Showing 156001 words to 159000 words out of 182697 words

Chapter 53 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22428

aisha yake hannunsu, dan haka za su yi miki tambayoyi ne" a take rumaisa ta ha?e rai, ta kawar da kanta gefe.

?aya daga cikin 'yan sandan ya ce "Baby girl, ki amsa mana tambayoyinmu, zai taimaka mana ?warai wurin binciko wanda suka yi garkuwa da ku".

Ruma ta zum?ura baki ta ce "Ni fa bana ri?e abubuwa, na manta komai, likita ya hana ayi mini zancensu"

"Ki yi ha?uri ki bamu ha?in kai, ba zancen su zamu yi miki ba, yaya aka yi aka sace ki? Yaya aka yi ki ka ha?u da aisha har ta baki jaririnta da ?ankwalinta?".

"Ni kawai sace ni aka yi, muka gamu da ita, ta bani yaron, na taho" yanayin yadda ta yi maganar zaka san ?arya take yi.

?an sandan ya sake nutsuwa ya ce "Ki yi ha?uri ki kwantar da hankalinki, a ina kuka ha?un da ita?"

Kawar da kanta gefe ta yi, irin idan ka gaji ka tashi ?in nan.
Duk yadda ya so lalla?a rumaisa sai da ta fara hasala shi, rarrashin duniya amma fafur ta ce ba ta san komai ba.
Mama ta yi kanta da zagi, Abubakar yana lalla?ata amma ta yi mursisi tana hawaye, ta ce ba ta san komai ba ita ta manta.

Mai sunan baba da tun ?azu yake jin su bai yi magana ba, sai yanzu ya tashi ya nufi gadonta, ya ture Abubakar shi ya zauna ya kalleta, ta sunkuyar da kai ?asa, cikin muryarsa mai razanar da ita ya ce "Kalleni" ta ?ago da ?yar ta kalleshi.

"Gaya musu abun da suka tambayeki" ta kallesu ?aya bayan ?aya sannan ta mayar da idonta kansa ta shiga girgiza masa kai.

Idonta ne ya cika da hawaye, amma ta kasa magana.

Mama ta ce "Ruma ba kya ji ana yi miki magana ne?".

Ammi ta ce "Ku bita a hankali, kar ku tsoratata".

"Ba zaki fa?a ba sai na saka sun saka miki sar?a sun tafi da ke, ana magana kina kallon mutane" yadda mai sunan baba yayi mata maganar cikin hargowa sai da ta tsorata, jikinta ya hau rawa, tana girgiza masa kai.

Ya sake kafeta da ido ya ce "Fa?i, komai ?acinsa da muninsa fa?i"

Cikin rauni idonta na zubar da hawaye ta ce "Bana son fa?a, bana son tunawa ne, labarin babu da?in ji, kuma babu da?in tunawa. Ta mutu!ta mutu! Ko sin ce sun kasheta? Ta mutu ne ba ta raye, kuma sun zo da mota sun ?auke ta tun a can, bana son tunawa, mutuwar anty aisha abu ne da ba zan manta ba, ta mutu! Ta mutu!! Ta mutu ku rabu da ni dan Allah tun da na gaya muku" ta yi maganar cikin hargowa tare da watso piliown kan gadon tana wani irin kuka, da sai da mai sunan baba ya rungumeta jikinsa a matu?ar sanyaye.

Takawa ta gani a tsaye a ?ofar ?akin, ya zuba mata ido da dukkanin nutsuwarsa, yana jin abun da take fa?a tamkar zubar dalma a tsakiyar zuciyarsa.

Ayshercool.
08081012143

*Littafin ku?i ne, a bani hakkina kan a karanta, ?500 ne via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143





Lumshe idonta ta yi, hawaye na tsiyaya daga idonta, mai sunan baba yana jin yadda zuciyarta ke bugawa da saurin gaske.

Duk wanda yake ?akin sai da yayi sak, cikin ammi ya ka?a yayi wani irin ?ugi, take ta fara fatan Allah ya sanya mafarki take ba gaske bane ba.

A hankali takawa ya tako cikin ?akin, sai a lokacin suka lura da zuwansa, ya ?arasa gaban gadon rumaisa, da take kwance a jikin mai sunan baba, hannunta ya kama ya yi wa wani irin mugun ri?o ya dubeta ya ce 'Ki ka ce matata ta mutu, ta yaya? Ya za ayi ki ce aisha ta mutu? Ke kin san mutuwa kuwa".

Ba ri?on da yayi mata ne ya sakata a cikin tashin hankali ba, abun da take gani a tattare da shi ne ya ?aga mata hankali, sai dai alamu sun nuna babu wanda yake ganin abun da take gani sai ita ka?ai.

Mai sunan baba ne ya shiga ?o?arin ?wace hannun rumaisa daga na Adam, amma ya kasa ruma kuwa ta ?ura masa ido tana wani irin kuka mai tsuma zuciya.

Ammi tamkar an dasata, ta ji maganar a bazata, ba ta ta?a tunanin abubuwa zasu cigaba da rikicewa haka ba.

Bashir ma ?o?arin ?wace hannun rumaisa suke yi, amma ri?on da ya yi mata ba na wasa bane ba.

"Ki ka ce matata ta mutu? Ta mutu fa ki ka ce, ki tashi daga baccin da ki ke yi ki gaya mini gaskiya, ba Aisha ce ta mutu ba".

Cikin kuka ta ce "Ka cikani kar ka ?alla mini hannu, tun da na gaya maka abun da ka ke son ji" tayi maganar cikin kuka.

Bai iya cewa komai ba, sai ganinsa suka yi ya silale a ?asa ya suma.

Sai a lokacin ammi ta samu hawayen idonta suka gangaro, mama da sauran mutanen wurin suka yi kan adam, sai dai ba ya motsi sam.

Da gudu Abubakar ya fita, sai gashi da likitoci sun biyo shi, suka yi umarni a kawo stretcher a ?au adam a kai shi emmrgency.

Mai sunan baba kuwa bai motsa ba, sai ma rungume rumaisa da yayi yana shafa bayanta da sigar rarrashi, saboda kukan da take yi, ruma kuwa da ta ga an kawo stretcher an ?ora adam a rikice ta ce "Wai shi ma mutuwa ya yi? Haka anty aisha fa ta yi ta daina motsi bayan ta yi ta fitsarin jini, jininta ya ?are"

Mai sunan baba ya sanya hannunsa ya rufe mata ido ya ce "Bai mutu ba in sha Allah, ki yi ta Addu'a".

Gaba daya ta kasa nutsuwa, mutuwar aisha ce ta dawo mata sabuwa fil a idonta, duk masifar mai sunan baba, tausayin rumaisa ya mamaye shi, yarinya ?arama tana ta gamuwa da iftila'in ?addara.

Ammi kuwa kuka ta din ga yi, kamar babu gobe ta yi iya ?o?arin ta amma ta kasa tawakalli ta jure, abu ka da mata abu na 'ya'ya, mama na son ta rarrasheta amma ita ma ta ?uge da kukan, daga baya suka bi bayan su Bashir, domin jin halin da Adam yake ciki, Yaya Abubakar ya tare su a hanya ya ce "Mama, ku je ku zauna in sha Allah babu wani abu, ga likitoci can sun rufu a kansa, ba za su bari ma ku shiga ba, ku yi ha?uri ku je ku zauna, ayi masa addu'a.
Yadda ammi take kuka zai tabattar maka da ba iya mutuwar ce ta dake ta ba, akwai tarin abubuwa cunkushe a zuciyarta.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, la'ila ha illa la Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam" sune abubuwan da ammi ke ta nanatawa.

Mai sunan baba ya numfasa ya ce "A duk lokacin da muka rasa abu mai muhimmanci a rayuwarmu, sai mu tuna Allah ne ya bamu, kuma Allahn da ya bamu yafi mu son abun, kuma ya fi mu sanin muna son abun, dan haka addu'a zaki yi ki daina kuka" da ruma yake maganar, amma a zahiri ba iya ruma yake yi wa nasihar ba, har da ammi.

"Mai sunan baba" ruma ta kira sunansa.

"Na'am"

"Ka ga laifina da na?i fa?a tun da farko? Ka ga shi ma zai mutu ya bar jaririn ko?"

"Ke da ki ka ce ba shi ne babansa ba, Meyasa ba kya so ya mutu?"

"Mai sunan baba" ta kuma kiran sunansa.

"Na'am" ya amsa mata.

"Idan sabir ya girma sai ya ji duk a gabana iyayensa suka mutu, idan ya tsane ni fa? bana son tunawa da mutuwar anty aisha, idan na tuna ji nake kamar na kashe kaina, da tsohon cikin nan fa dukanta suke yi, idan zasu dakeni ta hanasu, tun da suka taka mata cikinta take rashin lafiya, idan barde ya kawo mini abinci, tare muke ci, wataran ta ce in cinye ni 'yar baby ce ita ta ci girma. Mai sunan baba na yi ta yi musu magiya su kai ta asibiti suka ?i, kuma sun san ba ta da lafiya, na yi ta kuka ina ro?onsu ita kuma tana musu magiyar su kar?i ku?in fansata a wurin mijinta su sakeni ni yarinya ce. A hannuna ta mutu bayan na bata ruwa, babu wani ?an sanda da ya zo ku?utar da mu, kuma sai yanzu zasu zo su dameni wai sai na gaya musu tana ina? Me za su yi a kai bayan ta bar duniyar, na tsani duk wani jami'in tsaro tunda har anty aisha ta mutu ba wanda ya kawo mana agaji, sai wasu 'yan ta'addan ne suka ?wace mu, wallahi duk wanda ya kuma tambayata wani abu ba zan fa?a ba, dan babu abun da za su iya yi a kai" tayi maganar cikin ?unar zuciya tana rirri?e hannun mai sunan baba.

A hankali ya kwantar da ita, ya toshe mata bakinta, saboda kamar nema take ta fita hayyacinta, adduoi ya din ga yi mata, har ya samu ta yi shiru, amma maganganunta sun ?aga masa hankalin, shi daga nesa ma masu ciki tausayi suke bashi, saboda dakon cikin ma kawai ya ishe su, balle ace a taka mace da tsohon ciki, abun da ban tausayi.

Daga mama har ammi kowa sai goge hawaye take yi, sabir ne ya motsa ya fara kuka, mai sunan baba ya sanya hannu ya ?auke shi ya fita da shi waje.
Ya ?urawa yaron ido, sunan mahaifinsu rumaisa ta saka masa, ya tuna irin fa?i tashi da sadaukarwa da mama take yi a kansu, tun suna yara har zuwa yanzu da suka zama mutane ba ta daina ba, amma shi wannan ?an bai san wannan ba, hasali ma tasa uwar tana kawo shi duniya ta mutu ta bar shi a dokar daji a hannun yarinyar da ita kanta ba ta san ciwon kanta ba, ta yi kwanaki tana gararanba da shi a daji babu ko wando a jikinsa ga ?azantar haihuwa.
Wani irin tausayin yaron ya kama shi, ya rungume shi a ?irjinsa yana shafa bayansa, wata irin ?wallar tausayin yaron ta cika masa ido.

Abubakar kuwa tamkar wani daga cikin 'yan uwansa ne suka suma aka kwantar da su, sai kai wa yake yi yana komowa, sai da ya ga lokaci na neman ?ure masa sannan ya ?au jakarsa ya tafi.

Ko da su Usman suka zo mamaki ne ya kama su, ganin halin da su mama suke ciki, fuskokinsu ?auke da damuwa, idon mama yayi ja saboda kuka, ammi kuwa har a lokacin kuka take yi.
Aliyu ne ya fara maganatuwa ya ce "Mama lafiya kuwa? Meyafaru ne?"

Mama ta girgiza masa kai ta ce "Lafiya ?alau, ya kuka baro gidan an gama komai?".

Usman ya ce "Mama, ya zamu ga kuna kuka kuma ku ce lafiya ?alau, meyafaru?"

"Baban yaron nan ne babu lafiya, ashe mahaifiyar sabir da ake ta fama da rumaisa a kan ta yi bayani ta?i, ashe rasuwa ta yi, a hannun'yan bindigar ta rasu".

Dafe ?irji Aliyu ya yi yana Innalillahi wa Innalillahi raji'un, usman kuwa sak yayi duk da bai san matar ba, amma tausayinta ya kama shi.

"Mama rumaisa kuwa na da hankali, kuma shine ake ta fama da ita ta yi mursisi ta?i fa?a, saboda tsabar rashin kan gado"

"To ka san halinta da ba?in taurin kai, yanzun ma babana ne ya sakaya a gaba ya zare mata ido, amma yan sandan da suka zo suma ?in kula su ta yi".

Cikin damuwa usman ya kalli Ammi ya ce "Dan Allah ku yi ha?uri, wallahi yarinyar nan haka take sai a hankali wasu lokutan, bai kamata ta ?oye abu mai girma irin wannan ba, ku yi ha?uri Allah ya ji?anta da rahama ya sanya ta huta".

Ammi ta ce "Amin, ku daina ganin laifinta a kan gaskiyarta take, yanzu ihu ake bayan hari, kamata yayi a kai musu ?auki tun suna hannun 'yan bindigar. Ba ta yi mini komai ba, babu abun da zan ce wa rumaisa sai fatan Allah ya rayata, ya shiryata ya tsareta na gode sosai da sosai". Ta kai maganar tana kuka.

Usman cikin damuwa yake duban Ammi ya ce "Ki yi ha?uri, sai a gode Allah da ya ku?utar da ?an ta, ko ba komai za a kalla ace ga ?an Aisha, ku?utar yaron nan kawai ya ishi a godewa Allah, duk da ya kar?i uwarsa, komai yayi daidai ne, ki yi ha?uri, ki yi ha?uri Allah ya yafe mata, ya kula mana da jaririnta, ku yi ha?uri dan Allah kuka ba mafita bane, duk da dole ne jin zafi a duk lokacin da muka rasa makusanta mu da muke so, amma ayi ha?uri, duk jarrabawar da Allah ya yi wa bawa dai-dai ce".

Duk da ba wasu shekaru ne da usaman ba, amma ammi har cikin zuciyarta ta ji da?in yadda suka nuna damuwa a kan ta. Ta ce "Na gode Allah ya yi albarka"

?asan zuciyar ammi kuwa, tashin hankali ne mai yawan gaske, dan al'umar sun yi dagulewar da ba ta san ta ina zata kamo bakin zaren ba.

Sai wajen azahar rumaisa ta farka, ji take kamar ba a gaske ta fa?a musu mutuwar Aisha ba, mai sunan baba ta gani zaune a gefen gadonta, yana juya Sabir yana murmushi gefen baki, mai sunan baba da kan ka ga dariyar sa aiki ne ja, ruma za ta iya cewa tun da ta bu?i ido a duniya ba ta ta?a ganin mai sunan baba ya ?auki ?an wani ba, wani irin da?i ta ji da ta gan shi ?auke da Sabir.
Ya dubi ruma ya ce "Sannu kin tashi?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Babu wata matsala dai ko?"

"Eh babu, baban mama kana son mai sunan babanmu ko?" Ya jinjina mata kai, a lokacin da yake gyarawa sabir kwanciyar sa a hannunsa, duk da ba wani ?warewa yayi a iya ?aukar yara ba.

"Mai sunan baba dan Allah kar ku bari a rabani da shi, wallahi mamansa ta ce ta bar mini shi, da gaske nake ba wasa ba" kallonta kawai ya yi bai ce mata komai ba.

Ammi kuma na kan dadduma tana jin su, amma ba ta tanka ba.

Su Iman sun kira wayar ammi har sun gaji, dan ?arshe ma kashe wayarta ta yi ma gaba ?aya, dan ba ta san me za ta ce musu ba.
Adam kuwa ya shafe awanni a emergency ana fama, domin a ceto ransa, sam zuciyarsa ta ?i bugawa yadda yakamata, bpn sa ma an kasa picking ?in sa, ga numfashin sa ma yayi ?asa fiye da yadda ake so, su kansu likitocin sun fara fidda rai, da ?yar da taimakon Allah ya farfa?o ya samu bacci, sai da ya yi baccin ne sannan aka fito da shi a ka bashi ?aki.

Wunin ranar da su Aliyu aka yi ta sintiri a kan Adam, in an jima usman ya zauna ya yi ta yi wa ammi nasiha yana ba ta ha?uri. Sai da aka fito da shi, sannan aka ce ammi ta je ta ganshi.

Aka yi mata jagora har ?akin da yake, dan har ta fara fitar da rai a kan sa, jin shiru-shiru ba a fito da shi ba, ta zaci ko shi ma ya rasun ne.

Ta tsaya tana ?are masa kallo, ga robar ruwa nan a sa?ale, shi kuma idonsa a rufe yana bacci.

Ta kama hannunsa a cikin nata, ta saka hannunta ?aya tana shafa kansa ta ce "Na sani akwai wahala, amma ka ?ara jurewa, tun da na haifeka a kullum akwai fejin ?addara da kake bu?ewa babi babi, da an wuce wannan sai wannan, na sani da wahala amma ka ?ara jurewa addu'a ta tana tare da kai yarona. Allah ya shiga lamarinka Adam, Allah ya cigaba da dafa maka ya baka ikon cin jarrabawa" tayi maganar tana rushewa da kuka.

Bashir ya ce "Ammi, addu'a nan dai, ita zaki cigaba, kar jininki ya hau fa, kuma yanzu mun gano bakin zaren, tun da ta tabatta ta rasu, sai mu san abun yi na gaba, Allah ya yi mata rahama".

Aka din ga rarrashin ammi ana bata baki, daga bisani Bashir ya sallami direbanta, bayan magariba bashir ya ce zai mayar da ita gida, ya dawo ya zauna da Adam.

Mama ta ce "A'a, ita zata kwana a wurinsa"

Aliyu ya ce "Haba dai, saboda rashin kara ka wuni kana kaiwa da komowa, ita ma ta wuni a nan kuma ace ku kwana, ai ba wani abu, ko ni sai na zauna na kwana da shi".

Ammi ta ce "Kar a ?ora muku ?awainiya"

"Wallahi ba wata ?awainiya, Allah ya bashi lafiya kawai".

Daga gida har wurin adam kowanne tana son ta zauna, amma ya zama dole ta za?i tafiya gida, domin kuwa ba ta son kowa ya farga da abun da ya faru kan su sanar da kansu, ta san rashin zamanta a gidan, kan iya jefa zargi a wurin masu son ganin bayanta, dan haka a dole ta yarda Bashir ya ?auketa ya mayar da ita gida.

Aikuwa a falo ta tarar da su Nusaiba a zazzaune fuskokinsu duk babu da?i.

Nusai ce ta fara cewa "Ammi akwai matsala ne, tun safe mun kira wayarki ba kya ?agawa hankalinmu duk ya tashi, yanzu uncle Jamil ya bar gidan nan yana nema ya ?aga mana hankali wai ina takawa yake?"

Gaban Ammi ne ya fa?i, kar dai ya san wani abun ne, ta bu?e baki da ?yar ta ce "Ya ce muku wani abun ne?"

"A'a kawai dai yana tambayar mu wai ina yake, baya samunsa a waya, ya je gidansa ma baya nan"

"Babu wani abu, ban zaci zan kai haka ba nima, amma ai gani na dawo"

Buutt baba uwani ta fito cikin girmamawa ta ce "Allah ya ja zamaninki, ha?i?a yau mun wuni cikin zulumi da tashin hankali, mussaman da baki wuni a gida ba na tambayi su auta, sun ce ba su san in da ki ka tafi ba, ga wayarki ba ta shiga duk sun shiga damuwa kamar marayu".

Ammi ta ce "Gani na dawo, uzuri ne ya ri?e ni, zan shiga in huta, kar wanda ya shigo mini".

Iman ta ce "Ammina abinci fa?".

"Na ci" ta fa?a a ta?aice ta wuce sashinta.

Nusaiba ta ja hannun iman, ta yi ?asa da muryarta ta ce "Anya kuwa babu matsala?".

Jiki a sanyaye Iman ta ce "Nima haka nake tunani, amma ta ce kar wanda ya je in da take balle mu ji".

Nusaiba ta yi ajiyar zuciya ta ce "Bari mu jira zuwa Allah ya kaimu da safe mu gani"

Iman ta amsa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login