Showing 105001 words to 108000 words out of 182697 words
san direction ?in da zai nufa ya tarar da in da aka kai ruma da sai yaje ko da zai mutu a can, babban fatansa kar a lalata rayuwar ruma, gashi tun yana buga waya ya ji ya ake ciki, har ya ha?ura, dan babu wani labari mai da?i an doshi sati na biyu.
A hankali ya tashi ya bu?e ?ofar ?akin su ya fito tsakar gida, ya ga ?wan ?akin mama a kunne.
A hankali ya ?arasa ya tsaya ta window ?akinta ya le?a, mama na zaune ta ?aga hannayenta sama sai zubar da hawaye take yi.
Har ya shiga ?akin ba ta sani ba, ga furar da ya kawo mata da magariba ko ta?awa ba ta yi ba.
Motsin da ta ji ne ya sanya tayi saurin goge hawayen ta ce "Babana ba ka yi bacci ba?" Ya zauna a gabanta ya ?an kalleta ya ce "Ba ki sha furar ba, ki yi ha?uri ki daina zama da yunwa" ba ta iya ce masa komai ba sai kallonsa da take yi.
"In ?auko miki kofi ki sha?" Yayi maganar a hankali.
Hawaye ne ya cika idonta, ya mi?a hannu ya ?au kofin da ya kawo mata tun a lokacin, ya tsiyaya mata ya ce "Ki sha ko ka?an ne"
"Ba zan iya ba, na san ruma ba ta sha kamar wannan ba, kar su lalata mini 'ya babana na fara karaya" tayi maganar tana rushewa da kuka.
Kamar zai yi kukan shima, ya dake duk da yadda zuciyarsa take masa zafi.
Ya kai hannu yana goge mata hawayen ya ce "Duk abin da ya sameta dama Allah ya rubuta mata faruwar hakan, amma addu'armu tana tare da ita a duk in da take, damuwar ki kawai ta isa ta ?ara mana zullumi, ki kwanta ki huta ki cigaba da yi mata addu'ar.
Haka ya lalla?a mama ta kwanta, ba dan yana saka ran zata yi barci ba, sai dan fatan zuciyarta da ?wa?walwarta su samu salama.
Ya tashi cikin sanyin jiki, ya tafi ?akinsu, sai dai yana zuwa ya tarar da Huzaifa da Yasir sun ha?a kai da gwiwa suna ta uban kuka, Abubakar yana rarrashinsu, Abdallah ma ya ha?e kai da gwiwa usman kuwa ya zuba tagumi yana bin su da kallo, hannunsa ri?e da Alqur'ani, Aliyu ne kawai a kwance shima kuma ba bacci yake ba.
A hankali mai sunan Baba ya ja da baya, ya koma tsakar gida ya zauna, yama rasa ina zai saka kansa, shima da hali kukan zai yi, ya riga ya gama karaya.
Wayewar garin Allah, jikin ruma ya ?ara tsanani, sai rawar jiki take tana kwarara wani irin koren amai, ga kukan ciwon ciki da take yi duk ta fita hayyacinta.
Babu wanda ya damu da halin da take ciki, sai wannan matar, da a yanzu ba ta kanta take ba ta ruma take, saboda tausayin da take bata, sai sannu take yi mata, tun tana iya amsawa, har ta daina .
Cikin damuwa matar ta ce "Dan Allah bawan Allah ku taimaka ku kai yarinyar nan asibiti, kar ta mutu a haka, wallahi tana jin jiki sosai".
"Idan ta mutu meye naki? Ki ji da kanki mana uwar shishshigi" wani daga cikinsu ya bata amsa.
Cikin damuwa ta ce "Amma yarinya ce, dan Allah ku taimaka ko magani ku sai mata kar ta galabaita" banza suka yi mata suka cigaba da shaye-shayen su.
Kamar zata yi kuka, sai sannu take yi wa ruma tana dafa goshinta.
Ruma kuwa sai jujjuya kai take tana kiran sunan mama, duk ta fita kamar ta shekara tana ciwo.
Ko da rana ta ?an ?aga idon matar nan yayi ja, jikinta sai rawa yake saboda yunwa da take ji, ga ?an cikinta sai motsi yake, ga mura da ta addaba mata, amma tafi tausayin halin da rumaisa take.
Mijin iya ne wato dagaci a tsaye a tare da wannan dogon mutumin da su ruma suka ta?a ha?uwa da shi.
"Dan Allah dogo ku taimaka dan zatin Allah ku sako yarinyar nan, ko ku fa?i abin da za a baku, ba 'yar garin nan bace ba, a mayar da ita hannun ahalinta wallahi marainiya ce".
Dogo ya ce "Ni ba 'yan ?ungiyar mu ne suka kawo farmaki ba, kuma dama yarinyar na ga kanta yana rawa, tun da aka kai wannan lokacin ba su ce muku komai ba, wata?ila sun kasheta".
Cikin ki?ima dattijon ya girgiza kai ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan girman Allah tun da baka tabattar ba ka duba mini, wa?anda suka sako suka dawo gida, sun ce mana tana can a raye, dan girman Allah ka duba mini ka sanya baki a lamarin nan dan Allah"
"Ni ne zan saka bakin? Su sha tara ne fa suka yi aikin, ban maka wannan al?awarin ba, zan dai je na duba maka ko tana nan"
Dagaci ya ce "To shikenan, hakan ma na gode sosai"
***
Mummy na barin gidan wambai ta tafi gidan aminiyarta Hajiya Lubabatu, domin fesa mata labarin da ta guntso a gidan wambai.
Sam labarin bai yi wa Hajiya Lubabatu da?i ba.
Cikin hasala take cewa "Yanzu saboda tsabar wula?anci ace har yana shirin yin murabus amma ni ban sani ba".
"To da baki sani ba ni ba gashi na gaya miki ba, kuma shi yana can Germany ke kina nan ta ina zaki sani?"
"Amma shima wannan wamban ?asurgumin munafuki ne"
Waro ido mummy tayi ta ce "Rufa mana asiri kar wani ya ji mana, ke ai ba a wannan yakamata ki mayar da hankali ba, wai yana tunanin idan yayi murabus Adam za'a dawo wa da sarauta, sai dai na gyara miki hanya, dan na kunno mus wuta daga shi har uwarsa, dan sai da na tabattar da na fusata shi sosai a kansu. Yanzu dai ki nemi Jabir ku tattauna a kai, ku yi duk iya ?o?ari kar a rabaku da sarautar nan, Jabir ya gaji ubansa".
Hajiya Lubabatu ta ce "Ai fa?a ma ?ata baki ne, ai dan ubansa dole ya zo ya san abin yi, ya tare a gindin Adam sai ka ce ubansa".
"To wallahi ku san abun yi"
"Kar ki damu zaki ji ni" daga haka suka cigaba da hirarrakin su.
****
Kamar a bayi haka aka fara rabawa su ruma abinci, gurasa ?aya da ruwa ?aya, haka ake basu kullum, sai ranar da Allah ya kawo wannan mutumin, ya kan kawo mata abinci.
Wannan matar kuwa ko magana ta kasa saboda a wahale take, ji take kamar yunwa za ta kasheta.
Ko da aka bata gurasar nan ba ta tsaya komai ba, ta yi loma uku da ita, saboda azabar yunwar da take ji.
Ruma ta mi?a mata tata ta ce "Gashi ki ?ara da tawa ni na ?oshi".
Matar ta girgiza kai ta ce "A'a, ke ce baki da lafiya, ki daure ki ci, sai ki ji ?warin jikinki" ruma ta girgiza mata kai alamar a'a.
Matar ta saka gefen zaninta, ta sharewa ruma gumin da ta fara yi, saboda zazza?in jikinta ya sauka.
Mutumin da ya tinkaro su, ruma ta tsaya ta zubawa ido, sarai ta gane shi, mutumin da ya tare su yana tambayar wacece ita?
Kenan duk rabin mutanen garin abu ?aya suke yi kenan, satar mutane? Ta tanbayi kanta.
Suka gaisa da 'yan bindigar da suke wurin, ya yi musu magana da yaren da ruma ba ta iya ji.
Suka amsa masa, sannan ya shiga duba mutanen wurin, can ya nuno ruma, ya ce "Waccan ce".
?aton da ya ta?a dukan ruma da bakin bindiga ya tashi ya je ya dan?o ruma, kamar an yi cinikin kaza za a sayar haka ya fizgota, cikin dakiya ta fizge hannunta tana haki.
"Bata da lafiya ka yi mata a hankali" cewar matar da haryanzu ruma ba ta san sunanta ba.
"Ke idan baki kiyayeni ba, da shiga abin da ba a saka ki ba, wannan cikin naki ba zai hana na keta miki haddi ba a gaban jama'a ba, ki shiga hankalinki" daga haka ya mayar da idonsa kan ruma ya ce "Wannan ka ce ko?"
Dogo ya ce "Eh ita, ya ce ku taimaka ku fa?i abin da za'a bayar ku bayar da ita"
Ya ?ya?yace da dariya ya ce "Ai wannan ta zama tamu, ba zamu bayar da ita ba, ta ce sai da a kashe ta a wurin nan, dan haka muma muna so, su yi ha?uri su mance da ita, ko su fansheta da 'yan mata biyar, dan ni ba dan barde ya saka mini ido a kanta ba, da tuni ta zama yarinyata, kawai su je idan ubanta da sauransa yayi wani ?o?arin su haifi wata, wannan kuwa ba zamu bayar ba" yayi maganar yana ?o?arin rungumo ruma jikinsa.
Duk da yadda take a galaibaice, amma haka ta dun?ule hannu, ta ?irka masa duka a ciki.
Sak suka yi gaba ?aya suna kallonta, kamar wata zakanya, ta ja da baya ta dun?ule hannu "Wallahi idan ka kuma ta?ani sai na yi maka duka, ni ba 'yar iska bace ba, wane irin azzalumai ne ku? Ba kwa tausayinmu? Muma fa mutane ne kamar ku, kar Allah ya sa ku sake ni, ku kasheni ka kasheni idan kai ?an halak ne, ni a duniyar nan bana tsoron kowa sai Allah La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin" cikin tsananin ?warin gwiwa take maganar ga jikinta yana tsuma.
?are mata kallo ya yi, dudu tsayinta bai fi cikinsa ba, ko a shekaru baya tunanin tayi sha hu?u, ko maza surrender suke idan suka shigo hannu amma yarinya ?arama ta tsaya a gabansa tana wannan maganar.
"Dan Allah ka kashe yarinyar nan mu huta, sun hana a ta?ata sun ?i bari a saketa duk ta gallabi mutane, barde yana da matsala, kalli yadda take rashin mutunci fa" ?aya daga cikin mutanen yayi maganar yana gyara bindigarsa tare da saita ta a kan ruma.
"Kai kuma ban saka da kai ba, idan kuma na kasa da kai to ka kwashe, kuma in sha Allah ba zaku gama da duniya lafiya ba, sai kun ga abun da Allah zai yi muku".
Murmushi ?aton nan yayi cikin ?arfin hali, da jin kunyar dizgin da ruma ta masa ya ce "Idan ka kasheta a yanzu ai ta ci bulus, bari in gwada mata tabon da zata tafi lahira da shi, yau ko ni ko barde amma sai na nunawa yarinyar nan iyakarta, ni ki ka ce zaki daka ko?"
Ruma ta sake gyara tsayuwa ta ce "Wallahi kana ta?ani sai na ware ?wanjina, na rama kai ka san wace ruma kuwa?"
Dogo kuwa kamar soko haka ya ri?e hannu yana kallon ikon Allah.
Cikin magiya da kuka matar nan ta fara "Dan girman Allah kayi ha?uri, kar ka yi mata wani abun zafin ciwo ne"
Ruma ta ce "Ba wani zafin ciwo, a hankalina nake, wallahi ya ta?ani sai na rama, bana tsoron kowa a wurin nan"
Ya shammaci ruma ya dan?onta, zai fizge hijjabinta da yayi da?al-da?al saboda dau?a, ta ri?e hijjabin ta shiga kai masa duka da hannu ?aya tana wani gurnani da ihu kamar zakanya.
Ya saka kan bindiga ya ?wala mata a ka, ihu ta yi ta dur?ushe a wurin, sai ga jini ta hancinta.
Tasowa matar nan ta yi da ?yar ta nufo su, sai dai kan ta ?arasa ruma ta mi?e cikin tanga?i ta saka hannu ta dintsi ?asa da ciyayi, ta watsa masa a jikinsa, gaba ?aya suka taso suka yo kan su.
Ri?e ruma matar ta yi ta shiga tsakiya, ta ha?a hannayenta biyu cikin magiya ??
Ba ta yi maganar ba ya hanka?eta ?asa, ta fasa ihu jin kamar a take ?an cikinta zai fa?o, wani irin gigitaccen ciwo ya ?aure mararta zuwa ?afafuwanta.
Hankalin ruma ya koma kan matar, ta nufeta da sauri, amma mutumin nan ya kwarfeta, ya sanya bindiga ya dinga kwa?a mata, yana takata da ?afarsa, ihu take amma bakinta ya?i mutuwa "Idan ka isa azzalumi ka kasheni, kuma in sha Allah yadda Allah ya ku?utar da Annabi yunus a cikin kifi, ya ku?utar da Annabi Ibrahim daga cikin wuta, sai Allah ya ku?utar da mu, haka malamin mu ya ce mana mu yarda da Allah, in sha Allah zai saka mana" ya daka ya daka ya takata, ya sanya wani itace ya maka mata a baya. Wani irin ihu ta kuma yi, bakinta da hancinta na ta zubar da jini.
Tuni ta fara gani dishi-dishi, gadan gadan ya nufi ruma, ya dur?usa a kanta ya kama skirt ?in jikinta ya fara ja.
Ayshercool
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
?? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*
*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*
*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*
*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Salati da salallami mutanen wurin suka fara yi, duk rashin imanin mutanen, idan suka so keta wa haddi, suna barin idon mutanen da su, amma yana nema ya keta ruma a gaban su.
Wasu kuwa gani suke ruma ita ta janyo wa kanta, tsananin ciwon da matar nan ke ji bai hanata jan jikinta zuwa in da suke ba, ta ri?e rigarsa tana kuka tana girgiza masa kai. Wani irin mari ya kwa?a mata, da a take shatin yatsun sa suka bayyana a kan kuncinta.
?aya daga cikinsu ya zo ya saka hannu ya dinga jan matar a ?asa, ya wancakalar da ita a gefe.
Ya kuma dan?ar skirt ?in ruma, amma cikin ?arfin hali ta ri?e.
Ji yayi an fincikoshi ta baya, an kwa?a masa mari.
A gigice ya kalli wanda ya mare shi, barde ne wanda ruma ta bawa gya?a kuma yake kawo mata abinci wasu lokutan.
Wata irin ashar yayi masa, cikin ?araji ya ce "Me ka yi mata? Me na ce maka da aka kawo ta? Au har ka manta zaka karya yarjejeniyar?"
"Amma ai ka tsaya ka ji meyafaru kan kayi mini haka"
Cikin hasala barde ya ce "An maka ?in, wallahi da ka aikata abin da ka yi niyya, da sai na yi gunduwa-gunduwa da namanka a wurin nan" cikin huci ya nufi kan ruma, jikinta duk shaidar duka.
Ya ?agota ya girgiza ta, ta bu?e ido ta kalleshi, a hankali ta fizge hannunta daga nasa ta mirgina ta kwanta a gefe, tana kallon matar nan, da take ta sauke numfashi da ?yar, kamar sumammiya.
Bai sake ?o?arin ta?a ruma ba, ya ja ?aton nan yayi gefe da shi yana yi masa magana.
Ruma ba ta sake bi ta kansu ba, a hankali ta mirgina, ta ?arasa in da matar nan take kwance, tana numfarfashi, ruma ta ?ora hannunta a kan na matar, a hankali ta ji matar ta ri?e hannunta, ta sake matsawa jikin matar ita ma tana mayar da numfashi ba tare da wani ya tankawa wani a tsakanin ita da ita ba.
Dagaci kuwa tun da suka yi magana da dogo, a kan zai je ya bincika masa ruma, ya kira Aliyu ya sanar masa domin hankalinsu ya ?an kwanta, dan haka suka cigaba da dakon abin da dagacin zai ce masu, gashi Aliyu ya riga ya gaya musu yadda suka yi dagaci, dan haka mama kullum sai ta