Showing 33001 words to 36000 words out of 182697 words
miki lafiya da nisan kwana uwa ma bada mama"
"Amin ya rabb"
A ranar duk wanda ya shigo, sai ruma ta nuna masa kyaututtukan da aka bata, har a waya sai da aka kira mata yaya Abubakar ta gaya masa, tun ana tayata murna da Allah ya sanya albarka har ta fara ?ular da mutanen gidan. Dan hatta ma?wabta sai da ta shiga ta gaya musu ai tayi ?o?ari a makaranta an bata kyauta.
Da ta je Islamiyya kuwa, har ofishin shugaban makaranta ta je, shi ma ta gaya masa, ya tayata murna tare da sanya mata albarka, ta ?arasa staff room bayan sun gaisa da malaman suma ta gaya musu ai a makarantar boko tayi ?o?ari an bata kyaututtuka. Nan suka yi ta mata fatan alkhairi, ji take a duniya yau ta ?ure da?i tayi abin da ba ta ta?a ba.
"Malam to idan an idar da salla dan Allah a sanar"
Wani malami ya kalleta ya ce "A sanar da me?"
"Na yi ?o?ari a makarantar boko mana, har na ciyo kyauta, word kusan ?ari biyu da hamsin fa na haddace yadda ake spelling ?in su"
"To amma ai nan ba makarantar boko ba ce ba, ki bari idan ki ka yi bajinta a nan ma, sai a sanar wa ?alibai"
Ruma ta ce "A'a malam gara ai a sanar, saboda masu ce mini da?i?iya su san ?wa?walwata na aiki, wataran zan bayar da mamaki".
Malam Habibu ya yi caraf ya ce "?warai kuwa, dole a sanar da ?alibai wannan namijin ?o?ari da ki ka yi, nima ba rannan na yi ?ari kin iya ba, duk za a sanar kar ki damu" cikin jin da?i ruma ta ce "Yauwwa malam na gode"
Bayan tafiyarta ya yi dariya ya ce "Yanzu idan ba ku yi yadda take so ba, Allah ka?ai ya san wace tijarar zata yu, amma yanzu idan aka fa?a ?in, za ta ji da?i da ?ara samun ?warin gwiwa".
Ruma da ta ga an idar da salla, ana neman a watse ba a sanar ba, ta tafi ?ofar masallacin maza, ta le?a ta ce "Malam Habibu kar ka manta fa, na ji ba a fa?a ba".
Malam Habibu ya ce "To bari a sanar, ai yakamata wannan abin arziki haka"
Haka malam Habibu ya tashi ya ce "'yan uwa ?alibai da malamai, a taya 'yar uwa murna, wato 'ya ta rumaisa, bisa nasara da ta yi a wata gasa da aka shirya a makarantar bokon su, har ta samu kyaututtuka dan Allah ayi mata Addu'a, Allah ya ?aro nasarori"
Da?i kamar ya kashe ruma, masu dariya na yi, masu jin haushi na yi.
Huzaifa da suka yi salla sahu ?aya da Yasir ya ce "Ka ji abin da wannan mara kan gadon ta yi ko?"
"Bar motsatsiya, suma malaman da suka biye mata, idan ba tayi wasa ba sai na ?ona banzayen litattafan da aka bata, kowa ma ya huta".
Cike da annashuwa ruma ta tafi gida, ta je ta bawa mama labarin yau har a wurin salla, aka sanar da ta ci kyauta a makarantar boko. Tana shiga gidan ta tarar da Yaya Abubakar ya zo hutu, da kuma waa dattijuwar mata a zaune a tsakar gida.
Da sauri ruma ta nufi dattijuwar ta fa?a jikinta ta ce "Gwaggo Atine, yaushe rabon da na ganki?"
Dattijuwar ta washe baki ta ce "Dama ina zaki ganni, nayi-nayi da babarki ta din ga kai mini ke ina ganinki, amma ta ?i saboda ina ?auye".
Mama ta ce "Haba Yaya Atine, wallahi ba haka bane ba, kin san yanayin makaranta kuma ruma ba ta ji idan aka kai miki ita sai ta gallabe ku"
Ruma ta haye kan cinyar matar cikin jin da?i ta zauna.
Matar ta ?ora da cewa "Ba wani rashin ji, a kawo mini ita a hakan ina son ta, duk rashin jin ta. ?an uwana ya ?allafa rai a kan ta yana son ta, nima ina matu?ar ?aunarta da na ganta shi nake tunawa amma ba za a kawo mini ita ba, sai wannan ?artin ne kawai suke zuwa in da nake" ta yi maganar tana fashewa da kuka.
Mama cewa take "Allah ya baki ha?uri, in Allah ya yarda za a dinga kawota".
Ruma kuwa ta kalli Gwaggo ta ?yal-?yale da dariya ta ce "Dan Allah Gwaggo ki daina wannan kukan, ni wallahi fuskarki dariya take bani idan ki na yi, kin ga yadda ki ke yamutsa kuwa?"
Yaya Aliyu ya ce "Ai gara ta fara gwada miki halin"
Gwaggo ta tsaya da kukan ta ce "Rumaisatu, kukan nawa ne yake baki dariya?"
Ruma ta ce "Eh mana, amma ki daina ce mini wata rumaisatu, sai ka ce wata masara, kowa aka saka masa suna mai da?i a gidan nan, amma aka saka mini wata Rumaisa kamar masa"
Gwaggo ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah"
"Gwaggo wai ina wannan 'yar ta ki, mai kamar ni ?in nan?"
Jin ruma ta tambayi 'yar autarta ya sanya Gwaggo yin murmushi ta ce "Au Lawisa tana nan ?alau, ta na ta a gaishe ki, ita ana biki sun tafi da tuni tare zamu zo"
Ruma ta yi dariya ta ce "Wai Lawisa, ai har gara nawa sunan ma da nata, wata lawisa kamar za ace lawashi, ta fini girma yanzu?"
"A'a zaku yi tsayi ?aya da ita"
Ruma ta yi murmushi tana ka?a ?afa.
Abubakar ya ce "Ruma ?aga mata ?afa mana"
"A'a ?yaleta, ai haryanzu yarinya ce, Allah dai ya kai ni auranku ke da Lawisa"
Ruma ta ce "Amin, ki yi mini Addu'a, Allah ya sa na yi tsawo na isa aure, kuma Allah ya sa na auri kyakykyawa mai ku?i sosai"
Mama ta ri?e ha?a ta ce "Ruma, ?an?anuwarki da ke, har kin san wani miji mai kyau mai ku?i?".
Gwaggo ta ce wa mama "Wai ke ina ruwanki da mu ne, muna hira kina saka mana baki" ta mayar da hankali kan ruma ta ce "Amin 'yar albarka, Allah ya kai ki in da zaki huta, mu ci mu sha mu yi wada?a".
"Amin, kuma Allah ya sa na auri me kyau".
Aliyu ya ce"Da wannan shegen hancin naki kamar na aladae zaki auri me kyau?"
Gwaggo ta ce "?arya ka ke dan ubanka, wallahi kamar ta ?aya da babanku, kuma hanci ne da shi har baka, in Allah ya yarda sirikina kyakykyawa ne kuma mai abin hannu, tun da 'ya ta ba daga nan ba"
"Gwaggo kin san wa nake so na aura?"
"A'a sai kin fa?a"
"Kina kallon wrestling?"
Gwaggo ta ce"A'a ni ban san shi ba"
'To ball fa?"
"Ni ina zan ga wannan shirmen"
Ruma ta ce "Da kina kallo, da na gaya miki wanda zan aura a cikin su".
Cikin son katse surutun da ruma ke yi ba kunya ba tsoro mama ta ce "Ruma tashi ki canza kaya, zan aike ki" ruma ta mi?e daga cinyar Gwaggo ta tafi sauya uniform.
Tun da Allah ya sa Gwaggo ta zo gidan nan, ruma ta?ara ta ?aru, don ko me ruma za ta yi ba zata bari a yi mata fa?a ba, gashi kullum cikin fa?a take da mai sunan Baba, dan kome za ta yi idan ruma tayi laifi hukunta ta yake yi.
"Wannan yaro da fuska kamar bajimin sa, ba ka da imani, wannan 'yar tatsitsiyar yarinyar guda nawa take, da zaka dinga azabtar da ita wallahi Hauwa wannan ?an naki mugu ne"
Gaba ?aya ruma da Gwaggo suka gallabi gidan nan, ruma kuwa aka samu tikitin rashin ji dan ma tana tsoron mai sunan Baba.
Yau Malam Habibu yana babban aji, ruma tana tare da shi, yayi musu ?ari, tana ta wasanninta da ciye-ciye, sai da ya kammala yana amsa tambayoyi sannan ruma ta ce "Malam ka ce idan mace tayi mafarkin namiji sai ta yi wanka zata yi salla, to ni kuma kullum sai na yi mafarkin yayyena, Kuma ni sai zan tafi makaranta nake wanka watarana kuma mama ta ce bana fita tayi mini wanka, to yan.....
Kan ta ?arasa 'yan ajin suka hau dariya, dan ba zaka ta?a cewa hankalinta na kan abin da yake koyarwa ba.
Malam Habibu ya ce " 'ya ta ta kaina, ai wankan da mama take yi miki ya wadatar, duk ?ayane"
Ta ce "Au ho, na gane"
Tana dawowa daga islamiyya ta turke Abubakar ta ce "Yaya Sadik yau ka san meyafaru a makarantar islamiyya ?"
Sadik ya ce "A'a"
"Ka san na canza aji a islamiyya, saboda malaminmu baya ?aunata, Ajin su Yasir kuma ya ce idan na ?ara zuwar musu aji sai ya dakeni, sai na koma ajin malam Habibu gaba ?aya ajin 'yan sauka"
Abubakar ya ce "To ban da abinki kin ta?a ganin an fara gini daga roofing, ai daga tushe ake farawa"
"Oho dai koma yane, wani karatu aka yi nake son na tambayeka, da zan tambayi malam Habibu na manta"
"To ina jin ki"
" 'yan ajin ne da su da wasu na ga wataran ba sa salla fa, ko su ?i zuwa da Alqur'ani izifi sittin wai Haila suke yi. Na tambayesu sai suka ce mini wai ai mata ba kullum suke salla ba, idan ba su yi salla ba haila suke yi ko bi?i. Aikuwa nima na ?i yin salla, wata prefect ta ce me yasa ba na salla nima na ce bi?i nake"
Gwaggo da ta idar da salla ta ce "Subhanallahi" jin maganar ruman kamar saukar aradu.
Ita kuwa ko a jikinta, ta cigaba "Shi ne ta ce dan ubana ni na isa in yi bi?i, na ce ba dai ubana ba sai dai na ta, kuma tun da nima bi?i nake ba zan salla ba, ashe wataran mata ba sa salla amma ni kullum mama sai ta ce sai na yi"
Abubakar ya ce"To, wannan zancenku ne ke da maman ita zata baki amsa".
Ruma ta ce "Mama....."
Mama ta katseta ta hanyar cewa "Rufe mini baki, kar ki sake ki yi mini shirme, kuma ki tashi ki yi sallar da ki ka ce baki yi ba dan ubanki"
"To mama ai idan ana bi?i ba a salla"
"Bi?in ubanki, ke kin san meye bi?in ne?"
"To meye bi?in?"
"Ba zaki tashi ki yi sallar ba, sai na zane ki da bulugarin nan?"
Ta kalli Gwaggo ta ce "To ke gaya mini"
Kamar wadda ta tambayi meye wani babban zunubi Gwaggo ta ce "A'a ni babu ruwana, ga uwarki nan ta baki amsa ni zaki tambaya wannan babban al'amari ba a bakina ba, 'ya'yan binki wayewar ku ta yi yawa".
"Ohh ni ruma, komai na yi laifi ne, ai shikenan"
Tun daga lokacin ba ta kuma kula kowa ba, ta koma tayi shiru wai ita ta ji haushi.
Har zuwa sallar magariba, ba ta sake kula kowa ba, Gwaggo ma ta gaji da yi mata hirar, amma Ruma ta?i saurarata.
Yaya Sadik ne yayi gyaran murya ya ce "Ruma, wai ni kuwa idan kin girma me ki ke son ki zama ne? Da na je taron PTA ?in ku an ce da kun shiga primary 6, za'a fara shirin common entrance, shi ne na ce idan kin shiga Sakandire me ki ke sha'awa Art zaki yi ko science?"
Ta kalle shi ta ce"Wai in din ga drawing?"
"Wane irin drawing kuma?"
"To ai ji na yi ka ce Art, Art ba drawing ba kenan?"
"A'a ba wannan ba"
"Ni dai kawai sana'ar da zan samu ku?i nake so, ko kuma in zama 'yar sanda, in dinga tsayawa a titi ina bada hannu masu mota suna bani ku?i, ko kuma a bu?e mini kanti, ko na zama mawa?iya ko 'yar film!"
Ayshercool
08081012143
A TAIMAKA AYI SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ?INA NA COOL HAUSA NOVELS, KO IN KOMA POSTING SAU ?AYA A SATI ??*
[11/07, 4:25 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.
P11
Girgiza kai kawai Abubakar ya yi, ya ja bakinsa ya tsuke.
"Yaya ya na ji kuma kayi shiru?"
"To ruma ba dole na yi shiru ba, kowa yana nemawa kansa mafita a rayuwa, amma ke in da ki ka dosa daban?"
"To wai me na fa?a ba dai-dai ba?"
"Yanzu ke tsakanin ki da Allah, kin ta?a ganin mace a titi tana bada hannu a ?asar hausa?"
Ta ?an yi shiru sannan ta girgiza masa kai ta ce "A'a, to mawa?iya fa ko film?"
Abubakar ya ce "Ba kushe sana'ar wani zan yi ba, amma ki yi tunanin wani abun daban"
"To ba sai a bu?e mini kanti ba"
"Yanzu a unguwar nan gaya mini shagunan da ki ka ga mata ne a ciki suke sayar da abu?"
Ta yi farat ta ce "Ga maman Olu beyerabiya"
"To ke bayerabiya ce?"
"A'a amma dai....."
"Kin ga, ya isa haka, dama ni a kan career ki nake magana, tun da baki gane me nake nufi ba shikenan" ita sam ba ta ga aibun abin da ta ce tana so ba, dan haka ko a jikinta ta share.
Gwaggo ta fara shirin tafiya, su Yasir suna ta murna, dan dama duk ta ishe su da fa?a da azabar saka ido.
Shi kansa mai sunan Baba murna yake ta tattara ta tafi ta bar musu gida su huta, dan ta saka shi a gaba da yawa, dan ma Allah ya taimaki Abubakar bai fi sati ba ya koma makaranta.
Amma kullum cikin surutu takewa mama "Hauwwa wannan zagada zagadan yaran naki, duk sun isa aure amma kin tare su a gaba kina ado da su a gida, ga ?auye can muna da mata burjik, amma dan mugunta kin tare su kin hana su motsi'
Mama ta ce "Haba Gwaggo, guda nawa yaran suke, haryanzu su Baba basu ha?a talatin ba fa, duk girman jiki ne, kuma kina ganin irin rayuwar da ake sai godiyar Allah, babu mai ?wa?warar sana'a sai ?arfin hali, idan suka ?auko aure da yaya za su ri?e?"
"Ba wani nan, idan mutum yayi aure Allah zai warware, amma kallesu dan Allah tuma-tuman gwauraye ki na ado da su a gida, babu mai mata, kalli dai wannan zagaren, sai dai ya shigo fuska kamar bajimin sa, ya zo ya ?au abinci ya fita yana zazzare ido kamar wani zaki, ko fara'a ba ya yi, kai haka zaka yi wa matar ma idan an aureka?, ko da yake ma wace macence za ta auri mutum ba fara'a ba komai fuska kamar kunun kanwa ba rahama"
Lomar Abincinsa kawai yake kawai, ko motsi bai yi ba, balle ya nuna ya san da shi take, yana jin ta ya share ta.
Ruma kamar ta kwashe da dariya, jin an ce fuskar yaya Umar kamar kunun kanwa, amma sanin ruwa ba sa'an kwandon ba ne ya sanya ta ja bakinta ta tsuke.
"Umaru da kai fa nake" A hankali ya ?ago idanunsa ya yi mata wani irin kallo, ya mayar da kan sa ya cigaba da cin abinci.
"To Allah ya kyauta, ka ma dai mayar da ni mahaukaciya, ka je ka ?arata, tattara kayana ma zan yi na bar muku gidan ku, gobe goben nan zan bar garin nan.
A hankali yasir ya ce "Alhamdilillah, Allah ya raka taki gona"
A rikice ruma ta ce "Haba Gwaggo, ni bana son ki tafi, dan Allah ki zauna bamu gaji da ganinki ba".
Huzaifa ya yi ?asa da murya ya cewa Abdallah"Ji munafukar 'yar nan, ko a gidan uban waye bamu gaji da ganin na ta ba, mata duk ta addabi mutane?"
Abdallah ya ce "Ashe ka manta wacece ruma, ai wannan yarinyar tsaf sai ta ha?a ya?in duniya na uku, duk abin da ta san za ta aikata wanda ba a so shi take yi"'
Kamar wasa ruma har da kuka, wai kar Gwaggo ta tafi, ji suka yi kamar su yi wa ruma taron dangi su zaneta.
Ganin ruma na kuka, ya sanya Gwaggo ta ce ba zata tafi yanzu ba, saboda ruma.
*****
Sauri-sauri take yi, tana tafe tana duba agogon hannunta, tana daf da makara zuwa wurin da zata.
Tana ?arasawa harabar gidan ta ?an ?aga murya ta ce "Gali, gani na fito zo mu je na makara"
Cikin girmamawa da murmushi Gali ya taso ya ce "Allah ya taimaki 'yar gaban goshi, Allah ya ?ara miki lafiya uwar ?akina, ai tun ?azu ke nake jira, tun da tun hu?u ki ka ce mini"
"Kai dai bari, na tsaya na yiwa Ammi girkin dare, kar na je ban dawo da wuri ba ka san ba komai take ci ba"
Ya ce "Haka ne, bari na fito da motar" ya yi gaba ita kuma ta tsaya.
'yan mata ne su hu?u, suka fito ta ?ofar wani sashi na cikin gidan, suka tunkaro in da take wajen harabar gidan, hakan ya yi dai-dai da fito da motar da Gali ya yi.
Kai tsaye suka tinkari motar ba tare da sun kulata ba, suna ?o?arin bu?ewa su shiga.
Da sauri Iman ta ce "Kai, fita fa zan yi, zai kai ni unguwa ne"
?aya daga cikin su ta kalleta ta ce "Saboda ta ki fitar zamu fasa tamu ne?"
Iman ta ce "A'a ba haka nake nufi ba, na ga kun iya driving, kuma ga wasu motocin, ni Ammi ta hanani tu?i ne, kuma na yi magana da Gali tuntuni a kan zai kai ni unguwa"
Cikin tsawa ?aya daga cikin su ta ce "Shut up! Mu ki ke kallo ki ke gayawa haka, kin manta a tuna miki ne?"
"Me ku ke yi haka a tsatstsaye?" Gaba ?aya suka waiwaya suka kalli mai maganar.
Jikin Iman ne ya yi sanyi, tare da shiga wani yanayi mai wuyar fassara, bayan sanya idanuwanta a cikin nasa.
Fauziyya ta cire glass ?in fuskarta ta ce "Bro, wannan ?anwar ta ka ce take yiwa mutane rashin kunya, duk motocin gidan nan ta rasa wadda za ta hau, sai da muka zo muka ce a kai mu unguwa, wai ita ma tilas ita zata hau a fita da ita"
Ya tsuke fuska ya kalli Iman ya ce "Wato ke tsagerancin naki har ya kai ki din ga yiwa na gaba da ke rashin kunya ko? Sa'anninki ne su?"
Jiki a sanyaye ta kallesu, sannan ta mayar da idonta kan sa, sai dai ta kasa magana, sai hawaye da suka cika mata ido.
"Ina magana zaki yi mini kuka, get out from my sight, stupid girl"
Gaba ?aya ta rasa meya kamata ta yi, jiki a sanyaye ta nufi hanyar fita daga gidan.
"Ke zo nan" ta ji muryarsa ba tare da ta yi tsammanin hakan ba.
Ta juyo ta dawo in da yake tsaye.
"Ina zaki?"
"Napep zan je na hau"
"Wuce ki koma, ba zaki fita ba" yayi maganar cikin bayar da umarni. Ta kalli yadda motar da su Fauziyya suka shiga