Showing 30001 words to 33000 words out of 182697 words
?in da take yi saboda azabar omo.
Aka jima, ya ha?a wuta a dutsen guga, ta hau goge masa ita.
Abdallah ne ya dawo, ya tarar da ruma ta du?ufa tana guga.
Ya tsaya yana ?o?arin gane me take gogewa.
"Wai meye wannan ki ke gogewa haka?"
Ta ?ago ta kalleshi ta ce "Kayan yaya Umar ne, na ga ya sa?ale su a ?aki, na san wankewa zai yi, shi ne na wanke masa nake goge masa".
Abdallah ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ruma da me ki ka wanke shaddar nan haka?"
"To za ayi wanki ba da ruwa da omo bane?"
"Uban waye ya ce miki ana wanke shadda da omo?" Ai suna cikin maganar ruma ta ?one gaban rigar.
Dafe kai ta yi ta ce "Innalillahi, na shiga uku, Abdallah ya zan yi na ?ona masa shadda?"
Abdallah ya ce "Maganinki shegen karambani, kya san mai zaki gaya masa"
Hannu ruma ta ?ora a ka ta dinga kuka, dan ta san yau kashinta ya bushe, sai yadda Allah ya yi da ita.
Haka mama ta dawo ta tarar da ita, tana ta uban kuka, Abdallah ya gaya mata abin da ta aikata.
Cikin kuka ruma ta ce "Dan Allah mama ki bashi ha?uri, yau na san na mutu wallahi, dan Allah mama kar ki bari ya dakeni ko ya saka ni punishing".
"Ba ruwana, ai nima ba jin maganata ki ke yi ba".
Abu kamar wasa, har bayan la'asar ruma ba ta ci ko Abincin rana ba, sai kuka take yi.
Huzaifa ya ce "Ni ne mutum na farko da zai sanar da mai sunan Baba wannan ta?argaza da ki ka aikata masa"
Duk da mama a ?ule take da ita a kan laifin da ta yi mata jiya, amma hakan bai hanata saka ruma ta ci abinci ba, amma ruma ta?i ci sai aikin kuka. Ita kanta mama na tausayawa ruma hukuncin da zata fuskanta a wurin Umar idan ya dawo ya tarar da ?arna da ta aikata masa, sai dai ita ta janyo kanta, rashin jin ta ya yi yawa.
Mai sunan Baba bai dawo ba sai bayan sallar magariba, tun da ya shigo ta sake takurewa tana uban kuka.
Ya dube ta, cikin kakkausar muryarsa ya ce "Kukan me ki ke yi?"
Huzaifa ya gyara zama, ya wassafa masa ?arnar da ta aikata.
Duk da babu isasshen haske a tsakar gidan, ta tsorata da kallon da ya yi mata.
"Dan Allah yaya ka yi ha?uri, ba a son raina na aikata hakan ba, wallahi kawai niyyata na baka mamaki, na wanke maka na goge maka ban san haka abin zai zama ba"
Kalmar ta bashi mamaki sai da ta saka Aliyu dariya, ya ce "Lallai kin bashi mamaki kam"
Yadda ta firgice ne, ya sanya Yasir ya ce "Dan Allah yaya ka yi ha?uri, kuskure ne, tun da tsautsayin nan ya faru ba ta ci Abinci ba"
"Zaka ?au hukuncin da zan yi mata kenan?" Yayi maganar ba tare da ya kalli Yasir ba.
Yasir ya ce "Eh ni ka hukunta ni a madadinta, a tsorace take"
A ?an tsawace ya ce "Tashi ki ?auko mini kayan na gani"
Sumi-sumi ta tashi ta je ta ?auko kayan, ta mi?a masa.
Ya kar?a ya duba, gaba ?aya kayan sun tashi daga aiki, jikinta sai rawa yake yi.
"Tun da ki ke na ta?a saka ki wanki?" Ta girgiza kai.
"To Meyasa ki ka wanke nawa kayan?"
"So nake nima na yi abin arziki, ban zaci zai zama na tsiya ba"
Ya girgiza kai ya ce "Zubo mini Abinci" ta tashi tana ta tsuma, ta je ta zubo abinci ta kawo masa tana kallonsa.
Ya kar?i Abincin, ya ajiye a gabanta ya ce "Ci Abinci"
Fuska duk hawaye ta ce "Dan Allah ba zaka saka ni kama kunne ba?"
Ya girgiza mata kai ya ce "Ba zan saka ki ba" yayi maganar yana ?ebo Abincin ya kai bakinta.
"To ka ha?ura?" Ya jinjina mata kai alamar eh.
"To dan Allah ka yi ha?uri, tsautsayi ne"
"To, ci abinci" sai a lokacin ta ji ranta ya yi sanyi, har ta fara cin abinci, babu wanda bai yi mamakin yadda mai sunan Baba ya ?yale ruma ba, basu ta?a kawo zai rabu da ita ba.
Sai da ta ci ta ?oshi sannan ta ce "Me sunan Baba"
"Na'am"
'Dan Allah ka yi ha?uri, zan kar?i ku?ina na wurin mama sai na saya maka wata "murmushin gefen baki ya yi ya ce 'To Shikenan".
Bayan yaya Umar ya fita, Huzaifa ya lalla?a ya bi ruma ?aki yana cewa "Ruma, wace addu'a ki ka yiwa mai sunan Baba ya ?yale ki ne? Zo ki gaya mini"
Usman ya ce "Wallahi nima na yi mamaki duk ?arnar nan da ta yi masa ya ?yaleta"
Babu wanda ta kula a cikinsu ta kwanta tana yiwa Allah godiya.
Hidindimun Salla suka wuce, aka koma makaranta, ruma ta koma makaranta, sai dai fafur ta ?i zaman ajinsu, wai malaminsu baya son ta, wani malam Habibu ?an mai makarantar ta li?ewa, duk ajin da za shi ya yi ?ari sai ta bishi, gashi ta ma?alewa Auwal, yaya sama yaya ?asa haka take kiransa saboda yana sayen tsami gaye da goriba ya bata.
Yanzu ma 'yan ajin su Yasir suna jiran malam Habibu ya zo yayi musu ?arin Alqur'ani, sai ga shi ya shigo shi da ruma.
Yasir yana ganinta ya tsuke fuska, dan tun wancan hansfreen da ta yi masa a gida, ya hanata zuwa ajinsu, amma sai gata.
Malam Habibu ya zauna, ya ce ta shiga cikin mata ta zauna. Aikuwa ta shiga ta zauna, ta nutsu kamar gaske aka yi ?arin nan aka idar.
Aka zo kowa yana biyawa, aka zo kan Yasir shi ma ya biya, sai cewa ta yi 'Inyee ashe ka na ja, hmm da ba ka iya ba wallahi da sai na fa?a a gida, in ce kai ma baka iya karatu ba"
Dariya 'yan ajin suka hau yi suna kallon Yasir, ya sunkuyar da kai yayi mata shiru.
Kowa ya gama biyawa, ruma ta ce "Malam nima zan karanta"
Ya ce "To bisimillah"
Abun mamaki sai ga ruma ta karanta shafi guda, duk da tana yi ana cin gyaranta, amma ta kai shafi guda, ba ?aramin mamaki ta bawa Yasir ba, yarinyar da ta ce ita gejinta aya biyu kawai.
?ari biyar malam Habibu ya bata, tare da jinjina mata, dan babu wanda bai san ruma ba ta ja ba.
Da ya kammala ?arin ya ce ta ta so su tafi, amma ta kalli yadda Yasir ya ha?e rai ta ce "Malam ni ka bar ni a nan ajin"
Malam Habibu ya ce "To shikenan, duk malamin da ya zo ace masa ruma ajiyata ce, sanna ba ruwan kowa da ita kar a takura mata"
Suka ce to.
Yasir kuwa kamar ya zo ya rufeta da duka, dan ba zata ta?a zama shiru ba.
Ruma ta shige cikin 'yan mata, suna hirarsu, ita kuma tana shan farar ?asarta, amma duk tana jin me suke fa?a.
Yau har aka tashi tana ajin su Yasir, sai da aka tashi ta bar ajin.
Ta je ta samu tsohuwar da take sayar da kayan yara a a ?ofar makarantar, ya titsiyeta wai sai ta bata farar ?asa kyauta.
Duk shegen son ku?i irin na iya, sai da ta bawa ruma farar ?asarar nan, saboda shegen surutun ta da nacin tsiya.
Ta kar?i farar ?asarta ta yi gida, haryanzu makarantar nan ba ta da ?awaye, a cewarta ?aliban ba su yi mata ba, kuma ba komai bane su ?aliban sa'aninta kowanne ya mayar da hankali a kan karatunsa ne, ita kuwa ruma 'yar abi yarima a sha ki?a ce.
Tun da ta je gida take tafa hannu tana masifa, "Wallahi an mini laifi a gidan nan, kuma sai kowa ya hallara zan fa?i me aka yi mini" jin kowa ya shareta ya ?i kulata ya sanya ta ce "Mama yanzu dan Allah abin da ake yi mini a gidan nan ya dace?"
"Da aka yi miki me?"
"Mama a gabanki 'ya'yanki suke ce mini ?waila, amma baki ta?a hana su ba"
Mama ta dubeta ta yi murmushi cikin manyance ta ce "To ba ?wailar bace ba?"
Ruma ta bu?e baki ta ce "Au mama har da ke?"
Aliyu ya ce "To meye dan an ce miki ?waila, ai ?wailar ce"
Ruma ta ce "Kutt, ?waila fa wadda ba ta da nono kenan?"
Aliyu ya ce "Innalillahi wannan gingimemiyar maganar fa"
Mama ta ce "ke waye ya gaya miki haka?"
"'yan ajin su Yasir ne suke fa?a, matan nan ina jin su da kunnen nan nawa, sun zaci bana jin su"
Mama ta ce "To ke nonon ne da ke da ba za ace miki ?waila ba?"
"Mama gori dai ake yi mini kenan? Sai in je wurin Mai furar nan na bakin hanya, na sayo nonon, na zo na ?ulla a leda na dinga sakawa" cike da takaici mama take bin ruma da kallo, ta ma rasa me zata ce mata. Usman yana tsakar gida, sai ?ya?yata dariya yake ?asa-?asa lamarin ?anwar nan ta su sai Addu'a kawai.
Aliyu ya ce"Ke da ki ke ?anwar maza, me zaki yi da wannan abun? Ki yi zamanki a haka ai sai kin fi kyau"
Ta ce "Kuma fa haka ne" ta cire rigar islamiyyar, daga ita sai vest, ta sinsina rigar ta kuma cewa "Mama, dan Allah yaushe zan fara warin hammata, ina son idan na cire riga na sansana na ji tana ?an warin nan da ?amashin turare "
"Fitar mini daga ?aki dan ubanki, shashasha mara al?ibla fita ki bar mini ?aki".
AYSHERCOOL
08081012143
[08/07, 4:58 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.
*A TAIMAKA AYI SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ?INA NA COOL HAUSA NOVELS, KO IN KOMA POSTING SAU ?AYA A SATI ??*
10
?an tsayawa ruma ta yi tana kallon mama, cikin sangarta ta ce "Mama wai me na yi to?"
"Ban sani ba fitar mini daga ?aki, mara kan gado, ni ba dan a gida na haifeki ba, cewa zan yi an canza mini 'ya, idan an yi gabas sai ki arta ki yi arewa, me ake da wani wari ban da rashin kan gado irin naki?"
Tsayawa ruma tayi tana kallon mama tana wasa da gashin kanta.
"Ba zaki fita ki bar mini ?aki ba, sai na taso kan ki?"
Fitar ta tsakar gida yayi dai-dai da shigowar Yasir, da shi da Huzaifa.
Yasir ya aika mata da wani irin mugun kallo ya ce "Me na ce miki game da zuwa Ajinmu?"
Ta murgu?a baki ta ce "Ni wurinka na zo, ai ba wurinka na zo ba, ni da malam Habibu muka zo"
"To uban me ya hana ki je ajin su Huzaifa?"
Huzaifa ya yi caraf ya ce "Wallahi ta zo mana aji, sai na mata dukan tsiya, ta zo ?in ta gani"
Hararsu ta dinga yi, tana cewa wallahi sai ta je.
Bayan Huzaifa ya canza kaya, ya shiga ?akin mama ya ?au jakarta.
Ruma ta ?aga murya ta ce "Mama, ga Huzaifa nan ya ?aukar miki jaka"
Ya ce "To munafuka"
"Wallahi ni ba munafuka ba ce, mama Huzaifa zai satar miki ku?i"
Huzaifa ya ce "Mama aron naira ?ari zan ?auka"
Mama ta ce "Ajiye mini jakata, ba zan baka aron ba, idan ka ?aukar mini ku?i ba bani ka ke ba"
"Dan Allah mama ki bani, zan baki wallahi"
Daga kitchen mama ta ce "Ba zaka ajiye mini jaka ba sai na zo ?akin nan?"
"Mama wallahi bai ajiye miki ba"
A fusace Huzaifa ya ajiye jakara, yana yiwa ruma kallon banza, kamar ya kai mata duka haka ya fice.
Ruma ta ce "Dana sani na bar shi ya ?auka, nawa nake bin mama ba biyana take ba"
***
Yau za a rufe makarantar su ruma a tafi hutu, yau za ayi spelling B da aka bawa su ruma.
Sai bin malaminsu take tana ce masa ita fa sai an sakata a cikin masu spelling B.
Malamin ya ce "Ki kwantar da hankalinki, zamu san yadda za ayi".
Azabar nacin ruma sai da ya sanya aka sakata a cikin masu spelling B, amma aka ce kar ta yi magana.
?arshe dai ruma ce ta taimaki 'yan ajinsu, gaba ?aya kalmomin nan babu wanda ba ta haddace ba, ruma ta bawa malaman makarantar su da ?aliabai mamaki, dan ko bata takardar da aka yi, tsabar naci ne ya sanya a ka bata.
Ai kuwa ruma ta samu kyaututtuka sosai, karo na biyu a rayuwarta, da ta samu wani abun arziki a saboda harkar karatu.
Aka bata litattafai kaya guda, da kayan koyon karatu.
Ruma baki har kunne ta je gida, mama ta ganta da kaya ni?i-ni?i.
"Ke wannan kayan na menene?"
Ruma ta zubewa mama kayan ta ce "Mama, duk nawa ne a makaranta aka bani"
"Meyasa aka baki?"
"Wannan takardar da aka bani ce a makaranta, kowa ya ?i koya mini, na je na yi ta yi da kaina, shine fa aka yi yau na samu wannan kyautar"
Mama ta ce "Hmm, ai shikenan"
"Mama wai na ga kamar ba ki yadda da bayanin da na yi miki bane?"
"Eh to kusan hakan, dan abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa"
Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Mama wace gurguwar kuma?"
Cikin gajiya da halin ruma mama ta ce "Ki tashi ki cire uniform ki yi wanka"
Ruma ta tashi ta cire kayanta, ta ?ebi ruwa ta shiga wanka. Ta na tsaka da wankan, ta jiyo muryar Usman ya shigo, daga ban?akin ta bu?e murya ta ce "Yaya Usyy Albishirin ka"
"Ruma ban hanaki surutu a ban?aki ba?"
Ta ce 'yi ha?uri mama"
Ba dan ta gama wankan ba, cikin zumu?i ta fito daga wankan 'Yaya usman, bari na nuna maka wani abun mamaki"
Ba ta san a ya ta fito daga ban?akin ba, sai da mama ta daka mata tsawa, daga ita sai pant ta fito. Ta koma ta ?auko zani, sannan ta kwaso kyaututtukanta ta nunawa Usman.
Ya kalli ruma sannan ya kalli kayan ya ce "Ruma ban yarda da ke ba"
Ta ce "Saboda me?"
"Ina ki ka ga kwanyar da zaki yi wani abun arziki ke?" Tsuke fuska ta yi tana kallonsa ta ce "To me ka ke nufi?"
"?auko takardar da aka baki, na yi miki tambayoyi" ta mi?e ta je ta ?auko masa takardar ta mi?a masa.
Ga mamakinsa duk abin da ya tambayi ruma, sai ta bashi amsa daidai ko gyaranta ba ya ci.
Ya ajiye takardar, ya kalli ruma ya ce "Ni fa haryanzu mamaki nake, matar da take zuwa ta kusa da ta ?arshen aji, ita ta yi wannan ?o?arin"
Ruma ta yi murmushi sannan ta ce "Ikon Allah kenan, baku san haushin da nake ji idan aka ce mini da?i?iya ba, shi ya sa na dage na je na iya"
"Congratulations, ina ma zaki cigaba da dagewa da kin ga cigaba a rayuwarki"
Ta ta?e baki ta ce "A'a da wahala gaskiya, ka san ba?ar wahalar da na sha kan na iya wannan abun, dan a dai na ce mini da?i?iya daga wannan ba zan kuma ?aukar dala ba gammo ba"
Usman ya yi murmushi ya dafa kafa?arta ya ce "Haba ?ANWAR MAZA, rayuwa ce fa, kuma idan da rai da lafiya yanzu aka fara, kar ki sake ?arsawa ranki cewa akwai wani abu da zai gagareki komai wahalar sa, rayuwa sai da gwagwarmaya da fa?i tashi, musamman ga ?an talaka. Kar wani abu ya ?ara razana ki, ko ki yadda ke da?i?iya ce zaki iya komai kema"
Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Dan Allah da gaske Yaya Ussy?"
Ya jinjina mata kai ya ce "Sosai makuwa, ki dubi rayuwarmu a cikin gidan nan, tun baki da wayo, har zuwa yanzu a cikin gwagwarmaya muke, farincikinmu kawai ki ke gani, amma kowa akwai kalar ?alubalen da yake fuskanta, ki kalli mama ba ta yi karatu mai zurfi ba, amma ta cancanci a kirata jarumar uwa, ba lallai ki fuskanci me nake nufi ba a yanzu, amma ki saka maganganun nan a ranki akwai ranar da za su yi miki amfani. Amma ki tsaya a kan ?afafuwanki, ki fuskanci abin da yake baki tsoro, ke fa jaruma ce, bai kamata sunan da?i?iya ya biki ba"
Ruma ta ?an yi shiru sannan ta kalli Usman ta ce "Yaya Usy, in sha Allah zan dinga mayar da hankali na yi karatu sosai na daina wasa"
"Yauwwa ko ke fa, ai hakan ya fi deluwa"
"Kuma zan cigaba da ?o?ari, in zama mai ?arfi sosai, duk wanda ya tsokane ni, in yi masa dukan tsiya in farfasa masa baki da hanci, in kakkarya mutum"
Mama da take jin su ta ce "Ke kuma ba kya fatan ki girma ki yi hankali, sai rashin hankali ke ba kya fatan Allah ya shiryeki ki daina fa?ace-fa?acen banzan man a matsayinki na mace, fa?a ba na 'ya mace bane"
Ruma ta ce "A'a mama, gara ki bar ni na koyi ?arfi sosai"
"Sai kuma ki yi ai".
Usman ya kuma murmusawa ya ce "Ba irin wannan ?arfin ake magana ba, ?arfin zuciya da kaifin basira wurin sarrafa duk wata Matsala da za ta tinkaro ki, kar ki bari matsalolin ki su razana ki, ko sau ?aya kar ki bada wannan damar, ki turje ki dake ?alubale duk girmansa, ki yi gaba da gaba da shi"
Ruma ta ce "Mhmm, gashi dai hausa ka ke yi, amma bana gane me ka ke fa?a, sai na ji kamar ma wani yaren ka ke daban, ban wani gane me ka ke nufi ba"
"Ni ma na san ba zaki gane a yanzu ba shekarunki da hankalinki babu lallai ya kai, saboda ke a yanzu ba ki sa wata damuwa ko matsala. Tashi ki zubo mana Abinci mu ci" Ruma ta mi?e ta tafi kitchen.
Mama ta ce "Kai ma banda abinka, wannan zaka zaunar ka na wani gayawa wannan bayanan, me zata gane a ciki? Ita ban da wautarta da tambayoyin ta na rashin kan gado me ta sani?"
Usman ya ?an yi shiru sannan ya ce "Haka kurum mama ina jin tausayin yarinyar nan, jikina na bani za ta yi gwagwarmaya a rayuwa, gwagwarmaya a bugiren da ba zamu iya tsaya mata ba, ko yi mata wani taimako ba, gwagwarmayar da take bu?atar ta tsaya da ?afarta ta cimma nasara"
Mama ta ce "Tooo ikon Allah, to koma dai menene, ni dai addu'a kullum cikin yi muku ita nake, ba ku ka?ai ba, dukkan 'ya'yan muslmai baki daya, Ubangiji Allah ya shiga lamarinku, ya tsare gabanku da bayanku, ya kula da rayuwar ku"
"Amin mama, Allah ya ?ara