Showing 135001 words to 138000 words out of 182697 words

Chapter 46 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22405

zauna da ni, Allah ya sa kar na tashi daga baccin nan, mamana tsoro nake ji kar ki bari na farka"

"Ruma nima ji nake kamar mafarkin ne, ina ta gaya musu kin dawo kina waje amma basu yadda ba, Allah Alhamdilillah" tayi maganar tana sake rungume rumaisa.

Wata nurse ta shigo da tray na magunguna ta ce "Gaskiya bayin Allah kun yi yawa a ?akin nan ku ragu zan yi mata allurai, bacci muke son tayi ?aa?walwarta ta huta" ta yi maganar tana ?arasawa gaban gadon rumaisa.

Bashir ya ce "ki bi a hankali, watanni uku ba sa tare an saceta, ki bari ta ga ahalinta"

Nurse na ?o?arin ?aga hannun ruma daga jikin mama ta yi mata allura, a zuciye rumaisa ta yi jifa da trayn "So ki ke dole na tashi daga baccin? Bana so ki ?yaleni" ruma tayi maganar kamar mai shirin tayar da aljanu.

Sai a yanzu mai sunan baba ya ?arasa, ya zauna a gefen gadon, ya ?ago rumaisa daga jikin mama, ya rungumeta a jikinsa, ya ?ago hannunta ya ri?e ya ce "Yi mata abun da ya kamata"

Ta yi lamo a jikinsa, sai kuma ta ce "Mai sunan baba".

Ya ce "Na'am"

"Yau a mafarkin nawa ba zaka sakani kama kunne ba? Kullum idan ka zo sai ka sakani kamun kunne, amma ko zaka sakani kamun kunnen, ka zauna a mafarkina, tsoro nake ji bana son duhun nan" tayi maganar tana shirin fara fizge-fizge amma ya danneta a jikinsa ana gama allurar ta cigaba da bacci.

Bayan baccin ya ?an ?auketa, mama ta share hawayenta ta ce "Aliyu, ku je gida ku zo da ruwan zafi, ayi mata wanka, kan mutane su ji su fara zuwa"

Bashir ya ce "No, kar a ta?ata tukuna sai zuwa dare, muna jiran result ?in likita tukuna, sai ayi mata wankan, sannan akwai jariri da na tsince su tare, ta ce mini ?anta ne, duk da ni ban ga alamar hakan a tare da ita ba".

Mama ta ce "Jariri kuma?"

Asiya dake gefe ta mi?a musu jaririn ta ce "Gashi, bayan tafiyarka ta sanya rigima sai da aka ?auko shi".

Mama ta kar?i jaririn tana ?are masa kallo, Bashir ya ce "Ikon Allah, ban yi zaton yaron nan zai rayu ba, amma cikin ikon Allah kun gan shi, har da sauran ?azantar haihuwa a jikinsa na gansu".

Usman ya ce "to a ina ta samu jariri?"

Aliyu ya ce "Oho, tubarkallah gashi ?ato mai kyau.

Ruma tana baccin nan, aka juyata ana wanke mata raunin da yake ?eyarta, gashin kanta har da kwarkwata, ban da tarin datti da dau?a.

Mama ta din ga yi wa Bashir godiya, rumaisa ba ta da?e ba allurar ta saketa, sai dai ta kasa yadda ba mafarki take yi ba.
Kamar kullum Bashir ya din ga lalla?ata ta gaya masa, ina ta samu jariri, amma ta ce "Na gaya maka ?ana ne".

Mama ta ce "Rumaisa, ki gaya mana ko hankalinmu zai kwanta, ina uwar ?an take" rumaisa ta yi shiru tana tunani.

"Ba kya ji ne?" Mai sunan baba yayi maganar yana kallonta.

"?an wata mata ne" ta basu amsa.

Nan ta gaya musu iya abun da ta sani, ta ?oye musu wani abun.

Bashir na gama jin bayanin ruma, ya ce asibiti za a canza mata.

Suka shiga tambayarsa dalili, amma ya ce likita ne ya bada shawarar hakan.

Daf da magariba Bashir ya isa gidansu takawa, bayan yayi ta kiran lambarsa amma ya?i ?agawa.
A harabar gidan suka yi kici?is, Bashir ya tattara nutsuwartsa ya ce "Allah ya baka yawan rai, ina ta kiran lambarka ka ?i ?agawa".
?o?arin tureshi Adam yake ya wuce, amma Bashir ya?i matsawa ya ce "Tuba nake, amma ka tsaya ka saurareni, wallahi babban uzuri ne ya sameni, na gaya maka yarinya na tsinta, ta ku?uto daga hannun 'yan bindiga"

A fusace Adam ya ce "Ka je ka yi abun da kake so mana, ai ban yi maka magana ba, ambulance sarkin taimako ka je ka yi ta yi mana, tun da ni tawa bu?atar ba bu?ata bace".

Bashir ya ce "Dan Allah Adam ka saurareni ka ji"

"Ba zan ji ba, bana son ji" yayi maganar a fusace zai wuce.

"What if yarinyar tana da ala?a da aikin da ka bani? Ka rage zafin zuciya ka dinga cin ribar rayuwa, ka zo mu je zuwanka ka ganta yana da muhimmanci, za a iya samun muhimman bayanai a tare da ita, yanzu haka Ammi na asibitin". Cak Adam ya tsaya yana kallon Bashir.

"Ka zo mu je, ina tabattar maka da cewa, yarinyar nan za ta iya zama ita ce makarin abun da muke nema, ka yi ha?uri ka yadda mu je".

"Amma meya kawo ammi cikin zancen nan".

"Dole ce, dole ce ta shigo Ammi cikin lamarin nan, kuma har zuwa yaushe zamu cigaba da wannan ?oye-?oyen? Ka zo mu je" Adam bai kuma cewa komai ba, ya bi Bashir motarsa.

Wani katafaren asibitin ku?i Bashir ya sanya aka mayar da rumaisa, sai dai ba ta iya taka ?afafuwanta, saboda raunukan da suke jiki, mama tana yi mata wanka tana kuka, ha?oranta sun yi yellow, gashi nan a cukurku?e, fatar rumaisa duk cizon ?wari, haka zalika cikin kayanta duk ?wari, Mama ta sanya almakashi ta ragewa rumaisa gashinta, saboda tana da cukurku?a??en gashi mai tsayi.

Mama ta tsorata da ta ga uban gwal ?in da yake cikin ?an kwalin da yake ?ugun rumaisa, ko da mama ta matsa mata da tambaya, sai ta hau kuka.
Abinci ma da ?yar ta ci ka?an, ta kwanta ta cigaba da aikin bacci.

A hankali take motsawa, tana bu?e idonta da ka?an-ka?an, tana tsoron kar ta bu?e idonta ta ganta a duhun dajin nan, ko wurin su sule.
Ganinta ta yi a wani wuri na daban, dan har aka canza mata Asibiti mama tayi mata wanka, ba a hayyacinta take ba, ko ina farin tiles da farin ?wai, ga sanyin ac da yake ratsata, a hankali ta fara sha?ar wani irin dadda?an ?amshin turare, ta din ga kallon mutanen ?akin ?aya bayan ?aya, wata babbar mace ta gani a zaune tayi mata kama da wanda ta sani.
A hankali ta ga su Aliyu da Usman a wurin, ga wasu dogarai masu kaya kalar na bayi da mama ta ce mata.

Gabanta ne ya fa?i da ta yi tozali da Adam a kan gwiwoyinsa, rungume da jariri hawaye na zuba daga idonsa.

Cikin ihu ta ce "Wayyo Allah mama, kina ganinsa ko ni ka?ai nake ganinsa?"

Mama ta ce "Waye?"

"Wannan mugun mutumin" tayi maganar tana nuna Adam.

A rikice mama ta ce "Me yayi miki?"

Bashir ya ce "Rumaisa, ki kwantar da hankalinki, ba mugu bane ba, kwatancen da matar nan ta baki, shi na yi tracking, mutanen da ta gaya miki gidan sirikanta ne kuma iyayenta, Adam abokina kuma shi ne baban jaririnki, shi ne mijinta".

(Dan?ari!??)
Ayshercool.

?500 ne via 0009450228
Aishs Adam Jaiz bank
Sai a turo shaidar biya ta 08081012143


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

?? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*



*?ANWAR ?500 ne, via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143*



Kamar sokuwa haka ruma ta bi bashir da kallo, daga bisani ta ja wani uban tsaki ta ce "Dan Allah ka daina raina mini hankali, wai komai nawa sai wannan mutumin ya shigo ciki, to wallahi ba shi bane ba, ?ana ne ba shi ne babansa ba". Ko cikin gushewar hankali takawa ba zai manta wannan muryar me shegen kara?i da tsiwar tsiya ba. Shi kansa mamaki yake yadda aka yi rumaisa take shigowa cikin rayuwarsa a bazata. Ya ?aga jajayen idanunsa ya na ?are mata kallo.

Usman ya ce "Rumaisa, kin ga ki nutsu kin ji, shi a ina ki ka san shi?"

Ta kalli Bashir, sannan ta ?an kalli takawa, ta girgiza kai ta ce "Ni ban san shi ba, ku kar?o ?ana ku bani, ba shine babansa ba, ni ba shi ta ce mini ba".

Bashir shima ya ?arasa gaban rumaisa ya ce "Rumaisa, ba cewa ki ka yi tace miki ita 'yar turakin kano ba ce? Ta ce miki giwar Galadima ce sirikarta ba, to ai ga giwar Galadima nan, Adam kuma ?anta ne" ruma ta yi shiru ta tafi tunanin abun da ya faru ita da Aisha.

Lokacin da ta kammala bawa Aisha labarin abun da ya faru a tsakaninta da Adam, ta din ga yi mata dariya ta ce "Kamar na san mutumin nan da kike bani labari".

Rumaisa ta ce "Ta?, aikuwa idan ?an uwanku ne sai dai ki yi ha?uri dan ba shi da mutunci, bama ki san shi ba anty aisha".

Aisha ta kalli ruma ta ce "?an gidan marigayi Galadiman Kano ki ka ce ko?"

"Oho masa, amma dai kamsr haka aka ce"

"Amma da ?arfin hali kike ruma, dan ?arfin hali babban mutum ki yi masa wannan rashin kunyar?"

Ruma ta ta?e baki ta ce "Ai ni Allah ka?ai nake tsoro"

Aisha ta yi murmushi ta ce "To ki yafe masa mana my baby rumaisa" ruma ta daki ?asa ta ce "Ai ko shine zai zo gabana ya ce na yafe masa ba zan yafe masa ba, kin ga rashin muntucin da yayi mini, har da ce mini 'yar talakawa, yanzu da ciki ya fito mini da ya ta?a mini nono fa, ina zan saka kaina?"

Tayi dariya ta ce "Ai bai fito ?in ba, kuma gaskiya kar ki yi masa sharri dan kin tsane shi, you are still a baby, ina wani nono a nan banda sharrinki ruma? Ko kwatan nawa ba su kai ba fa, ko ganinsu ba ayi"

Rumaisa ta ce "Wallahi sun fara fitowa, mama ta ce duk wanda ya ta?a ciki zai fito mini, kuma korata za su yi daga gidan su, yanzu da ya sa an koreni fa, ni fa bana son ma su fito, idan ba haka ba mama zata hanani yawo ba riga, yanzu ma hanani take yi"

Aisha ta yi dariya ta ce. "gaskiya ki daina zaginsa tun da dai ba a korekin ba, kin yi masa sharri, ina wani abun ta?awa a nan" tayi maganar tana sake tuntsirewa ruma da dariya.

Ruma ta ce "Wallahi ya ta?a, kuma idan Allah ya sa na bar nan idona idonsa zai gane bashi da wayo, ana i gobe zan zo katsina, yayi mini wanka da kwata a tsakiyar layi, wai har da cewa na yi masa sharri da nace ya ta?ani, wai zuwa yayi ya duba ya ga ko akwai wani abu a ?irjina ki ji ?an iska fa"

Aisha ta dafe ?irji ta ce "Wayyo zuciyata, haba baby rumaisa sunan mijina adam, kar ki sa kishina ya tashi. Amma ni nawa Adam ?in shima yana da zafin zuciya, baya son raini ga miskilanci, amma idan ki ka fahimce shi, mutumin kirki ne, mai son kulawaga iya soyayya, sai dai...." ta ?an yi shiru sai kuma ta ce "Ruma zaki auri Adam?"

Ruma ta waro ido ta ce "wane Adam ?in? Ni da ban yi tsawo na girma ba za ayi mini aure?".

"Adam da kuke fa?a, ki yafe masa ko dan albarkacin yana da sunan mijina"

Ruma ta tur?una fuska ta ce "Ai wallahi ko yayanki ne ba zan yafe masa ba, da in auri Wannan gara na mutu ba aure, kuma ni miji kyakkyawa nake so, kuma mai ku?i"

"In dai ku?i ne akwai su ruma, kuma ai kyakykyawa ne"

Rumaisa ta dubeta ta ce "Ba fa mijinki ba, wannan da muke fa?a nake gaya miki, mai suffar mugwaye da wata banzar motarsa in sha Allah sai an sace motar ma".

"In an saceta ma zai sai wata, kuma ya sai miki kema, banda fa?an rashin gaskiya ke fa ki ka fara zaginsa a social media, amma tsabar rigimarki kina ta zaginsa, kin ci sa'a da bai ?aureki ba, ko ya sa a zaneki ba".

"Oho ni dai ban yafe ba"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "I love your confidence my dear, you can face the challenges. Jikina na bani wani abu game da ke, zaki iya ruma" tayi maganar tana jan kunatun rumaisa ta ce "Kamar haka mijina yake wasa da kumatuna".

"Anty Aisha, yake ta?aki? Ba a wasa da maza fa" ba ta bawa ruma amsa ba, sai dariya da take yi mata, tana fatan Allah ya tabbatar da abun da take ji game da ruma.

Ranar da zata rasu bayan ta haihu, ta ri?e hannun rumaisa ta ce "Baby rumaisa, idan Allah ya sa kin ku?uta, ni 'yar gidan turakin kano ce, amma kar a nemi mahaifina kai tsaye a nemi sirikata, idan ba zaki iya ri?e jaririn nan ba, ki dan?a mata shi, Hajiya Binta giwar Galadima, uwar gidan galadiman kano, sirikata ce ita zaki dan?awa jaririn nan, ?an ta shine mijina" a lokacin gaba ?aya ruma ta manta da wani adam balle ta kawo shi a lissafi da aisha ta yi zancen galadima.

Ko da ruma ta zo nan a tunaninta sai ta tambayi kanta 'Kenan da gaske shi ne mijinta?' a zahiri kuwa ta fashe da kuka ta ce "Wallahi ba shi ne babansa ba, ni ba shi ta ce mini ba" a bata iya tafiya ta fara ?o?arin dirowa daga kan gadon tana mi?a hannu ta ce "Ni ku bani jaririna, ba ?ansa bane ba, ni ba ta ce mini in bawa kowa ba, ku bani ?ana" mama tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.

Bashir ya mi?awa Adam hannu ya ce "Ka ga Adam, kawo yaron nan, gaba ?aya a ru?e take, kamar ba ta hayyacinta ne ma, kawo a bata shi kan muga yadda hali zai yi".

"Bashir ka haukace ne? Taya ka ke cewa in baka ?ana ka bawa wani?".

"Wallahi ba ?ansa bane ba, ku bani ?ana" ruma tayi maganar tana kuka.

Bashir ya kar?e yaron, ya mi?awa rumaisa, ta rungumeshi tana fashewa da kuka ta ce "Cewa ta yi idan ba zan iya ri?e shi ba, in bawa giwar Galadima ni ban santa ba ma, ban san a in da take ba, amma ni dai zan iya ri?e yarona, ai cewa ta yi ta bar mini shi har abada nice mamansa". Gaba daya ?akin aka zubawa sarautar Allah ido.

Ammi da tun ?azu take zaune kamar an shukata, ta kasa magana sai tasbihi kawai da take yi, ta tashi sannu a hankali, ta je kusa da rumaisa suka matsa mata ta zauna.
Ta dafa kafa?ar rumaisa idonta fal hawaye ta ce "'ya ta, nice giwar Galadiman kano mai rasuwa, Adam kuma ?ana ne, shine mahaifin wannan jaririn, kuma mijin Aisha".

Ruma ta girgiza kai ta ce "A'a wallahi ba shi bane ba, ni fa ba zan bawa kowa ba, ni ta ce ta barwa shi".

Ammi ta ce "To shikenan, na ji babu mai rabaki da yaronki, Ubangiji Allah ya baku lafiya gaba ?aya, yanzu ki bayar da shi a mayar da shi sashen kula da yara".

Rumaisa ta girgiza kai ta ce "Ba zan bayar da shi ba, haka kurum ya bishi ya sace shi, da in bashi ?ana gara na koma wurin 'yan garkuwa da mutanen".

Huzaifa ya ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login