Showing 138001 words to 141000 words out of 182697 words

Chapter 47 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22392

"To fa ana wata ga wata".

Ammi ta ce "To shikenan, rungume shi da kyau, kin ga bacci zai yi kema ki kwanta ki huta" a'a ba zan rufe idona in je ya gudu da shi ba.

Mi?ewa Adam yayi jikinsa yana rawa, amma Ammi tayi masa wani irin kallo, tayi masa nuni da ya fita, yayi gaba ya tsaya ya waiwaya yana kallon rumaisa, da jaririnsa da yanzu ya shiga tunanin ina uwarsa? A wane hali kuma take ciki?".

Suna tafe a hanya babu wanda ya iya cewa komai, sai Bashir da yake yi wa Adam nasiha "Adam dole sai mun bi yarinyar nan a hankali har yanzu a rikice take, kuma a cikin firgici ba ?aramar azaba ta sha kan ta fito da yaron nan ba, kaga Yarinya ce ?arama ikon Allah ne ya fito da su, dan ita ma ba gama sanin ciwon kanta tayi ba, a sannu zamu bita mu ji a ina ita Aishar take, sai mu zo mu yi shiri".

Daga Ammi har takawa, babu wanda ya ce wani abu, kowa da abun da yake sa?awa a zuciyarsa, adam bai ta?a tunanin abubuwa su cukurku?e masa haka ba.

Suna zuwa gida ammi ta wuce part ?inta, adam ma bai jira bashir ba, ya rufa mata baya.
A falo nusaiba ta tare ta tana tambayarta, "Ammi wai ina ki ka tafi haka, mun dawo daga islamiyya kawai muka tarar ba kya nan, kalli dare har ya fara yi fa" sai dai fuskar ammin ta nuna mata ba lafiya ba. Kan ta yi magana ta ga adam ya shigo ya bi bayan anmi, hakan ya sanya ta sha jinin jikinta.

A ?aki ya tarar da ammi, ta ajiye carbin hannunta da mayafinta, hawaye tuni ya wanke mata fuska.

"Ammi dan Allah ki tsaya ki saurareni, kar ki yi mini haka".

Ta kalli Adam ta ce "In saurareke ka gaya mini me adam, yanzu a duniya akwai abun da zaka iya ?oye mini? Ta ina zamu kalli duniya mu fara bayanin abun da ya faru? Ta yaya duniya za ta yadda da cewar jaririn nan ?anka ne? Da yaya zaka yi wa turaki bayanin abun da ya samu 'yar sa, shikenan mun zama masu son kai kenan, idan maganar nan ta ya?u ina zan saka kaina, ina ta ?o?arin toshe waccan kafar wannan ta ?ullo, adam kana me garin yaya haka ta faru ka ?oye mini, ?an da ba a san da cikinsa ba kawai mu ce ga ?a meye shaidarmu ba ?arya muke yi ba, ina ita Aishan?"

Adam da ya gama rikicewa ya ce "Dan Allah ammi ki fahimce ni, zan yi miki bayani bani da laifi, ba domin na ?oye miki na yi duk abun da na yi ba"

Ammi ta katse shi ta hanyar cewa "To domin ka faranta mini ne? A tunaninka zan yi murna da hakan ne?".

Ya girgiza kai tare da goge hawaye ya ce "A duniya bani da makusancin da ya fiki, daga ni har aisha, kin san komai Ammi, kamar yadda muke ta neman magani tsawon shekaru hu?u, aka dace cikin jikinta ya zauna, bayan ?ari da take ta yi babu ?a??autawa a dalilina, cikin nan babu wanda ya san da shi, bayan ke sai mu, wanda hakan shawarar ki ce, har zuwa lokacin da kika bayar da shawarar ta je Saudiyya wurin ?an uwanki kawu mahadi, ta zauna ta raini cikin a can, idan ya isa haihuwa ta dawo Nigeria, duk dan kaucewa hatsarin da ka iya faruwa da cikin, muka yi nesa da juna ni da ita.
Bayan na kai ta ta yi watanni hu?u, na sake komawa Saudiyya umara, na dubata, na dawo babu da?ewa ta ce mini ita ta gaji da zaman Saudiyya so take ta dawo gida. Ta ce mini wannan kakar ta ta, mari?iyar mamanta babu lafiya, dan haka ita so take ta dawo ta je ta ganta, kar ta rasu basu gana ba. Gudun ?acin ranki, ya sanya ta dawo babu wanda ya sani, sai dai a lokacin cikin yayi girma sosai ta sanya rigima a kan lallai sai ta je duba matar, an ce ba ta gane kowa, wankin ?oda ake yi mata ma. Duk sau?in kan Aisha, haka ta kafe a kan lallai sai ta je katsina duba matar, a daidai lokacin kuma ni tafiya Abuja ta kamani, bayan tafiyata ta sanya ?aya daga yarana, masu tsaron lafiyarta ya kai ta katsina. Ta turo mini sa?o a waya tana bani ha?uri a kan ita fa ta tafi, ba zata iya jira na dawo ba, a tsorace take kar kakarta ta mutu. Bayan dawowata daga Abuja, sai samun sa?o na yi, an tsinci gawar yarona da motar, ita kuma ba a san in da take ba, tun da ga wannan lokacin nake ?o?arin gano in da take, har zuwa wannan lokaci, daga ni sai Bashir muke ta ?o?ari, dan ko su Jabir basu sani ba, na san na yi laifi ammi amma ba da gayya na yi ba.

"Adam nika ?ai zan fuskanci wannan bayanin naka, duk mutane sun san da cewa tana Saudiyya, babu wanda ya san ta zo Nigeria haka zalika babu wanda ya san tana da cikin ma, kawai sai mu ce ga ?a to ita tana ina, na gaya maka bana samunta a waya, amma ka yi ta yi mini ?arairayi, dama akwai abun da zaka iya ?oye mini Adam? Me zaka cewa Turaki?".

A raunane Adam ya ce "Ko babu wata cikakkiyar shaida,ni na san da cewa ?ana ne, babu yadda za ayi yarinyar nan ta san wasu abubuwan idan ba gaya mata tayi ba, amma ammi ni yanzu ba abun da mutane zasu ce ne ya dameni ba, samo aisha ne ya dameni, babu wata hujja da nake jira yaron nan nawa ne, ko a fuskarsa kamanni na ne, sannan da kaina zan gayawa turaki komai, duk hukuncin da zai yi mini zan ?auka".

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Zan cigaba da yi maka Addu'a, Allah ya kawo mana mafita, amma yarinyar nan ka bita a hankali dan Allah, in sha Allah yadda jaririn ya ku?uta, ita ma zata ku?uta".

Adam ya jinjina kai kawai, ya tashi ya fita daga ?akin, su Nusaiba suna falo a tsaye cirko-cirko, adam ya zo ya fice.
Cikin rige-rige suka tafi ?akin Ammi, amma suka tarar ta shiga toilet, ko da ta fito umarni ta basu, na su je su kwanta sai da safe, dan kar su bi diddigin abun da ya faru, sai dai a tsorace take da abun da ka iya faruwa idan zancen nan ya fasu.

A asibiti kuwa, Aliyu ne ya dubi rumaisa ya ce "Ke dai a rayuwarki ba a ta?a rasaki da matsala, an samo uban yaro kin ce ba shi ne ubansa ba, sai ki nuna mana waye ubansa?"

Usman ya ce "Ai ko da uban me ki ke yawo, sai an mayar musu da ?an su"

Mama ta ce "Yanzu dai a bar wannan maganar, Allah ya dawo mana da ita, daga dawowarta sai a bari ta sarara kan a hau yi mata fa?a, Ali ku je gida haka, kwa sanar da mutane an ganta"

Mai sunan Baba ya ce "Eh amma kar su sanar da Asibitin da take, kar azo a takura mata, ko ayi ta surutu saboda jaririn nan, a bari komai ya daidaita"

Mama ta ce "To hakan ma babu laifi, kar ku gayawa Abubakar a daren nan tun da ba a samu wayarsa ba, ku bari sai da safe kar ya ce zai bsro dutse yanzu"

Usman ya ce "In sha Allah"

Mai sunan Baba ya saka hannu, ya kar?i jaririn da ga hannun rumaisa, sai bin sa take da ido, kar ya fita ya bawa Adam yaron, ya ?arewa yaron kallo ya ce "Bari na bawa nurses ?in nan, su mayar da shi ?akin da ake kulawa da sh, mama gobe in Allah ya kaimu zan zo mu koma ki ga likitan ki"

Mama ta ce "Ga mara lafiya ni ina zani? Dama rashin lafiya tawa saboda ita ne"

Ya ce "Duk da hakan, yakamata ke sai da safe, ki nutsu ban da gardama da taurin kai ki yi addu'a ki kwanta ki huta"

Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ce "Dan Allah mai sunan Baba kar ka bawa kowa shi, wallahi zan iya rasuwa idan aka rabani da shi" bai ko waiwayo ba ya fice daga ?akin.

Mama ce ga rungumota tana rarrashinta ta ce 'Ba wani zai bawa ba kin ji, ki yi ha?uri ?akin da ake kula d shi zai kai shi" rumaisa ta yi lamo a jikin mama, can ta ce 'Mama"

Mama ta amsa mata da na'am.

"Ba mafarki nake ba ko, ba zan kuma farkawa na ganni a dajin ba, na ga kun da?e a wannan mafarkin nawa".

Mama ta shafa bayanta ta ce "Ba mafarki bane ba, duk muna tare da ke".

"Mama kin ga yadda ki ka rungumenin nan? Haka maman yaron nan take rungumeni tana rarrashina idan na tunaki ina kuka, sar?arta da zobuna ne a cikin ?ankwalin nan, ?an kunnen da ki ka cire a kunnena shi ma nata ne, mama ba zan manta da ita ba" rumaisa ta yi maganar cikin kuka.

"To ya isa, ita ma in sha Allah zata ku?uta cikin amincin Allah" rumaisa ta cigaba da kuka, dan ba wanda ta gayawa aisha ta rasu.

Aliyu suna zuwa unguwarsu, ya wuce gidan su Habiba, lokacin kusan ?arfe goma na dare, ya aika yaro ya ce yana sallama da Habiba.
Maimakon Habiba sai babarta ta fito tana masifa, wani watsatstsen ne ya zo neman habiba a wannan daren, yar habiban guda nawa take?

Tana ganin Aliyu ta yi sak, ta ce "Ya aka yi ne, ko laifin ta kuma yi maka, ko ?anwar ta ka ta kuma duka ka zo rama mata, duk da ance an yi garkuwa da ita"

Ya ce "Ba ?aya, wani abu zan gaya mata".

"Wani abu ne kenan?"

Aliyu ya ce "Shikenan tun da na ga hankalinki bai kwanta ba"

Sai kuma ta ce "A'a, bari na taso ta" ta koma cikin gida, mintuna uku sai ga habiba ta fito tana mutsutsuka ido.

"Habiba" ya kira sunanta, ta kalleshi ta ce "Yaya Aliyu ina wuni"

"Albishirnki" yayi maganar cikin murmushi.

Ta ?an yi saroro ta ce "Goro".

"To zaki bani goron nan, Alhamdilillah addu'a ta kar?u, rumaisa ta ku?uta yau, tana asibiti ma"

Gigicewa ta yi ta ce "Innalillahi, dan Allah da gaske, dan Allah kar ka ce da wasa kake yi, dan Allah mu je in ganta".

"No, ba a zuwa wurinta yanzu, ba ta da lafiya, amma zan zo da kaina na kaiki ki ganta"

Hawaye ta fara matsewa tana "Allah sarki ?awata, Alhamdilillah, Allah na gode maka"

Ya ce "Maza ki je ki cigaba da baccinki, Sai da safe"

"Dan Allah yaushe zaka zo ka kaini na ganta, gobe?"

"A'a zan zo dai, ki je ki cigaba da baccinki" yayi maganar yana ?aga mata hannu ya tafi.

Ta shiga gida da gudu tana murna.

Adam kuwa yana zuwa ?aki ya zauna ya fashe da kuka kamar yaron goye. Wai matarsa ce ta haihu a daji a hannun 'yan bindiga, ko a yaya ta haihu oho, ko a wani hali take sanin gaibu sai Allah.

"Why aisha, meyasa ki kasa jira na dawo ki ka tafi? Duk yadda muka tssra rayuwa bayan kin haihu, ?arshe a tsinto mini ?ana babu ke, haba aisha kin ga sakamakon rashin jin magana ko, matar da ki ke so ki je ki duba ita bata mutu ba, amma ke kin shiga wahala. Amma bakomai, Allah ya sa kina cikin ?oshin lafiya, zan fito da ke ko da zan rasa rayuwata ne!


?ANWAR ?500 ne, via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143*

Ayshercool
08081012143.


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

?? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*


*?500 ne, via 0009450228 Aisha Adam, jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*





Haka Adam yayi ta surutai, kamar zai zauce.

Mama kuwa kwana tayi tana salloli tana mi?a godiyar ta ga Ubangiji, na bayyana mata rumaisa da yayi, idan aka jima sai ta je ta le?a fuskar rumaisa, kasancewar ita da Abdallah ne a wurin ruma, Abdallah yana gefen gadon rumaisa sai kallonta yake yi, shima ganin abun yake kamar wasa wai rumaiss ta dawo.

Mama tana tsaka da salla, ruma ta farka daga bacci tana cewa zata yi fitsari, Abdallah ya ?agata cak ya kaita ban?aki, mama tana ta gyaran murya, amma ya kai ta tayi fitsarin, sannan ya mayar da ita kan gadon ya kwantar.

Ta kalleshi ta ce "Yaya Abdallah"

"Na'am rumaisa".

"Kaga haryanzu ban tashi daga baccin ba"

Yayi murmushi ya ce "Ai a gaske ki ke ba bacci bane ba".

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Ai na kasa ganewa ne, wataran sai in ganni a dajin, wataran a nan amma dan Allah mai sunan Baba bai bashi jaririna ba ko?".

"Bai bashi ba, yana can ?akin yara".

"Alhamdilillah, ina son yaron nan bana son a rabani da shi"

Abdallah ya ce "To maman boy"

"Abdallah ban zaci zan rayu ba, na sha wahala sosai, ranar da aka tafi da mu, na din ga kuka na gaji da tafiya, aka goyani a babur, aka kaini wurin".

"Amma dai basu yi miki wani abun ba ko?"

"Wallahi sun yi mini, abubuwa ma da yawa, zan baka labari da safe, wannan ciwon na ?eyata ne yake mini zafi, jikina ma duk babu da?i, kwanana uku fa ina tafiya a daji".

Gaban mama ne ya fa?i, jin rumaisa ta ce an yi mata abubuwa da yawa tana matu?ar tsoro da fargabar ace sun lalata rumaisa, gashi haryanzu likita bai fa?i sakamako bincikensa ba.

Da safe mama ta tashi rumaisa, ya yi salla, ta wanke mata baki, ta yi mata wanka, ta saka mata wata 'yar riga domin ta samu ta sha iska, nurses suka shigo suka yi wa rumaisa dressing ?in raunukan jikinta. Mama ta kalleta ta ce "Ko kina bu?atar wani abun? Ga kayan marmarin nan, wanne zan baki a ciki ki ci?".

"Ba ko ?aya, kawai ki zauna a kusa da ni in rungumeki in ji ?uminki" mama tayi murmushi ta ?arasa kusa da ruma, ta rungumeta.
Abdallah ya koma gefe ya ?an samu bacci, saboda daren bai yi bacci ba saboda farinciki.

"Rumaisa" mama ta kira sunanta, ruma ta ?aga kai ta kalli mama.

"Ina fatan babu abun da suka yi miki, lokacin da ki ke wurinsu?"

Ta mayar da kanta ta kwantar a jikin mama ta ce "Mama ni meye ma ba ayi mini ba, bana son tunowa tsoro nake ji, mama ki ?auko jaririna shi ma ayi masa wanka".

"Na ji, amma ina fatan..." Ba ta ?arasa ba, ruma ta katseta ta hanyar cewa "Mama dan Allah ki daina tanbayata a kan mutanen nan, tsoro nake ji, dan Allah ki daina tuna mini" mama ta ce "To shikenan, bari in kar?o yaron".

Mama ta je ta kar?o jaririn, har nurses suke gayawa mama a kowane lokaci zasu iya sallamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login