Showing 90001 words to 93000 words out of 182697 words

Chapter 31 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22419

san me nake nufi".

Nusaiba ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, na daina cigaba da aikin ki, zan je na ce masa bacci ki ke kawai"

Iman ta jinjina kai alamar to.

****
Tafe suke su uku, ruma na ta shan tsamiyar biri tana zubarwa a hanya, mayafinta a kafa?a. Su fuskarsu duk da hoda da kwalli, ruma kuwa tata yadda take haka take kamar namiji, kunneta babu ko ?an kunne.

"Kai ku tsaya" ruma tayi maganar tana kallon wata bishiyar mangwaro, 'yar gajeriya amma tayi 'ya'ya fal.

Suka kalli ruma suna son jin dalilin tsayar da su ?in.

"Mangwaro zan tsinka".

A ?an razane Zaliha ta ce "A'a ruma, a garin nan fa bakomai ake ta?awa ba, baki ga gonaki duk an yi girbi ba, amma ba a ?auka ba,masu garin ake jira su zo su yanke harajin da za a biya sannan a ?ebi amfanin gona, yanzu idan suka zo wucewa suka ganki, zaki saka mu a matsala.

"Suwaye masu garin?" Ta yi maganar cikin ko in kula.

Lawisa ta ce "Ke dai ki bari kawai ruma, ki bari idan muka je gida sai a saka a samo miki"

Ruma ta cire mayafinta, ta ?orawa lawisa a kafa?arta, ta nufi bishiyar nan, suna ?wala mata kira, amma ba ta tsaya ba, ta kama bishiya ta haye kamar buranya, hawan katanga da bishiya ba abu ne mai wahala a wurin ruma ba.

Ta na?e doguwar rigarta, ta tara mangwaron sannan ta saukko, su kuma suna ?asa suna jiranta cikin tsoro suna cewa ta sauko.

Bayan ta sauko ta kar?i mayafinta ta zuba a ciki, ta sa?o abunta tayi gaba ta ?yalesu.
Bin ruma suka yi da kallo, ta ci uwar ubansu a rashin ji, haka suka rufa mata baya suna kallonta.

Suna cikin tafiya suka ga ta saki hanya ta shiga wata gona, tarin masarar da aka jingine ta je ta fara ?auka.

"Innalillahi, dan Allah ruma kar ki janyo mana masifa, dan Allah ki fito mu tafi, duk wanda aka gani a gona bayan girbi ba a biya haraji ba kashe shi za ayi".

"Kisa kuma sai ka ce cinnaka, guda biyar kawai zan ?auka gasawa zan yi na ci"

Zaliha ta ce "Dan Allah ki fito kar su ganki".

"Wai suwaye ne? In sun ganni ba ruwanku ni ka?ai na ?auka" ta zuba masarar a mayafinta ta fito. Kamar suna tsoron ruma suka sake rufa mata baya suna zazzare ido.

Sun yi tafiya mai nisa sun kusa gida, suka ji ana musu magana "Ke daga ina ku ke?" Gaba ?aya suka tsaya suka waiwaya, wani dogon mutum ne a tsaye, sanye da rawani hannunsa saye a cikin tsummar rigarsa, ya ma dai fi kama da mahaukaci.

Ruma ta ?are masa kallo za ta yi gaba abinta.

"Ke ina magana zaki tafi?" Ya daka mata tsawa.

Cikin tsiwa da rainin hankali ruma ta ce "Haba babana ke fa ka ce mana, kuma na ga dai ba aikenmu ka yi..."

Da sauri zaliha ta ri?e hannun ruma ta ce wa mutumin "Dan Allah ka yi ha?uri, ba?uwa ce ne a garin".

"Ba?uwa amma mara tarbiyya ko? Ba ta san nan ina ne ba? Kuma ba ta iya ladabin yin magana da manya ba, Meye wannan ta ri?o?"

Ruma ta ja da baya ta ce "Nifa ban gane ba, me na yi maka zaka ce mini mara tarbiyya? Mangwaro ne da masara" tayi maganar tana bu?e masa mayafin.

"Waye ya baki izinin ?aukar masarar?"

Ruma da haushi ya fara kamata ta dake ta ce "Yi ha?uri ban san gonarka bace, idan yayana ya zo ?aukata daga birni zai baka ku?in masararka, ni na tafi sai kun taho" ta ?au kayanta tayi gaba.

Su kuwa jiki na rawa suka tsaya suna sauraren mutumin.

"Lallai dagaci, wato har da kawo ba?i marasa ?a'a ba tare da ya nemi izini ba, har su zo su karya mana doka, to zai gane kuskurensa da mu yake zancen, ku wuce ku tafi".

Da gudu suka tafi gida domin sanar da abin da yake faruwa.

Suka tarar da iya na tuhumar ruma ina ta samo wannan kayan, amma tayi shiru ta ?i magana.
Su zaliha ne suka kwashe komai suka gaya wa iya.

"Mun shiga uku ruma, ai mu garin nan ba a mana haka, a zaune muke ?ar?ashin umarnin 'yan bindiga, suke da garin, ki daina haka ba ruwanki da kowa, duk wanda ki ka gani a garin nan girmamashi to ba ruwansu da ke, amma idan ki ka yi musu rashin kunya sai su yi miki illa".

"To ku mayar da ni gidanmu mana, ni ba wanda ya isa yayi mini wani abu, dan ni ?anwar maza ce zane mutum yayyena za su yi. Kawai sai ya ce mini mara tarbiyya shi tarbiyyar ce ta saka yake yi wa mutane magana a haka, ni a kano kowa ya san ina girmama mutane raini ne ban so, ni na zata ma mahaukaci ne".

Iya ta kwantar da murya ta ce "To na ji, amma dai dan Allah ki kula, bari Alhaji ya shigo zai je ya basu ha?uri, 'yan bindiga ne sai su illataki, muma bin umarninsu ne ya sanya muke zaune lafiya"

Ruma ta ?an yi shiru sannan ta ce "Wai iya su waye 'yan bindigar nan?"

"'yan tayar da ?ayar baya ne, Allah ne kawai ya san meye a?idarsu"

Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Meye ?ayar baya kuma, sai ka ce wasu kifaye?"

"Ba zaki gane ba ko na yi miki bayani, amma dai bisa umarnin su muke zaune, sai abin da suka ce muke yi"

"To suma shugabanni ne za?arsu ake yi, na ji kin ce ba kwa komai sai da izininsu, ko 'yan sanda ne su?"

"Babu ?aya ruma, kawai dai ku yi ta mana addu'a, muna zaune ne dan kawai mun san ko mun bar nan ba in da zamu je, bamu da wurin zuwa"

?wa?walwa ruma ta shiga wani tunanin na daban, ba ta kuma cewa komai ba, ta shiga wata sabgar.

Tana missing ?in gida sosai, ga wayarta ta mutu ba caji tama barota cikin kaya a gidan gwaggo.

Kullum da safe cikin bata rubutu da banka mata haya?i ake a gidan, wai maganin tsarin jiki na baki maita da aljanu.
Ruma kuwa ta ce ita ba zata sha wani rubutu ba, warin tawadar nan amai zai sakata. A kwanaki biyu kacal ruma ta fara buwayarsu, saboda sai ?o?ari take sai ta aikata wani abu da zata tsokano mutanen nan.

Yau da yamma kasuwar ?auyen take ci, dan haka suka shirya su uku zasu tafi kasuwa, iya tayi ta jawa ruma kunne a kan rashin ji da kuma yi wa mutane tsiwa, sannan ta basu ku?i suka fita suka tafi.

Kasuwar ?auye ce dai, amma ta burge ruma sosai da sosai, ga kayan gargajiya nan kala-kala.
Sai dai abin da ya bata mamaki, yadda ta kan ga wasu mutane masu rufaffiyar fuska suna kaiwa suna komowa, hannayensu saye a cikin rigunan su.

Shagon wani mai awo suka shiga suka zauna, za su sai wake, da alama su lawisa sun san shi, sai hira suke. Suna cikin hirar wani mutum yayi sallama suka amsa masa, ya shigo ya zauna, bai ce musu komai ba, suma kuma ba wanda ya tanka masa.

Ruma ta ce "Ni fa hausar nan taku dariya take bani".

Mai awo ya ce "to hausar mu tafi da?i ai, na ji kamar hausar kanawa ki ke yi ko?"

"Eh mana, ni 'yar kano ce, hausarmu mai da?i, garinmu ma yafi naku kyau sosai da sosai"

Mai awon ya ce "Ai mu ma dan nan ?auye ne, amma garinmu yana da da?i da kyau".

Ruma ta yi dariya ta ce "Ba wani nan, garin naku da baku da iko da komai, wai sai an baku umarni mutum da kayansa, kano kuwa ba haka bane, abu idan naka ne naka ne kawai. Kuma ku ba damar ba?o ya zo sai a din ga tuhuma waye wannan, kano kuwa ba a haka?. Haka wani zan?alelen mutum kamar mahaukaci ya tsayar da mu yana tambaya wai wacece ni?"

Zaliha ta ?an daki cinyar ruma tana ?ifta mata ido, amma ruma ta?i shiru.

"Wai me awo suwaye masu yawon nan da rufaffiyar fuska kamar munafukai" a tare suka kalli ruma, sannan suka kalli mutumin nan na zaune.

"Ya naga kuna kallona kamar an ritsa mara gaskiya? Bawan Allah ko kai ka san su?" Ta yi maganar tana kallon mutumin

Ya girgiza kai ya ce "A'a, amma ina ga ko sune masu garin da ake fa?a".

"Wai sune 'yan ta'addan?"

Ya rausayar da kai ya ce "Wata?ila"

Ruma ta ce "Amma kuwa ba su kyauta ba, ba su yi wa kansu adalci ba, su dinga ?wacewa mutane kaya, nima fa da zamu zo garin nan a kan bindigogi na zo, ina 'yan ta'addan ne a mota ?aya muka hau da su"

Ya ?an waro ido ya ce "Haba dai, baki ji tsoro ba?"

Kamar ya kunna ruma, ta gyatta zama ta ce "Ni ban ji tsoro ba, a cikinsu fa wani har kaza ya sai mini, yayi kalar masu kirki, amma ban san meyasa suke kashe mutane ba, kullum a rediyon mama sai an ce sun kashe mutane, abun tausayi, ku yi ta Addu'a kuna musu nasiha, ko zasu daina".

Mutumin yayi murmushi ya ce "To shikenan, kuma kanawa ku tayamu da Addu'a, amma na yi mamaki da ki ka ce a kan bindigogi ki ka zo, kuma ba ki ji tsoro ba"

Ruma ta yi wani irin murmushi ta ce "Baka sanni bane ba, yayyena maza bakwai" ta yi maganar tana nuna masa da yatsunta.

Sannan ta ?ora da cewa "Ni ba komai ne yake bani tsoro ba, na ce musu dan Allah su bu?e mini in gani ko da gaske suke bindiga ce, kai ka ga yawan bindigar? Allah ya kyauta kawai" ta mi?e tsaye ta ce "Bari na je na sayo gya?a" tayi waje.

Lawisa ta yi ?asa da murya ta ce "Zaliha tashi mu gudu kar yarinyar nan ta ja a harbemu a tsakiyar kasuwar nan".

"Ya ya za ayi mu gudu mu barta?".

Mai awo ya ce "Ranka ya da?e ayi mata ha?uri ba?uwace kuma yarinya ce, ayi ha?uri dan Allah" mutumin bai ce komai ba ya cigaba da danna wata waya mai madannai.

Gaban mai gya?a marau ruma ta du?a, tana saya wani mutum ya wuce tare da bigeta da wani abu, kuma ko waiwayowa bai yi ba yayi gaba abunsa.

Da gudu ta tashi ta bishi "Malam ka bugeni, ba ka ji ba na ce ka bugeni fa"

Ya waiwayo yana kallon ruma.

"Ba ka ji ka buga mini wani abu a bayana, kuma ba ka bani ha?uri ba"

Ya sauke takunkumin fuskarsa ya ce "Ni ne zan baki ha?urin?"

"Eh mana, wani abu fa ka bugeni da shi a bayana, ai ka waiwayo ka bani ha?uri ko?"

Zai yin?ura kenan ya ji an dan?i hannunsa an ja shi. Wani mutum ne shima mai rufaffiyar fuska ya ri?e shi.

Cikin tsiwa ta ce "Bana yi wa manya Allah ya isa, amma wallahi ban yafe ba, Allah ya ha?aka da wanda yafi ?arfinka kaima ya ci zalinka"

Idon kowa ya dawo kan ruma, ita kuwa ko a jikinta, ta koma ta sai gya?arta da ruwan leda, ta koma shagon mai awo.
Ko da ta koma, ta bi su ta bawa kowa leda ?aya ta gy?a, har da wannan mutumin da ya shigo ya zauna.

Ta kalli mutumin ta ce "?an uwanmu kana da 'ya'ya?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Ta kuma bashi ?auri biyu ta ce "To ka kai musu wannan, ga ruwa ma na baka. Ku kuma ku tashi mu tafi, 'yan garin nan ba su da mutunci, wani ya bugeni da wani abu a baya, kuma ya?i bani ha?uri ni kuwa na masa Allah ya isa, kuma wallahi na koma gida sai na je na gaya wa 'yan sanda, abin da ske a garin nan da abin da na gani ana yi! Sai na fa?i komai"

Ayshercool.

*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*


Ba ta ji ko ?ar ba da ta yi maganar, ta ?au abubuwan da ta saya, mutumin nan ya bi ruma da kallo, har zata fita daga shagon ya ce "?awata yaushe zan zo kano na kawo miki ziyara, in ga Kanon da ake cewa ta fi garinmu kyau?"

Murmushi ta yi ta ce "Idan ka zo kano ka ce wurina ka zo sai yayyena sun na?a maka na jaki ni ma su karairayani, cewa za su yi kai saurayina ne, amma dai Kano tana da kyau sosai, sai watarana ?an uwanmu"

Ta yi waje, su lawisa suka bita kamar munafukai.

Jerin babura ne suka din ga shigowa cikin kasuwar ko ta ko ina, suna ?aukar mutanen nan masu rufaffiyar fuska suna barin cikin kasuwar.

Ruma ta ce "Zaliha wai wannan mutanen idan suka idan su ka bar nan ina suke tafiya a kan bauran nan?"

Jiki a sanyaye zaliha ta ce "Cikin daji suke tafiya, ruma mutumin nan fa na cikin rumfar nan shima fa sune, ?an uwansu ne" waro ido ruma ta yi ta ce "Haba dai? Amma nake hira da shi?".

"Shiyasa ake ce miki ki iya bakinki, kin zage sai zuba ki ke har da cewa zaki gaya wa 'yan sanda".

"To ba gara a gaya wa 'yan sandan ba, tun da ku tsoronsu ku ke ba za ku iya ba, ai taimakonku zan yi, ke nifa DPO ?in unguwarmu ma ya sanni, tun da na karya wata yarinya ya sanni, dan haka sai na je na gaya masa".

Lawisa ta ce "Ke waye ya ce miki aikin 'yan sanda ne?, sojoji ma fa ake turowa, amma haryanzu abu ya gagara mu samu tsaro "

Tunawa ta yi da batun da aka yi, na da sanin wasu daga jami'an tsaro ake zirga-zirga da makamai amma ba yadda suka iya.

?arar wani abu ruma ta ji, da bata ta?a jin sauti irinsa ba, sai gani tayi mutane suna gudu, mutumin da yake tafiya a kusa da su ya fa?i cikin jini.
Aka bu?ewa mutanen kasuwar wuta. Tuni ta nemi su lawisa ta rasa sun arta, ita kuwa ta kasa gudun, ta kasa gaba ta kasa baya, sai rungume kayan sayayyar ta da tayi tana rarraba ido, mutane sai fa?uwa suke cikin jini.

Ji ta yi an kama hannunta an ja ta da gudu, an bi ta bayan kasuwar da ita, ba ta san ko waye ba, sai da suka bar cikin kasuwar, sannan suka tsaya.
Mutumin da ya zauna a rumfar mai awo ne, sai dai shima a wannan karon fuskarsa a rufe take, da kayansa da kuma muryarsa ta gane shi ya ce mata "Yi sauri ki bar wurin nan, ki tafi gida" daga haka ya juya ya barta.

Ikon Allah ne ya kai ruma gida, dan ba ta ta?a ganin tashin hankali kamar wannan ba, mutane kwance a cikin jini an kashe su.

Ko da ta je gidan babu kowa, ta zube kayan hannunta a tsakar gida ta zauna, ta yi shiru tana cigaba da jiyo ?arar harbe-harbe sama-sama.

Ta yi kusan mintuna ashirin, sai ga iya da su lawisa sun shigo, da alama ita suka tafi nema.
A gigice iya ta ?araso in da ruma take tana fa?in "Rumaisa babu abin da ya sameki ko? Bari gobe in Allah ya kaimu da sassafe azo a mayar da ke, mutanen nan sun sake waiwayo mu, ina fatan babu abin da suka yi miki"

Ta kalli jikinta, ba abin da ya sameta sai dai jini duk ya ta?ata. Iya ta saka ruma ta yi wanka ta canza kaya.

Sai dai ruma ta kasa magana, dan ta tsorata da abin da ta gani, gawar mutane kwance a cikin jini.

Da ?yar ta iya cin abinci, ta nemi wuri ta kwanta, sai dai bacci ya gagari ruma sai tsananin zurfin tunani.

Ruma tana jiyo iya da sauran mutan gidan, suna mayar da zance da irin ?arnar da aka yi a harin na yau, a nan ta ji irin masifu da tashin hankalin da suka fuskanta a baya, wanda haryanzu suna kai.

Tun da Allah ya sa ruma ta bu?i ido, ba ta ta?a ganin tashin hankali kamar wannan ba.

****
Takawa jiki yayi kyau, ya daina jin abin da yake ji, ya cigaba da sabgoginsa a Abuja, sai dai duk yadda ya so ya gama abin da yake ya dawo kano abu ya gagara.
Tattaunawa ce ta musamman suka yi, ita ma tattaunawar sai dare suka yi ta, sai bayan sha biyun dare sannan suka gama, ya fito zai tafi masaukinsa, dan ko direban bai nema ba yau.

Ya biya wani restaurant ya ci abinci, sannan ya nufi makwanci. Tun safiyar yau yake fama da fargaba da ya rasa dalilinta. Yana tsaka da tu?i gabansa yayi wata irin mummunar fa?uwa gabansa ya fa?i, ?irjinsa yayi wani irin bugawa da sai da burki ya kusa ?wace masa a tsakiyar titi. Da ?yar yayi parkinh ya kifa kansa a kan sitiyari, ya dafe ?irjinsa sa hannu ?aya, yana jin yadda zuciyarsa ke tsananta bugu.

***
Gari yayi tsit kamar an yi ruwa an shanye, duk wannan balahira da ta faru har aka yi aka gama, babu jami'in tsaro ko ?aya da ya bayyana a wurin, sai da ?ura ta lafa wa?anda aka karkashe wa 'yan uwa, suka je suka ?ebo gawarwaki, aka yi musu sutura ana jiran gari ya waye a sallacesu, wasu gawarwakin ma ba a samu ?ebo su ba saboda tsoro.

Dare ya tsala sosai, farin wata ya haske gari, ko ?wa?w?waran motsin wani abu ba ka ji, ciki har da ?wari.

Idanunta tarwai, babu alamar bacci zai ?auketa ko da kuwa ?arawo ne. Daga can ?asa-?asa ta fara jiyo jiniyar babura suna kusantowa. Ta runtse idanunta tana hango yadda a abubuwa suka faru ?azu a kasuwa, sai dai ?arar baburan suka cigaba da kusantowa yana cika mata kunne.

Hannu ta saka ta toshe kunnuwanta, tare da sake rintse idanuwanta. Dan ?arar baburan na sake hasko mata abun da ya faru
Ba ta san iya adadin lokacin da ta kwashe a haka ba, ta sauke hannuwanta, iface-iface ta din ga jiyowa ana salatuttuka, hayaniya ta yi yawa a ilahirin kewayen gidan.

Muryar mijin iya ta jiyo yana fa?in "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mutanen nan sun sake dawowa, mai kuma suke nema da mu? Me suke bu?ata?"

Iya ma cikin kuka take salati tana "Allah kana gani, Allah bamu da wani gata sai kai, Allah ka duba mu".

Wani irin ihu da gurnani kunnuwan ruma suka jiyo mata, kai daga jin ihun ka san wadda take yi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login