Showing 144001 words to 147000 words out of 182697 words

Chapter 49 - KANWAR-MAZA-1_2-COMPLETE BY AYSHACOOL

12 Jul 2024

22402

damuwa iman ta ce "Tare fa muka kwana muka tashi da ke, ban san komai ba, nima dai na shiga damuwa da mamaki, wani abu yana faruwa amma maybe ba sa son mu sani ne".

"Amma ko menene wannan, abu ne mai girman gaske, tun da har ta kai ga ammi ta ce kar wanda ya je wurinta, ga takawa tunda suka fita da abokinsa bai dawo ba" suka koma suka zauna suna tattaunawa a falo.

Baba uwani ce ta same su ta ce "Yaran nan meya samu giwar Galadima ne yau, daga ita har ?an gidana na kasa gane kansu yau, ko abinci ba ta bari an shigar mata da shi ba, shi kuma ina magana bai ko kalleni ba, duk da miskili ne amma ba ya shareni idan na gaishe shi"
Iman ta ce "Zancen da muke yi kenan, bamu san meyake faruwa ba"

"To Allah ya sa dai lafiya" tayi maganar ba tare da ta ji da?in rashin samun wani bayani ba.

?amsshin turarensa da ya daki hancinta ne ya sanya ta san shine, a take ta ?ara tsuke fuska.

"'yan matan ammi, ya na ganku kun yi tsilli-tsilli da ido kamar marasa gaskiya ne?"

Nusaiba ce ta fara cewa "Uncle J ina wuni?"

"Lafiya lau" ya amsa yana ?arewa iman kallo. Banza ta yi masa ta?i kulashi.

"Iman ba zaki kulani ba?" Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta.

Ya ja wata irin ajiyar zuciya ya ce "Ina ammi ne?"

Nusaiba ta ce "Tana hutawa ne, ta ce kar a dameta yau"

"Takawa fa, tun jiya rabona da shi, ga wayoyinsa ba sa shiga gaba ?aya, a gidan nan ya kwana ne ko gidansa?"

"Eh a nan ya kwana, amma yanzu baya nan"

Ya ?an yi shiru sannan ya kuma cewa "Ba ku san in da ya tafi ba?"

Nusaiba ta waro ido ta ce "Uncle J, takawa ne zai gaya mana wani wuri da za shi? Bamu sani ba".

"Wai ya nake ganinku duk wani iri ne, ko akwai abun da ku ke ?oye mini?".

Nusaiba ta ce "A'a Bakomai".

Mi?ewa iman ta yi zata bar falon "Iman" ya kira sunanta.

Ta tsaya cak ta waiwayo tana jiran abun da zai ce.

"Zo ki zauna ina da magana da ke"

Ji ta yi tamakar ta ce ba zata dawo ba, amma ta nemi wuri ta zauna.

Yayi wa Nusaiba alama da ido, a kan ta basu wuri. Ba musu Nusaiba ta tashi ta bar falon.

Kujerar two seater da iman ke kai, ya zo ya zauna, ya ?an tsura mata ido, amma ta takure jikinta, kamar yana motsawa zata zura da gudu.

"Iman" ya kira sunanta, ta ?an ?ago amma ba ta kalleshi ba.

"Meyasa ki ka yi blocking ?ina a what's app, da phone ?inki gaba ?aya?" Tayi shiru tana sauke numfashi.

"Am talking to you, or just because i ask for your pictures, you can deny it if you don't want, meyasa zaki yi blocking ?ina, bari abun da ki ke ta gudun kar in fa?a, i love you, ina son ki iman, kuma zan bi ta in da na san zan samu abun da nake so kai tsaye, kin san tsarin gidan sarauta ai, so gara ki kwantar da hankalinki ki daina kaucewa" hawaye ne ya cika mata ido, amma ta yi ta ?o?arin kar su zubo. Ya gama surutansa ya tashi ya tafi.

Kamar zata kifa haka take sauri, yau ko bari ba ta yi daren yayi ba, saboda yadda maganar ke mimtsininta ji take idan ba ta je ta kai rahoton ba, wani zai rigata.
Sashin Mummy ta isa, ta nemi iso aka yi mata, mummy na ganin yadda baba uwani ta shigo jiki na rawa ta san akwai magana, dan haka ta sallami barorinta, ya rage daga ita sai baba uwani. Ta dubeta ta ce "Meyasa ki ka shigo mini a yanzu? Sai kin saka an fara zargin mu, ina fatan dai abun da ki ka zo mini da shi, mai muhimmanci ne ba shirme ba?"

"Allah ya baki yawan rai, wani ?wai ne yake gangarowa daga kan dutse, kuma da alama idan ya fashe zai yi warin da zai addabi kowa".

Mummy ta yi ajiyar zuciya ta ce "Bani labari".

"Alamu sun nuna akwai wani abu da giwa take ?oyewa ita da ?an ta, dan tun jiya sun kasa sukuni, sun gaza zaune sun gaza tsaye, dan ita yau ta hana kowa ya je in da take har 'ya'yanta, shi ma kuma tun da ya fita shi da wani abokinsa bai kuma dawo ba, suna ta ?umbiya-?umbiya, amma ina nan zan sanya ido, da na ji ?yas zan kawo miki rahoto"

Mummy ta ?an yi shiru sannan ta ce "Ta ka?aice ta hana kowa zuwa in da take, ciki har da 'ya'yanta, lallai abun da yake cikin ?wan nan, ba ?arami bane ba, ki cigaba da sanya ido, ?wan ya fashe a kan idonki, kuma da zarar ya fashe ina son ki riga kowa sani, ya kuma nice wadda za ta fara jin ko menene, ina nan ina jiranki, haka zalika nima zan sanya ido a nawa ?angaren"

"Allah ya baki masara, in Allah ya yarda za ayi duk abun da ki ka ce, na barki lafiya" Mummy ta ?aga mata hannu alamar zata iya tafiya.

Baba uwani ta tashi tana murnar yadda ta sanya farantawa uwar ?akinta ta ?oye.

Unguwar su ruma ta ?auka cewar ta dawo, magana har islamiyyar su, gaba ?aya unguwa ta ?auka, aka din ga yi musu addu'a da tayasu murna.
Huzaifa ne yayi hankalin cewa a kira katsina a waya a sanar musu da anga rumaisa, dan gaba ?aya ma sun manta da batun su.
Sai da mai sunan Baba ya kai mama ta ga nata likitan, sannan suka tafi Asibitin da rumaisa take.
Gaba ?aya rumaisa ta kasa daina kuka, saboda farincikin ganin 'yan uwanta gaba ?aya a tare da ita, da ta motsa a tambayeta me take bu?ata.

'yan uwa da abokan arziki kuwa da ma?wabta tuni suka fara sintiri a asibitin, domin duba ruma, kowa yazo da ?an abun alkhairinsa da zai bawa rumaisa.

'yan uwansu na kano kuwa suma tuni suka cika asibitin, wannan su zo wannan su tafi, sai ga hauwwaliya ma sun zo da sandarta ta dogarawa, kasancewar tun karayar da ta yi kan a sace rumaisa ba ta warke ba. Suka rungume juna.

Ruma ta ce "Hauwwaliya gurguwa ki ka zama ne? Na ganki da sanduna"

Hauwwaliya ta ce "Ke ba gurguwa na zama ba, kin manta na karye ne?"

Ruma ta ce "Au haka ne fa, ban zo na ganki ba ma fa aka saceni".

"Allah sarki rumaisa, kin ga idi, zaman hannun 'yan bindiga an ce wahala ake sha fa"
Ruma ta yamutsa fuska ta ce"daina tuna mini dan Allah, wuya ko da magani babu da?i"

Likita ne yayi sallama shi da nurse, mama ta yi musu sannu da zuwa, mai asibitin ne da kansa ya kalli ruma ya ce "Sai ka ce mun kwantar da shugaban ?asa, 'yan dubiya daga wannan sai wancan, kamar ba wani mara lafiya sai ke" ruma tayi murmushi tana kallon trolleyn da suka shigo da ita, tana fatan ba za ayi mata allura ba.

Yayi murmushi ya ce "To yaya jikin naki?"

"Da sau?i, amma ha?ar?arina fa yana mini ciwo haryanzu"

Ya ce "Mu ga wurin, ya aka yi ha?ar?arin yake yi miki ciwo?"

"Sule ne ya takani a wurin, wani jibgege, nauyin ?afarsa kamar tsauni". Yayi murmushi yana ?o?arin mi?a hannunsa ya ?aga rigarta ya duba, amma ta ri?e rigar ta tsareshi da ido.

"Dubawa zan yi na gani"

Aliyu ne ya taso, ya kama rigar tata zai ?aga "Yaya Aliyu ni kar ka bu?e mini jiki a ganni"

Aliyu ya ce "Ke dallacan, ina tsintoki a ka yi kanki ko ?an kwali babu, wa zaki yi wa iyayi? Ko shi wanda ya taka kin kin yi masa iyayin?"

Tana zum?ura baki ya ?aga rigar, likitan ya danna ha?ar?arin, ta saki wani marayan kuka.

Ya ce "Is ok, zan rubuta muku hoto in sha Allah, ayi mini hoton wurin, da kuma kanki".

"Wurin mai hoto za a kai ni? Ayi mini a waya mana, bana son motsawa ko ina ns jikina ciwo yake"

Ya girgiza mata kai ya ce "X-ray nake nufi, ba hoton passion ba, sauko yau ki taka ?afar nan na gani" ta girgiza masa kai ta ce "Tana yi mini ciwo fa"

"Sai fa kin taka yau saukko, da yayi ki ka yi gudu ki ka fito daga daji?".

Shiru ta yi sannan ta ce "Ikon Allah ne ya fito da ni" ta fara ?o?arin saukowa a hankali ta tsaya a kan ?afarta. Likitan ya ce "Good, taka a hankali mu gani". Tana ?o?arin ?aga ?afar, amma ji take kamar ba a jikinta take ba, dan haka ta kasa.

Likitan ya ce "Ri?e hannuna, ki ?aga ?afar a hankali, bana son ganinki a kwance kullum"

No?e kafa?a tayi, ita ba zata ri?e hannunsa ba.

Ya saka hannu ya ri?o na ta hannun, ya ?an ja ta sai da ta ?aga ?afar sai da ta yi ?ara saboda ciwon da ?afar take yi.

Usman ne ya taso, ya cire hannun ruma da ga na likitan ya ce "Zamu zagaya da ita in sha Allah, in dai ?afar ce zata din ga takata" murmushi yayi ya girgiza kai, ?iri-?iri ba sa iya ?oye kishinsu a kan ?anwarsu, zai duba mata rauni, Aliyu ya taso ya bu?e masa da kansa, yanzu kuma Usman ya zare hannun ruma daga nasa.

Ya rubuta musu duk abun da yake so a kawo masa, ya fita daga ?akin.

Hauwwaliya ta dogaro sandarta, Usman kuma yana ri?e da rumaisa suka fita zagaya asibiti.

A hankali rumaisa tana takawa, har suka je ?akin da jaririnta ke kwance, nurses na kula da shi, sune suke yi masa komai. Ruma ta da?e a wurinsa, sanann suka fito, a wurin komawa ?akimta kuma ?afa ta?i takuwa, ?arshe sai Goyata Usman yayi ya mayar da ita ?aki.

Ammi ba ta fito ba sai la'asar, shi ma da ta fito tea kawai ta saka a kai mata, shi kawai ta iya sha, kai da ka ganta ka san a tashin hankali take.
Wayar Adam take ta kira amma ba ta shiga.

Ta fito falo ta tambayi barorinta ko Adam ya shigo? Suka ce mata tun safe da ta raka shi ya fita, bai kuma dawowa ba.
Ammi ba ta samu wayar Adam ba sai magariba.

"Ina ka ajiye wayarka nake ta kira amma ba ta shiga?".

"Ammi na kashe wayar ne, saboda bana son a dameni da kiran waya".

"Wannan ba hujja bace, ka san dole zan neme ka ai, ya ake ciki akwai wani abu ne, ko yarinyar ta yi magana a kan Aisha?"

Kamar yana gaban Ammi, ya girgiza kai ya ce 'Ta ?i magana, ta ce bata san komai ba".

Cikin rashin fahimta Ammi ta ce "Kamar yaya?"

"Haka dai ta ce"

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ka zo ka sameni, asibitin zamu tafi yanzu ".

Ya sauke numfashi ya ce "To gani nan" ya ajiye wayar yana jin yadda kan sa ke sara masa, saboda damuwa da tunani.

Sai kusan ?arfe tara na dare sannan Takawa ya zo tafiya da ammi, sai a lokacin su Iman suka samu damar ganin ammi.

Cikin damuwa Iman ta ce "Ammi ina zaki?, yau gaba ?aya bamu ganki ba"

Cikin ?arfin hali Ammi ta ce "Ku yi ha?uri, wata unguwa zamu je, yanzun nan zamu dawo ba da?ewa zamu yi ba" daga haka ta yi gaba ta bi bayan takawa suka fice.

Iman ta ce "Yaya Nusaiba, akwai matsala fa, Ammi suna ?oye mana wani abu ba sa son mu sani".

Nusaiba ta ce "Nima na gani, amma bari mu jira mu gani".

Ita iman abubuwan sun yi mata yawa, ga maganganun wambai, ga zancen da yake yawo a kan su da takawa, ga abun da take gudu Jabir ya furta wai yana son ta.

Kamar kurame haka su Ammi suka ?arasa Asibitin da rumaisa take.

'Yan dubiya duk sun watse, sai Mama da Abdallah mai sunan baba suna ta shirin tafiya gida, Mama ta wanke jaririn nan tas, an ha?a madara an bashi, ya gama sha ruma tana rungume da shi, tana kallonsa tana tuna irin yadda suka sha gwagwarmaya kan su ku?uta.

A hanyar barin asibitin, mai sunan Baba suka ha?u da Adam da Ammi, ?an kallon kallo suka yi da shi da takawa, amma babu wanda ya kula wani, suka wuce.

Sallamar su Ammi ce ta dawo da rumaisa daga tunanin da take yi, ta ?aga kai ta kallesu ba tare da ta amsa sallamar ba, Abdallah da mama suka amsa suna yi musu barka da zuwa.

Ruma ta ?an ?are musu kallo, fuskar takawa kamar ta mai amai da gudawa, duk yayi wani iri, mama ta basu wurin zama, suka gaggaisa ammi ta dubi ruma ta ce "Maman baby ba magana?"

"Ina wuni" Ammi ta ce "Lafiya lau, ya jiki ya baby kuma?"

"Lafiya lau".

Ammi ta ce "To Alhamdilillah"

Mama ta ce "Jiki da sau?i kam, domin yau har ta tattaka, gobe in Allah ya kaimu zamu je mu kaita hoton ?afar da kai, da kuma ha?ar?ari da take kuka da shi".

Ammi ta ce "Allah sarki, karki damu, zan aiko s kaita".

Mama ta ce "A'a kar ?awainiyar ta yi yawa, zamu kaita in sha Allah"

Ammi ta ce "?awainiya ta wuce tserato wa da ta yi da wannan jaririn, ai duk abun da muka yi mata bamu fa?i ba".

Mama ta ce "Rumaisa kawo jaririn su ganshi mana".

"Amma mama kar ki bashi ?ana"

Mama ta ce "Shi wa?"

"Wancan mutumin" tayi maganar ba tare da ta kalli Adam ba.

Guntun tsaki mama ta yi, ta kar?i jaririn, ta mi?awa Ammi shi, Ammi ta kar?e shi tana murmushi tana ?are wa yaron kallo, kamannin adam ne sak yaron ya kwaso.

Ta dubi ruma ta ce "To maman baby, ba a saka masa suna ba haryanzu?".

Ruma ta ce "Na saka masa suna, sunansa Mahmud!" A tare Ammi da Adam, suka ?ago suka kalli rumaisa, ita kuwa ta basar dan ba ta san me ta yi ba.

Paid book ne ?500, via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank
Ayshercool.
08081012243










https://chat.whatsapp.com/G9XU8tDJMjq02zlZMHurZ5*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

?? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*








*?500 ne, via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*



Ammi sai da ta ?an yi jimm, sannan ta dubi rumaisa ta ce "Ita aishan ce ta saka masa wannan sunan?"

Ruma ta ce "A'a, ni na saka masa, sunan babana ne, ina son sunan sosai"

"Ba shi ne sunan da na yi niyyar sakawa ?ana ba, ba zan saka wannan sunan ba" Takawa yayi maganar cike da iko, sai da mama ta ?an ji babu da?i, ko da zai canza sunan bai kamata ya fa?a a gaban ruma haka ba, ba za ta ji da?i ba.

"Ka ga ba fa ?anka bane ba, tun da ni ta ce ta barwa shi, ?ana ne Mahmud na saka masa, kuma ba zan canza ba" ta yi maganar tana yi masa kallon banza.

Ammi ta ce "Madalla, suna mai girma da karama, Ubangiji Allah ya raya Mahmud,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login