Showing 117001 words to 120000 words out of 182697 words

Chapter 40 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22416

nake ji, dan dai kar in dameku ne, ina ma san ranar da zata dawo".

Mai sunan Baba ya girgiza kai ya ce "Shikenan, dama lokacin shan maganinki yayi, zauna in baki ki sha ki kwanta ki huta, Allah ya dawo mana da ita lafiya, ya tsare mana ita a duk in da take".

Kamar ?aranar yarinya mama ta ce "Kai ma kana kewarta ko babana?"

"Mama ?anwata ce fa, duk halinta jininmu ?aya ina kewarta, zauna to" haka ya zaunar da mama da ?yar, ya bata magani, dan mama har likitan ?wa?walwa liktanta ya bada shawar ta gani, saboda depression na neman kamata.

***
Tamkar ciwo jira yake dare yayi, ciwo ya tayar wa Aisha, sai dai ta daure ta ?i nunawa saboda kar ruma ta tayar da hankalinta.

Ruma da hannunta ke kan cikin Aisha, ita kuma ta ri?e hannun ruma, ruma na kwance lamo ba bacci take ba, can ruma ta ce "Laaa, Anty Aisha wallahi jaririnki ya motsa, baki ji ba?"

Da ?yar ta yi murmushi ta ce "Na ji ruma, yana raye Allah ya sa ina da rabon ganinsa".

"Amin, bari in yi musu magana su kai ki asibiti "

Ta ri?e ruma ta ce "?yalesu, ba zasu kai ni ba, na ji sau?i ki zauna mu yi hira"

Ruma ta ce "Ni bana son hirar, so nake na ga kin koma kamar da"

Cikin dakiya ta din ga yi wa ruma hira, tana sakata dariya, amma a ?asanta kuwa jini ne yake zuba sosai.

Jin tana cigaba da numfashi da ?yar, ya sanya ruma ta tashi, ta tafi wurin 'yan bindigar nan ta ce "Dan Allah sha tara ku kai ta Asibiti, bata da lafiya sosai wallahi"

Duk da duhu ne, ya kunna fitila ya haske in da Aisha take, sai jujjuya kai take, zaninta yayi sharkaf da jini.

A aljihunsa ya sanya hannu, ya ciro wayarsa, ya kira wata lamba.

"Oga, matar nan fa kar ta mace mana, ya ake ciki azo a fita da ita ko zuwa wayewar gari ne"
Ruma ta kasa kunne, sai dai ba ta jiyo me na cikin wayar yake cewa ba. Sha tara ya kashe wayar ya ce "Da safe za a kaita asibitin, tafi ki kwanta"

Ruma ta tashi ta koma wurin Aisha, tana gaya mata ai da safe zaa kaita asibiti.

Aisha ta jinjina kai, ruma ta ce "Anty Aisha, wai daga ina jinin nan yake fitowa, ko fitsarinsa ki ke yi ne?"

"A'a ruma, amma dan Allah matso in din ga jinki a kusa da ni, jiri nake ji".

Ruma ta matsa ba tare da ?yamar jinin ba, ta rungume Aisha.

"Rumaisa ina ?an kwalina da na baki?"

"Yana ?unguna na ?aure shi, na baki ne?"

Ta ce "Yauwwa sannunki baby rumaisa, ina ?aunarki sosai"

Ruma da kuka take ta ce "Nima ina sonki sosai Anty Aisha".

"Idan na haifi mace sunanki zan saka mata, idan namiji ne kuma sunan wannan abokin naki da ya ta?a miki ?irji, ya ma ki ka ce sunansa?" Ta yi maganar cike da zolaya, da son kunna ruma.

Aikuwa ruma ta ce "Wallahi ba za'a saka masa sunansa ba, ke me yayi miki zafi, zaki saka sunan ?an iska, ba gara a saka sunan Barde ba, tun da dai yana bamu abinci"

Ta yi dariya ta ce "To a saka mai sunan Baba"

Ruma ta ce "Kaii, ban baki wannan shawarar ba, fa?ansa ka?ai ya isheki".

Aisha tayi wa ruma wani irin ri?o tana nishi, sannan ta ce "Kawo kunnenki ki ji wata magana".


AYSHERCOOL.
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

?? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*






Gaba ?aya jikin ruma yayi sanyi, bayan ta gama gaya mata abin da zata gaya mata, sai da ruma ta yi shiru ba ta ce komai ba, tana nazarin abun da ta gaya mata.
Haka suka wanzu, ba su rintsa ba a daren, sauran mutane sai dai wanda yayi juyi ya yi wa Aisha sannu. Lokaci lokaci kuma sai ta dan?i hannun ruma tana wani irin yin?uri da kakari, ita ka?ai ta san abun da take ji, ruma kuwa sai dai tayi ta mata sannu da addu'a Allah ya bata lafiya. A haka har gari ya waye, ta ?aga ruma ta ce ta je ta yi salla.

Da ?yar ruma ta iya tashi, jikinta da jinin nan ta yi salla, dan ba ta da wasu kayan, kuma ba ta da ruwan wankewa, jikin ruma duk a sanyaye yake.

Tana idarwa ta nufo in da Aisha take, amma ta ga wasu daga cikin matan wurin sun kakkare Aisha, suka hana ruma ?arasawa, sun kewayeta.

Ruma ta ?an ?are musu kallo ta ce "Wai me ku ke yi haka ne?, da can baku kulata ba ta kwana babu bacci, sai yanzu, ku bari na ganta mana meyasameta?" ?ayar ta ce 'yi ha?uri, zaki ganta ne haihuwa za ta yi "

"To shine zaku wani kareta, ba amayo shi kawai za ta yi ta bakinta ba, ku matsa dan Allah"

Kakarin Aisha ta jiyo tana salati, tana kiran sunaye daban-daban, ta shiga kiran sunan ruma.

Ruma ta gigice, sai dai matan suka cika mata ido ta kasa yi musu rashin kunya, dan duk da girmansu.

"Anty Aisha, kin ganni a nan sun hanani zuwa wurinki, meya same ki?"

Jin kukan jariri ruma ta yi ya kara?e ko ina, sai hamdala Aisha take tana nishi sama-sama. Ba su farga ba, sai ganin ruma suka yi a tsakiyar su.

"Anty Aisha kin haihu? Sannu"

"Yauwwa ruma, kin gani ashe babyna bai mutu ba"

Sam hankalin ruma bai kai daga ina ?an nan ya fito ba, ita dai ta ga jaririn a kan Aisha ta ce "Ai dama na gaya miki yana motsi, yana nan da ransa bai mutu ba" ruma ta mayar da hankalinta kan jagwalon da yaron yake ciki, ga jini face-face abun babu kyawun gani, yaron ?ato da shi sai tsala ihu yake, bakinsa yana karkarwa saboda sanyi.
Matan suka shiga laliben abin da za a yanke cibiya da shi.

Aisha kuwa ta ri?e hannun ruma sai murzawa take tana cigaba da salati.

Su kansu 'yan bindigar rasa abun yi suka yi, tausayawa Aisha za su yi, ko yaya za su yi mata, basu ta?a kamo wadda ta haife musu a wuri ba, sai a wannan karon.

Ruma hijjabinta ta bayar, aka nanna?e jaririn, sannan aka saka shi a mayafin Aisha, aka ?ora mata shi a jikinta.

Haka ta yi ?o?arin rungumeshi, amma ta kasa ?aga hannunta, sai ruma ce ta ri?e mata shi, ta din ga kwarara masa Addu'a, tana saka masa albarka daga baya ta koma yi wa rumaisa Addu'a.

"Anty Aisha, to ki tashi zaune mana, idan barde ya zo ya kawo abinci sai ki ci, ki ba shi ya sha kuka yake"

"A'a ruma, ba zan iya tashi ba, ki yi masa addu'a kawai, na bar miki shi halak malak, na bar miki shi har abada, daga yau ke ce ummansa, ubangiji Allah ya raya miki shi da imani, ki saka masa duk sunan da ki ke so"

"Kar dai zafin ciwo ya sa ki ce kin bar mini shi, daga baya ki zo ki ce ba haka ba"

Ta yi murmushi ba ta ce komai ba, ?aga kai ta kalli yadda jaririn yake ta motsi a cikin zani, ko arzikin wando bai samu ba.

Hawaye ya zubo daga idonta ta ce "Allah ya rayaka, ka kula mini da baby rumaisa na".

"Dan Allah anty aisha ki daina wannan maganganun, ni bana jin da?i, tsigar jikina ma duk tashi take yi. Sun ce za su kai ki asibiti, yanzu jira zan in ga gudun ruwansu, idan basu zo sun kai ki ba, in je in tayar da tarzoma, in tayar wa da kowa hankali".

Ta girgiza kai ta ce "Ba zaki canza hali ba ai" tayi maganar cikin ?arfin hali tare da murmushi.

A hankali take salati tana juya kanta, ruma ta mi?e da jaririn ta bawa wata mata ta ce "Goya mini shi". Matar ba ta yi wa ruma musu ba ta goya mata shi, dan kamar tsoron ruma suke ji, sun ga yadda su kansu mutanen ke lalla?ata, sun tsoron su ?ata mata rai, a kashe su.

Ta juya wa aisha bayanta ta ce "Ya ki ka ganshi a bayana?"

"Yayi miki kyau sosai, Allah ya raya miki, amma baki gaya mini sunan sa ba"

Ruma ta yi murmushi ta ce "Zan gaya miki, sai an kai ki asibiti tukuna".

Ta ja numfashi ta ce "Dan Allah samo mini ruwa na sha ruma".

Ruma ta tafi da sauri ta kar?o ruwa a wurin su sha tara, sai buga waya suke suna magana a kan Aisha".

"Wai dan Allah yaushe za a kaita asibitin ne, tana shan wahala fa sosai ".

"Za'a kaita, mota muke jira a kawo" suka fa?a dan kwantar mata da hankali.

Ta dawo ta sake kallon jikin Aisha, tamkar an tsomata a bokitin jini, ta yi jalaf kamar an zuba mata.

Ruma ta ?agota ta fara bata ruwan, ma?warwa biyu kawai ta yi ta ce "Alhamdilillah" daga nan bata kuma magana ba.

Ruma ta ce "Masha Allah, ai gara ki yi baccin sai ki huta, Allah ya sa motar ta zo da wuri.

Ta ?ulle bakin ledar pure water, ta ajiye, ta gyara wa aisha kwanciyar kanta.

Ta koma tana ta zagayawa tana jijjiga jaririn da yake bayanta, sai dai yaron ya din ga tsala ihu, kamar ana tsoma shi a wuta.

Ruma ta koma wurin Aisha ta tatta?ata ta ce "Anty Aisha, ki tashi ki gwada shayar da shi, kin ga sai kuka yake yi" shiru Aisha ba ta motasa ba.

"Anty Aisha, har baccin naki yayi nauyi haka? Ki tashi kuka yake" taga matan da suka kar?i haihuwar suna kallon kallo, suna kallon ruma.

"Dan Allah ku zo ku tasheta mana" tayi maganar tana sake jijjiga Aisha.

?aya daga cikinsu ta zo ta tatta?a aisha, suka ha?a ido da ?aya daga cikin 'yan bindigar, mai dukan ruma wato sule, ta girgiza masa kai, yayi mata alamar ta yi shiru.

Ta kalli ruma ta ce "Ki ?yaleta, bacci ne a kanta, ki bari ta huta kin ga haihuwa ta yi".

"To ai ba ta da nauyin bacci, bari mu gani to zuwa anjima, bari na bashi ruwa, Allah sarki Anty Aisha ai gara ki huta, kin sha wahala"

Da haka suka rufe ruma, ta bawa jaririn nan ruwa sai da ya ?oshi da ruwan pure water, sannan ta sa aka mayar mata da shi bayanta, ta cigaba da jijjiga shi a bayanta".

****

Kusan mintuna biyu da shigowar Jamil ?akin, amma takawa bai san ya shigo ba, saboda yadda yayi nisa a cikin tunani.
"Takawa, wai meye ne? Wannan wane irin tunani haka da ?arancin shekarunka, ka tsaya tunani zai kassaraka".

Adam bai motsa ba, da ido kawai ya kalli Jamil, ya mayar da idonsa ya lumshe, tabbas ba dan jarumta irin ta ?a namiji ba, da kuka zai yi ko zai samu sassauci, komai ya dagule masa, abubuwan duk da ya sako gaba suna neman su gagare shi, ya kasa komai.

Jabir ne ya fito daga toilet, ya tarar da Jamil yana yi wa takawa mita.

Jabir ya gya?a kai ya ce "Wallahi Jamil tun kan ka shigo nake yi masa nasiha, a kan ya mi?a lamuransa ga Allah, tunani bawa wata cutar damar shigarsa ne, amma ya?i ganewa".
Idanun Adam suka yi jawur, ya kalle su cikin tsananin damuwa ya ce "Ya ku ke mini abu kamar wani wanda ya rasa imaninsa ne? Ina da hankali ina da imani, na yarda da ?addara, ina tunanin yadda zan shawo kan matsalolin da suke gabana ne, a wannan halin da nake ciki, wambai yake kirana yana ci mini mutunci, na rasa laifin me na yi masa, ba wannan ne ma ya dameni ba, wani rumors ne yake yawo wai na yi shaye-shaye na yi yin?urin yi wa iman fya?e, ?anwata ko da ina haukacewa wasu lokutan amma na san iman ta haramta a gareni, ban san meyasa ?addarorinmu ke tafiya a kusan tare ba, ni idan sunana ya ?aci normal ne, ba wannan ne karon farko ba, iman yarinya ce zuciyarta ta yi ?an?anta da duk wannan pressures ?in, tun da maganar nan ta isketa, ta burkice ba lafiya, jikin Ammi na neman tashi, gashi kuma still wai wambai na nemana, ya ake so na yi ne?" Ya ?arasa maganar cikin wani irin zazzafan huci mai cike da tsantsar damuwa da tashin hankali".

Jamil ya dafa shi ya ce "Takawa, mun san komai amma ka sani, ita rayuwa haka take, yau fari gobe tsumma, ka cigaba da addu'a kawai".

Jabir ya ce "Shiyasa na ce ka bani auren iman, ni zan jure duk wani ?alubale, amma ka dage wai ba zaka bani ba, na rasa menene a zuciyarka".

Cikin son sauke fushinsa ya kalli Jabir ya ce "Babu komai a raina, amma ba zaka auri iman ba"

"Kai zaka aureta kenan?"

"Eh" ya bashi amsa.

Jamil ya ce "Duk wannan ba ta taso ba, dan Allah ku yi ha?uri, ni tafiya ce ma ta kamani ta gaggawa, na zo ?aukar system ?ina"

Jabir ya ce "Sarkin hijira, yau kana nan gobe kana can, kamar mara gaskiya".

"Ni ne ma takawa, na san duk yawona ban kai shi ba, shi ne mara gaskiya lamba ?aya" yayi maganar cikin zolaya, da son saka Adam murmushi, amma Adam ya tashi ya bar musu ?akin gaba ?aya.

***
Kusan har la'asar ta gabato, ruma ba ta ga aisha ta tashi ba, ha?urinta ya fara ?arewa ta fara yi musu halin nata, a kan sai an kai aisha asibiti, haryanzu ba ta tashi daga bacci ba. Ta kai ta kawo ta duba aisha, ta cigaba da tsiwar azo a kai ta asibiti, su dai sauran mutanen da suka san mai ya faru, suka yi tsit aka rasa mai fahimtar da ita.

Sule ya fara ?o?arin zare mata ido, dan ta ishe su, amma ya tuna tashin hankali da barazana ba sa aiki a kan rumaisa.

Ta wannan sur?u?in aka shigo da wata mota, ruma ta ce "Alhamdilillah" ta cigaba da jijjiga Aisha tana cewa "Anty Aisha tashi, ga motar da zata kai ki asibiti".
Wasu mutane suka saukko, mutum biyu sun sanya farar PPE gown, sauran kuma mutanen da suka zo ne masu ba?a?en kaya.

Suka ?arso kan gawar Aisha, ruma ta ce "Ku bayin Allah da zaku zo kaita asibitin, amma baku zo da wuri ba duk ta galabaita tun ?azu ta?i tashi daga bacci?".

Basu kula ruma ba, hannayensu sanye da gloves, suka na?e Aisha da zaninta, da yake kaca-kaca da jini da ?azantar haihuwa, suka fito da wata leda, suka fara ?o?arin zura gawar a ciki.

A ki?ime ruma ta ce "Ya hakaz'? ya zaku sakata a leda kamar wani kifi, idan ta mutu fa?"

?aya daga cikinsu ya ce "To uban waye ya ce miki tana da rai? Ta mutun ai" wata irin gigicewa ruma ta yi, ta dan?i gawar Aisha ta ce "?arya ka ke yi, wallahi ba zaku sakata a leda ba, bama zaku kaita asibitin ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login