?arasa fuskar ta a ha?e, dan har ga Allah ba ta ?aunar zani sam.

Mama ta ?aura mata sannan ta kalleta ta ce "Ga farar hoda can a kan mudubi, ki ?an shafa sannan ki saka kwalli"

"Mama farar hoda kuma kamar wata 'yar tashe, ni ki bar mini fuskata a haka kawai, bana son shafa mata komai, kwallin nan ma idan na saka zazzagowa yake fuskata ta koma kamar ta boka"

Mama ta mi?e ta dan?i hannun ruma, ta ja ta zuwa gaban mudubi ta ce "Wallahi sai kin saka kwalli, ba zaki fita da ido kamar jan nama ba" ruma har da kuka mama ta gwale idonta ta saka mata kwalli, ita ruma a rayuwarta duk wani abu ma shafe-shafen kwalliya na mata, bai dameta ba ba tayi, dan basa burgeta. Ta sha zagi wurin mama kan ta tafi aiken nan.

***
Takawa kuwa lokacin da ya shiga ?aki, kan sa ciwo yake yi masa sosai, dan bacci ma yake ji a lokacin.
Kwanciyarsa babu da?ewa bacci mai nauyi ya fara ?aukarsa, sai dai baccin bai je ko ina ba ya fara jin wannan muryar a kunnensa tamkar ana yi masa ra?a "Sarki mai koriyar alkyabba" a hankali ya bu?e idonsa, ya hau dube-dube a ?akin, amma babu kowa.
Kawai sai ya ji ba ya son kwanciyar, dan haka ya tashi da sauri ya fito daga ?akin.

Iman kuwa sai da ta tsaya ta share hawayenta, sannan ta shiga sashen Ammi.

Ammi tana nan a in da suka bar ta a falo ba ta tashi ba, Iman ta ?araso cikin ya?e ta ce "Ammi, kin ga Mummy ce ta kirani ta bani"

Cikin mamaki Ammi ta ce "Ke da ki ka fita kaiwa Jabir lemo, me kuma ya kai ki sashin su? Kin san bana son zuwanki in da suke"

Iman cikin dakiya da ?o?arin danne hawayenta ta ce "Yaya Mahmud ne ya kirani, ya ce Mummy na nemana shi ne ta bani, bari na je na gwada" ta na gama maganar ta yi gaba, dan kar Ammi ta fahimci wani abu.

Takawa na tsaye a falon, har Iman ta yi gaba, ta ji ya janyota ya dawo da ita, ya ?an ?ura mata ido.

"Me suka yi miki?"

"Wai ni? Babu komai fa, kaya kawai ta bani"

"Me suka yi miki?" Ya kuma maimaitawa.

Tunanin ?aryar da zata yi masa ta hau yi, amma kan ta kai ga furta komai ya daka mata tsawa, hakan ya sanya jikinta fara rawa. Cikin razani ta gaya masa abin da ya faru.

"Wuce ki tafi" ya fa?a yana nufar ?ofar fita daga falon.

Ammi ce ta tare shi ta ce "Ban lamunta ba, kar ka kuskura ka je in da suke, da gayya suka yi, ka ?yale su kawai"

"Ammi, ba saboda Iman kawai nake wannan abun ba, na san a duk lokacin da aka ta?ata, kai tsaye ka aka yiwa, Ammi ko tausayin yarinyar nan ba sa ji?"

Ita kanta Nusaiba da ke zaune tana cin abinci, al'amuran gidan sun fara isarta, tana tausayin Iman sosai da sosai.

Ammi ta ce "Na fahimce ka takawa, amma tun da ka ga ina kawar da kai, to kai ma ka dinga ha?awa da ha?uri, ka koyi kawaici ba a komai zaka yi magana ba, kar ka kula su".

Baba Uwani da ke 'yan kaye-kaye a falon ta ce "Ayi ha?uri uban gidana, ban san ka da yawan hasala ba, Allah ya huci zuciyar magajin Galadima, ayi ha?uri"

Da ?yar Adam ya ha?ura, ya nemi wuri ya zauna, ya na jin yadda zuciyarsa ke tafasa, shi dama ba ta Mummy yake ba, Mahmud kawai yake son ya yiwa kashedi a kan rayuwarsu.

Nusaiba tsam ta mi?e, ta nufi ?akin Iman, ta tarar da Iman ?in zaune ta zuba uban tagumi, tana kallon kayan da aka yi amfani da damar bata, aka ci zarafinta, kayan da basu wuce ta yi kyauta da ninkin su ba.

Nusaiba ta dafata ta ce "Masoyiya"

Iman ta kalli Nusaiba ta ce "Na'am Anty Nusyna"

Kallon idon Iman Nusaiba ta yi, idonta ya nuna ta yi kuka sosai.

"Be brave iman, kiyi ha?uri, ban san yadda zan fasalta miki abin da nake ji ba, idan aka cutar da ke ba, muna sonki sosai Iman, kin san yanayin halin da ki ke ciki, dan Allah ki daina damuwa ko ?ata ranki"

Iman ta yi murmushi ta ce "Kar ki wani damu, yayata ai na ma riga na saba"

Nusaiba ta zauna sosai ta ?ora da cewa "And yakamata ki daina nuna ki na jin tsoron su, musamman yaya Mahmud kamar mara tunani, abin da aka gaya masa kawai da shi yake amfani, ai gara ma yayi ya koma in da yake karatu mu huta masifaffen banza"
Iman ta toshe baki ta ce "Sai na gaya masa abin da ki ka ce, babu ruwana" tayi maganar tana dariya.
Ajiyar zuciya Nusaiba tayi tana murmushi, ganin yadda murmushi ya bayyana a kyakkyawar fuskar Iman.

***

"Ohh ni rumaisa sai girma nake, mama, ta bakin naki kwanci tashi asarar mai rai, na shiga jss2 fa"

"Aikuwa dai, kina ta girma amma babu nutsuwa ba"

"Kai mama, Allah ya nuna mini lokacin da zaki yabeni, ke kullum bana abin arziki a wurinki mamancy"

Mama ta girgiza kai ta ce "Ai ke gaba ?aya abin tsiyarki ya ninka na arzikin yawa"

"Mama"

"Ina jinki"

"To ?an kalleni mana"

Mama ba ta kalli ruma ba ta ce "Sai kuma kiyi ai"

"Dan Allah ki sai mini shayi da indomie, kin san bana son tuwon nan "

"Rumaisa ai ni ce ma Indomien, zo ki gutsiri in da ki ke so ki ci, tuwo kuma ban yi miki dole ba, ki barni da kayana"

"Allah ya ji?an matar da ta ?ir?iro tuwo idan musulma ce, amma ta cuceni zuciyata tafi raya mini a zamanin tsunburbura ta zo"

Ruma ta ?araci soki burutsunta, da gwasalewa mama tuwo, mama ta?i kulata.

Hankalin ruma ne ya tsaya a kan rediyon da mama take ji, wata mata tura wasi?a, tana son a bata maganin da zata sha, tun da tayi yaye ?irjinta ya zube kullum mijinta cikin yi mata gori yake.

"Kan uba, amma wallahi maza basu da kai, dan Allah meye ha?insa da kallonta?" Mama ta ja rediyon ta kashe.

"Mama ya zaki kashe, ki bari mu ji mana, nifa bana son harkar watsewa, wallahi ka gaya mini maganar banza sai na tafi gidanmu, wannan ai rashin tarbiyya ne, ya ya zai din ga yi mata kallon ?urilla, kuma mama ba kin ce mini ?oyewa ake yi ba? Ita ma har da ita"

Mama dai ta basar, tayi mata shiru, can ta kuma cewa "Hmm kin san Allah mama, nima na gani fa, 'yan ajinmu na islamiyya suka ce, wai idan mace tana tafiya ba ta saka hannu a hijjabinta, maza kallonta suke yi, haka ma idan ta juya bayanta, jiya da na je gidan Asabe ban samo gawayi ba na je titi, daga nan na tsaya sayen mai, kin san riga da skirt na saka, sai mayafin abayat, wani mutum ya tsurawa gurin zamana ido, ai ban sani ba, ina waiwayawa muka ha?a ido, na ce malam kalli gabanka mana, baki ganshi ba babba da shi na saka hannu na kare abina har na zo gida".

Abdallah ya ce "Sannu jikar faisal, duk 'yan matan da suke kaiwa suna komowa a wurin, ba wadda ya kalla sai ke ?waila, wani ?an abu kamar falanki, saboda asara ke zai tsaya kallo"

"Wallahi ni ba ?waila bace ba, kuma ka je ka tambayi kowa na wurin ka ji, kallona yake yi, ni kuwa na saka hannu na rufe"

Mama ta ce "Ya isa haka, kuma saboda tsabar rashin sanin ciwon kai ki tafi har titi da ?an ?aramin mayafin da bai fi ayi kallabi da shi ba, duk ranar da Allah ya nuna mini, sai na zane ki. Kuma zan saka bababana ya je islamiyyar lallai a raba muku aji da wannan yaron, dan sun fi ?arfin tunanin ki"

Da sauri ruma ta ce "Ki yiwa Allah da ma'aikinsa, kar ki aika mai sunan Baba, kin san yanzu ?iris yake jira yayi mini aure".

"Aikuwa ina daf da gaya masan, idan har baki nutsu ba, kin daina wannan rashin kan gadon ba, gara ya aurar da ke na huta"

Ruma ta saka hannu ta kama la??anta ta ce "Na daina da yardar Allah"

***

"Takawa, wai yaushe zaka je ka ?auko yarinyar nan ne?"
Ya ?an lumshe idonsa ya bu?e sannan ya ce "Zan ?aukota ne, gara ta ?an huta ta nutsu tukuna, visarta har yanzu da saura"

Ammi ta ce "To shikenan, yauwwa ya maganar tafiyar da na ji Jabir ya ce zaka yi? Meye gaskiyar maganar?"

"Ammi ki manta da shi kawai, ?an rainin hankali ne a wurin aiki ne za a tura mu wani bincike".

Ammi ta numfasa sannan ta ce "To, Allah ya yi jagora, amma dai duk da haka kamar yadda ya ce ka din ga kula takawa, ka san currently a ?adamin da kake, kar ka janyo mana wata wahalar wadda muke ciki ba ta ?are ba, dan Allah ka dinga komai a sannu, sannan ka ri?e addu'a kamar yadda nake jaddada maka"

"In sha Allah Ammi, kar ki damu ina iya ?o?arina wurin yin Addu'a".

"Haka ake so, Allah ya yi maka jagora"

"Amin Ammi".

Daga haka ya ?auko wayarsa yana duddubawa, yana tsaka da duba wayar, Ammi ta kuma cewa "Ko yaushe Mahmud zai koma makaranta, na ga kamar lokacin komawarsa yayi, kuma ance mini haryanzu ana ganin gilmawarsa a gidan nan"

Takawa ya sauke wayar, ya dubi Ammi ya ce "Ammi, ba babarsa tana kallo bai koma ?in ba ta zira masa ido, dan Allah ki daina damuwa da abin da ya shafe su, ki din ga ?agawa kan ki hankali".

Ammi ta girgiza kai ta ce "Da kai da su ni duk abu ?aya ne a wurina, ba zan so rayuwar wani daga cikinku ta samu tangar?a ba".

"To Ammi tun da ba sa yi da ke, ai mu mun isheki rayuwa, dan Allah ki manta da su"

Ajiyar zuciya Ammi ta yi, ba ta sake cewa komai ba.

***
Yau kamar korarriya haka ruma ta shigo gida, sai cika take tana batsewa, ba ta kula kowa ba ta cire uniform ta yi wanka, ta zubo abincin ta ta fara ci.

Kamar wadda aka tsikara ta ce "Yaya Aliyu, wai ina ce makarantar 'ya'yan gwamna ne?"

Yayi murmushi ya ce "Mai yafaru?"

"A'a tambaya kawai nake yi"

"A manyan makarantu suke, wasu a turai ma"

"Suna zama a ?asa, ajinsu babu abin zama?"

Yayi dariya ya ce "Amma kin ci kai, 'ya'yan gwamna ne zasu zauna a ?asa? Zama a ?asa a makaranta wannan ai sai ?an talaka"

"To meye banbancin mu da su? Dukkanin mu ba mutane bane, kuma muma ba 'ya'ya bane?"

"Kuna da bambanci mai tazarar gaske, dukkaninku mutane ne, kuma 'ya'ya ne, amma iyayensu ke ri?e da madafun iko, abin da zaku yi ku taimaki kanku a matsayin yaran talakawa shi ne, kuyi karatu komai wahala, idan ba haka ba kuwa ku ?are a bayinsu da 'ya'yansu"

Tamkar ruma zata fashe da kuka ta ce "To wallahi zan yi Allah ya isa, aka ce duk 'yan ?asa ?aya muke, bencinmu ya karye, dama wasu a ?asa suke zama, kullum sai kayana sun yi datti, uniform ?ina duk sun fara ko?ewa. Ga malaman namu ma sai a hankali, wallahi malamin English ?in mu bai iya turanci ba kame-kame yake yi, malamin math ?in mu kuma Arabic yayi ba uwar da muke ganewa, ga ajinmu azababben zafi window ?aya ce, bana gane komai a makarantar kamar na daina karatun. Kuma jiya nake ji a radion mama uban ku?in da ake saiwa wasu manyan motoci sai ka ce motar aljanna, ko meye sunansu oho na manta, to wallahi duk wanda aka raba da ha??ina ya cinye ban yafe ba, zama a ?asan da nake a matsayina na 'yar ?asa"

Mama ta ce "Ruma wa ki ke yi wa Allah ya isa, ban hanaki wannan ?abi'ar ba ruma?"

"Mama ba zaki gane halin da muke ciki ba, ga rashin abin zama, ga zafi ga rashin malamai ga duka kamar an samu jakai, har noma ake sakamu fatanya a makaranta, gaba ?aya makarantar mu 'ya'yan talakawa ne, shikenan mu ba mutane bane".
Ruma kenan, gaba ?aya tunaninta da maganganunta sun shallake shekarunta, wata?ila hakan yana da ala?a da yawan jin radion da mama take yi, da yawan tattauna matsalolin da ?asa ke ciki da yayyenta suke yi.

Babu wanda ya kuma tanka mata, tayi bambaminta ta gama, dan ta wani fannin tabbas Ruma tana da gaskiya, amma babu yadda za ayi a gaya mata tana da tazarar da wa?anda take hange take kamanta kanta da su ta gane.
Haka ta ?are cin abincin tana mita, kuma bil ha??i har cikin ranta, take fa?ar yadda abin yake yi mata ciwo.

Kasancewar yau Alhamis babu makarantar islamiyya, Huzaifa da Yasir duk suna gida.

Huzaifa ya nutsu yana ta kallon tiktok a wayarsa, ruma ta lalla?a ta zira kanta tana kallo.
Huzaifa ya ?auke wayarsa ya kalli ruma ya ce "sai ka ce mayya, mara zuciya kawai"

"Eh na ji, ni kunna dai mu gani"

"Ba zan kunna ba, ke ki ke saya mini data?"

"A'a, amma ?an kunna gani kawai zan" ya ha?e rai ya ce "Ba zan kunna ba, bar nan wurin ko na dakeki"

Ta tashi tana zum?ura baki ta ce "Mutum dai idan tsiya tana bin sa, ko ka ra?eshi haushin ka yake ji?"

"Ni ne tsiya take bi ko? Wallahi ki ka bari na zo kanki, saina kwa?a miki mari"

Cikin tsiwa da rashin kunya ta ce "To kar ka barni da rai ma mana, idan da rai nima zan yi wayar nan" Jin yadda take ?aga murya ya san idan ya biye mata, fa?a za su yi, ran mama ya zo yana ?aci, kawai ya shareta ya cigaba da danna wayarsa.
A hankali ta lalla?a ta koma wurin Yasir, shi kuma Yasir Instagram yake kallo, dan haka sai ka ce dole ta ?an ma?ale tana le?awa dan kar shi ma ya koreta.
Ya ?aga kai ya kalleta ya ce "Dawo ta nan ki kalla, madam no heart"

"Ai in dai zaka barni na kalla, to babu damuwa kafi wancan tsiyar muka rako duniya". Yasir ya yi murmushi bai ce komai ba.
Sai dai tamkar zata shige cikin wayar, ko ta ?wace masa wayar.

Duk hoton ko videon da ta gani sai ta tsaya ta yi liking. ?arshe sai sakar mata wayar ya yi, ya tashi ya bata wuri.

Sai da mama ta tashi ruma ta aiketa, sannan ta tashi daga kallon wayar.

?aukar ni?a mama ta aiketa a can titi, ta ?auki kayan sa?arta ta tafi da su, tana tafe a hanya tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login