Showing 51001 words to 54000 words out of 182697 words
kwakwa a bakinta.
Yayi murmushi ya ce "Ai ba prison zan kai ki ba, magana za mu yi"
"To rantse" kallon ruma suka yi gaba ?aya, wai DPO take cewa ya rantse.
Aliyu ya ce"Yalla?ai, dan Allah ka yi ha?uri yarinyar ba ta da cikakken hankali, magani ake nema mata"
Ta yi farat ta ce "Wallahi lafiyata ?alau"
Aliyu ya kai mata duka ya ce "Ni ne nake yi miki ?aryar?"
DPO Ya ce "Na fuskanta, zo ki ji kin ji baby girl, magana za mu yi" Ruma ta ?an matsa gaban teburinsa, amma ta?i ?arasawa in da yake.
"Garin yaya ki ka iya karya mata hannu?"
Ruma ta ce "Ka na kallon wrestling?"
Ya ce "Sosai makuwa"
"To a nan na koyi ?arfi, kuma yayyena fa maza ne, su bakwai ne ni ce 'yar auta a gidanmu, ina da ?arfi sosai, irin yadda shemaus yake yi a wrestling na gwada ban zaci ana karyewa ba wallahi "
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kun ga ka?an daga rashin fa'idar kallon irin wannan abubuwan ga yara kenan. to meya ha?aki da ita ki ka karya mata hannu?"
"Zane ta yi mini a littafina, na yi mata magana ta yaga min littafi, na rama, shi ne ta din ga zagina, tana yi mini ashar ni kuma bana zagi, ta ce wai babata tsohuwa, shi ne ni kuma na zana babarsu a allo, ta dakeni kuma aka bani rashin gaskiya, ni kuma washegari na rama, ina ga aljanuna ne suka tashi, na yi mata irin na 'yan wrestling, amma wallahi ban san za ta karye ba, raina ne ya ?aci sosai"
Headmaster da tun da aka zo bai ce komai ba, sai girgiza kai kawai da yake yi, dan ya rasa me ma zai ce, bai ta?a zaton haka rumaisa take ba.
Headmaster ya numfasa ya ce "Yanzu dai tun da sabga ce ta yara, ayi ?o?ari a sulhunta kowa ya yi ha?uri"
Babar Asiya kuwa kallon ruma kawai take, yadda take bayani da confidence, tana ciye-ciye kuma aka rasa mai tsawatar mata, sai ma nema ake a goyi bayan ruman.
DPO ya kuma kallon ruma ya ce "Matso nan kusa da ni 'ya ta, magana za mu yi"
"A'a, ba na zama a kusa da maza, Huzaifa ya ce idan ina zama a kusa da maza haihuwa zan yi, kuma korata za ayi daga gidanmu, idan aka koreni kuma ban san in da zani ba, rannan ma Allah ne ya taimakeni, da malam Habibu ya ta?a mini hannu ban haihu ba, mama ta ce lafiyata ?alau ba ni da ciki".
ba ?aramin dariya ruma ta basu ba, Aliyu ya dafe kai ya sunkuyar ?asa, ita ruma ba ta san rufi ba, ko zaka kasheta za ta fa?i gaskiya ne".
Duk yadda aka so yin sulhu, babar Asiya ta?i yarda.
DPO ya ce "Yanzu Madam, so ki ke a kai ku kotu ke da wannan yarinyar jikarki ko kuwa?"
Aliyu ya ce"Yalla?ai, ta ?irga abin data kashe, in sha Allah ba zai gagara ba sai a biyata"
Sai da ta ji haka hankalinta ya ?an kwanta, ta lissafa ku?i dubu talatin da biyar ta ce a biyata.
Aliyu ya ce"Yalla?ai a nema mana sassauci, wallahi yarinyar nan marainiya ce, kuma na gaya maka, tana da matsalar ?wa?walwa, ana kai ta shan magani, ana ta abin da za a ci ga karatun ta, ga rashin lafiya abun da yawa"
"Wallahi lafiyata ?alau, ni bana rashin lafiya sai zazza?i, ko gudawa, amma dai wataran idan raina ya ?aci sai na ji aljanuna sun tashi, ?arfina ya ?aru, idan na kama mutum na dun?ule hannu na dinga dukansa ko hmmm ba a magana, da na ce na daina dambe saboda mama ta daina fushi, ita Asiyar ce ta janyo muka yi fa?a".
Aliyu ya ce "Dalla rufewa mutane baki, Yalla?ai ba ta da cikakkiyar lafiya"
Headmaster ya ce "Amma ai mu da ku ka kawota makarantar baku gaya mana ba"
Babar Asiya ta dage, ba zata rage ko sisi ba, DPO ya ce zai biya dubu ashirin a aljihunsa, su ruma su biya dubu goma ".
Aliyu 'yan ku?in registration ?in sa ne da yake tarawa, haka ya biya, suka din ga bada ha?uri shi da ruma.
Duk da wannan abu, babar Asiya ba ta huce ba, dan ta so a zane ruma, sai dai bisa ga mamakinta yarinyar sa'ace da ita, babu wanda ya daketa, sai ma nasiha da DPO ya yi mata, yana cewa Aliyu "Ka ga irin wannan yaran, idan aka yi ha?uri, suna da ?oyayyiyar baiwa da Allah ya yi musu, da al'umma za iya amafana, ku yi ha?uri ku cigaba da kai ta Asibiti tana ganin likita, da sau?i tun da har tana iya zuwa makaranta, sannan ku kiyaye abin da zata din ga kallo".
"Kaii wallahi ni babu wani likita da nake gani, nifa lafiyata ?alau, wato Yaya Aliyu kana nufin ni mahaukaciya ce?" Harar ya watsa mata yana yi mata da?uwa suka cigaba da magana da DPO.
bayan sun fita daga ofishin, Headmaster ya ce ruma ta zauna a gida, sai wani satin sa duba su gani idan zasu iya bari ta cigaba da zuwa makarantar.
Tsalle ta yi tana fa?in Alhamdilillah.
Aliyu ya girgiza kai ya ce "Mara hankali kawai"
******
"Takawarka lafiya magajin galadima, Allah ya baka yawan rai, ya ja kwanan hajiya" ?aya daga cikin hadiman Mummy kenan, da ta ware ma?ogwaro, take ta zabga wa Adam kirari kamar za ta dungura, ma?ogwaronta ko zafi ba ya yi mata.
Hannu ya ?aga mata, ya cigaba da tafiya zuwa cikin falon.
Sanyi A.C ya cika ?akin, ga ?amshin turare da ya ha?u ya gauraye falon.
Risunawa ma'aikatan da ke cikin falon suke yi a gareshi, tamkar sun ga sarki.
Jinjina musu kai ya yi, ya nemi wuri ya zauna a ?aya daga cikin kujerun falon. Ya shafe a ?alla mintuna takwas, sannan ta fito cikin wata ha?a?iyar shadda sai ?aukar ido take yi.
Ta na ganin Adam, ta yalwata murmushin fuskarta ta ce "Hutawarka lafiya takawa, fatan ana lafiya? Kuma ina fatan ba a gaji da jirana ba, ina shiryawa ne"
Girgiza mata kai yayi ya ce "Barka da wannan lokacin"
"Yauwwa barka dai, an dawo lafiya ya ibada?"
"Alhamdilillah"
Ta sake yin murmushi sannan ta ce 'Ai har na fara shirin zuwa da kaina na kwashi gaisuwa, na ji labarin ka dawo, amma ba ka zo mun gaisa ba, kuma har aka yi bikin gidan Turaki aka gama ban ganka ba, ko jikin ne?"
Ya ?aga idanuwansa ya kalleta, amma bai bata amsa ba.
"Well, kun ha?u da Mahmud kuwa?, yazo gari shima ya kusa komawa ma, ya dawo lokacin kana saudiyya"
"Dama zuwa na yi na gaishe ki, and a gayawa su Fauziyya ba na son yawan fitar nan" yana kaiwa nan a maganarsa ya mi?e, ya fara takawa sannu a hankali.
Murmushi ta yi ta bi bayansa da kallo. "A zahiri mutum har mutum, amma ba?ini ba wanda ya san cikakken waye, kamar bil adama kamar kuma wani abu daban, da ni ki ke zancen Binta, sai na rabaki da komai sai na tabattar da na huce a kam abin da kk ka yi mini" ta yi maganar a hankali tana bin bayan takawa da kallo.
Ya kai tsakiyar falon, Mahmud ya bu?e ?ofar ya shigo, ganin junansu ya sanya suka yi turus, suna musayar kallo, kamar abokan gaban da suka yi shekara da shekaru ba su ha?u ba sai yau.
LITATTAFAN DA NA RUBUTA SUN HA?A DA.
ABDULJALAL (FREE BOOK)
A?IDATA (BOOK1 FREE 2 PAID)
WATA KISSAR SAI MATA (FREE)
WUTA A MASA?A (FREE)
RU?IN ?URUCIYA (BOOK1 FREE 2 PAID)
GABA DA GABANTA (1FREE 2 PAID)
?ANWAR MAZA (1FREE 2 PAID)
Mai bu?ata ni zai tuntu?a ta lambata Please, a din ga biya kan a karanta, in kin sai littafi baki fa?i ba, atleast kin taimaki marubuciyar da bata ?warin gwiwa ??
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban ha?a 1k subscribers a channel ?i na ba, anya akwai amana kuwa??*
Taku har kullum
Ayshercool
08081012143
[24/07, 7:43 pm] JAKADIYAR AREWA: *?ANWAR MAZA*
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHE?I TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*
*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban ha?a 1k subscribers a channel ?ina ba, anya akwai amana kuwa??*
Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro
Page 16
Kallon-kallo suka shiga yi wa juna, aka rasa wanda zai bawa wani hanya, Mahmud ne ya fara janye nasa idon ya wuce yana wani irin taku cike da rainin hankali, ya bawa Adam hanya.
Cikin hanzari Adam ya bar falon, yana jin wani abu yana tsikarar zuciyarsa.
Adam na fita, Mummy ta taso ta na fa?in "Mahmud ya haka, meyasa ba zaka tsaya ku gaisa ba, kamar ba ?an uwanka ba?"
Mahmud ya ce "Mummy, ni baki ga abin da ya yi mini ba? Lokacin da ya sauke girman kai ya du?a mini, wata?ila na fara saurarasa"
"Haba Mahmud, shi ne fa gaba da kai, ya zaka ce haka? ni fa bana son ace ina ziga ka, kuma ko ba komai ya ci sunan mai martaba, ya cancanci ka girmama shi, kuma idan Allah ya sanya sarautarmu ta dawo gidan nan, ka san shi ne magajin babanku, shi zai zama galadima tun da shi ne babba"
Ya dubi Mummy ya ce "Ni wata sarauta ko wani abu makamancin haka bai dameni ba, a na?ashi sarki ma gaba ?aya, wannan shi ta shafa, look Mummy, a bar wannan zancen ni bani da lokacinsa, bari na je na karya" yana gama maganar ya wuceta, ya na bada baya, Mummy ta yi murmushi ta ce "Haryanzu ina wasana yadda nake so, Mahmud dole na ?arsa maka za?in mulki da ?aunar sarauta, sannan kuma azo a rasa sarautar gaba ?aya mu je zuwa".
****
Aliyu suna tafe a hanya, yana ta yiwa ruma fa?a.
"Dan ubanki ku?in makaranta na, na registration na fara tarawa, yanzu kin saka na kwashe na bayar a banza, ban ci ba ban sha ba, dan ma Allah ya sanya DPO ya biya mafi yawa daga ku?in. Saboda ba ki da mutunci ina kareki ki na ?aryata ni, ni dama na ?yaleta ta yi miki shegen duka".
Ta waro ido ta ce "Kaii, idan ta sumar da ni fa?"
"Ai gara ta sumar da ke ?in, tun da ke dai har abada ba kya hankali, wai ki ka karya 'yar mutane saboda tsabar kanki ba da?i"
"To ba kai ne ka ce mini mahaukaciya ba, wai ana kai ni asibiti"
"To meye marabarki da mara hankalin? Zaki gane kurenki ne, bari mu je gidan sai na daki ku?ina" har suka isa gida, ruma ba ta sake cewa komai ba.
Mama na ganin Aliyu tare da ruma sun dawo, ta fito daga ?aki ta na tambayar ko lafiya?
Ruma ta ?an sosa kai tana kallon Aliyu.
"Zaki dai na kallona ko sai na tsokane idon? Sai ki yi mata bayanin abin da ki ka yi ai".
Ruma ta kalli mama, kamar zata yi kuka ta ce "Wallahi mama tsautsayi ne"
"Tsautsayin me? Me ki ka aikata kuma?" Ruma ta yi tsilla-tsilla da ido.
"Ba zaki gaya mata ba"
"Mama, da wasa fa na gwada irin na wrestling ?in nan, shi ne wata ta karye"
A ?an hasale mama ta ce "Kai ka gaya mini abin da ta yi mana, ka tsaya ka na mini wasa da hankali".
Aliyu ya yiwa mama bayanin abin da ruma ta aikata, da yadda suka yi, zuwansu police station yanzu.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ka shiga lamarina, Allah ka dubeni a kan halin wannan yarinyar".
"Mama dan Allah ki yi ha?uri ba zan sake ba, ita ta fara tsokanata na rama, ban san zata karye ba wallahi"
Mama ta dube ta ta ce "In dai kece, ba zaki canza hali ba, yanzu ruma har ta kai ki ga zuwa police station ruma, kaf yaran nan yayyenki babu wanda ya ta?a zuwa wurin 'yan sanda, sai ke ruma ko? Allah ya yi miki magani, ki je ki yi ta yi kar ki fasa" mama na gama maganar ta shige ?aki ta bar ruma a wurin.
Ruma ta kalli Aliyu ta ce "Kai baka da rufin asiri, wallahi da yaya usy ne zai rufa mini asiri, amma na fuskanci da kai da Yasir, da Huzaifa baku ta?a rufa mini asiri ba, ?iris ku ke jira .....
"Dalla rufe mini baki, tun ban daki ku?ina a jikinki ba, dubu gomar nan ta tsaye mini, ni Wallahi da ma ?yaleki na yi su yi miki duk abin da suka ga dama" ?ata fuska ta yi, ta bi bayan mama, sai dai mama sam ta?i kulata, wanda hakan ba ?aramin tayar wa ruma hankali yake ba.
Wunin yau gaba ?aya aka rasa mai saurara ruma, duk wanda ta yiwa magana sai ya hantareta gaba ?aya haushin abin da ta yi suke ji.
"Hmm huzaifa ni fa Allah ne ya taimake ni, da matar cewa ta yi sai ta dakeni, ka ganta kuwa, ?atuwace sosai da sosai fa, a kan benci ta zauna, kaga hannun ta a cure da nama, idan ta dakeni ai ji zan kamar an buga mini guduma"
Usman ya ce "Sai na zubar da ha?oranki, ba zaki nutsu ba ko?, ki ke cigaba sa kwatanta yadda take, ina ma Alin ya bar ta ci ubanki, ke ban da rashin kan gado, kawai ki je ki karya 'yar mutane saboda tsabar wauta ta yi miki yawa, sai ka ce wata rainon ga?a-ga?a?"
Aliyu ya ce "Kai ba ka san abin takaicin ba ma, har da wani cewa ai aljanunta ne suka tashi, ba a hayyacinta ta daki yarinyar ba, tsabar cin kai"
Mama ta ce "Ba ku ne ku ke zigata ta ?auko magana, ku ka ce kun tsaya mata, dole ta yi abin da ta ga dama ai, kuma daga yau duk wasu tashoshi na wrestling a gidan nan sai an sauke mini su, an daina kallon sa a gidan nan, kai kallon ma sai an daina"
Ruma ta waro ido ta ce "Mama, shikenan sai na daina ganin saurayina na wrestling"
Usman ya ce "Au ke har wani saurayi ne da ke a wrestling ?in?"
"Eh mana, ba ka san shi bane, Huzaifa ya ma sunan sa, ?an tuna mini, idan na ganshi har wani da?i nake ji".
Huzaifa ya ce "Ke ki ka san shi ni ban san shi ba"
Yasir yayi tsaki ya ce "Wallahi Mama mi bamu go ahead, mu yi wa yarinyar nan ru?iyya ni da Huzaifa, mu samo tsumangiya in cu?a mata jikinta in ha?a da ayar Allah wallahi dolen aljanun na ta su magantu"
"Wallahi ni ba ni da aljanu sai raina ya ?aci, kuma na sha tabara da ayatul kursiyyu, na fi ?arfin aljani da makiri ko tsunburbura na fi ?arfinta"
"Ke dalla ware, ai ke kin fi tsunburburar ma rashin ji" suka din ga caccakar ruka kamar zasu daketa.
Ita damuwarta a kan mai sunana Baba ne, hukuncin da zai ?auka a kan ta, na abin da ta aikata, sai ta ji bai ce komai ba ma, yayi shiru kamar bai san me aka yi ba.
***
Tsaye yake a bakin wardrobe ?in, yana ?arewa kayan ciki kallo kamar ba nasa ba, ya saka hannu da nufin ya ?auko kaya, hannunsa a sauka a kan koriyar alkyabbarsa.
Kamar ya na jin tsoron Alkyabbar, ya zarota ya na kallonta.
*Sarki mai koriyar alkyabba a dawo lafiya, ka ?anani a kan dokinka ko ka bani kyautar doki*
Shiru ya ?an yi ya na tunani, ta yaya zai ji murya ?aya a mabanbantan wurare, kuma haryanzu bai kai ga ganin fuskar wacece ba, gashi a duk lokacin da zai ji muryar, sai ta kira shi da sarki!.
Ajiye Alkyabbar ya yi, ya ?auko wata dark blue ?in suit, ya shirya a cikinsu ya ?auki jakarsa ya fita.
A ?aki ya tarar da Ammi tana sallar walaha, ya zauna ya jira ta idar.
Ta idar ta kammala Adduointa, sannan ta kalli Adam ta ce "Barka da wannan lokaci takawa".
Yayi murmushi ya ce "Barkanki Ammi, zan wuce ne"
Cikin tausayawa ta kalleshi ta ce "Ka na ganin babu matsala, zaka iya zuwa aikin?"
"Babu wata matsala in sha Allah"
"To matso na yi maka addu'a" ba musu ya matsa kusa sa Ammi, ya dur?uso mata da kansa, ta ?ora hannunta na dama a kan nasa, ta dinga kwararo masa Adduoi.
Wata irin nutsuwa ya din ga ji ta na ratsa shi, ya lumshe idonsa, sai da ta idar, sannan ya ri?e hannun ya sumbaci hannun ya ce "Allah ya ja zamanin giwar Galadima, ya baki yawan rai, Allah ya ji?an Galadima"
Murmushi ta yi, tare da jin maganar har cikin ran ta ta ce "Amin takawa, Ubangiji Allah ya tsare" ya mi?e yana fa?in Amin, ya bar ?akin.
***
Tun da abin nan ya faru, an kai ruwa rana sosai, kan malaman su ruma su yarda ta cigaba da zuwa makarantar, bisa sharu?ai sannan ruma ta cigaba da zuwa makarantar.
Tun baya da aka yi sulhu a police station, duk ranar juma'a sai mama ta aika wani ya tasa ruma a gaba sun je duba Asiya, sun kai wani abu, amma kullum babar Asiya babu godiyar Allah, kullum suka je sai ta yi complain, ita kuma ruma kan su taho,