Showing 150001 words to 153000 words out of 182697 words
hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Tsayawa yayi cak ya ?ura mata ido, sai yayi mata kwarjini sosai da sosai, hakan ya tilasata yin gum da bakinta tana cigaba da bin sa da kallo.
Hannu ya saka ya ?auko jaririn daga kusa da rumaisa, ai kuwa ta tashi zaune sosai ta tsatstsasreshi da ido, ko ?iftawa ba ta yi, dan kar ya shammaceta ya gudar mata da jariri.
Ya nemi wuri ya zauna, ya ?an tsurawa yaron ido, a hankali ya kai bakinsa kunnen yaron, yayi masa hu?uba da Mahmud kamar yadda ammi ta bu?ata, ba kuma dan yayi niyyar sanya sunan ba.
Ya sauke yaron a hankali yana cigaba da kallonsa, ya ?aga kai ya kalli rumaisa ya ce "A karo na babu adadi, ina sake tambayarki ina aisha take? Bana son ki kai ni bango, in yi miki abun da ba shikenan ba, ki bani amsar tambayoyin da nayi miki, matata na cikin hatsari dole na san in da take"
Kawar da kanta ta yi gefe, ta ?i kallonsa.
"Am talking to you" yayi maganar cikin tsawa ganin yadda take nema ta mayar da shi mahaukaci.
Sake kawar da kanta gefe ta yi, ta dafe kanta da hannayenta, tana ?un?uni.
"Da ke nake, ki bani amsa" ya sake maganar kamar zai kai mata duka.
"Wai dan Allah me kake so na ce maka, ni na san a in da take? Nima fa saceni a kai, ko garinmu ne da zan san ina ne, ka je da kanka mana ka duba, ni na san sunan wurin ne? Kuma wallahi kar sake yi mini tsawa bana so"
Ya yin?ura zai sake magana mama ta yi sallama. Ya ha?iye maganar ya waiwaya ya kalli in da mama take.
Cikin girmamawa suka gaisa, mama ta ce "Ashe ka zo, na je sayo mata magani ne a waje"
Adam ya ce "Eh na zo, ban jima ba, amma ku din ga kai takardar pharmacy zasu baku ba wani abu".
Mama ta ce "A'a basu da shi ne, ai yakamata muma mu din ga ta?ukawa, masu shagunan ne ma basu fito ba, saboda ha?ar?arin da take kuka da shi, ya sanya na fita dubawa".
Adam ya kar?i takardar hannun mama, ya ?au hotonta, ya kalli mama ya ce "In anjima Bashir zai zo, zai taho da maganin sannan ya kai ku wurin X-ray ?in".
Mama ta girgiza kai ta ce "A'a, mun gode ?awainiyar ta yi yawa, hakan ma Allah ya saka da alkhairi yayi maka albarka, ka bari kawai wannan zamu yi ba zai gagara ba da yardar Allah"
"Nima ?an ki ne, ba zan ji da?i ba idan ki ka nuna ba kya son na yi muku abu"
Tsidik ruma ta sanya baki ta ce "A'a bama so, yaya Abubakar zai zo su kai ni, idan ma wayo kake yi mini na fika wayo in gaya maka" ta yi maganar tana harare-harare.
Da ido ?aya yayi mata wani irin kallo, mama kuma ta yi mata da?uwa ta ce "Ke bana ciki da rashin hankalinki, sa'anki ne ko wani ya saka baki da ke? Kin ma ta?a yi masa godiyar ?awainiyar da yake da ke?"
Ruma ta yi shiru tana basarwa, kar mama ta cigaba da yi mata fa?a a gabansa ya rainata.
Huzaifa ne yayi sallama da kwandon kayan abinci, suka amsa masa bayansa kuma Gwaggo ce da lawisa.
Nan suka zauna suna gaggaisawa, Huzaifa ya ?arasa ya kar?i Mahmud a hannun takawa ya ri?e hannun jaririn ya ce "Mai sunan babanmu, kana lafiya?" Yayi maganar kamar jaririn zai amsa masa.
Takawa kuwa bin su yake da ido, lawisa ma ta bi Huzaifa tana cewa ya bata ta ?auke shi.
Adam ya tashi yayi musu sallama ya fice, tabbas ranar da zai kar?i jaririn nan akwai daru, mussaman a wurin uwar ri?onsa rumaisa, yarinyar da ta riga ta fara shi kai bango saboda halinta.
***
"Ammi kin yi shiru baki ce mana komai ba"
Ammi ta ce "To Nusaiba me zan ce muku?"
Iman ta ce "Ammi kina ?oye mana abun da yake faruwa, amma gaba ?aya yanayinki da na takawa a 'yan kwanakin nan ya tabattar da akwai wani abu a ?oye, bama jin da?in yanayin nan sam".
Nusaiba ta ce "Ni fa ina daf da sanarwa Anty laila, wata?ila ki gaya mata meke damunku ku ka ?i gaya mana"
Ammi ta numfasa ta ce "Kar ki kuskura ki ha?a ni da laila, koma menene dole zaku ji, amma ba yanzu ba"
"Yanzu Ammi haka zamu cigaba da kallonku a haka, ba fa haka muka saba rayuwa a tsakaninku ba, taya zamu yi adopting hakan lokaci guda, ammi walwalarki ce fa tamu" Nusaiba tayi maganar kamar za ta yi kuka.
Iman kuwa tuni idonta ya tara hawaye ta ce 'Ammi ko dai nice, idan saboda ni ne, ki kai ni Gombe can family house ?in ku, zan zauna, kuma duk wanda ki ka za?a mini zan aure shi, amma dan Allah ki cigaba da walwala muna ganin murmushin ki"
Tausayin Iman ya kama Ammi, ya kamo hannun iman ta ce "Haba iman ?ina, ki na tunanin akwai wani ?alubale da zai ta so na rabu da ke ne? Kar ki kuma wannan maganar, wani abu ne yake faruwa daban, amma komai zai daidaita in sha Allah".
"Ammi wai muma 'ya'yanki baki yadda da mu ba, muma munafukai ne kenan yaya takawa ne kawai mai iya ri?e sirrinki?" Nusaiba ta yi maganar har cikin zuciyarta.
Duk da halin da Ammi ke ciki, sai da Nusaiba ta bata dariya, ta girgiza kai ta ce "Ba abun da ku ke tunani bane ba Nusaiba, wata yarinya aka tsinto a katsina da jariri" sai kuma ta yi shiru.
"Ammi to meye ha?in hakan da damuwar da kuke ciki?"
Ammi ta ce "?an takawa ne"
Nusaiba cikin rashin fahimta ta ce "Wane takawan? Ta ina za a tsinto yaro a katsina kuma ya zama ?an sa?"
"?an sa ne" Ammi ta basu amsa.
Iman ta ce 'Amma Ammi, ta yaya?"
"?an Aisha ne, ta kawo ?an kwalinta da gwala-gwalanta"
Nusaiba ta ?an dafe goshi a rikice ta ce "Ammi kin hargitsani ban gane ba, ta yaya Anty Aisha da take Saudiyya za'a tsinto ?an ta da ?an kwalinta a Nigeria kuma a katsina, anya ba ?arya yarinyar take yi ba, ko wani abun ake shiryawa ba"
Hawaye ya cika idon ammi, ta ?auki wayarta, ta bu?e ta nemo hoton jaririn ta mi?a musu.
Cikin tsananin mamaki suke kallon hoton, babu in da yaron ya bar Adam saboda kamanni.
Iman ta ce "Ammi, ni fa haryanzu ban gane ba, a ssudiyyan ta haihu ko kuma yaushe ta dawo Nigeria har aka tsinci jaririnta, ita tana ina?"
Nan Ammi ta warware musu komai, kamar yadda takawa yayi mata bayani.
Nusaiba ta dafe kai ta fashe da kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ammi yanzu mai za'a cewa mai girma turaki, tayaya za'a warware wannan lamari? Anty Aisha a hannun 'yan bindiga tsawon wannan lokaci babu wanda ya sani? Kuma Ammi ki ke ?oyewa, idan zancen ya ?ullo ta wani wurin daban fa, kar ki manta ba'a san da cikin nan ba, kuma cewa aka yi zata ?aro karatu, aka yi ta surutu a kai, tayaya za a dawo ace ba ?aro karatu ta tafi ba, har ta je ta dawo an saceta ya haihu sai ?a da ?ankwalinta da gwala-gwalanta, ana ma da tabbacin tana raye?"
Gaban Ammi ne ya sake fa?uwa, jin abubuwan da Nusaiba ta fa?a, take hawaye ya fara gangarowa daga cikin idon Ammi.
Iman ta ce "Anty Nusaiba, komai da muhallinsa, kan ?alubalen ya zo, za a nema masa mafita, wannan maganganun naki zasu sake jefa ammi cikin damuwa"
Iman ta dubi Ammi a tsanake, ta fara goge mata hawayen fuskarta ta ce "Ammina, ki yi ha?uri ki kwantar da hankalinki, duk wani surutu da ?azafi da zs ayi mana, ba zai kai wanda aka yi mana a baya ba, na san da tashin hankali, amma ammi ba zaki ta?a yanke hukuncin da zai cutar da wani ba balle mu. Ki na ji ammi ?addarar haihuwar yaron nan ce ya sanya anty aisha dawowa ?asar nan, kuma suka ?oye miki, duk da yadda suke biyayya ga umarninki, kar ki ?ata ranki ammi, kin san addu'a da ki ke yi mana ce ta zama katanga daga dukkanin sharri. In sha Allah mai girma turaki zai fuskance ki. An tambayi yarinyar ina Anty Aisha take?".
Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Haryanzu fama ake ba ta yi magana ba tukuna".
"To shikenan, in sha Allah za ta yi magana, Sai a bi komai a hankali Allah ya sa tana lafiya, shi kuma jaririn Allah ya raya shi" iman ta sake ?aukar wayar Ammi, tana kallon hoton jaririn.
Nusaiba ta ce "Ba wai tayar muku da hankali zan yi ba, amma kar ku manta masarautar nan ba a iya samun bala'i ba, idan aka sako mutum a gaba da baki da surutu sai zaman garin nan ya nemi ya gagare shi".
Iman ta ce "Haka ne, amma in sha Allah babu abun da ya gagari Allah, Addu'a zamu du?ufa babu dare babu rana. Amma Ammi yaushe zamu je asibitin mu ga yaron muma?".
Ammi ta ce "Ba yanzu ba, ku ?an bani lokaci, bana son mutanen gidan nan su fuskanci wani abu tukuna"
Haka suka cigaba da tattaunawa, sai dai Nusaiba ta kasa magana domin kuwa ta riga ta gama karaya.
****
?aton katafaren office ne, mai ?auke da duk wani kayan alatu na jin da?i da more rayuwa, Senator Usman wakili na zauna a ?aya daga jerin kujerun office ?in, sai kuma ba?onsa da yake zaune a kan kujerar da take fuskantar sa.
"Kana ?aya daga cikin makusantan wancan yaron, da ya dage kai da fata sai ya ga bayana, sai dai kuma kwana biyu na ji shi shiru, duk na gama duk wani shiri da zan yi maganinsa, ko kuma akwai wani abu da yake ?ullawa da ban kai ga sani ba, kar yayi mini bazata".
"Ranka ya da?e shi ?ain banza ja da ikon masu ?asa? Ku ne fa ?asar nan yadda ku ka dama haka ake sha, shi da duk masu goya masa bayan gayyar rashin sanin ciwon kai ce, dan tabbas manyan ?asar nan akwai masu goya masa baya, wanda nake kyautata zaton 'yan adawarka ne".
Wakili yayi murmushi ya ce "Ba abokan adawata bane ba, domin abokan adawata muna aiki tare ne, mabiya kawai muke rainawa hankali".
"Haka ne Yalla?ai, amma a yanzu haka dai, bana tunanin wani shiri yake yi, dan a 'yan kwanakin nan akwai abun da ya ?auke masa hankali, ko office bai fiye zuwa ba, ya ce bashi da lafiya, amma babu tabbas a maganar ta sa"
Wakili yayi murmushi ya ce "Yaro bai san wuta ba sai ya taka, shikenan ka cigaba da sanya mini ido a kan sa, da kawo mini rahoton duk abun da yake ciki, sannan zamu cigaba da shirye-shiryen tsayar da khalifa takarar gwamna, shi ma ba zamu baro ya ?ata masa suna ba".
"Amma ranka ya da?e, na ji wancan satin majalisa ta na?a kwamiti, domin bincikar gaskiyar abun da hukumar dss suke zarginka da shi, ya za'ayi da wannan"
Wata iri dariya wakili yayi ya ce "Duk sa?atta juyatta ne na siyasa, domin juya tunanin talaka baibai, ka san shi talakan Nigeria idan har zai ci ya ?oshi, duk abun da zaka ?ora shi a kai zai bi a haka, babbar damuwar ?an Nigeria ya ci ya ?oshi ne, daga haka ba shi da wata damuwa da yadda abubuwa suke wakana, suma Dss ?in muna nan zamu yi abun da ya dace a kan su"
Mutumin ya jinjina kai ya ce "Yanzu ranka ya da?e wannan kwamitin da aka na?a na binciken shi ma plan ne?"
Kamar mara imani haka wakili ya sake ?ya?yacewa da dariya ya ce "Ka je ka cigaba da yi mini aiki, nima zan yi amfani ?arfin kujerata da fa?i a ji na ?asar nan, na cika maka naka burin".
Risunawa mutumin ya yi yana jinjinawa wakili yana fa?in "Allah ya ida nufi, wakili na kowa"
Yayi maganar yana kamabama wakili, yayin da shi kuma yake ta ?a??aka dariya.
***
Kamar yadda Adam ya fa?a, da azahar bashir ya zo, zai kai rumaisa wurin X-ray, amma mai sunan baba ya ce bai yarda ba, su zasu kaita kar son banzan na su yayi yawa.
Bashir cikin mutuntawa ya ce "Haba Yalla?ai, rumaisa fa ta zama ?anwarmu mu ma, ko ma in ce maka 'yar mu, duk abun da muka yi mata bamu fa?i ba, ka duba girman aikin alkhairin da ta yi mana, ai tafi ?arfin abun da muke yi mata a wurin mu, dan Allah kar ka damu, wallahi ba son banza bane, idan dai har ku?i ne, akwaisu adam ba shi da matsalar su, ku kwantar da hankalinku, dan Allah ka bari a kaita".
Mai sunan baba ya ce "Wanda ku ke yi mana, da wanda ku ka riga ku ka yi mana ma mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, amma muma a matsayin mu na ahalinta yakamata mu tagaza".
Bashir ya ?an langa?e kai ya ce "Zaku ja mini magana a wurin uban gidana, ga kuma uwa uba Ammi, ba za ta ta?a jin da?i ba, sun ?ora ni a kan kula da komai, dan Allah ku yi ha?uri wallahi baku da wata damuwa a kan hakan, ?aukar ?awainiyarta ba yana nufin gazawarku bane ba, yana nufin nuna godiyarmu da jin da?inmu ne a gareku, da yaba karamcinku, duk da mun san ba biyanku zamu yi ba".
Abubakar ne ya ce "Shikenan ?an uwa babu damuwa, Allah ya saka da alkhairi".
Bashir ya ce "Yauwa ?an uwa Amin, ku gama kintsawa sai a fito da ita ga mota can a waje" yana gama maganar ya fita.
Mai suanan baba ya ce "Malam wannan wane irin abu ne, shikenan sai mu zuba musu ido suna ?awainiya da mu, bana son nan gaba su yi amfani da wannan damar, su ce zasu juyamu ka san ba zai yiwu ba".
Abubakar ya ce "Haba dai, in sha Allah babu abun da zasu yi".
Sai da rumaisa ta tabattar da mama ta goya Mahmud, wanda take wa la?abi da Sabir, ta ce saboda ha?urin yaron take kiransa da sabir, tun da suka baro daji bai fiye kuka ba, ba kamar ?an wata malamarsu ba jarababbe mai kukan masifa.
Suka ?unguma suka tafi kai rumaisa x-ray, mama na ta fatan Ubangiji Allah ya sa lafiya babu wata matsala.
***
Adam ya idar da salla yana zaune a kan sallaya, yayi shiru ya rasa abun da yake yi masa da?i, babu tsammani ya ji an turo ?ofar bedroom ?in sa.
Jabir ya gani, ya shigo bakinsa ?auke da sallama.
Ya amsa masa a ciki, yau ya manta bai yi wa masu gadi warning na kar su bar kowa ya shigo ba, koma yayi musu ya san basu isa su hana Jabir shigowa wurinsa ba.
"Adam, wai ina ka shiga ne a kwanakin nan, na zo gidan nan ba adadi, bana samunka idan na je can gida ma baka nan, ina ka shiga haka?".
"Ina nan" ya fa?a a ta?aice.
"A'a, ?an tsaya meyake faruwa ne, ka wani rame, ga fuskarka duk ta kumbura har idonka, menene?"
Tashi Adam yayi ya ninke sallayar, ba tare da ya kula Jabir ba.
"Adam magana fa nake yi maka, ka wani shareni, ni ne fa nake yi maka magana, meya sameka haka?"
"Idan ka tashi tafiya, ka sanarwa masu gadi, kar wanda ya sake zuwa wurina" yayi maganar yana ?o?arin hawa gadonsa ya kwanta.
Ture shi jabir yayi ya tsaya a gabansa ya kalleshi ya ce "Kalleni, da Jabir kake magana, har akwai wani abu da kake ?oye mini a rayuwa? Muna ?oyewa juna wani abu ne?".
Adam ya dafe kansa ya zauna, yana ajiyar zuciya, ya dubi Jabir ya ce "J, gaya maka matsalata ba shi ne maganinta ba, ka yi mini addu'a kawai".
"Mu kan tattauna abubuwan da suke damunmu a tsakanin mu, ko da bamu da mafita, sai dai hakan yana ?ara mana yarda da juna da jin matsalar ?ayanmu ta dukkaninmu ne, dan haka babu bu?atar ?oye mini komai".
Adam ya kama hannun Jabir, suka zauna a tare, ya kalli Jabir ya ce "Ha?i?a ka tuna mini abun da na kusa mantawa, tabbas damuwar ?ayanmu, ta dukkaninmu ce, duk da ina ta ?oye abun, ban bari kowa ya sani ba, amma a kowane lokaci na san dole komai zai fito, amma a yanzu ku ?aga mini ?afa please ".
Jabir ya jinjina kai ya ce "Shikenan" ya fice ya bar Adam, da ganin s yadda ya fita Adam ya san bai ji da?in abun da yayi masa ba, sai dai shima dole ce babu yadda ya iya.
Sai daf da magariba sannan Bashir suka dawo da rumaisa daga wurin X-ray, yanzu tana iya taka ?afafuwan ta sannu a hankali.
Sai bayan sallar magariba, sannan Bashir ya yi musu sallama, mama ta yi ta masa godiya da sanya albarka.
Daga nan asibitin bai wuce ko ina ba, sai gidan Adam, ya tarar da shi ya dawo daga masallaci sannan, lokacin an yi sallar isha'i.
Bayan sun gaisa Bashi ya ce "Yauwwa, mun je an yi mata hoton, likita zai ganta gobe in