Showing 99001 words to 102000 words out of 182697 words
ce mu jira abin da 'yan bindigar suka ce sai a sanar musu, muna nan muna jira haryanzu dai ba su yi mana aike ba".
Mai sunan Baba yayi shiru ya ma rasa abin da zai ce, ?arshe ya yanke shawarar a kai shi wurin 'yan sandan domin ya ji meye abin yi.
?anlami ya ?auki mai sunan Baba suka tafi, sai dai daga ?auyen da aka sace su ruma zuwa wurin 'yan sandan uwar tafiya ce mai zaman kanta, da ko menene zai samu 'yan garin ba lallai su samu ?aukin jami'an tsaro.
Ganin girma da kwarjini da kuma ganin cewa Umar ba ?an garin bame ya sanya DPO garin tsayawa ya saurare shi.
"To ?an uwa idan zan baka shawara ka koma gida kawai ku yi addu'a, bin bayan mutanen nan aikin sojoji ne bana 'yan sanda ba, mu mun yi iya namu ?o?arin, sai dai mun bar sallahun idan sun yi wata magana a sanar mana, haryanzu dai ba su ce komai ba"
Shiru kawai mai sunan Baba yayi, ba zaka ?ara sanin lamarin tsaron ?asarmu ya ta?ar?are ba sai wani iftila'i ya afka maka.
Ba tare da samo wata mafita ba, mai sunan Baba ya kamo hanyar kano.
Gidansu ruma kuwa tamkar an yi mutuwa, ko magana mai sauti ba sa iya yi, tun da mama ta ?an samu ?warin jikinta ta hau sallaya, canza alwala ce kawai take ?agata, yunwa kuwa ko jinta ba ta yi.
Ba yadda ba su yi da mama ba a kan ta ci abinci, ta ce su ?yaleta kawai.
Ko da ta ji sallamar mai sunan Baba, ji ta yi kamar zai ce mata ga ruma nan ya dawo mata da ita, amma ko da ya shiga ?akinta ta kalleshi ta ganshi shika?ai, sai ta sunkuyar da kanta ?asa, ta ji zuciyarta ne neman karyewa.
Ya ?arasa gaban mama ya zauna, su Abdallah duk suka zubo masa ido, amma ya rasa ta ina zai fara yi musu bayani.
Mama ta sake ?aga kai ta kalli ta mai sunan Baba, ya girgiza mata kai ya ce "A dage a cigaba da Addu'a kawai"
Wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya mama ta sauke, ta sake sunkuyar da kanta ?asa.
Huzaifa ya fashe da kuka, Yasir ma ya taya shi.
Cikin dakiya mai sunan Baba ya ha?e rai ya ce "Meye haka kamar wanda ba su je islamiyya ba, ba ku yi imani da ?addara bane? Yanzu kuka ne ya kamace ku ko kuma addu'a?" Haka ya din ga yi musu fa?a alhalin shima da zai samu space kukan zai yi. Ya tashi fuuu ya tafi ?akinsu, yana zuwa ya tarar da Abubakar a zaune yayi shiru ya lula duniyar tunani.
Mai sunan Baba ya zauna a kusa da shi, ya ce "Akhi na dawo?"
Banza yaya Abubakar ya yi masa bai kula shi ba.
"Na san na yi maka laifi, amma yakamata ka yi mini uzuri, ba a hayyacina nake ba, idan ka gama fushin sai mu yi magana" ya yin?ura zai tashi Abubakar ya ce "Yaya ku ka yi da ka je, an samu labarinsu?"
"Babu wani labari mai da?in ji, sai ma kayan takaici, ance mu saurara idan sun kiramu sun ce mana wani abu shikenan sai mu sanar".
"Idan kuma ba su kira ba a haka zata cigaba da zama a hannunsu?"
"I have no idea" mai sunan Baba ya fa?a cikin damuwa.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Aki meye abin yi?"
"Addu'a" ya bashi amsa a ta?aice.
Dare ya tsala, wasu daga cikin al'umma sun kwanta suna hutawa, yayin da wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da iyalansu suke kwanan zaune, ciki har da mama da yaranta maza yayyen ruma gaba ?aya mama ta manta da wani abu wai bacci a wannan halin da take ciki, a zaune take tamkar an dasata tun tana iya lazimin da addu'a har ta kasa ta rasa abin da ma zata ja.
Zuciyarta sai zafi take mata, da tunanin a wani hali ruma take ciki.
Wurin baccin ruma ta kalla, da yanzu tana nan mama tana faman gyara mata kwanciya ko tashinta fitsari, da yanzu ta yi ?ai-?ai sauro na cizonta mama tana mita tana sake gyarata, ko ta ?aro fanka idan ta fuskanci zafi yayi mata yawa, ko ta kashe fanka ta lullu?eta idan sanyi yayi yawa.
"Ruma ko a wani hali kike? Ko kina raye? Ko kin ci abinci? Ya in da ki ke kwance? Sanin gaibu sai Allah, ya rabbilarshil azim, dan girmanka Allah ka tsare mini 'ya ta da sauran 'ya'yan musulmi, Allah ka dawo mini da ita cikin aminci" ta ?arasa addu'ar kuka yana kufce mata, sai a lokacin ta ?an ji nutsuwa da ta samu hawayen idonta ya zuba.
?akin 'yan mazan ma gaba ?aya idonsu biyu, wasu da Alqur'ani wasu a kan sallaya, wasu suna kuka, dan basu ta?a tsintar kansu a cikin mummunan tashin hankali kamar wannan ba.
Ruma ta yi rigingine a filin Allah, wani irin sanyi yana ratsata ga cikinta kamar ya ha?e da bayanta saboda azabar yunwar da take ji, ga ?ai?ayi da jikinta yake mata saboda rashin wanka, ga wani irin sauro na bala'i da ?wari suna gasa mata cizo.
A hankali ta furta "Mama, mai sunan Baba" sai kuma ta yi shiru hawaye ya fara zirarowa ta gefen idonta.
Tana tsaka da tunanin, wurin yayi tsit, mutanen sai kewayasu suke yi da manyan bindigogi.
Wani irin sauti ruma ta din ga jiyowa na motoci ?asa-?asa, daga bayan dutsen da ke nesa da su.
"Sha tara ga motocin smoke can suna aiki fa" cewar ?aya daga cikin 'yan bindigar.
" 'yan wahala ba, ni mamaki nake yadda suke iya fitar da sabgar nan ba wata matsala" ?ayan ya bashi amsa.
"Haba, sun gama sai ta komai nake gaya maka, babu wanda ya isa ya tare musu hanya, babban controller na ?asa ma fa nasu ne, kuma akwai na sa kason a ciki mu suka mayar 'yan iska kawai".
Sha tara ya ce "Aikuwa sai mu yi tawaye, ko dai su yi wani abu a kai ko mu bujure, haba ma'adanan nan fa da suke kwasa ba dan muna gyara musu aikin nan ba da ba zai yiwu ba, amma kura da shan bugu gardi da kwashe ku?i".
"Kai ni ba wannan ba ma, oga nake jira ya zo ayi wadda za ayi a san yadda za ayi da mutanen nan"
"Eh gobe zasu shigo ai"
Haka suka cigaba da hirarsu, amma kan ruma ya ?aure, wasu ma'adanai ake kwasa meye ma ma'adanan?
"Zan yi fitsari" ta fa?a cikin rawar murya".
"Yi a nan" ?ayan ya bata amsa.
"Ina jin yunwa ma"
"Idan ki ka kuma magana sai na taka ruwan cikinki"
Guntun tsaki ruma ta yi, tayi juyi wani abu da ba ta san menene ba gasa mata cizo, wata uwar ?ara ta saki, ta mi?e tana kuka.
"Wai wannan wace irin iblishiyar yarinya ce meye kuma?"
"Wani abu ne ya cijeni" ta yi maganar a gigice tana soshe-soshe.
"Nemi wuri ki zauna ki rufewa mutane baki, ni wallahi da oga ya zo da na da?e da harbe wannan shegiyar yarinyar da ba ta rasa matsala".
"To ku mayar da ni in da kuka ?auko ni mana, meyasa zaku kawo ni nan" tayi maganar a sangarce
Hasketa ?ayan yayi da hasken fitila, ta saka hannu ta kare tana motsa baki, saukar wani abu ta ji a goshinta mai nauyin tsiya, daga haka ba ta sake sanin in da kanta yake ba.
Bayan sallar asuba, su Abdallah suka sanar da abin da yake faruwa a masallaci, tare da ro?on bayin Allah su taya su da addu'a, Allah ya fito da rumaisa cikin aminci da ?oshin lafiya.
Mutane da yawa sun ka?u da jin abun da ya samu ruma, dan ruma ta mutane ce, da yawan mutane sun santa, kan gari ya gama haske unguwar su ta cika da labarin yin garkuwa da ruma.
Gari na gama yin haske aka din ga sintirin zuwa yi wa mama jaje, tare da addu'ar Allah ya bayyana ta.
Mama duk yadda ta so ta jure, ta kasa haka ta dinga share hawaye, masu cewa ta daina kuka kuwa kallonsu kawai take yi, gani take ba su san a cikin tashin hankalin da take ba ne.
Hatta daga islamiyya su ruma haka aka yi tawaga guda, suks zo yi wa mama jaje suka gabatar da Adduoi, tare da yi wa mama al?awarin za su cigaba da addu'a da karatun Alqur'ani har zuwa lokacin da Allah zai bayyana rumaisa.
Rumaisa kuwa a hankali ta motsa, ta fara ?o?arin bu?e idonta, amma ta ji goshinta yana mata zafi, a hankali ta kai hannu goshin ta ji ya kumbura, ga busashshen jini ta shafo.
Cikin ?arfin hali ta tashi zaune, sai dai wani irin jiri ne yake ?aukarta, saboda azabar yunwa, ga zafin dukan da aka mata da bakin bindiga.
Wani narkeken mutum ta gani, yana zagaya su, yana ?are musu kallo.
"Ke a ina aka ?aukko ki?" Yayi mata maganar cikin tsawa. Ba ta kai ga bashi amsa ba, ta ga mutumin da ta bawa gya?a a kasuwa.
Yayi saurin kawar da kansa da ga kallon ruma.
"Ke ya ina miki magana kin mini shiru?" Yayi maganar cikin muryarsa mara da?in ji.
Gefe guda ta ja, ta tan?washe ?afarta, tana jin yadda take jan numfashi da ?yar.
A fusace ya saka hannu ya fizgo ruma, amma ta ta?ar?are iya ?arfinta ta fizge hannunta ta ja da baya tana huci. Kallon kallo suka shiga yi, tsakanin shi da rumaisa.
Yin?urawa yayi zai maketa, mutumin nan ya shiga tsakaninsu, ya ce "Yi ha?uri, yarinya ce"
"Ban gane yarinya ba, bani bindiga kasheta zan yi"
Ya girgiza masa kai ya ce "A'a, da alama ubanta wani ne, za a samu ku?i a hannunsu, ka bari mu kar?a sai a kasheta".
"Ni bani da uba" tayi maganar cikin ?warin gwiwa.
"Ina magana kina saka baki? Zan ?yaleshi ya kashe ki" da ?yar ya shawo kan mutumin ya ?yale ruma.
Ya ?auki wata leda ya jefa mata, buredi ne a ciki sai ruwan pure water. Tamkar ta shekara ba ta ci ba, haka ta dirarwa buredin nan, tana ci tana yin?urin amai.
Tana zaune tana cin abincinta, tana kallon yadda ake kar?ar lambobin wa?anda aka ?auko su tare, ana cinikin nawa za a biya a kar?esu kamar wasu dealer kaya.
Mutumin nan dai na ?azu, ya zo kan ruma ya ce "Bani lambar babanki".
"Dama ana zuwa kabari da waya?"ta tambayeshi.
"Kamar yaya?"
"Na gaya maka bani da uba ya mutu ai"
"Bani lambar wani ?an gidanku"
Rumaisa ta ce "Ka ga nifa gidanmu in dai ku?i zaka ce musu su kawo, basu da shi, sai dai ku yi mini abin da zaku yi mini"
Ya ?are mata kallo ya ce "Haka ki ka ce?"
"Eh"
Ya mi?e tsaye ya ce "Biyoni".
Ayshercool.
Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Gaba ?aya suka bi ruma da kallo, ita kuma ta ?are masa kallo ta ce "in biyo ka mu je ina?".
"Cewa ki ka yi sai dai ayi miki duk abin da za ayi miki, abinda yakamatan zan miki ai".
Ruma ta ce "Koma mene ka yi mini a nan ba in da zani"
Mutumin da yake ta ?o?arin bata kariya ya fara fusata ya ce "Wai ke wace irin yarinya ce?, duk yadda za ayi a kare mutuncinki a rabu lafiya ana yi, amma ke sai ka ce baki san ciwon kanki ba, ke kin san me zai miki ?in ne ki ka tura baki kina cewa ayi miki koma menene?".
Cikin kuka ta ce "Ta ina kake kare mutuncin nawa, da kuka ha?amu maza da mata kuka rabo ni da 'yan uwana, yanzu ka gama cewa a kasheni, wallahi babu in da zani daga nan, koma me zaku yi mini ku yi mini ni na gaji"
Su kansu wa?anda aka kamo su tare da ruma mamaki suke yi, yadda take rashin mutuncinta yadda ta ga dama.
?aton nan ya sanya ?afarsa iya ?arfinsa ya taka ?afar Rumaisa, ta ri?e kanta ta yi wata irin ?ara, ba ta warke daga waccan azabar ba ga wata ana gana mata, ji ta yi kamar ya karyata, saboda azabar da ta ji, dan ?ato ne na gaske.
Mutumin da haryanzu ba ta san sunansa ba ya ce "Ina ga daga yanzu ba zan sake magana ba, su yi miki duk abin da zasu yi miki, akwai dalilan da yasa nake baki kariya, amma tun da ke na fuskanci baki da hali, duk abin da aka yi miki ke ki ka saya, idan baki nutsu ba haka zaki ta shan ba?ar wahala, kina raye amma na lahira sai yafi ki jin da?i, ki cigaba mara kunyar banza".
Fuska duk hawaye cike da dakiya ta ce "Eh ayi mini ?in, ku kasheni daga nan sai me?, wallahi ba zan daina magana ba sai kun gaji kun kasheni, kuma ba lambar wanda zan bayar a gidanmu, ku da Allah ba zan yafe muku ba, ba laifin da na yi muku kuke cutar da ni, Allah ya saka mini duniya da lahira".
Bu?e baki yayi yana kallon rumaisa, ga fuska duk busashen jini, amma sai kwaroroto take ba tare da ta na tsoron ayi mata wani abu ba.
Aikuwa ?aton nan ya dinga takata da ?afarsa, yana dukanta tana ihu tana "La'ila ha illa anta, subhanaka inni kuntu mina zalimin" shine kawai abin da take maimaitawa, dan idan ya takata ji take kamar ana buga mata itace, ko wani nannauyan ?arfe.
?ayan kuwa yana kallo bai kuma cewa komai ba, sai da ?aton nan yayi mai isarsa ya ?yale ruma, ba dan ta yi shiru da bakinta ba, sai dai ihun ma da ?yar take iya yin sa saboda ta galabaita. Haka kowa ya zura mata ido yana kallonta, duk wurin ita ce ?arama sauran duk da girmansu, amma tafi kowa baki da rashin mutunci.
A gigice mama ta dafe ?irjinta, hawaye na zuba daga idonta, mutane na ta bata ha?uri, amma a zuciyarta take jin kamar wani na faruwa da rumaisa, mussaman da zuciyar ta ta ta tsananta bugawa.
Idan ka ga mama sai ka zata wani ciwon tayi, duk da ba mace ce mai ?iba dama, amma ba ramammiya bace ba, tana da kumarinta, amma lokaci guda duk ta zube sai tsawo.
Ba ta iya cin abinci sai su Abubakar sun yi da gaske, da rarrashi da ban baki, ake samu ta ?an sha abu mai ruwa-ruwa. Duk wata walwala da ake a gidan nan suka dainata, bacci kuwa sai dai ?arawo, babu mai iya yin sa yadda yakamata a gidan.
'yan uwa da abokan arziki ana ta shige da fice, ana yi wa mama jaje tare da addu'a Allah ya baiyyana ruma.
Habiba ce ta fa?o gidan su rumaisa a gigice, ta din ga kallon yayyen rumaisa da mutanen da suke zazzaune, can ta hango mama, ta ?arasa wurinta da gudu, ta zube a kan gwiwoyinta "Mama, wai da gaske an sace ruma?"
Mama ta ?ura mata ido, amma ta kasa magana.
Ma?wabciyar su ruman ce ta ce "Eh da gaske ne, yanzu ku je ku yi ta yi mata addu'a, Allah ya bayyanata cikin aminci, ya tsareta a duk in da take".
Rushewa da kuka habiba ta yi, tana wata irin sheshshe?ar kuka, gaba ?aya ta gigice tana wani irin kuka.
A fusace mai sunan Baba ya ce. "Dalla ku fitar mana da mai ihun nan, da wane zamu ji?"
Aliyu yayi saurin cewa "A'a ba haka yakamata ayi ba, akwai sha?uwa a tsakanin su, bai kamata a hantareta ba"
Aliyu ya fita ya je ya samu Habiba, ta ha?a hawaye da majina tana kuka, ya tuna fa?ace-fa?acensu na ?uruciya tsakaninta da rumaisa, kullum cikin sintirin kan ?ara ake, da yadda yake zaneta ita da yayanta a kan ruma, amma yau ta tayar da hankalinta saboda ?atan ruma.
Hannunta ya kamo ya ja ta gefe yana rarrashinta, amma babu alamar za ta yi shiru, duk jijiyon kanta sun ?aga idonta yayi jawur saboda kuka.
"Kiyi shiri kar kanki yayi ciwo, sannan addu'a zaki taya mu, Ubangiji Allah ya bayyana mana ita, ki daina kukan, mu je na raka ki gida"
"Allah ya sa kar a kasheta, Allah ya sa ta dawo gobe" ta fa?a tana sake fashewa da kuka.
?walla ce ta cika idon Aliyu, domin kuwa dauriya kawai suke yi, ya wayance ya ce "Amin ya Allah, dan idan kin yi salla ki din ga sakata a addu'a kin ji"
Habiba ta jinjina kai, tana cigaba da share hawaye. ya saka ta a gaba ya rakata gida, amma yanayin tashin hankalin da take ciki, zai tabbatar maka da ta ka?u sosai da ?atan ruma.
Hauwwaliya ma da take a zaune tana jinyar karayar da ta yi kafin tafiyar runa, ita ma haka ta burkice, dan da har tana mitar ruma ta tafi ba ta zo ta dubata ba balle su yi sallama, sai labarin an yi garkuwa da rumaisa suka ji.
Hatta malamansu ruma na makarantar islamiyya da take gallaba, gaba ?aya suka shiga damuwa, makarantar kanta kamar ana zaman makoki, saboda babu wanda bai santa ba da halinta. Ita kanta tsohuwar da take sayar da kayan yara a makarantar, da suke yawan fa?a da ruma sai da ta yi kuka, dan wataran idan sun yi fa?a wata ran suna shiryawa, dan idan ruma ta zo da abinci wataran tare suke ci, duk rashin jin ta akwai shiga rai.
Takawa yana kwance a ?aton falonsa a kan doguwar kujera, yayi zurfi sosai a cikin tunanin da yake yi, abubuwa da dama sun yi masa yawa, gaba ?aya ya rasa wace matsalar yakamata ya fara tsayawa ya nemi mafita a kai, duk matsalar da ya tunkara, sai abubuwa sun ?ara ta?ar?arewa.
Wani irin zazzafan zazza?i ne ya kama ruma, saboda wahalar da ta sha, ga azabar cizon sauro da kuma sanyi suka haddass mata zazza?in.
Babu wanda yake ta tata, balle ya taimaka mata, tuni wasu aka fara bayar da ku?in fansarsu, idan sun ga dama su bayar da mutum, idan ba su ga dama ba su kar?i ku?in sannan su kashe mutum su ja gawar zuwa bayan wani babban dutse da yake nesa ka?an da in da suke ajiye mutanen su yar gawar ba tare da suturta gawar ba.
Ruma na kwance ta takure tana ta rawar sanyi, ga azabar ciwon jiki, saboda dukan da ta sha, wasu mutane suka zo a kan babur, wanda aka goyo hannunsa ?auke da ?atuwar jaka, ta ?aga ido dan ta ga su waye, wa za ta gani, dattijon bafullacen nan, da ta ha?u da