Showing 168001 words to 171000 words out of 182697 words

Chapter 57 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22423

bani ?ana ko ba ka so, ko kuma ka ga matakin da zan ?auka".

Adam ya ?are mata kallo ya ce "Idan aka baki shi, gaya mini da me zaki shayar da shi? Kalleki fa".

"To ai dai na ga ba shayar da shi ake yi ba, madara ake bashi, kuma idan na girma na zama babba sosai zan dinga shayar da shi".

Ya girgiza kai ya ce "An daina ba shi madara yanzu ai, ni nake shayar da shi, tunda na san nesa ba kusa ba, na fiki abun bashi, tashi ki wuce mu tafi".

AYSHERCOOL.
08081012143


paid book ne, ?500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu bu?atar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*


Shiru ta yi ta bishi da ido, tana nazarin maganarsa, ta yaya namiji zai shayar da jariri ita tun da take ba ta ta?a gani ba, ko dai raina mini hankali yake?' ta tambayi kanta.

"Ki tashi mu tafi ina magana kina kallona" ta ji maganar sa cikin tsawa, da sauri ta tashi ta yi gaba ta wuce shi, ba tare da ta waiwayo in da yake ba ta mi?a ta tafi hanyar harabar gidan.

Usman na ganinta ya ce "Ke kuma ina ki ka tsaya, sai da ki ka saka a koma nemanki, wato dai ba ki ji abun da mama ta gaya miki ba ko?" Ta girgiza kai alamar a'a.

"Ba ki ji ba mana, idan muka koma gida sai na gaya mata" ita dai ta yi shiru ba ta ce uffan ba.

Adam ya ?araso ya nufo motar, rumaiss kallonsa take ta ga ?irjinsa a cike yake yadda zai shayar da yaro, amma ta kasa gane komai, kasancewar dogayen kayane a jikinsa.

Adam ya shiga ya kunna motar, usman ya bu?ewa ruma baya ya ce ta shiga, amma ya ga ta tsaya cak, ta zubawa gate ?in gidan ido.

"Wuce mu je" usman yayi maganar yana tunku?ata cikin motar.

Cikin motar wani irin sanyi da ?amshin turaren Adam suka cika mata hanci, sai dai ta din ga jikinta wani iri, kamar wani mara da?i na tunkaro in da suke.

Adam ya kunna motar, ya nufi gate, sai ga motar Jabir ta shigo, jabir ya tsaya dai-dai in da motar adam take ya ce "Yaa ina zaka kuma? Daga gidanka nake".

"Eh wani muhimmin abu ne ya taso mini"

Samha ta ce "Barka da rana yaya" ?aga mata kai kawai yayi ba tare da ya amsa ba, ya ce wa jabir "Ka jirani da daddare, zan nemeka in sha Allah"

"Ok, dama na je na kuma yi wa turaki gaisuwa, Samha ta ce idan nan zan taho zata zo ta sake yi maka gaisuwa".

"Na gode, zan je na dawo yanzu in sha Allah".

Tun da samha ta sanya idonta a na rumaisa, ta ji wata mummunar fa?uwar gaba da fargaba, kamar ta san idon rumaisa amma ta manta a ina ta santa, gashi ruman ta rufe fuskarta da facemask, ita kanta ruma ba ta san yadda aka yi ta tsare samha da ido ba, ko ?iftawa ba ta yi, kamar wani abu mai muhimmanci take son ganowa a tattare da Samhan, amma ta kasa gano ko me take son ganowar. A haka Adam ya ja motar suka bar gidan.

Tun da suka fara tafiya, rumaisa ba ta iya cewa komai ba, ras ba ta manta samha ba, sun ta?a ha?uwa, kenan 'yar uwar su takawa ce ko kuwa oho?.

Har suka ?arasa gidan turaki, kasancewa tafiyar ba wata ta azo a gani bace, ruma zancen zuci kawai take yi.

Ko da aka bu?e gate ?in gidan suka shiga, kamar wadda ta farka daga bacci ruma ta ce "Kai, ai na san wannan gidan".

Usman ya ce "A ina?"

"Ni da hauwwaliya muka ta?a zuwa gidan, wai akwai ?awarta ana bikin ?anin babarsu, wata fiddausi sunanta ko jannatu na manta, har na ga waccan da muka gani a motar ?azu mai bluen kaya, tana ta hantarar mutane ba ta da mutunci, har muka yi fa?a da ita".

Adam bai ko nuna ya san mai rumaisa take cewa ba, usman ya juyo, yayi mata inkiyar ta yi shiru, amma ina kamar ya tunzurata "Wasu mutanen dai yan uwansu ka?an ne masu kirki, duk masifaffu ne, ta din ga yi wa mutane tsawa, na fito kawai muka yi karo da ita, wai ke ba kya gani ne, nace eh bana gani, yo ni za ta yi wa gatse, bana son in ga ana wula?anta mutane"

"Ke ya isa rufewa mutane baki" usman ya yi mata maganar cikin tsawa, jan facemask ?in ta ta yi, ta bu?e motar ta fita, kasancewar tuni adam yayi parking.

Hadimai na ta risunawa, suna gaishe shi, yana ?aga musu hannu maimakonsa ya amsa, hakan ya ?ara sanya rumaisa jin haushin takawa, tare da ganin yana wula?anta mutane.

Adam ya yi musu jagora, har cikin babban falon gidan, nan ma rumaisa ta sha kallo, gidan ya so yayi shige da na su Adam, sai dai na su ya fi kyau sosai a kan nan.

Adam ya ce wa usman "Ina zuwa, bari na shiga na sanar masa da zuwanmu".

Usman ya ce "To shikenan"

Adam na barin wurin, ya matsa kusa da rumaisa ya ri?e kunnneta ya yi ?asa da murya ya ce "Dan ubanki me aka gaya miki a gida, wato ke ba a isa a fa?a miki ki ji ba ko? Ki ke ta zuba kina surutu, kina cewa wata ba ta da mutunci ke mutuncin ne da ke?"

Ri?e kunnen ta yi ta fa ?o?arin fara kuka, wata mata ta fito ta ce musu "Bisimillah, an yi muku iznin shiga"

Suka tashi suka bi bayan matar. Subhanallah wani irin ?aton falo ne, ko ina ya sha kilisai da lallausan carfet, sai ?amshi yake yi.
Daga nesa ta hango dattijon jawurr da shi a zaune, sanye cikin kayansa masu sau?in nauyi, sai rawani sai dai ya sauke takunkumin fuskarsa.

Maimakon rumaisa ta nutsu, sai ta yi ta kalle-kalle tana kallon abubuwan gidan sarauta da ba ta ta?a gani ba.

Usman ya ce wa dattijon "Barka da wannan lokaci, fatan mun same ku lafiya?".

Turaki ya jinjina kai ya ce "Alhamdilillah".

Usman ya sake du?awa ya ce "Ya ?arin ha?uri na wannan rashi, Ubangiji Allah ya ji?anta da rahama, ya bada ha?urin jure rashin"

Turaki ya amsa da "Amin 'yan samari, madalla Allah ya yi albarka"

Rumaisa ya kalla da take ta kalle-kalle, usman ya zungureta tayi maza ta kalli turaki ta ce "Ina wuni?" Yayi ?uri yana kallonta, amma bai amsa ba.

Kallonsa tayi, ta kalli adam sannan ta kalli usman, ta kuma cewa ina wuni.

Adam ya risuna ya ce "Tuba take, ba ta san kan gaisuwar gidan sarauta ba, kamar yadda na yi maka bayani a baya, wannan ita ce wadda ta zo da jaririn wurin marigayiya". Adam ya ?arasa maganar yana yi mata alamar ta sauke facemask ?in ta.

Harar Adam ta yi, ta sake jan facemask ?in ta, ta rufe fuskarta.

Turaki ya yi mata ?uri da ido, tsananin kwarjininsa ya sanyata sunkuyar da kai, ta ji kamar jikinta zai hau rawa, saboda kwarjininsa, sun fi mintuna biyar bai ce komai ba.

Adam ya kuma yi mata nuni da ta sauke facemask ?in ta, amma ta?i sai da usman ya kalleta, sannan ta cire.

Turaki ya cigaba da kallonta sannan ya ce "Iko, sai Allah yanzu wannan ?aramar yarinyar ce ta ceto yaron wurin fulani"

"Eh Allah ya baka nasara, ita ta zo da shi"

Ruma a ranta ta ce "Ta?, wanna wace irin wahala ce, da ban cire facemask ?in ba, kenan haka zamu yi ta zama ba zai yi magana ba?'.

Turaki ya ce "Bamu labari, ya aka yi aka ha?u da fulani, har aka zo mana da jaririnta?"

Rumaisa ta ?an waiwaya ta ce "Wace fulani kuma?"

"Aisha" Adam ya bata amsa.

Sai ta yi turus, ta sunkuyar da kanta ?asa.

Usman ya ce "Ki yi magana mana"

Ta yi shiru ta shiga wasa da ?asan rigarta.

Turaki ya ?ura mata ido ya ce "Ke muke sauraro yarinyar kirki" ?aga idonta ta yi tana kallon adam, da ya murtuke fuska saboda ?uluwa da ya fara yi, da iskancin da rumaisa ke yi.

"Ko su bamu wuri ne?" Turaki yayi maganar yana nuna su adam.

Ta jinjina masa kai alamar eh, ya ce "To babu laifi, takawa a bamu wuri, kar a damu a bamu wuri mu tattauna".

Takawa bai ta?a zaton iskancin rumaisa ya kai haka ba, ?in yarda da shi ta yi masa bayanin abun da ya faru, ya sanya yayi zaton a gaban turaki za ta yi bayani, amma mirsisi ta?i magana sai sai ya fita.
Ganin yadda adam ya harzu?a, ya sanya turaki yi masa alama da ya kwantar da hankalinsa.
Sai dai ba iya adam ?in ne ya ?ulu ba, har usman ya ?ule da abun da rumaisan ta yi.

Haka suka tashi suka bar falon.

Turaki ya mayar da kallonsa ga rumaisa ya ce "Matso kusa da ni nan ki yi mini bayani"

Rumaisa ta ?an ?ara matsawa daf da shi, ta hango hoton aisha a bayansa, ta ?urawa hoton ido, da har sai da turaki ya waiwaya ya kalli hoton.

Ya ?auko hoton a hannunsa, ya shafa shi ya ce "Kin ganta nan, a cikin 'ya'ya na kusan goma sha rayayyu da wanda suka rasu, babu wadda nake jin da?inta nake zartar da hukunci komai ?acinsa ta kar?a sai Aisha. Na tafka babban rashin da ba zan iya maye gurbinsa ba, Allahn da ya bani ya fi ni son ta, ban so ta mutu a wula?ance haka ba, sai dai ba zan zargi sirikina ba, ?ana ne shima, kuma ba zai cutara da aisha ba"

Rumaisa da hawaye ya fara zubo mata ta ce "Tabbas anty aisha tana da kirki, kowa cewa yake yi bana jin magana, amma ita ta fara cewa rashin ji na yana burgeta. A makaranta bana gan karatu, amma ta ce mini mai kaifin basira ce ni, ta yi ta kula da ni a hannun 'yan bindiga kan ta rasu, amma mijinta ne ba shi da kirki ko ka?an, shiyasa na?i magana a gabansa".

Turaki ya yi murmushi ya ce "Tabbas takawa yana da zafin rai, amma mutumin kirki ne sosai".

"Na san a ?ule yake da ni, yanzu ba dan kai ba tsaf sai ya zaneni a wurin nan, ita rayuwa idan mutum yana son ya ci ribar abu ba ha?uri ake a bishi a sannu ba? Idan haka zai din ga yi komai ya tunkara sai ya fa?i. Kuma dai naga ?an sanda ne shi, mai ya hana ya kai mana agaji lokacin muna hannun 'yan bindigar, da bakinsu fa suka ce jami'an tsaro ne suke basu gudunmawa, to yanzu kuma dan Allah me zai yi bayan mai faruwa ta faru".

Zuba mata ido kawai turaki yayi, yadda take zaro magana, tana arranging ?in ta, tamakar tana karantowa, kuma ba zaka ta?a cewa yarinya ce mai kamar shekarunta take fa?a ba.

Ya gyara zamansa ya ce "Haka ne, kema kin yi magana mai kyau, amma yanzu dai ina jin ki".

"Baba"

Ya ce "Na'am yarinyar kirki"

"Amanatun amana, zan gaya maka komai, gani ake ni Yarinya ce amma ina da wayona, ta ?arfin tsiya fa ya ?wace mini ?a, ko tausayina ba ya ji alhalin anty aisha ta ce ta bar mini shi halak malak. Zan gaya maka komai, amma shi ba zan gaya masa ba, kuma wallahi na san abubuwan da shi bai sani ba".

Duk girman turaki, ruma ta iya kallonsa ta ce masa amanatun amana, tare da yi masa kashedin, kar ya gaya wa kowa abun da za ta gaya masa.

?warin gwiwar ta, da rashin tsoronta a ?ananun shekarunta ne ya fi bashi mamaki, kuma tsara zancenta da kaifin basirarta ya burge shi.

Ya ce "Kar ki damu, babu wanda zai ji wannan maganar, daga ni sai ke sai Allah".

Nan rumaisa ta gyara zama ta fara yi masa bayanin abubuwan da suka faru, duk a hirarta ta ya fuskanci ba komai ta gaya masa ba, amma a hakan ta yi ?o?arin yi masa duk wasu bayanai da yakamata ya sani, sai dai kan ta kammala, hawaye ya wanke mata fuska, sai gogewa take da hijjabinta.
Shi kansa turaki kasa jurewa yayi, cikin dabara ya goge hawayen da yake shirin zubo masa, yana jin labarin wai-wai a kafafen watsa labarai, bai ta?a zaton masifa da tashin hankalin ya kai haka ba, kuma ta bakin rumaisa ne idan aka fara ha?awa da 'ya'yan masu fa?a a ji ana sacewa wata?ila a mayar da hankali a kan maganin abun, kuma abun kunya ne ga jami'an tsaro, ace an sace matar jami'in tsaro kuma an kasa ceto ta har ta rasa ranta.
Uwa uba azabar da rumaisa ta sha kan ta fito da jaririn, shi kansa ya isa abun tausayi duba da ?ananan shekarunta, gashi sai nanatawa take ita fa aisha ta bar mata ?a, amma adam ya ?wace mata.

Ya duba gefen sa, ya ?auko wani handkerchief mai matu?ar kyau da taushi, sai ?amshi yake yi, ya mi?awa rumaisa ya ce "kar?i nan ki goge hawayenki, kukan ya isa haka".

Kar?a ta yi, amma ta kasa gogewar, saboda kukan da ya ci ?arfinta.

Usman kuwa ba ?aramar mita yayi ba, a kan abun da rumaisa ta yi, tun da suka fito yake mita.
"Ban ta?a ganin yarinya mai azababben taurin kai, na tashin hankali kamar rumaisa ba, gaba ?aya yarinya kamar wata majanuniya, ita duk wata hanya ta masalaha ba ta santa ba, idan ta akasin masalahar ma aka biyo mata ta fi misbehaving, ba a gane gabanta da bayanta kamar ?an wake".
Adam kam azabar takaici, bai bari ya iya tankawa ba, gani yake gaba ?aya yarinyar ta gama raina masa hankali.

A nutse turaki ya din ga rarrashin rumaisa, yana yi mata nasiha, har sai da ya sanya ta ?an yi murmushi ta ce "Baba ka iya magana a nutse wallahi, ni yadda kake magana ma da?i yake yi mini"

Abun da ta fa?a ?in sai da shi ma ya sanya shi murmushi, ta kai handkerchief ?in da ya bata fuskarta,
Ta lumshe idonta ta ce "Wayyo ?amshi, baba ban ta?a jin turare mai da?in wannan ba, kamar na suma dan da?i".

Jan rawaninsa yayi ya rufe fuskarsa, dan dariya rumaisa take neman ta saka shi.

Hadimai ne suka yi sallama, suka shigo masa da kwanukan abinci a kuloli da kuma akushi, aka zo aka jere su a gabansa.

Rumaisa ta dinga kallon fulasai na alfarma.

Turaki ya ce "Ga abinci nan, bu?e a ciki ki za?i wanda ki ke so ki ci".

"A'a na ?oshi, mama ta hanani cin abinci a waje".

"To ai nan gidanku ne, ki ci duk abun da ki ke so".

Ta nuna masa akushi ta ce "Wannan menene?".

Ya ?auko akushin ya ajiye a gabanta ya ce "Sunansa akushi".

"Akushi da rufi, sai sarki, kenan kai ma sarki ne?"

Ya girgiza mata kai ya ce "A'a, ni ba sarki bane ba".

"To dama ba duk masu rawani ba sunansu sarki ba"

Turaki ya murmusa ya ce "A'a ba kowane mai rawani ne sarki ba, kowa akwai sunan mu?aminsa"

Ruma ta din ga kallon akushin nan, ta saka hannu ta bu?e, ta ga dubulan fal a ciki" tayi iya ?o?arinta wurin tuna sunan sa amma ta kasa ta ce "Mmm ya ma, abun da ake kaiwa idan an yi aure mai sugan nan sunan shi kenan".

Ya kuma mi?o mata wani akushin, ya ce "Gashi nan, duk duba ki ci wanda ki ke so".

Ta bubbu?e kulolin nan, wata irin miya ta alfarma, ta sha naman kaza yanka manya manya. Ta ce "Mama ta yi mini kashedi a kan banda rashin ji, kuma idan na yi wani rashin ji, yaya usman ya gaya mata zaneni za su yi".

Turaki da bai ji ya gaji da surutun rumaisa ba, kuma bai jin zai gajin ya ce "Ki ci ba zan gaya masa ba, ba zata sani ba".

"Hmm ba ka san halin mama ba, yaya usman sai ya gane, amma dai bari na ci wannan".

Ta saka hannu ta ?au dubulan, ta fara ci, dama rumaisa gata mayyar suga, tana ci tana lashe baki.

Kallon rumaisa kawai yake yana murmushi, yarinya ce ?arama, ita a yanzu babu abun da yake damunta, sai dai ta yi ciye-ciyenta ta fa?i abun da take ji a ?wa?walwarta shi ne dai-dai, sai dai yanayin yarinyar ya nuna ba za ta yi ?arya ko ha'inci ba, kuma tana da ?an karen wayo.

Hajiya Sauda ce ta shigo, sai dai ta yi turus, ganin yarinya zaune a gaban turaki tana cin abinci a kwanonsa, duk da ta bawa ?ofa baya, ba ta iya sanin kowacece ba.

"Mai girma turaki wannan kuma wacece? Meyasa take cin abinci a kwaonka, kwanon da ko 'ya'yan cikinka ba su da wannan damar".

?an turus rumaisa ta yi, amma ba ta waiwayo ba, ta kuma mi?a hannu, ta ?auko alkaki, tana taunawa tana jin za?in sugan har cikin kunnuwanta.

Turaki ya ?aga kai ya kalli mama ya ce "Ba?uwata ce?".

"Ba?uwarka kuma kamar yaya kenan?"

Ya kalli rumaisa ya ce "Yarinyar kirki, je ki ki kirawo mini takawa"

Rumaisa ta mi?e ta ce "To baba".
Sai a lokacin ta juyo suka yi ido hu?u da mama.

Rumaisa ta wani lumshe ido, ta ce "Ina wuni". Kallon banza ta yi wa rumaisa, ta ji gaba ?aya yarinyar ba ta yi mata ba, idonta kawai zaka kalla ka gane tattacciyar mara kunya ce.
Rashin amsawar ta ta bai ?a?a ruma da ?asa ba ta fita falon.

Usman na ganinta ya harareta, sai dai bai tsinke da lamarin rumaisa ba sai da ya ga tana lashe hannu tare da gutsurar wani abu a hannunta.

"Kar dai yarinyar nan ciye-ciye ta je ta zauna ta na yi? Ya tambayi kansa.

"Wai ka zo in ji baba mai rawani" ta yi maganar tana kallon adam ba tare da ta kama sunansa ba.

Bai ko kalli in da take ba, ya cigaba da danna wayarsa.

"Magana nake maka, ana kiranka"

Still bai amsa mata.

"Takalmawa ake ce maka ko me?, sunanka dai Adamu ba wani Adam ba to ka zo in ji baba mai farin rawani"

Wata irin tsawa aka bugawa rumaisa, wadda sai da ta tsorata, ta kusa fa?uwa!

AYSHERCOOL

paid book ne, ?500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu bu?atar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*


A razane ta waiwaya tana kallon in da aka yi mata tsawar, wasu dogarai ne su biyu suka shigo suna baza riga, shigowar ta su yayi dai-dai da lokacin da rumaisa ke gatsali da sunan takawa.

"Hattara dai yarinya, hattara 'yar talakawa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login