Showing 78001 words to 81000 words out of 182697 words

Chapter 27 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22431

a gaba zuwa gida, suna tafe yana ?are mata zagi.

Wajen ?arfe biyar takawa ya tashi daga aiki, a gaggauce ya nufo gida, dan yau bai samu zuwa gidan ba sai yanzu.
A gate jami'an tsaro suka sanar sa shi zuwan wata yarinya, da take son ganinsa amma suka hanata shiga gidan, suka sanar masa da ta ba wa sabuwa takarda ta ajiye masa.

Bai kawo komai a ransa ba ya shiga gidan, yana tunanin wacce yarinyar ce haka?.

Yana yin parking ya wuce sashin Mummy, ko da ya shiga falon, Fauziyya ya tarar, jiki na rawa ta yi masa sannu da zuwa.

Bai amsa ba ya ce "Kira mini Baba sabuwa" ta mi?e tana tunanin me yasa yake neman Baba sabuwa a yammacin nan?.

Baba sabuwa ta risuna tana gaishe shi, ya mi?a mata hannu ya ce "Bani sa?ona" babu musu ta fito da takarda ta mi?a masa. Ya juya ya fice.

Fauziyya ta ce "Sabuwa, takardar mecece?"

"Wallahi wata yarinya ce ta tsareni a ?ofa, ta ce a bashi ban san yarinyar ba ma"

"To meye a ciki?"

"Ai kin san ba iya karatu na yi ba"

"Kuma da baki iya karatun ba, mai ya hana ki kawo mini, tashi dalla usless" Sabuwa ta tashi cike da haushin tsawar da Fauziyya ta yi mata, duk da ba yau ta fara ba.

Bai tsaya duba takardar ba, ya jefata a cikin jakarsa ya tafi wurin Ammi.

Gaba daya ya manta da takarda, sai washegari da daddare yana neman wasu takardu, takardar ta fa?o.
Ya bu?e takardar wasu 'yan ?ananan rubutu ne, marasa kan gado a cikin takardar, bai yi zaton rubutun zai karantu ba sai da ya fara karantawa, duk an gwamutsa Capital da small latter's.

*Da farko dai zan fara da yi maka Allah ya isa, dan da alama baka da ?anne mata shi ya sa ka yi mini abin da ka yi mini. Kamar yadda ka saka aka nemo ni, nima sai da na gano gidanku. Ka saka aka ?auko ni, ka zageni kuma ka ci mini zarafi, to wallahi ban yafe maka ba ta?a mini nono da ka yi, ina ta kaffa-kaffa da mutuncina, ina kula da kaina amma ka sha?oni hannunka yana ta?a wurin, kuma bayan idan namijin da ba muharramin mutum ba ya ta?a shi ciki yake yi, to wallahi Allah ya isa ban yafe ba, kuma idan ciki ya sameni sai na kwaso maka yayyena mun zo har gidanku na gaya wa mamanka abin da ka yi mini, kuma na fa?a an saci ku?in talakawa an je karatu ?asar waje. Mu zuba mu gani daga ma?iyiyarka RUMAISA MAHMUD ?AN?ARA ?ORAYI TUNGA ?ANWAR MAZA Kazo ka kasheni*

Zuruu takawa ya yi yana bin takardar da kallo, zuciyarsa na sake karkata ga ruma aljana ce. Ya maimaita sunanta *RUMAISA!* Tunani ya tafi yi, ko ya ga wani abu mai kama da nono a ?irjinta ranar da aka kai masa ita.

Ta yaya aka yi ta gano gidan su har ta kawo wannan takarda? Rubutun nata cike yake da wauta da ?uruciya.

"Zan ?ure miki gudu, zan gane idan ma ba mutum ba ce, da ni ki ke zancen" ya maimaita wasi?ar nan ya fi sau goma, babu abin da ya fi ?ular da shi irin wai ya ta?a mata nono, duk da bai ri?e cikakkiyar suffarta ba, amma shi ba ya tunanin akwai wani nono a jikinta.


Mama ta ha?awa ruma kayanta cif, da zummar gobe da sassafe za su tafi ita da yaya Aliyu, yau kuma Alhamis za ta je za su yi exam ta ?arshe, haka kurum mama ta ji ba ta son tafiyar nan da ruma, amma ta bar hakan a alhini, kasancewar ruma ba ta ta?a nisa da ita na kwanaki ba, ga kuma rashin ji irin na ruman.

Uniform ?in ruma sun sha guga, karin nan ya tsaya ?o?ar Abdallah ne ya goge mata su, sai ?amshi take, sai dai kamar kullum tana tafe tana zira hannu a aljihunta tana ciye-ciye.
Kamar a mafarki ruma ta ga an wanketa da ruwan kwatamin ruwan sama da aka yi ya kwanta, ?azantar ruwan har fuskarta. A gigice ta tsaya cak, ta bu?e idonta, dan ta ga wani mara mutuncin ne ya ci mata zarafi haka?

A hankali ya sauke glass ?in motar, suka yi ido hu?u da Rumaisa. Bakinta mutuwa yayi ta ma kasa magana gaba ?aya.

Bu?e motar ya yi ya fito yana ?are mata kallo.

"Ko zaki rama ne, ko da yake ba ki da abin ramawa ai, banbancin talaka da mai arziki kenan, na ga sa?onki, abin da ki ka ce na ta?a ?in ni ban ganshi ba ranar, shi ne na biyoki yanzu in duba in gani ko akwai".

"Wai kai ?an iska ne?" Tayi maganar ba tare da jin nauyinta ba, ga babban mutum kamar Takawa, saboda ya kaita bango.
Maganar ta dake shi, amma ya ce "Eh shi ne, yayyen naki maza da ki ke ta?ama da su, sai na kamasu na rufe, kuma na rushe gidan na ku, na ga ta tsiya".

Karo na farko da ruma ta tsaya aka sakata kuka, hawaye ya wanke mata fuska.

"Wallahi sai ka yi dana sanin abin da ka yi mini, daga yau ba zaka sake yi wa wani abun da kayi mini ba, ba dai ta?amarka ku?i ba, to ni nan Rumaisa kai da ku?in naka da sarautar ta ka sai ka dur?usa mini a kan gwiwoyinka, kuma ka saka a ranka nice nan abokiyar gabarka" tayi maganar har da dukan ?irjinta.

Girgiza kai ya yi, ya bu?e motarsa ya shiga, ta dur?usa ta ?ebi ta?on wurin ta fara watsa wa motarsa, ya taka reverse ya sake wanketa da ta?on wurin ya tafi.


(*ALHAMDILILLAH, TIRKA-TIRKA, YA KUKE GANIN ZATA KAYA A TSAKANIN RUMAISA DA TAKAWA? WACE IRIN LARURA CE DA TAKAWA, KUMA MEYE ALA?ARSA DA MAITA DA HAJIYA JAMILA TA FA?A? YA ZATA KASANCE? WANE DEAL NE KHALIFA YA SAKA SAMHA? MEYE TARIHIN GIDAN SU TAKAWA, DA ASALIN GABARSA DA ?AN UWANSA. ME ZAI FARU IDAN RUMA TA JE KATSINA??? WA RUMA ZATA AURA, SHIN ZA TA NUTSU KO KUWA? KAR AYI BABU KU, MAI BU?ATAR BOOK2 YA TUNTU?ENI TA LAMBAR WAYATA 08081012143 YA YI PAYMENT*


Ayshercool
Whats app only, ban da kira Please ?? 0808101214




[8/22, 11:40 PM] Maman Aslam: *Na gamaku da zatin Allah kar wanda ya ha?a mini document ?in littafina, mallakina ne, nike da alhakin amfani da abina yadda nake so, kar wanda ya juya mini abin ta kowacce siga, duk wanda ya ha?a mini document ?in littafi ya fitar ban yafe masa ba! Kuma ina fatan Allah ya bi mini hakkina!*
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

*AYSHERCOOL*




Cikin damuwa Huzaifa ya dube shi ya ce "To me ka gani da ba ka yarda da shi ?in ba?"

Cikin sanyin jiki Yasir ya ce "Wallahi kawai, ni mutanen cikin motar ne ba su yi mini ba"

Tsaki Huzaifa ya yi ya ce "Ka fiye matsala wallahi, dan Allah kar ma muje gida ka yi wannan zancen ka ?aga mata hankali" Yasir bai kuma cewa komai ba, suka tafi gida, sai dai shika?ai ya san abin da yake ji a jikinsa.

Ruma kuwa da suka tafi, sai kallon hanya take, tana murmushi dan tun da take, ba ta ta?a tafiya mai nisa ba, kuma ta yi sa'a a wurin taga take, dan haka take ta le?e tana murmushi. Sai dai tun shigarsu, Aliyu ya lura da Mutanen da suke zaune a gaban su, tun da suka hau motar mutanen suke waya da wani yare, wayar ta?i ci ta?i cinyewa, gashi ba mai iya fahimtar abin da suke fa?a a wayar.

Ruma kuwa sai surutu take wa Aliyu, kamar an jefeta a ka, ta ce wannan ta ce wancan. Aliyu dai bai tanka mata ba, sai Adduoi yake yi yana cigaba da kallon mutanen da tsarguwa da wayar da suke ta yi.

Ruma ta ?auko wayar nan ta wurin Yasir, ta din ga ?aukar kanta a hoto, ga wayar duk a ragargaje amma sai ?agawa take tana hoto, har da hoton hanya ?auka take, ta hau yin videon cikin motar tana ?aukar mutane.

Ko da suka bar gari suka shiga jeji, sai wannan mutane suka ce wa direba ya sauka daga kan kwalta, ya tafi ta gefen titi kan burji, ba tare da musu ba kuwa direban ya bi umarninsu, kuma aka rasa wanda zai yi magana a kan hakan kowa yayi shiru.

"Wai ya na ga ana bin gefen titi, ga kwalta ?o?ar a lailaye?" Ruma ta yi maganar har sai da kowa ya waiwayo yana kallonta. ?aya daga cikin mutanen ya yi murmushi amma ba wanda ya kulata.

"Ke uban wa ki ka ji yayi magana, sai ke hazi?a mazaru?s, kar na sake jin bakinki ko na make ki" Aliyu yayi mata maganar cikin kashedi. Tura baki ta yi ta kawar da kanta gefe. Sai dai ba aje ko ina ba, ruma ta fara cewa Aliyu ita fa wannan zaman motar ya isheta.

"Wallahi idan baki kiyayeni ba sai na zane miki jikinki, ni na yi dana sanin tahowa da ke, babu wanda ake jin bakinsa sai ke? Ki rufe mini baki na gaya miki"

Kamar zata yi kuka ta ce "To ni fa na gaji ne, kuma yunwa nake ji, su wannan mutanen na gaba, ba tun da muka taho suke waya ba suke surutunsu, babu wanda ya damesu sai ni zaka ce na ishi mutane, ni wallahi yunwa nake ji ulcer ta zata tashi"

Ri?e kunnenta Aliyu ya yi ya ce "Yi mini shiru, a gidan uban wa ki ke da ulcer?"

"Cikina ne ya fara ciwo, yunwa nake ji"

"Wallahi zan zaneki idan baki shiru ba" haka ruma tayi shiru tana ?o?arin goge hawaye.

Sai da suka zo wani ?aramin ?auye, mutanen nan suka ce a tsaya, nan ma direban ya bi umarninsu ya tsaya, kowa yana son yin magana amma yana tsoro.

Aliyu ne ya fara fusata ya ce "Direba ya na ga an tsaya? Mu da muke sauri?"

Direban ya ce "Dan Allah ku yi ha?uri, wani sa?o za su kar?a mu wuce, yanzun nan ba da?ewa zamu yi ba in sha Allah"

Aliyu ya ce "Amma ai ba a haka, sai a nemi alfarmar na mota ba a tsaya kawai ba, wannan shiga hakki ne ai"

Sai da Aliyu ya yi magana, sannan sauran mutanen cikin motar suma suka fara ?orafi a kan abin da aka yi.
Yayin da mutanen suka yi shiru ba su kula kowa ba.

Sun kai mintuna sha biyar, sannan wasu mutane suka ratso cikin dajin a babura, mutanen suka sauka, suka kar?o wata uwar jaka, sannan suka dawo motar. ?aya daga cikin su ya dubi ruma cikin gur?atacciyar hausar sa ya ce "Ke ki ka ce ki na jin yunwa ko?" Ta ?aga masa kai alamar eh.

Ya bata wata ba?ar leda, ta kar?a ta ce "Na gode" Aliyu ya bi ruma da kallo dan ya rasa me yakamata yayi mata, kawai ba ta san mutum ba ya bata abu ta kar?e.

Gasashshiyar kaza ce a ciki, da ruwan roba, ta waro ido ta ce "Laa yaya kaza ce"

Ya harareta ya ce "Mayya, tun da baki ta?a cin kaza ba, idan ki ka ci sai na miki dukan tsiya"

Ta ?ata fuska ta ce "To in mayar masa, in ce ka hanani ci?" Banza yayi mata, ganin bai kulata ba ya sanya ta saka hannu ta hau cin abarta.

Da ta ci ta ?oshi ta ?aure sauran, ta kwanta a jikin Aliyu ta hau bacci.

****
Lafiya Adam ya sauka a Abuja, ya sauka a hotel ?in da zai zauna na kwanaki biyu, dan ba ya son a san da zuwansa, shi ya sanya ya sauka a hotel, sai dai gabansa ya tsananta fa?uwa ya rasa dalili, ya kira Ammi ya kai sau uku, amma ta ce masa komai lafiya babu wata matsala.
Da yamma ya shirya ya ce bari ya ?an fita ya je wurin abokansa, ko ya ?an rage damuwar da ya rasa meya haddasa masa ita.
Sai dai yana fita harabar hotel ?in, ya ji kansa ya wani sara, yayi ?o?arin basarwa ya fita, amma ya kasa ?afarsa ta yi masa nauyi ya ji yana nema ya fa?i, a hankali ya juya ya koma ?akin da ya sauka, ya nemi wuri ya kwanta, saboda yadda yanayin jikinsa ya sauya tamkar zai fita hayyacinsa.

***
Ruma na farkawa daga baccin da ta yi, ta cewa Aliyu kashi take ji, shi kuma ya ce sai dai ta ri?e kayanta sai sun sauka, don ko zata yi hauka ba zai saka a tsaya ba, ba zai bari ma ta yi kashi a daji ba.
Ta din ga matse ?afa tana nema ta yi masa kuka, har sai da ta fara janyo hankalin mutanen da ke motar.
"Wai kai ba ka ga yarinya bace ne? A tsaya ta yi mana" cewar ?aya daga cikin mutanen da Aliyu ya kasa yarda da su.

Aliyu ya ce "A'a ba zata yi ba, idan mun je in da zamu ta yi" ya bawa mutumin amsa yana tsuke fuska. Ai bayan batun kashi ta cigaba da kuka, ita fa zai zubo, kuma ta gaji da zaman motar nan. Kan Aliyu ya yi magana motarsu ta yi faci, a tsakiyar jeji.

Fasinjoji suka din ga tsaki suna mita, masu ruwa suka ?aura alwala kasancewar azahar ta yi, suka yi salla.

Wanda ya bawa ruma kaza ya kalli Aliyu ya ce "Abokina tun da an tsaya gyara motar, ka shiga da ita ta samu wuri ta biya bu?ata mana".

"?an uwa ai na gaya maka ba abin da zata yi sai mun je, ?yaleta ?arya ma take ba wani kashi da zata yi"

Kowa yayi salla amma banda wannan mutanen, ana ta fafutukar sauya taya, tabbas da a gari motar nan ta lalace, da ba abin da zai hana Aliyu ya canza musu mota, saboda bai yadda da mutanen nan ba, shi ya san me ya gani, kuma yana tsoro yayi magana su cutar da su.
Aliyu yana salla, ruma ta tsaya tana ta ?arewa dajin kallo tana ?aukar hoto da akwalar wayarta kamar abin da ta fito yi kenan.

"?an uwanmu ku ba kwa sallar ne?" Ruma tayi maganar tana zama ?an nesa ka?an da ?aya daga cikin mutanen.

Ya kalleta ya ce "Sai mun je gida zamu yi"

"To wai Meyasa kuke ta sawa ana tsayawa a hanya ne? Duk ku ka ja muka da?e fa"

Ya ce "Sa?o muka kar?a a wurin 'yan uwanmu"

Ruma ta jinjina kai ta ce "Sune suka baku kaza ku bani na ci?"

Ya waiwaya ya kalli wanda ya bawa ruma kazar ya ce "Tun da ki ka cewa yayanki yunwa ki ke ji, yayi wa 'yan uwanmu waya, ya ce su sayo kazar, dama zamu kar?i sa?o a wurinsu, shine ya kar?o miki ya baki"

Ta yi murmushi ta ce "Allah sarki, kuna da kirki, to ku baku da gida, 'yan uwan na ku a daji suke ba gida ba?Na ga daga daji suka fito kuma babu gida a cikin daji ai"

"Eh, bamu da gida a daji muke rayuwarmu".

Cikin mamaki ta ce "Kai sai ka ce wasu kuraye, ku wane yarene to?"

Ya ha?e rai ya ce "Ke kin isheni fa, bar nan gurin"

Ruma ta ce "Yi ha?uri, dama ko a gida haka ake cewa na fiye tambaya, na daina, ina son sanin abubuwan da ban sani bane".

Bayan ta yi shiru, sai ta hau tatta?a jakar hannunsa ta ce "Wai kai ba zaka ajiye kayan nan ka huta ba, ba ka jin nauyi"
Saurin janye jakar yayi yayi mata shiru.

"Na ji kamar wasu ?arafa, kayan gwan-gwan ne a ciki? Su kuma kna zaka kai su"

A fusace ya ce "Ke tashi ki bar nan wurin kan na illata ki?" Yayi mata maganar cikin tsawa, ko girgiza ba ta yi ba, sai ma tsare shi da ta yi da ido, wata lamba ce a jikin jakar, wannan jaka dai ba za ace kaya ne a ciki ba, sai dai lambobin jikin jakar sun ?au hankalinta sosai.

Aliyu ne ya figo hannunta yana zaginta.

"Yarinya ce, ka daina dukanta mana babu kyau yarinya ce ?arama" yayi wa Aliyu maganar yana ri?e hannun Aliyu.

Aliyu ya rasa ha?in mutumin nan da rumaisa, da ya yi mata fa?a sai ya hau ce masa ya ?yaleta yarinya ce, ko ina ruwansa oho.

Haka ya ha?ura ya ?yale ruma, tun da mama ta kira ya ce mata haryanzu basu isa ba, ya sanya mama shiga cikin damuwa, saboda ya ci ace sun je, amma ta ji suna hanya.

A haka aka gyara motar suka hau suka cigaba da tafiya. Ruma ta dur?usa ta ta?a wata jaka da kuma buhu da ke ?ar?ashin kujerar da take kai.

"Wai dan Allah kayan waye wannan da ba za a saka masa su a ?asan kujerarsa ba sai ta mu, ni fa sun isheni na yi kawaicin na gaji, sun addaba mini".

Mutumin nan dai ya waiwayo ya ce wa ruma "Yi ha?uri, mun kusa sauka ma, namu ne zamu ?auke".

"Wallahi ?an uwanmu ba dan naka bane ba, sai an cire mini su, da na wannan mai jakar ne da ya hantareni sai ya kwashe kayansa ya mayar da su wurinsa, ?azu daga tambaya ya yi mini tsawa".

"To kiyi ha?uri" ?ayan ya waiwayo ya kalli ruma, ruma ta zaro masa ido kamar tana kallon yaro.

Aliyu dai ya sunkuyar da kai yana cigaba da addu'a, shi ba abin yayi wa ruma magana ba ko ya rufeta da duka ba.

Sun shiga katsina, a wani ?aramin ?auye suka tsaya zasu sauka, mai jakar nan ya kalli ruma ya ce "Ke sauko, zamu ?auki bindigoginmu".

Tsit kowa ya yi, ruma ta ce "Wace irin bindigogi kuma?"

"Zaki sauko ko sai bomb ?in ciki ya tashi da ke?"

Tanka?ata Aliyu yayi suka sauka, aka ?aga musu kujera, aka fara fito da jaka.

"Dan Allah da gaske bindiga ce a ciki?"

Yayi murmushi, ya zugewa ruma jakar, ?ananan bindigu ne, ?irar pistol.
Ya ce "Waccan jakar kuma da kike tambaya meye a ciki ?azu, bullet ne a ciki"

Ta ?an waro ido ta ce "Kashe mutane ku ke yi kenan, tun da dai na ga ku ba 'yan sanda bane kuma ba sojoji ba?"

Ya girgiza wa ruma kai ya ce "A'a 'ya ta, aikin Allah muke yi ake biyanmu"

"Aikin Allah ai ba a biyan mutum, Allah ne zai biya mutum da lada"

Yayi murmushi ya ce "Ba zaki gane ba, Ubangiji Allah ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login