Showing 102001 words to 105000 words out of 182697 words
shi har ya rakota gida a garin su Gwaggo.
Kallonsa take, amma ya kawar da kai kamar bai ta?a ganin ruma ba, ya basu jakar, shima suka bashi wata jakar ya hau babur ?in aka bar wurin da shi. Tunani ta shiga yi a kan abubuwan da ya gaya mata, da kuma tunanin meye ala?arsa da wannan mutanen? Kenan duk shiri ne?" Idonta ya sauka a kan lambar dake jikin jakar, sak irin lambar jakar da aka nuna mata bullet a ciki lokacin da za su zo katsina!
Guntun tsaki ta ja, a lokacin da ihun wani mutum ya dawo da ita hayyacinta, kan ta gano dalilin da ya sanya mutumin yake ihun, sai ganin abu ta yi a jikinta kamar an watso ruwa, jinin mutumin ya ?ata su an kashe shi.
Gaban ruma ne ya tsananta fa?uwa, ta ma rasa wani halin yakamata ta shiga, tashin hankali ko kuma fargaba, ga jikinta babu da?i, ta fara fidda rai da samun mafita.
A hankali ta tashi zaune, ta ?arasa gaban wanda ya kashe mutumin, ta kalleshi ta ce "Dan Allah nima ka kasheni"
"Saboda me zan kasheki?"
"Na gaji da zaman wurin nan, dan Allah ku kasheni nima" tayi maganar cikin magiya.
Ya kwashe da dariya ya ce "Ai ke zaki yi mana amfani, ko zamu kasheki sai mun koya miki hankali tukuna, dan ba zaki ta?a barin hannunmu ba, an jaddada mana mu kula da ke, bakinki ba shi da linzami, ko mun kar?i ku?in fansarki kashe ki zamu yi".
"Idan kuma baku kar?a ba fa?" Ta tambayeshi.
Ya bata amsa da "Nan ma kasheki zamu yi"
"To ku kashe ni, dan ba wanda zai baku ku?in fansata, bamu da ku?i talakawa ne mu"
Dariya yayi, ya cigaba da busa sigari, ya share ruma.
***
"Daddy, ina ganin kamar yadda nace ka bar komai a hannuna, komai ya kankama, kawai mu cigaba da abin da muka saka a gaba"
Senator usman wakili ya girgiza kai ya ce "Ni fa haryanzu a raina ban gama gamsuwa da shirin nan naka ba Khalifa"
Khalifa ya gyara zama ya ce "Please Daddy, ka yarda da ni, ba zan baka kunya ba kamar yadda na yi maka al?awari zan cika, Ni dai na riga na saka rai, bana son damar ta wuce ni".
"Ni kaina ba zan so damar ta wuce mu ba Khalifa, amma yaron nan yana da taurin kai da nacin tsiya, bana tunanin zai ?yalemu, ina matu?ar jin tsoron kar ya tona mana asiri"
Khalifa ya ?an girgiza kai ya ce "Amma daddy, sauran members ?in naku ma sun san abin da ake ciki?"
"Sun sani sarai, abin da nake tunani, akwai masu bashi goyon baya da ha?in kai a kan ya kawo ?arshena, ba wannan ne ya fi ?aga mini hankali ba, ina tsoron ya banka?o mu, dan ko last week na ji yana Abuja ku san kwanansa bakwai a can".
Cikin damuwa da tashin hankali Khalifa ya ce "To yanzu shikenan daddy, babu wani abun yi?"
Usman wakili ya kwashe da dariya ya ce "Abun yi kai, ka zuba ido kawai yaro, babu wani abu da zai iya, muna da wani shiri a ?asa".
"Allah daddy, shirin menene?"
"Kar ka damu, idan ya tabatta za ka gani, kaima ka je ka cigaba da naka ?o?arin zan gani idan zaka iya zama magajina"
Khalifa ya yi murmushi ya ce "To shikenan daddy, ba ka da matsala da ni"
***
Iman ce zaune a falo, an saka mata lalle ja, tana ta kwa?e fuska za ta yi kuka, wai ita ta gaji ammi sai mita take ta ce "Aikuwa kina tashi sai ranki ya ?aci, ku kamar ba mata ba mutum yayi ta fama da ku a kan ku dinga ado".
"Ammi fitsari fa nake ji" tayi maganar a shagwa?e.
"Yi a nan a wanke".
"Mhmm ammi zan yi kuka fa ya matseni".
"Ki bari na zo na sameki a wurin nan kin cire lallen nan, ki ga yadda zan yi da ke".
Jabir ne yayi sallama, Ammi ta amsa ya ?arasa cikin falon yana kallon iman.
Kan nan nata babu ?an kwali, gashin kanta sai ?aukar ido yake ya sha mai, ta tufke shi. Ha?e rai ta yi ta kawar da kai, ya zauna suka gaisa da Ammi, daga nan ya hau zuba kamar an kunna shi, amma hankalinsa ba akan hirar da suke take ba, a kan iman take da ta basar kamar ba ta san da zamansa a wurin ba.
Ganin ba shi da niyyar tashi ne ya sanya Iman tashi, dama a iya hannu aka saka mata lallen, ta wuce ?akinta.
Ko da ta koma ?akin zama tayi tai shiru, tana tunanin irin balahirar da jabir zai jefata a ciki muddin ya ce yana sonta, kuma yadda yake da ammi babu abin da zai hana ammin amsawa, dan kamar ?a shima ta ?auke shi.
Baba uwani ce ta yi wa ammi ?arya a kan zata je ta dawo, ammi ta bata izinin fita.
Tana fita ba ta tsaya ko ina ba, sai harabar gidan ta tabbatar da babu wanda ya ganta ta yi wuf ta fa?a sashin Mummy, ta ?arauniyar hanyar da ta saba bi.
A ?aki ta iske Mummy, Mummy ta dubeta cikin mamaki ta ce "Uwani, me ki ka shigo yi nan da yammacin nan sai an ganki".
"Allah ya huci zuciyarki uwar ?akina, Allah ya baki yawan rai, wani labari ne nake tafe da shi, ban sani ba ko zai yi daidai da abin da ki ke son ji ba".
Mummy ta numfasa ta ce "Ina jinki".
"Dama wani al'amari nake ta sanyawa ido, in tabattar da shi, amma ina hasashena yana daf da zama gaske, Jabir naku na gidan Galadima mai ci a yanzu, kamar shi ne yake sinsina iman, akwai alamun yana daf da cewa yana sonta".
Wani uban tsaki Mummy ta ja, "To ni ta ina hakan ya shafeni, ni abin da na saka ki ki yi mini kenan? Ki saka mini ido ki kawo mini labari a kan abin da ya shafi ahalin gidan nan kin kawo mini maganar bare wadda ko gashi ba ta da shi a cikin gidan nan, ni ina ruwana na saka ki aikin samo mini maganin da suke yi wa wancan uban ciwon Adam amfani da shi, amma haryanzu shiru kin tsaya kawo mini shirme"
Baba uwani ta du?a ta ce "Tuba nake, Allah ya huci zuciyarki, Allah ya sanyaya ruhinki".
"Tashi ki bani wuri, kar ki sake zuwa in da nake idan har baki kawo mini abun da na ce ba".
"In Allah ya yarda ba zan dawo ba sai da sa?onki, tuba nake".
Kwanki goma kenan da sace ruma, amma babu wani labari a kan ta, tun mai sunan Baba yana buga waya ko da wani labari, har mama ta ce yayi ha?uri ya daina kiran wayar.
Shi kansa dagaci ba yadda bai yi ba ayi sulhu, su fa?i abin da suke so a basu su sako wanda suka kama, amma suka ce ba zasu bayar ba, yayi musu maganar rumaisa amma suka ce su ba zasu iya gane wata yarinya da suka ?auka a gidansa ba.
Ruma kuwa sai gwada musu halin take na azabar taurin kai da rashin kunya, wataran ta yi borin amma sun ?i su kasheta kamar yadda take fata, sannan suka fara yi mata horon yunwa, basu cigaba da takurata a kan sai ta bayar da lambar wanda za a kira a gidansu ba, suka ?yaleta sai dai tana ganin azaba, idan ta ishesu da rashin mutunci, da kan bindiga suke dukanta.
Duk jikinta yayi tsami, ta fita hayyacinta kamar ba ita ba, ga rashin lafiya da take ta fama, wasu ko ba a kashe su ba wahala ce take kashe su a wurin, ruma ta fara sanya ran ita ma wahalar ce zata yi ajalinta.
Tun ruma na iya addu'a har ta fara sarewa, tayi kukan ta kira maman har ta ha?ura ta zubawa sarautar Allah ido.
Tana nan kwance kamar matacciya, ta ji wani irin ?amshin turare mai da?in gaske ya gauraye wurin.
Wata mata ce take kuka, amma kamar iyayi matar take a cikin kukan, ruma ta ?ago da ?yar ta kalli matar.
Tsohon ciki ne a jikin matar, duk da ruma ba ta san kan ciki ba, amma yadda cikin matar yayi girma kana gani ka san ta kusa haihuwa, matar na sanye da wani irin farin leshi mai ?aukar ido da hankali, mai ?auke da golden a jiki, hannunta zuwa kunnenta duk gold ne. Kai da gani ka san ba a wahala take ba, gata fara sol kamar ba ta shiga rana, sai kuka take ?afarta na ta zubar da jini tana haki.
"Rufe mana baki, ko mu harbeki a ciki" suka yi mata tsawa toshe bakinta ta yi da hannunta ta zauna tana kuka, tana ?arewa wurin da taken kallo.
Tausayinta ne ya kama rumaisa, ita wannan ?aton cikin na matar ne yafi ba ta tausayi. Ita kuma ko a ina suka ?aukota oho?.
Fatar matar duk tayi bur?un-bur?un, tayi jaa, alamar ?wari duk sun cijeta a hanya kan su ?araso.
Ayshercool.
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
?? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*
*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*
*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*
*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*.
Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
https://youtube.com/@CoolhausaNovels?si=Uv_ZJT91QMMuaNxG
Ku yi subscribing YouTube channel ?in mu domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.
Cikin ?arfin hali da kuka, matar ta ce "Dan Allah ku yi ha?uri, ku tausaya mini halin da nake ciki, ku sallameni, ko dan halin da nake ciki, cikina saura kwanaki ka?an na shiga wata tara, dan girman Allah ko nawa ku ke so ku kira gidanmu, za su baku ku sake ni".
"Ke ki rufe mana baki, ke zaki gaya mana abin da zamu yi?"
"Ba abin da zaku yi nake gaya muku ba, taimaka mini zaku yi, dan Allah ku duba halin da nake ciki"
Banza suka yi da ita suka cigaba da abin da ya dame su.
Ruma tana fama da kanta, amma sai bin matar take da kallo, ?arshen tausayi matar ta bata. Galibin wa?anda aka ?auko ruma da su, da wa?anda ta tarar an sallami wasu, wasu kuma an kashe su, sannan kuma kusan kullum akwai wanda mutanen za su kawo.
"Ki yi ha?uri ki daina kuka, ki yi addu'a" ruma tayi maganar cikin sanyin jiki.
Matar ta kalli ruma ta share hawayenta, ta ce "To, Allah ya ku?utar da mu, sun kashe mini direbana ma, ya iyalinsa za su ji?" Tayi maganar cikin kuka.
Ruma a ranta ta ce "Lallai wannan 'yar gata ce, har direba ne da ke"
A haka dare yayi, matar nan na ta kuka, abinka da farar fata ta koma jawur saboda kuka.
Suna nan a zube a wurin kamar shara, ga wata irin iska da ake yi mai sanyin gaske, ga yunwa na damun ruma ga ciwo, dare ya tsala ruma ta kwanta ta takure, saboda yadda sanyi ya takura mata. Matar nan kuwa tana zaune tana cigaba da aikin kuka, gaba ?aya a tsorace take da wurin sai waige-waige take, ita ma tana sake dun?ule jikinta saboda sanyin da take ji.
Idon ruma biyu tana kallon matar, a hankali ta matsa kusa da ruma zata kwanta a ?asa, saboda ta gaji da zaman ga ?an cikinta ya dun?ule mata wuri guda, cikinta yayi mata babu da?i, hannunta ne ya ta?a na ruma, ta ji yadda jikin ruma ya ?au zafi sosai, ta sake kai hannunta goshin rumaisa ta ji kamar an kunna wuta. Ta ?an jijjiga ruma amma ba ta motsa ba.
Ta cire ?ankwalin kanta ta rufawa ruma a jikinta, ta kwanta ta mi?e ?afafuwanta, sai dai ba aje ko ina ba, matar ta fara tari da atishawa wanda hakan ba ya rasa nasaba da sanyin da yayi mata yawa.
***
Katafaren falo ne mai girman gaske, kai kace wata fadar ce, saboda girma da tsaruwar falon, Hajiya Jamila ce zaune a kan wani lallausan carfet a ?asa, yayin da wani babban mutum ke zaune a kan kujera.
"Ina jinki Jamila, ina fatan dai ba wata matsalar ba ce?"
Ta sake du?awa ta ce "Allah ya ja kwanan mai girman wambai, matsala kam ba za a rasata ba".
"To Ubangiji Allah ya warware mana, meke faruwa?"
"Allah ya taimake ka, tatsuniyar gizo dai ba ta wuce ?o?i, ?arar giwa na kawo maka" sai kuma ta yi shiru.
Ya ce "Ina jinki".
"Allah ya baka yawan rai, na rasa gane in da ta dosa, ban san menene a ranta game da ni da yarana ba, 'ya'yanta ne manya, nawa ?anana ko da kishi a tsakanin mu, ai bai kamata zumuncin yaranmu ya ta?u ba, shikenan ina son ganin su Nusaiba amma ba sa zuwa in da nake, shi kansa mai babban suna sai ya shafe wata bai taka in da nake ba, wataran tamkar zai dakeni, na rasa irin wannan abu. yaranmu ai abu ?aya ne a ganina, amma sam yaran nan ban san kallon me suke yi mini ba, gaisuwa sai sun ga dama suke yi mini, mussaman wannan buzuwar yarinyar ni na gaji da irin wannan zaman da muke yi" ta ?arasa maganar cikin damuwa.
Wambai ransa ya ?aci ya ce "Shi takawan da kansa yake wannan rashin albarkar? Aikuwa albasa ba ta yi halin ruwa ba, haka ya canza hali? Har galadima mai ci yana batun zai yi murabus, mun fara tattaunawa a kan akwai yiwuwar a dawo muku da sarautarku, tun da ya kawo ?arfi, kuma shi galadima babu lafiya, ina daf da kai maganar ga mai martaba, to a haka za a bashi mulkin yana wannan rashin ?a'ar?"
Gaban Mummy ne ya fa?i, jin batun wambai na cewa za a dawo da sarauta gidansu a bawa Adam.
"Allah ya baka yawan rai, ni ba ziga ba, kuma ba wai ina kushewa bane ba, amma takawa ai ba zai iya jagoranci ba, ya fiye zafin zuciya da saurin fushi, abu ka?an idan su Fauziyya suka yi masa ba ka ga cin mutunci ba, kuma kar ka manta bashi da cikakkiyar lafiya, larurar nan da yayi tun yana yaro haryanzu fa tana tashi, ai gara a bawa mahamud duk da shi ma da sauran ?uruciya a kansa, ko a barwa Jabir kawai"
Cikin mamaki wambai ya ce "Kina nufin haryanzu takawa bai warke ba, amma ta ja bakinta tayi shiru balle a cigaba da nema masa magani? Meke damun Binta ne?"
"To ban sani ba idan ka shiga lamarin ko a samu mafita, amma takawa bai dace da sarautar nan ba ba zai iya ba, gara Mahmud amma Mahmud haryanzu hankalinsa da saura, ai gara a bawa Jabir, idan yayi murabus shine yakamata ya gaje shi"
Wambai ya ce "Wannan ba huruminki bane ba, sai abin da muka yanke, tashi kije zamu san abun yi".
Mummy ta du?a ta ce "Allah ya baka yawan rai, a huta lafiya" ta tashi ta bar gidan.
***
Mai sunan Baba ne yayi rigingine yana kallon saman roofing, zuciyarsa sai bugawa take yi, yana ji a ransa da ya