Showing 54001 words to 57000 words out of 182697 words

Chapter 19 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22384

sai ta aikata wani abun da za ta sake tunzarata tayi ta masifa.
A haka duk suka ce sun daina zuwa, yau mama ta ce dan Allah mai sunan Baba ya saka ruma a gaba su je.
Tun da Allah ya sa babar Asiya ta yi arba da fuskar mai sunan baba, ta shiga hankalinta, ko maganar kirki ta kasa sai kame-kame.
Tun da suka gaisa, ya bata abin da zai bata, ya ce ruma ta tashi su tafi, ko yaya mai jiki bai ce ba balle ya ce Allah ya kyauta.

suka taho hanya, ruma a nutse take babu tsokana da hauma-hauma, saboda kura ta san gidan mai babban sanda.
da suka zo bakin layin su, cikin girmamawa ruma ta kalli mai sunan Baba ta ce "Mai sunan Baba, mama ta ce na taho mata da kayan miya a wurin Hudu"

Ya kalleta ya ce "Idan kin ga dama, ki tsaya hauma-hauma da neman magana a hanya, zaki zo ki sameni".

"In sha Allah ba zan yi ba"

Ganin da mutane a wurin Hudu, ya sanya ruma ta tsaya ta na jira, sai dai kan ya kawo kanta, ta ?au wu?a ta din ga daddatsa masa kabewa bai sani ba.

Da ta gaji ta ce "Malam hudu ka sallameni mana"

Ya ce "Yi ha?uri na fara sallamar matan aure, su da zasu ?ora girki"

Ruma ta yamutsa fuska ta ce "To da me matan auren suka fini? Nima fa watarana matar auren nan ce"

Yayi murmushi ya ce "Eh, amma dai yanzu ?waila ce, Allah ya nuna mana kin zama matar aure ruma"

Ta ha?e rai ta ce "Gaskiya malam Hudu ka daina gaya mini wannan kalmar ta watsewa, ?waila fa iskanci ne"

?an bu?e baki yayi ya na kallonta, sai kuma ya ce "To Allah ya baki ha?uri" sai da ta bawa mutanen wurin dariya.

Can ta kalli Hudu, ta kalli lafcecen billensa kamar an yi masa da gatari ta ce "Malam Hudu, na da?e da tambayar nan a zuciyata wai meyasa aka yi maka bille?"

Yayi murmushi ya ce "Delu billen mahauta ne"

"To amma dai da wu?a aka yi maka ko?"

Ya ce "A'a, aska ce, billen gado ne na mahauta"

"To kai baka gaji ku?i ba sai bille, da babanku ya mutu sai aka raba muku billen?"

"Ke na gaji da wannan wula?ancin naki, mai zan baki?" Ruma ta mi?a masa ku?i, ta yi masa bayanin abun da zai bata, ya sallameta ta tafi gida.

Da ta je gida, ta ha?a kayan miyan, ta gyara su ta tafi kai marka?e.

****
Tsaye take a harabar Hotel, tana sanye da doguwar riga ja, ta na?e kanta da jan mayafi, fuskarta sanye da tabarau da kuma takunkumin fuska, dan haka idan ba wanda yayi mata cikakken sani ba, ba yadda za ayi ka ganeta.
Wayarta ta ?auko ta kira wata lamba, ta kara a kunnenta, a ?an hasake ta ce "Gani nazo ka na ina?"

"Room A7, Vip" ta ajiye wayara, ta shiga cikin hotel ?in, babu wanda ta tambaya da kanta ta gano ?akin, ta tsaya a bakin ?ofa, ta kuma kiran wayar "Gani a ?ofar ?akin" ta fa?a a ta?aice.

Wani mutum ne ya bu?e ?ofar ?akin ya le?o ya ce "Ke ce ba?uwar yalla?ai?"

"Kai ka san wani Yalla?ai, ka je ka gaya masa gani na zo"

"Ok, to dama cewa ya yi a shigo da ke"

"Ba zan shigo ba, idan ya matsu ya fito idan kuma ba a matse yake ba zan yi tafiyata, bana son jira".

Ya ?an yi jimm ya ce "Amma kamar maganar ki ta yi tsauri"

A fusace ta ce "Kai ka san wacece ni kuwa? Na yi mai wuyar ai da na zo nan, idan ba zai fito ba zan tafi"

Juyawa mutumin ya yi ya koma cikin ?akin, babu da?ewa sai ga wani mutumin ya fito, shi ma fuskarsa rufe da takunkumi.

"Ki shigo mana, zuwa bai yi miki wahala ba sai shigowa?"

"Ba zan shigo ba, ka gaya mini koma menene a nan ina jin ka"

Ya ce "Well, mu je ?asa to, sai mu yi magana"

Tare suka sauka ?asa, suka samu wuri suka zauna, ya dubeta ya ce "To sauke takunkumin mana"

"Ba zan sauke ba, wai tukuna kai wayene naga kamar ka na ?o?arin raina mini hankali"

Murmushi ya yi, ya sauke takunkumin fuskarsa ya ce "Khalifa senator usman, na san kin sanni kuma kina jin sunana, kuma kin san me nake nema"

Ajiyar zuciya ta yi, ta sauke na ta takunkumin ta ce "Dama kai ne? To Meyasa ka ke nema na?"

"Samha kenan, kin san ita kasuwar muradi babu in da ba ta kai mutum, ba wani abu ne ya sa nake neman ki ba, sai dan mu ha?a hannu na taimake ki, ki taimake ni. Ban sani ba ko baki sani ba, amma na san kin san Adam, Adam ya na barazana ga mutunci da rayuwar mahaifina, da kuma ni kaina da career ta, dan haka nake son ki taimakeni na kai shi ?asa, zan baki ku?i ko nawa ki ke bukata" yayi maganar yana tsareta da ido.

Ta cire gilashin fuskarta, ta dube shi ta ce "Da ka tashi binciken ba ka binciko da cewa, Adam ba ?an uwana ne ba kawai, shi ne mutumin da nake so, kuma nake muradin aure"

?an waro ido ya yi ya ce "Kuma!"

"?warai kuwa, sannan kar ka manta, ni 'ya ce da na fito daga gidan sarauta mafi daraja a nahiyar Afirka, sarautar Kano, dan haka kar ka yi zaton zaka ru?eni da ku?i, kuma kar ka sake nemana"

Khalifa ya ce "A'a Samha, kar ki yi gaggawa, ki yi tunani dai"

"Babu wani tunani da zan yi" ta tashi ta mayar da tabaranta, ta na ?o?arin tafiya, Khalifa ya sha gabanta ya ce"Samha ki na abu kamar ba wayayyiya ba, ki rubuta ki ajiye, za ki neme ni da kanki a nan gaba"

Ba ta kuma tanka masa ba, ta ra?a shi ta wuce.

***
Abdallah ya na ta wanke kayan mama tare da na ruma, mama kuma tana aikace-aikacenta, ruma tana ta yanka salak, sai ta ajiye wu?ar ta ri?e ha?a ta ce "Mama, kin san wani abu?"

"A'a"

"Ba kin ce mini mutane ta baki suke haihuwa ba?"

Mama ta ce "Eh"

"To wallahi akuyoyi ta ?uwawu suke haihuwa, ta wurin kashinsu in gaya miki, ?azu da na kai marka?e na gani a gidan"

Abdallah ya ce "An zo wurin"

Mama ta yi tsuru ta rasa me zata gaya wa ruma.

"Wallahi mama da gaske nake, ta wurin kashi suke haihuwa, akuyar ta din ga kuka, baki ga abin ?yama ba, na tsura mata ido, ta bani tausayi, Allah ya taimaki mutane ta baki suke haihuwa, idan ka haihu ta wurin kashi, ai idan ka na ji kashi sai dai ya zubo, dan wurin ba zai rufu ba"

Mama ta share ruma, ba ta ce mata uffan ba, hakan bai sanya ruman ta gaji ba ta kuma cewa "Mama kaji ma fa ta wurin kashinsu suke yin ?wai, to Meyasa mutane suke haihuwa ta baki, na ga dai baki ?arami ne".

A ?ule mama ta ce "Ke ki ?yaleni, idan na kuma aiken ki kai marka?e, ki ka kai gidan sai na zane miki jikinki, ita ma saboda wauta ta bari ki ke kallon haihuwar akuya"

Ruma ta yi shiru ta sunkuyar da kai, Abdallah kuwa kamar ya bushe da dariya, ganin yadda mama ta hasala, gashi ba abin kayi wa ruma bayani ba, ka na gaya mata abin da kan ta bai ?auka ba, zata kuma gangamo maka wata maganar.

Ko da dare yayi, ruma ta na shirin kwanciya barci, ta ce "Mama, dan Allah ki tasheni na yi sallar dare, zan ro?i Allah abubuwa da yawa"

Mama ta ce "To, Allah ya sa silar shiriyar kenan"

Ruma ta kwanta ta ji da?in katifar, bacci ya fara ?aukarta, ta ce "Mama ko na baki sallahun Addu'ar ne, ina ga ba yau ba, ba zan iya tashi ba, ki yi mini addu'a Allah ya sa na samu saurayi nima na din ga zance, 'yan ajinmu na islamiyya su yi ta bayar da labari, ni kuma ban san me ake ji a zancen nan ba, amma dan Allah kar ki ro?o mini mummuna mama"

Mama kawai ta cigaba da abin da take, ruma ta gama surutanta, bacci yayi awon gaba da ita.

Da safe kowa yana ta azamar ya kammala abin da zai yi da wuri ya fita, ruma kuwa sai cin abinci take sannu a hankali ta na murmushi.

Abdallah ya kalleta ya ce "Ke lafiyarki kuwa?"

Ta yi murmushi ta ce "Mama jiya kin yi mini addu'ar da na baki sallahu kuwa?"

"Ruma addu'a, ai kullum cikin yi muku nake"

Ruma ta sake murmushi ta ce "Abdallah ka san mafarkin me na yi yau?"

"A'a"

"Mafarki na yi wai ana bikina, kai ka ga angon mai kyau, kai Allah dai ya sa na yi tsayi ayi mini aure, dama Hudu mai kayan miya jiya ya?i sallamata, wai ni ba matar aure bace ba, ba ka ga angon ba, sai so nake na ?ago na kalleshi ina ta irin sunkuyar da kan nan na amare, ina...... Shiru ta yi da idonta ya sauka a cikin na mai sunan Baba a tsaye, ya na?e hnnayensa ya na kallonta.

AYSHERCOOL
08081012143
[26/07, 9:03 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban ha?a 1k subscribers a channel ?ina ba, anya akwai amana kuwa??*

Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.



P 17






*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHE?I TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban ha?a 1k subscribers a channel ?ina ba, anya akwai amana kuwa??*

Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.

*Ina yiwa 'yan uwa musulmi barka da shigowar, sabuwar shekara musulunci, Ubangiji Allah ya sada mu da alkhairan da yake cikinta, akasin haka kuma Allah ya iya mana*



Shiru ta yi ta kasa cigaba da maganar, ta zuba masa ido ta na jiran ta ji mai zai ce.
Ya tako a hankali ya zo gabanta ya tsuguna, ya na kallon idonta. Cikin sauri ta sunkuyar da kan ta ?asa, tana jin yadda abincin da ta ci ya tsaya mata a ?irji, ga wani irin ?ugi da cikinta yake yi mata saboda tsoro.

"Aure ko, shi ki ke so?" Da sauri ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Ki je ki dawo daga makarantar, za mu yi magana in dai aure ne baki da matsala, za'a aurar da ke tun da shi ki ke so" da sauri ta ?ago, ta kalleshi za ta yi magana, amma ya sanya yatsansa a kan le?ensa ya ce "Shhh, tashi ki wuce ki tafi makaranta"
Kamar wadda aka gayawa mummunan sa?o, jiki babu ?wari ta bar gidan ta tafi makaranta, sai dai kamar ta fa?i a hanya, dan jefa ?afarta kawai take yi, maganar mai sunan Baba ta tsaya mata da yawa.

***
Samha ce zaune a kan gado, hannunta ri?e da waya, ?aya hannun kuma tana wasa da gashin kanta, amma hankalinta ba a kan wayar ba, zancen zuci take yi.
?arar bu?e ?akin ne ya dawo da ita hayyacinta.
Fauziyya ce ta shigo, ta ajiye jakarta ta zauna a kan gadon, ta dubi Samha ta ce "Ke jiya ki ka shanya ni ina jiranki, amma ki ka ?i zuwa"
Samha ta ?an lumshe ido, ta bu?e tare da ajiyar zuciya.

"Ke wai meye haka ne?"

"Ke bari kawai"

"Ban gane in bari ba, kin san ba ma 'yar haka da ke, explain kawai madam"

Samha ta dubi Fauziyya ta ce "Jiya na je mun ha?u da gayen nan fa"

Fauziyya ta waro ido wace ta ce "Ki na da hankali kuwa? Mutumin da baki sani ba ki ka je wurin sa?"

"Eh tare da security na je, sai dai ban bari ya sani ba, kin san waye ma tukuna?"

"A'a, sai kin fa?a"

"Khalifa Usman wakili"

"Meye ha?inki da shi? Ko ya na ciki ne?"

Samha ta yi tsaki ta ce "Ke ba wannan ba, wai yayi bincike a kaina, so yake na taimaka masa ya kai takawa ?asa, saboda yana barazana ga feature ?in sa, da mahaifinsa"

Fauziyya ta zaro ido ta ce "Yaya Adam dai?"

"Shi fa"
"To me ki ka ce masa?"

"Fauza, kin san ina son Adam, ba zan goyi bayan a cutar da shi ba, dan haka nace masa ba zan iya ba, kar kuma ya sake nemana"

"To meyasa?"

"Fauza yayanki ne fa, kuma kin san abin da yake zuciyata game da takawa"

Fauziyya ta jinjina kai ta ce "Na san yayana ne, amma ke yanzu haryanzu ki na nan a kan bakanki kina son sa, ana barin halak dan kunya fa"

"Ke ki ka san ta, ita halak ?in, bari na shiga wanka" ta yi maganar tana mi?ewa.

?an shiru Fauziyya ta yi, ta fara zancen zuci 'wannan ai wata damar ce ga Mummy, tabbas Khalifa wakili zai yi wa mummy amfani' da hanzari Fauziyya ta tashi ta fice daga ?akin.

***
Yau wunin ranar ruma ba a hayyacinta take ba, duk ta rasa abin da yake yi mata da?i. Allah ya taimaketa mai sunan Baba bai dawo ba sai dare, tun da ya dawo ta rasa sauran nutsuwarta, tana jiran mai zai ce mata.
Sai da ya gama abin da yake, har ta kwanta ta fara bacci, ta ji ana dukan gefen katifarta.
Gabanta ne ya fa?i da ta yi tozali da shi, ta tashi zaune tana rarraba ido.
Da hannu yayi mata nuni da ta fito ta biyo shi.
Haka ta fito ya na gaba tana baya, zuwa tsakar gida.
Ya ja kujera ya zauna, ita kuma ta zauna a ?asa tana sunkuyar da kai.

"?ago ki kalleni" ya fa?a a kausashe, amma ta kasa ta sake sunkuyar da kanta ?asa.

"Aure ki ke so ko?" Nan ma ba magana sai girgiza kai.

"Shikenan, na fahimta na baki nan da kwana uku, ki kawo wanda zaki aura ?in, ranar juma'a in Allah ya kaimu sai a yi miki auren kowa ya huta"

Da sauri ta ?ago ta kalleshi, "Wallahi yaya ba haka nake nufi ba, wallahi ba aure nake so ba"

"?arya ki ke yi, baki da aiki sai zance da tambayoyin batsa, aure ki ke so"

"Wallahi a'a, ban san batsa nake tambaya ba"

"Na gaya miki, sai kin fito da miji, ranar juma'a za a ?aura miki aure"

"Wallahi bani da saurayi, saurayina bai sanni ba"

"A ina saurayin naki yake?"

"A cikin tv nake ganinsa, ?an wrestling ne, amma ban san a ina yake ba"

Mai sunan Baba ya kalleta ya ce "To tun da baki da saurayi, ni zan nemo miki, ba har da mafarki ana bikinki ba, to sa?onki ya isa za ayi abin da ki ke so"

"Wallahi yaya ba haka nake nufi ba"

"To ya ki ke nufi? Da kunnena fa na ji ki na cewa, ayi miki aure ayi addu'a ki yi tsawo ayi miki aure, tukuna ma me ake yi a auren da ki ke son auren?"

Cikin kuka ta ce "Wallahi ban sani ba"

Ya sake tsuke fuska ya ce "?arya ki ke yi, sai kin gaya mini ko na taka cikinki a wurin nan"

"Wallahi ban sani ba, 'yan ajinmu na islamiyya dai sun ce ana soyayya, kuma ina son in ga an sai mini kujeru da kuma sabuwar katifa"

"Wace irin soyayya?"

"Wallahi ban sani ba, na ji dai suna cewa, soyayya ta na da da?i, kuma ana soyayya idan an yi aure, shi ya sa nake son na yi saurayi na ji me ake a soyayyar, amma wallahi ba aure nake so ba".

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, yanzu dai tun da baki da saurayi, ni zan samo wanda nake so na aura miki, tashi ki je ki kwanta, ranar juma'a ?aurin aure"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan girman Allah ka yi ha?uri, manya ake yiwa aure ban da yara"

Cikin zafin rai ya ce "Ni zaki gayawa abin da zan yi, tashi ki bani wuri" jiki na rawa ta tafi ?aki, tare da fashewa da kuka.
Gaban mama ta je tana kuka ta ce "Mama dan Allah ki saka baki, wai aure mai sunan Baba zai yi mini"

"To ai haka ki ke so ruma, Allah ya sanya alkhairi, duk wanda ya za?a miki shikenan"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah mama ki saka baki, wallahi wasa nake yi, ni ba da gaske nake ba wallahi"

Mama ta ce "Maganarku ce ke da shi, babu ruwana, ni gafara nan na kwanta, gobe in Allah ya kaimu na tafi kasuwa na fara yi miki sayayya"

Mama tayi kwanciyarta ta bar ruma, kuka wiwi kamar ba gobe, haka ruma ta din ga yi, ?arshe a nan wurin bacci ya kwasheta.
Da safe kuwa wasan ?uya aka shiga yi tsakaninta da mai sunan Baba, ta?i yadda su ha?u, ko karyawa ta kasa yi, haka ta tafi makaranta.

Ruma fa gaba ?aya hankali ya tashi, ta rasa nutsuwa ko maganar kirki ba ta iya yi, tamkar wadda wani mummunan abu ke shirin faruwa da ita.
Mama tana kallonta, abinci sai dai ta cakala idan ta ?uya sai kuka, duk ta rasa sukuni.
Mama ta shiga ban?aki ta lalla?a ta ?au wayarta, ta kira Abubakar.
Yana ?agawa ta fashe masa da kuka, har sai da gabansa ya fa?i "Ruma, menene? Meyafaru?"

"Yaya, mai sunan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login