Showing 120001 words to 123000 words out of 182697 words
ku ajiyeta zata tashi daga baccin nan da kanta"
Hanka?eta suka yi, suka sanyata a ledar nan, suka sakata a mota, ?ayan ya ?aga waya ya ce "Eh, ku jiramu a boda, da wannan motar zaku zo, sai ku kar?eta"
Bayan sun sakata a motar, ?ayan ya dubi bayan ruma da ta ga gama hargitsewa tana ta sambatu, ta kasa Addu'a, ya ga jariri a bayanta dan haka ya tunkareta, amma sule ya sha gabansa ya ce "me zaka yi mata?".
"Jaririn nan zan kar?a"
Sule ya girgiza masa kai ya ce, ka ?yalemu, da kaina zan kar?i yaron nan na kashe shi, yanzu idan kace zaka kar?e shi ta ?arfi, sai dai ka kasheta ko yi mata illa, dan duk in da kake tunanin wata halitta mai azababben taurin kai da kafiyar masifa, aka samu wannan yarinyar an gama magana, idan kuma wani abu ya sameta, fa?a zai faru tsakaninmu da su barde, dan tana zaune ne bisa yarjejeniya, akwai yaranmu a wurinsu, idan ta cutu zasu kashe su, mu kuma ba zamu ?yale ba".
"Amma ka tabatta zaka kashe yaron? Muddin yaron nan ya rayu, asirinmu zai iya tonuwa, kuma ina fatan yarinyar nan ba zata bar wurin nan ba, da duk sauran wannan mutanen?"
Sule ya ce "Lokaci kawai muke jira, kar ku damu"
"To shikenan, muna kan tattaunawa da mijinta, zai kawo mana ku?in fansarta, zuwa jibi zai kawo, idan ya kawo ku kar?a ku ajiye mana, sai a gaya masa ta mutu ita da ?an cikinta".
Sule ya jinjina masa kai, mutanen suka shiga cikin motar, suka kunna.
Ruma kuwa ta din ga kurma ihu tana "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na fa bata ruwa ta sha, wallahi ba ta mutu ba, haba Anty Aishana, haka muka yi da ke, ba tare muka ce zamu tafi gida ba, har ki ka ce zaki zo gidanmu, haba Anty Aisha kin san fa na sha?u da ke ina sonki, meyasa ki ka tafi ki barni da jaririnki, a ina zan gano danginki?".
Sha tara ya ce "Ke rumaisa! Wai ke baki san ?addara ba, to sai ki bita in da ta tafi, tun da uwarki ce".
"Eh zam bita, idan ka isa kai ?an halak ne ka kasheni in bita, tun yaushe nake muku magiya, wata?ila da kun kasheni da ban santa na saba da ita ba. Ba zan yafe muku ba, Allah ya bi mana hakkinmu, kun sa an haifi jairiri a dajin nan babarsa ta mutu, wa zai shayar da shi? Kuna da imani kuwa, anya kun san Allah?"
"Idan baki rufe mana baki ba, wallahi sai na kashe jaririn nan kamar yadda na yi al?awari" sule yayi maganar yana kallon ruma cikin takaici.
"Wallahi ka kashe yaron nan kai ma sai na kashe ka da hannuna, na shirya yin fito na fito da duk wanda ya ta?a mini ?a, sai dai ku fara kasheni"
Sha tara ya ce "Ohh, barde ya barmu da bala'i, dan girman Allah ku bashi yarinyar nan kamar yadda ya bu?ata mu huta da masifar wannan yarinya mai kama da tsaka".
Ruma ba ta iya kuma cewa komai ba, ta dur?ushe a kan gwiwoyinta, ta fashe da wani irin matsanancin kuka, tun da mama ta haifeta ba ta ta?a jin wani abu mai ra?a?i da ya daki zuciyarta irin mutuwar Aisha ba, tayi kuka tayi kuka, tun mutanen wurin suna rarrashinta suna sanya ran ta yi shiru, har suka gaji suka rabu da ita. Kan fa?uwr rana idonta suna kumbure, da ?yar ka ke iya gani tsagar idonta saboda kumburi, ga yaron sai kuka yake, da yayi kuka sai ta tuttula masa pure water ta cigaba da rarrashinsa.
Gaba ?aya haka suka ?arasa wunin ranar cikin jimami, domin Aisha akwai kirki duk da rumaisa take sabgoginta, amma dai ta shiga ran Mutanen wurin, kuma sun ji mutuwarta sosai da sosai.
A haka har dare yayi, yaron ya fara karkarwa saboda jikinsa babu sutura, ga shi jikin masa duk busashshen jinin haihuwa, babu wanka babu wanki.
Ruma ta du?un?une shi a jikinta ta cigaba da kuka, ta shafi ?irjinta da babu wani abun kirki a wurin sai ?irgar dangi, balle ta bashi, to idan ma ta bashi mai zai zu?o tun da dai ruwa ake sha a ciki, to ita nata guda nawa yake balle a ji wani ruwa a ciki.
"?ila ma idan da ruwan, ba zai fi cokali ?aya ba" ta bawa kanta amsa.
"Ke wallahi sai kin kawo yaron nan an kashe shi, uwar me zaki bashi duk ya cikawa mutane kunne?"
Duk da tana cikin matsananciyar damuwa, hakan bai hanata cikin ?un?uni cewa "uwarka zan bashi ba".
Sule ne ya tako ya zo gaban rumaisa ya zauna, ya ce "Bani na ga jaririn"
Juya masa baya tayi, tana sake ?an?ame yaron.
"Ganinsa kawai zan na baki, babu abin da zan yi masa".
"Ta?, ai Allah ?aya ne kawai zaka ce mini na yarda da kai, wallahi ba zan bayar ba, na san kashe shi zaka yi".
"Ke ki na ji na ko? Ki kawo yaron nan a basu, dan dole zasu dawo wurin nan, kuma kin ga za a ?au hakkinsa, tun da dai uwarsa ta mutu, ki bani shi gobe sai a basu gawarsa kema ba iya raino zaki yi ba"
Share shi ta yi, ta cigaba jijjiga yaron a jikinta, cikin zafin nama ya dan?o ?afafuwan yaron zai ?aga shi, ruma ta dan?ara masa cizo a hannun, zafin cizon ya sanya ya saka hannunsa ?aya ya daki kanta.
Sai da ta daina ganewa na wucin gadi, kanta ya juye gaba ?aya, amma hakan bai saka ta saki jaririn ba.
"Wallahi sai na kashe yarinyar nan, uban kowa ma ya huta, sai dai duk wadda zata faru ta faru".
AYSHERCOOL
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
?? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*
*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*
*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*
*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Sha tara ya ce "A'a sule, ka san yadda mu ka yi da su barde, ka ?an ?ara ha?uri, bana son fitina ta shiga tsakaninmu da su ne".
"Wallahi na tsani yarinyar nan, iskancinta yayi yawa, tun da na fara harkar nan ban ta?a ha?uwa da ?an rainin hankalin da yake abin da ya ga dama ba irin ta".
Banza ruma ta yi masa, kamar ba ta san me yake cewa ba, ta rungume jariri ta cigaba da kuka, ji take ina ma tun kan ta san Aisha suka kasheta, wani irin so da tausayin jaririn nan suka rufeta, haka yake tik jikinsa babu kaya.
Sule kuwa a ?ule ya ce "Yanzu haka zamu cigaba da zama wannan ?an tayin yana cika mana kunnuwa, uban me zamu ba shi?".
"To ba ita ta ga zata iya ba, sai ka ?yaleta ai".
"Amma mun riga mun yi da su a kan cewa zamu kashe yaron nan, yanzu me zamu ce musu?".
Sha tara ya ce "Ai babu lallai su dawo, ko ma zasu dawo kan su dawo ?in zamu san abin yi"
Sauran matan wurin babu yadda ba su yi ba, a kan ruma ta bayar da jaririn su tayata rarrashinsa, amma ta ce ba zata bayar ba, dan bata yarda da kowa ba, gashi ?an ruwan da take ?a??aka masa ya ?are.
Haka dare yayi, salla idan zata yi, sai ta bayar a goya mata shi, jaririn yana kuka ita ma tana kuka, gwanin ban tausayi.
Dare yayi sosai, amma ruma tana tsaye, tana aikin jijjiga yaron nan, sha tara ya kalleta ya ce "Wannan Yarinya da gani irin maita ce, kalli dan Allah dan bala'i yaro ya hanata bacci ya hana mutane sukuni, amma ta?i bari a kashe shi, sai wahala take yi, shegiya taurin kai kamar jinjirar jaka".
Sule ya ce "Ko kuma kafuran farko ba, wallahi da ka barni da saina harbesu su duka, kowa ma ya huta".
"?yaleta dai tukuna, mu ga iya gudun ruwan barde".
Haka ruma ta shafe awanni ta na fama da yaron nan, ta ro?i su sha tara su bata ruwa ta kuma bashi, amma suka ce ba zasu bayar ba.
Sai da yayi mai isarsa, sannan ya yi shiru, ta koma wajen bishiyar da Aisha ta mutu, ta jingina tayi shiru tana tuna yadda suka yi ta hira daren jiya, amma yanzu wai babu ita a doron duniya sai ?an ta. A haka wani ?arawon bacci ya kwashe rumaisa.
****
"Yaya Jamil, ya jikin takawa kuwa?" Samha ta yi maganar tare da tattara hankalinta a kan Jamil.
"Ya ji sau?i".
"Sau?i sosai dai, ni fa na tsorata da yanayin da na ganshi a ciki, kaga abun da yayi wa iman kuwa?"
"Kenan kune ku ka je ku ka ce yayi shaye-shaye yayi yin?urin yi wa iman fya?e, kun sanya 'yar mutane a wahala jikinta ya rikice".
Waro ido samha ta yi ta ce "Mu kuma? Yaushe? Wallahi ni ban fa?a ba".
"To yaya aka yi wannan banzan zancen mara ma'ana ya fita, ke kin san dai takawa ba ya shaye-shaye, idan ma kin yi haka ne dan cimma ?udurinki, ba zai aureki ba, ke ma kin san ko da aure bai haramta a tsakaninku ba, amma a al'adance takawa ya haramta a gareki a yanzu dan haka tun wuri ki shiga hankalinki, kuma ki nemi wani a manemanki ki yi aure ki huta, ko kuma ki cigaba da dakon soyayyar sa a banza da babu abun da zata amfana miki".
Shiru Samha ta yi, ta san babu tantama makircin Mummy ne da Fauziyya.
"Kun fara wuce gona da iri, ina bin ku ne don kawai na ga in da ku ka dosa, amma kina za?ewa hajiya Jamila " tayi maganar a zuciyarta.
"Ai kai Jamil wata?ila idan ka gaya mata ta ji, tun da ni ban isa na gaya mata ba, tun wuri na ce ki fita a sabgar yaron nan, komai ki ke yi ba kya gabansa, amma ki nace samha kamar shine autan maza, yaron nan bashi da mutunci ko ka?an, ni kaina uwarku wani gani-gani yake mini, amma daga ke har Jamil sai wani shishshige masa ku ke yi".
Jamil ya ce "Mama, kin san halinsa yana iya ?o?arin sa wurin mu'amalantar kowa yadda ya dace, amma tare muka taso, dan haka bashi da wasu abokai sai mu, tun da duk tsatso ?aya muke, wannan yarinyar ce dai idan har bata shiga hankalinta a kan sa ba, zata cigaba da shan wahala ne".
Zum?ura baki Samha ta yi, ta tashi ta bar ?akin, dan babu mai gaya mata ta ji, in dai a kan takawa ne, son sa ma yanzu ta fara.
***
Da sallama takawa ya shiga ?akin ammi, in da iman ke kwance a kan gadon ammi, ta rufe rabin jikinta da bargo, Nusaiba na ta jera mata sannu.
Yana shigowa suka ?ara nutsuwa suna gaishe shi, ya amsa musu sama-sama, ya ?arasa gaban gadon ya ce "Iman, ya jiki?"
"Da sau?i yaya" ta amsa a sassanyar muryarta.
Yayi ?asa da murya ya ce "Am sorry, duk laifina ne abubuwa suke ta faruwa a haka, amma dan Allah ki yi ha?uri kin ji, bana son wani abu ya sameki, ba zamu iya jurewa ba, ki mayar da komai ba komai ba, sannan ki toshe kunnenki a kan duk abin da za a fa?a".
Ta jinjina masa kai ta ce "Ina sha Allah yaya, kuma kar ka damu, in sha Allah komai zai wuce ne".
Ya ce "Ina fatan hakan, ga jabir can yana son yayi miki sannu, taso mu je falon".
Ji ta yi kamar ta ce a'a, amma ta san ba ta isa ta ce a'a ?in ba, dan haka ta ?au hijjabinta ta saka, Nusaiba ta rungumo iman suka fito falon tare.
Sai dai da suka fito, takawa ya tarar da Samha a falon a zaune.
Basarwa yayi bai ko nuna ya ga samha ba, Jabir kuwa ya kafe iman da ido kamar maye.
Samha ta gyara zamanta cikin iyayi ta ce "Yaya ya ?arfin jiki?" Ya ?ago ya kalli Samha, ya ?an ?ura mata ido, amma bai ce komai ba.
Nusaiba ta ce "Uncle J ina kwana?".
"Lafiya lau, ya gida ya Ammi?"
"Ammi na lafiya, ta fita ne".
Jabir ya mayar da idonsa kan Iman ya ce "Iman, ashe baki ji da?i ba, ya jikin?"
Cikin yanayinta na rashin son magana da kuma ?osawa ta ce "Da sau?i"
"Allah ya baki lafiya autarmu, duk na kasa sukuni tun da aka ce mini jikinki ya motsa, amma na yi mamakin da na ganki a gida, takawa ba za a kaita asibiti ba?".
"Eh na za a kaita ba, amma tun da ha ka ka zo, sai ka kaita?".
"Kar ka gaya mini magana mana, daga tambaya, dole na tuhumi yadda ake nema ayi sake da lafiyar auta". Ha?e rai iman ta kuma yi, ba ta ce komai ba, dan gaba ?aya ta ?osa da zaman.
Samha kuwa da zancen iman ya fara ?ular da ita, ta yi gyaran murya ta ce "Takawa duk ka rame wallahi".
Jabir ya ce "Ba dole ba, ya sanya tunani da damuwar a ransa, gaba ?aya ya koma wani iri".
Samha ta din ga zubo zance, amma takawa ya ?i kulata, ya kashingi?a yayi musu shiru.
Iman ta ce "Ni dai zan koma ?aki jiri nake ji, sai anjimanku".
Takawa ya kalleta ya ce "Ko na mayar da ke ?akin?".
Samha ta yi zumbur ta tashi, ta nufi iman ta na fa?in "Haba dai, gani a zaune, bari na rakata tun da jiri take ji" sai da gaban iman ya fa?i, sam ba ta so haka ba, dan ta san da biyu ta ce zata kaita ?aki.
Ta rungumi iman, ta nufi sashin Ammi da ita, iman ta ce "A'a ?akina zan koma".
Samha ta ce "Bakomai, bari na rakaki" tayi maganar kamar gaske.
Sai da suka shiga ?akin iman, sannan ta ta?ar?are, ta hanka?a Iman kan gadon, ba tare da tausayin halin da iman ?in ke ciki ba.
Ta murtuke fuska ta ce "Ke 'yar tsintuwa, kalleni da kyau, ya muka yi da ke?".
"Anty Samha me na yi miki?".
Cikin ?ulewa Samha ta ce "Ke fa tsohuwar munafuka ce, kullum na yi magana sai ki ce mini, ke babu komai a tsakanin ki da takawa, amma kullum cikin nani?e masa ki ke, ko abun da ake fa?a ?in gaske ne, kina kai masa kanki?"
Iman ta yi shiruu, zuciyarta na yi mata wani irin zafi, amma ba ta da bakin magana, 'yar tsintuwa ce kamar yadda Samha ta fa?a.
Maganar samha ce ta dawo da ita hayyacinta, "Wallahi idan ki ka cigaba da shishshige wa Adam, sai na sa kin yi dana sanin zuwanki duniyar nan, sai na mai da ke matacciya da rai, sai na yi miki illar da ba kya zato, ki kiyayi adam ki daina yi masa shishshigi idan ba haka ba zan aikata abin da na fa?a, banza mai kyan banza 'yar tsintuwa, ke ban da abinki ma, har kina tunanin ha?a jiki da jinik sarauta ?as?antacciya irinki, da babu wanda yake da taabbcin 'yar halak ce ke, ?ila ma 'yar gaba da alfatiha ce"
Duk yadda Samha ta din ga yi wa iman