Showing 24001 words to 27000 words out of 182697 words
saka shi aka ?auraye.
Kafin mama tayi magana mai lallai ta kira mama, suka gaisa.
Mai lalle ta ce "Mama, wallahi kar ki ga lallen ruma bai yi kyau ba, ana saka mata wai sai an cire ba ta so ta gaji, da na ?i cire mata, ta cire abinta wai kashi take ji"
Mama ta ce "To shikenan, kar ki damu na gode sosai" ta kalli in da ruma ta tsaya ta ci magani kawai ta jinjina kai ba ta ce mata komai ba.
Tun magariba, ruma taga mama ta kwa?a lalle kaya guda, ba ta kawo komai a ranta ba, ta cigaba da harkokinta.
Sunanta da mama take kirane, ya sanya ta san asuba ta yi, ta yin?ura zata tashi, ta ji motsin leda a ?afarta, ta tashi zaune amma ta ga hannunta da ?afarta duk leda.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mama me ya sameni?"
"A ina?"
"Wannan ledar mecece?"
Mama ta ce "Ahh, ruma ai ba ke ka?ai ki ka san ta kan tsiya ba, na sai miki kaya ba godiya ki ka raina, na biya ku?i ayi miki lalle ki ka ?i zama, ai da ni ki ke zancen, kina wannan shegen baccin na yi miki dungulmi da shi zaki yi sallar, tsohuwa ta fa?a kwata ba, irin wanda nake yi, kuma kitso ma gidan Hanne zan saka Huzaifa ya kai ki, tayi miki zane hu?u ba dai ba kya ji ba, ai daidai nake da ke, ina sane nake kawar miki da kai".
Ruma ta kalli yadda aka ?unshe mata ?afa har ?wauri, ga hannayenta kuma ana batun ayi mata zanen Hausa guda hu?u a ka tayi salla, ta tuna uwar rigar da zata saka a matsayin kayan ssllarta, ta ?ora hannu a ka ta zunduma ihu.
DAN ALLAH MASU NEMA DAGA FARKO KU DINGA TAMBAYA A GROUP KO DUBA WATPAD KO AREWABOOKS NA GODE
AYSHERCOOL
08081012143
[03/07, 2:14 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following ?ina a arewabooks a kan account ?ina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode
*Ina mi?a sa?on godiya, ga wa?anda suka yi mana ta'aziyya na rashin uba da 'yar uwa Naima Suleiman (Nimcyluv) ta yi, muna fatan Ubangiji Allah ya ji?ansa da rahama.*
*TA?ABBALALLAHU MINNA WA MINKUM, INA TAYA AL'UMMAR MUSULMI BARKA DA BABBAR SALLA, UBANGIJI ALLAH YA KAR?I IBADUNMU YA MAIMAITA MANA*
P8
Da rige-rige Usman da Abdallah suka shigo ?akin, suna tambayar meyafaru da ruma take wannan uban ihun.
Kallonta Usman ya yi, ya kalli mama ya ce "Mama meya sameta ne?"
Mama ta ce "Ku tambayeta mana, ba gata nan a zaune ba"
Abdallah ya ce "Ke menene?"
Nuna masa hannunta ta yi, tana sake fashewa da wani uban kukan.
"Wannan ledar ta meye haka a hannunki, kamar wata miskiniya"
?are baki tayi, ta cigaba da kuka iya ?arfinta.
"Dalla ki rufewa mutane baki, kiyi mana bayanin menene?" Usman ya daka mata tsawa.
"Ba mama ce ba"
"Me maman tayi?"
"Ta yi mini lallen tsofaffi wai tsohuwa ta fa?a kwata ina bacci, wallahi dariya za ayi mini idan aka ganni da shi".
"Kuma saboda baki da mutunci, ki ke mana wannan uban ihun da Asubar nan, ke dai ba zaki yi hankali ba ko?"
"Wallahi mama ba ta sona, ban san meyasa ta tsaneni ba, wayyo Allah na"
Abdallah ya ce "Allah ya ?ara, a wannan shegen baccin naki, har aka yi miki lallen baki sani ba".
Mama ta ce "Ki tashi ki kwance lallen nan kiyi salla".
Ko motsi ruma ba ta yi ba balle ta tashi.
Abdallah ya ce "Wai wane irin lalle ne tsohuwa ta fa?a kwatar ne?"
Cikin kuka ruma ta ce "Irin fa wanda mama take yi a ?afarta"
Dariya ce ta ?wacewa Abdallah, ya ce "Haba mama, ya zaki yi mana haka?"
Mama ta ce "Hukunta ta nayi, duk rashin jin da take yi ba ta zaci ina da hanyar hukunta ta ba, na bada ku?i ayi mata abin arziki na zamani, amma ta?i zama, ai da ni ki ke zancen, kuma ajima da kaina zan kai ki kitso zane hu?u za ayi miki".
Sosai ruma take kuka, Usman kuwa ficewa yayi ya cigaba da sabgarsa, Abdallah ne ya kaita bakin rariya, ya tayata ya cire ta wanke, aikuwa hannunnan yayi jawur, lalle ya kwanta ?o?ar hannunta da ?afarta.
Da gari yayi haske kuwa, Huzaifa ya ga lallen rumaisa, ya zauna ya sakata a gaba ya dinga yi mata dariya, har da kifawa, wai hannunta kamar kuturwa.
Ko Abincin safe ruma ba ta ci ba, sai kuka da goge hawaye, wajen ?arfe goma na safe, mama ta sakata a gaba zuwa gidan kitso.
Kamar yadda mama ta fa?a, kitson hannu biyu aka yiwa ruma, gashi ta sha azaba a wurin mai kitson, saboda da ta ?i tsayawa, mama na dukanta, matar kuma ta matse mata kai a tsakanin cinyoyinta, ga kitson azabar zafi tamkar za a zaro ?wa?walwarta saboda yadda matar ke jan gashin.
Ko da aka gama kitson, ruma ta ha?a gumi ga hawaye da majina saboda azabar zafi, mama ta sakata a gaba suka tafi gida.
Ruma da ta kalli hannunta ranta yake ?aci, saboda hannun ganinsa take kamar ba nata ba.
Har ana gobe salla ruma bata farin ciki, ji take ina ma ace an fasa sallar idi wannan shekarar, saboda wannan yankan ?auna da mama tayi mata.
Har bata son a aiketa, dan idan ta fita ta ga yara sun sha kitso da ?unshi, sai ta yi kuka, saboda yadda ta ?arfi ita aka mayar da ita zamanin mutanen da.
Yanzu haka tana tafe a hanya, zuwa aiken da mama tayi mata, ta gaji da tafiya ga ?acin rai, ta samu wuri tayi zamanta a kan wata baranda, tana share hawaye.
"'Kukan me ki ke yi ne haka, ba aiken ki aka yi ba?"
Ta ?aga kai taga mai maganar, Auwal ne, na makarantar islamiyya da ta yiwa bori rannan.
Shiru tayi masa tana tura baki.
"Meyasa ki ke kuka?"
Mi?ewa ta yi tsaye tana fa?in 'Babu komai"
Ya ?an girgiza kai ya ce "Ina Yasir?"
Cikin ?un?uni ta ce masa bata sani ba, tayi wucewarta.
Mamaki ne ya kama shi, duk in da ta ganshi ko ba zai kulata ba, sai ta yi masa magana, amma yau tayi masa wula?anci.
Aiken da bai fi tayi shi a mintuna ashirin ba, sai da ta shafe awa biyu da rabi, ta koma gida Aliyu sai da ya mur?e mata kunne, saboda yadda ta je ta da?e.
Da safiyar salla kuwa, an kai ruwa rana da hajiya ruma kafin tayi wanka, dan cewa ta yi ba zata je idi ba.
Huzaifa kuwa musamman ya ?i shiri da wuri, sai ya ga shigar da ruma zata yi yayi mata dariya.
Ta na kuka, mama ta watso mata wannan atamfa da ta zauna ta dinga kushewa.
"Mama dan girman Allah ki barni na saka tsofaffin kayana, wallahi bana son kayan nan".
"Ni ki ke gayawa ba kya son kayan nan, zaki saka ki wuce ko kuwa?"
Za ta tsaya gardama Aliyu ya yi mata tsawa, ya ce ta ?au kayan ta saka su wuce sallar idi.
Ga lalle dungulmi, ga kaya ?inkin mutanen farko, ga kai babu kitso mai kyau, ba yari ba sar?a koma kamar 'yar ?auye.
Huzaifa kamar ya shi?e don dariya.
"Yarinya kin yi kyau kamar bafulatanar ?auye" Yasir ya yi maganar yana dariya.
"Babu ruwanka da ni Yasir, zan maka rashin mutunci wallahi".
"Na kuma jin bakin ki sai na ?arara da ke, maza wuce mu tafi" Aliyu yayi Maganar yana nuna mata hanyar fita.
Usman ne ya mi?o mata sabon hijjabi ya ce "Gashi nan ba dan hakinki ba".
Ajiyar zuciya ta yi, ko ba komai hijjabin zai taimaka mata ta rufe wannan buhun ?inkin, tun da hijjabin dogo ne.
Kar?a tayi tana yi masa godiya, ta saka suka tafi idi.
********
"Masha Allah, looking take away my beautiful angel" Ammi ta fa?a tana kallon Iman.
Murmushi iman tayi ta ce "Ammina, an yi salla lafiya"
"Alhamdilillah my dear, ina fatan dai an yi mini Addu'a"
Murmushi ta yi ta ce "Ba dole ba Ammina"
Wata matashiyar budurwa da ke zaune a kan kujera, ta ?ago ta ce "Wai mu Ammi baki ganmu bane?"
"Na ganku mana"
"Ai shikenan Ammi, wannan wariyar launin fata tayi yawa, mu shikenan ba za ki dinga kallanmu ba, sai wannan mai kama da bafulatanar dajin" cewar ?aya yarinyar.
Ammi ta ce "Kun dai ji kunya, da ku ke kishi da ?anwarku"
Iman tayi musu gwalo ta ce "Iya wuya dai, nice ta gaban goshin Ammina"
'Ta mayar da ke ciki, ko a saka ki a zanin goyo a baki Nono, ?arshen ?auna"
Ammi ta girgiza kai ta ce"Allah ya shirye ku, Iman ki je ki shirya direba zai kai ki gidan zinariyar Galadima, ki kai musu Abincin salla".
?ata fuska Iman tayi ta ce "Ammi"
Kan ta ?arasa maganar, Ammi ta ?ora yatsanta a kan lips ?in ta ta ce "Shhhh, bana son musu, tana ta complain ba kya zuwa" ?an gya?a kai Iman tayi ta ce "Shikenan Ammi, bari na shirya"
*****
"Ke ba zaki ta so ki fara kai tuwon nan ba"
Ruma ta kwa?e fuska ta ce "Dan Allah mama ki yi ha?uri, ki bawa su huzaifa su kai wallahi idan na fita dariya za ayi mini"
"Ni nake aiken ki, ki ke cewa na aiki wani ruma, ni ko ruma?"
"A'a mama ba haka bane ba, wallahi dariya yara suke yi mini" tayi maganar hawaye na taruwa a idonta".
"Tashi ki wuce ki je aiken da aka yi miki" Usman ya daka mata tsawa.
Jiki na rawa ta tashi, ta ?au kwanukan da mama ta zuba tuwo, ta fara kai wa.
A hanya ta ha?u da wasu 'yan makarantar bokon su, cikin fara'a ?ayar ta ce "Laa ruma, ya ki ke ina kayan sallar ki?"
Ruma ta kalleta ta ce "Ji masifa, to ba ni da su, ba a ?inka mini ba"
"Daga tambaya sai masifa?"
"Eh, ina ruwanki da ina kayan salla na, tsirara ki ka ganni?" tayi maganar tana saye hannun ta a cikin hijjabi.
"Kutmelesi, ruma meye wannan a ?afarki?" Gaba ?aya suka kalli ?afar ruma, da take sanye da silifas ?an madina, ga ?afa tayi maroon da lalle, kasancewar ruma ba iya ?aurin zani ta yi ba, zanin ya ?age har ?waurinta, kuma hijjabin bai gama rufe ?afar ba.
"Kutmelesi, wane irin lalle aka yi miki, lallai mai lallen nan ta cuceki, kut kamar ?afar tsohuwa"
Dariya yaran suka kwashe da ita suna sake le?a ?afarta.
Cikin takaici, ta juya zata tafi, amma wata za?a?urar yarinya, ta biyo ruma tana ?age mata zani.
Mai jiran ?iris ya samu a sarari, tuni ruma ta yi watsi da kwanuka, ta fara sana'ar ta ta dambe.
Kasancewar a ?ule take dama, ta rasa in da zata sauke fushinta, dan haka ta zage ta kama yarinyar nan ta dinga jibagarta kamar Allah ya aikota.
Suna cikin damben Allah ya bawa yarinyar sa'ar ketawa ruma hijjabi, hakan ya ?ara tunzura ruman, ta danne yarinyar tana duka.
"Wannan yarinya an yi jarababbiya, duk in da ta tsuguna sai dambe, sai ka ce annoba" cewar wani mai awo a gefe, da bai raba su ba sai zance.
?agowa ta yi cikin masifa ta ce "Wallahi ni ba annoba bace ba"
Ta du?a ta cigaba da dambenta. ji tayi an yi sama da ita, ta fara kokowar ?wacewa tana kai duka.
"Zaki nutsu ko sai na kakkarya ki" yaya Aliyu ne ya tsare ta da ido.
"Dama abin da ta aiko ki kenan?" Ta yi shiru tare da sunkuyar da kai.
"wuce mu tafi, dage uwar fa?a"
Haka ta kwashi kwanukan, da yagaggen hijjabinta a hannu ya tasa ta a gaba, zuwa gida.
Mama na ganin ruma ta shigo tare da Aliyu, a yadda ta shigo kawai mama ta gane halin ta je ta gwada a waje.
"Damben ki ka je ki ka yi kenan ko, mara kintsi?"
Wage baki ruma tayi zata fara yiwa mama bayani, amma mama ta katseta ta ce "Ban tambayeki ba ruma, ki je ji yi tayi, bakin mutane kawai ya ishe ki"
Gefe ta koma ta zauna, tana jin yadda ba ta gamsu da dukan da ta yiwa Hauwwa ba, saboda dariyar da suka yi mata.
Yaya Umar ne ya fito daga ?akin su, cikin wata dakakkiyar shadda dark blue, ya karya hula sai ?amshi yake zubawa.
Tsuruu ruma ta yi da ido, tana jiran ya sauke mata masifa, tun da ya ji ance ta yi dambe.
Nufota ya yi, ita kuma ta ?ura masa ido ko ?iftawa ba ta yi.
Ya kalleta ya ce "Na canza miki ne?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a ka yi kyau ne"
Murmushi ya yi, ya mi?a mata leda ya ce "Je ki ka gwada wannan" da sauri ta tashi, ba tare da sanin meye a ciki ba ta kar?a ta shiga ?aki.
Doguwar riga ce ta shadda kalar kayansa, da mayafi da sabon takalmi da yari da sar?a.
Ko da ta saka ta fito ba ?aramin kyau ta yi ba.
"Mama kin ganni, na yi kyau"
Aliyu ya ce "Saboda son kai, shine ku ka yi kaya iri ?aya babu ko labari"
Cikin tsananin farin ciki ta ce "Yaya Ussy, kalleni dan Allah na yi kyau?"
"Eh to, babu laifi sai ki ka zama kamar budurwa, duk da ?waila ce".
Cikin tsananin farin ciki, ta fa?a jikin yaya Umar tana murna "Yaya na gode sosai, Allah ya saka maka da alkhairi ya sa ka gama da duniya lafiya"
Ganin yadda take murna ya sanya shi yin murmushi na gefen baki ya ce "Allah ya sa ki daina rashin ji".
"Iyee, lallai mai sunan Baba, ni sai ka ha?ani da atamfa kala uku, amma kai da ?anwarka ka yi muku kaya iri ?aya, wato an fi son ta a kaina" mama tayi maganar cikin sigar wasa.
Murmushi ya yi, dan ya san halin mama da barkwanci wasu lokutan.
Mama ta shiga ?aki, ta fito da wata ?atuwar leda, ta mi?awa ruma ta ce "Gashi nan, ba dan halinki ba, kayayakin da suka yi miki ne, na wannan sallar na?i nuna miki dan in hora ki"
Rikicewa ruma tayi, dama suna yi mata ?inke-?inke, amma sallar bana bata san sun yi mata ba, dan a ?alla ta tashi da kaya ku san dozen, banda hijjabai da abun hannu da sauransu.
"Wayyo Allahna, dama kuna so na haka? Duk nawa ne wannan mama kin ga fa duk nawa ne"
Gaba daya suka kewaye ta suna murmushi, ganin yadda ta rikice tana murna.
Bin su ta dinga yi ?aya bayan ?aya tana yi musu godiya, tana zuwa kan Huzaifa ya wani maze ya ce 'Kar ki damu, wannan fa bakomai bane ba, idan har zaki dinga biyayya".
"Ba zan yi biyayyar ba, na san ma ba uwar da ka saya mini, duk gidan nan waye ya kai ka talauci da son banza?"
"Laaaa, ke fa ba a abin arziki da ke ko?"
"A'a yi ha?uri mama, shi ?in ne zai ?ata mini rai, yanzu a cigaba da zuzzuba tuwon ina kaiwa, amma wallahi duk in da na san ba za a bani ku?i ba, sai dai Yasir ko Huzaifa su kai"
Haka tayi ta rabon Abinci cikin annashuwa, gidan da aka bata ku?i tayi ta murna, idan ba a baya ba tayi ta jin haushi.
********
Ba zata iya ?ayyade rabonta da gidan nan ba, dan haka ta ?aga kai take ta na kallon sauye-sauyen da aka yi a gidan.
Ya ?awatu, duk da ginin yana nan a yadda yake, amma an yi wa gidan gyara sosai.
Da haka ta ?arasa cikin ?aton falon da ke cikin gidan.
Hadimai ne ke ta kaiwa suna komowa a cikin tangamemen falon, suna aikace-aikace.
?aya daga cikin hadiman ce ta kalli Iman da fara'a ta ce "Maraba da zuwa".
Iman ta ce "Yauwwa sannunku da aiki, Ummma fa?".
"Tana cikin turaka, bari ayi miki iso"
Babu jimawa hadimar ta fito, ta kalli Iman ta ce "Bisimillah, ta ce ki shiga"
Bayan hadimar Iman ta bi, zuwa turakar Ummma.
Shigarsu ?akin ke da wuya, gaban Iman ya fa?i, bisa tozali da mutanen da ba ta son ko ha?a hanya da su, ba dan jinin Ummma bane su, to tabbas da kai tsaye zata iya cewa mutanen da ba ta ?auna.
Fa?a?a murmushi Ummma tayi ta ce "Masha Allah, Iman dama talaka na ganinki?"
Murmushin ya?e iman ta ?a?alo, ta dur?usa a kan gwiwoyinta tana gaida Ummma.
Cikin mutuntawa Ummma ta amaa mata, tare da tambayarta ya Ammi.
"Hajiya Iman, manya manyan 'ya'ya a gidan Galadima, ya kike ya school?" cewar wata matashiya da ke zaune a gefen Ummma.
Ko ba a gaya mata ba, ta san da biyu budurwar ta yi wannan maganar, ta dake ta ce "Lafiya lau Anty Soafy, an yi salla lafiya?"
"Hmm lafiya lau, irin wannan ado haka, Ummma wannan leshin kamar irin sa Khairiyya ta saka ranar kamunta ko?" Tayi maganar tana ?arewa Iman kallo.
Umma ta ce "Eh irinsa ne"
"Wow, it worth 120k fa, lallai autar gidan Galadima, kin ri?e wuta".
Iman jin ta take tamkar a kan wuta, dan haka a gurguje ta ce "Ummma dama abincin salla ne, Ammi ta ce na kawo miki, kuma nazo mu gaisa, bari na tafi".
"Kai Iman tun da wur haka, ke dai ba kya son mutane, shikenan bari na baki barka da salla".
"A'a Umma, ai na girma da barka da salla" iman tayi maganar tana mi?ewa .
"?aniyarki, tsaya ki kar?a mana" girgiza kai iman tayi, ta fice daga ?akin da sauri.
Har ta kai tsakiyar falon, ta ji an ri?e mata jaka.
Ta waiwayo tana kallon wadda ta ri?eta.
"Duk na san kin ci kin ta da kai, Ammi tana ji dake, na san kina da ku?i baki rasa komai ba, amma yakamata ki kar?a tun da kin san baki da gado a cikin dukiyar gidan Galadima?"
Cikin rauni Iman ta ce "Anty Soafy me kuma ya kawo wannan maganar?"
Cikin ko in kula Soafy ta ce "Yau aka fara gaya miki irin wannan maganar ne, ai gara a dinga yi ana tuna miki, ko ba haka ba?" Ta fizgi jakar iman, ta saka mata ku?in, ta sa?ala mata jakar a kafa?arta ta koma ciki.
Gwiwa a sa?ule, iman ta nufi fita daga falon, tuni idanunta suka cika da hawaye, sai dai tana fitowa ya sha gabanta, ya ?ureta da idanuwansa.
?o?arin ratsewa take ta wuce, amma ya ce "Me ta ce miki ne, har ta saka ki kuka?"
Girgiza masa kai tayi alamar bakomai.
Yayi murmushin gefen baki ya ce "Anyway, kin yi kyau sosai a outfit ?in nan, ashe yayanki yana Saudiyya babu ko sallama?".
"Uncle J, am sorry sauri nake, Ammi na jirana"