Showing 66001 words to 69000 words out of 182697 words
sa?a, ta ?auko ni?a ta taho gida, sai dai ni?an da nauyi.
Ba tsammani ta ji an ce "Sannu ko" ta ?aga kai ta kalli mai maganar, ba ta amsa masa ba ta cigaba da tafiya. Biyota ya yi ya ce "Daga ina haka?"
Ruma ta tsaya ta kalleshi ta ce "Ba dan ka kusa sa'an yaya Usy ba, da sai na ce maka kai ka aike ni da zaka tsareni da tambaya?"
Ya girgiza kai ya ce "No, yi ha?uri kawo na tayaki ?aukar kayan"
Ruma ta ce "Yauwwa, kamar ka san na gaji kuwa" ta ajiye masa ni?an ya ?aukar mata.
Suna tafe yana yi mata tambayoyi, ita kuma hankalinta yana kan sa?arta.
Babu zato babu tsammani sai ganin Yaya Aliyu ta yi a gabansu, gabanta ya fa?i ta ce "Yaya"
Rai a ha?e ya ce "Waye wannan?"
Ta kalli mutumin ta ce "Oho kawai ganinsa na yi"
Mutumin ya yi murmushi ya ce "Ashe yayanmu ne, barka da yamma"
Aliyu bai amsa ba ya ce "Malam meye ha?inka da ita?"
"A'a babu komai, kawai dai na tayata ?aukar ni?an ne, sannan dan Allah idan babu damuwa, ni dai ina son ta ne, dama na biyo ta ne domin na ga.....
"Haba bawan Allah, ina kai ina wannan yarinyar 'yar cikinka, meye wani abin soyayya a wurinta ban da salon ?ata tarbiyyar yarinya"
Ruka kuwa ta bu?e baki ta ce "wai sona ka ke ka zama saurayina, ta? to ai ni ba zan yi aure ba"
Yayi murmushi ya ce "Eh mana, yayanmu ni zan jirata ko nan da shekara nawa ne idan muna raye zan jirata"
Aliyu ya sake tsuke fuska ya kalli ruma ya ce "Wuce ki tafi gida"
Ruma tayi gaba tana ?ata rai, ya ce "Zo ki kar?i kayan naki"
Ruma ta ce "Ka ajiye wa Yaya Aliyu ya taho da su"
Aliyu ya ce "Ni ne zan taho miki da aiken"
Kwasa ta yi da gudu, ko waiwayowa ba ta yi ba, dan kar ma ya ce sai ta ?auko ni?an dan ta gaji.
Kamar korarriya mama ta ga ruma a cikin gidan, tana ta sauke numfashi.
"Lafiya ina aiken? Ko fa?an ki ka je ki ka yi?"
Ta girgiza kai.
"To menene, ina aiken?" Ruma ta sake tura baki.
"Ke magana nake miki kin shareni"
Kan tayi magana Aliyu ya shigo, da ni?an Mama.
Ya dire ni?an yayo kan Ruma, ta zura da gudu ta shige bayan mama.
"Wai meyene, lafiya?"
Aliyu ya ce "Ita ta san me tayi ai, wani bagidajen gaye ne, da wani tattararren ?afar wandonsa, wai wannan bagidajiyar yarinyar ya biyo wai yana son ta, sai da na kusa ?u??ura masa ashar, banda son lalata tarbiyyar yarinya, uwar me yake nema a wurin wannan yarinyar mai rabi hankali rabi hauka?"
Mama ta ce "Aliyu, ba ina sukar matakin da ka ?auka bane ba, amma wanda ya ce yana son naka ai ba ma?iyinka bane, duk abin ku fa ko kuna so, ko ba kwa so dole watarana sai kun aurawa wani ta bar gidan nan, ku daina wula?anta mutane Sabo sun ce suna son 'yar uwarku".
"Ni bana son shi, ?afarsa busu-busu ko mai bai shafa ba, kuma sai warin rana yake"
Hannu mama ta saka, ta mako ruma daga bayanta, ta din ga yi mata fa?a.
Duk da ita ruma ko fa?an ka yi mata ba ganewa take yi ba.
***
Iman ce ta shiga sashen Ammi da sauri, sai dai Ammi ta ?an razana ta ce "Lafiya kuwa?"
Iman ta ce "Ammi, ina ga yaya Mahmud ne zai koma makaranta, na gansu a haraba kamar airport Mummy za ta kai shi".
Da sauri Ammi ta tashi, ta zaga ta ventilation ?in ta, ta le?a ta window, ta hangi Mahmud ya bu?e bayan mota ya shiga, Mummy ma ta shiga an kunna motar sun yi gaba.
Jiki a sanyaye Ammi ta saki labulen, ta shiga ambaton sunan Allah, Iman ta rungumota ta na fa?in "Ammi kina lafiya? Ki yi ha?uri ki kwantar da hankalinki fa, kar ciwonki ya tashi" sai dai kan Ammin ta yi wata magana numfashinta ya fara sama-sama.
(Book 1 free ne, book 2 paid ne).
Ayshercool
08081012143
[04/08, 9:06 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
P 20
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHE?I TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*
*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban ha?a 1k subscribers a channel ?ina ba, anya akwai amana kuwa??*
Ku yi subscribing YouTube channel ?in
@Cool Hausa Novels, domin samun da?a?an litattafan hausa na sauraro.
P20
*Page ?in sukutum guda naki ne masoyiyya Zainab kumurya, idan kin ga dama ki yayyaga shi ki zubar ko ki kashe Ruma, tun da naki ne??. Ke kuma marubuciyar mijin malama Nimcy ki ji tsoron Allah, wallahi ana ta ?orafi kin sako jaruma da masifu amma kin yi burus da mutane, zan kar?e rubutun mijin malamar nan fa?? wanda bai karanta ba ya garzaya mijin malama an gama book1 labari mai tsayawa a zuciya*
A gigice Iman ta ri?o Ammi tana jera mata sannu, jinjina mata kai kawai Ammin ke iya yi, amma ta kasa magana.
Iman ta rungumota ta zaunar da ita a kan gado, cikin damuwa ta ce "Ammina, dan Allah ki yi ha?uri, ban nuna miki dan na tayar miki da hankali ba"
"Kar ki damu Iman, ba ki tayar mini da hankali ba, kawai dai tari ne ya taso mini, kawo mini ruwa a fridge mai sanyi na sha.
Cikin rawar jiki Iman ta tafi ta kawowa Ammi ruwa, ta kar?a ta sha, sannan ta ?an kwanta ta lumshe idonta. A take ?wa?walwaarta ta shiga tariyo mata abin da suka wakana a shekarun baya, daga kafuwar gidan zuwa yanzu, abubuwa da dama sun faru masu matu?ar wahalar mantawa da kuma ru?ani, wanda haryanzu a haka ake, komai sake dagulewa yake yi. A hankali ta gyara kwanciyarta tana son ta kawar da tunanin daga zuciyarta, amma sai kaiwa da komowa abubuwa suke a ?wa?walwarta suka hanata sukuni.
***
Ruma kuwa a 'yan kwanakin nan ta addabawa Yasir, kusan kullum tana li?e da shi tana kallon waya, idan anjima ta ?au wayar Usman ta fara game, ya zo yayi ta zaginta ya ?wace, sai ta koma gefe ta ?au wayar mama, ta yi ta yi wa ?awayenta fulashin, wasu su biyo wasu kuma suma su yi ta mata fulashin, babban abin da yake ?onawa mama rai fulashin, wataran wayar haske kawai take yi, ko sai ta fara ringing ta zo ?agawa ta katse, mama ta yi ta masifa ta ce "Idan baki kiyayeni ba, da ke da ?awayen naki sai na sa?a muku, gayyar rashin hankali".
Yasir yana ?an ta?a gyaran wayoyi, ya iya harkar jagwal, shine gyaran waya, system da sauran kayan electronics.
Wata waya ya samu, ta sha jiki, ya sayo layin data, ya saka a wayar, ya bawa ruma ya ce "Gashi nan, ki dinga kalle-kallen ki a wannan ki ?yale mini wayata, kuma ki daina ?aukar wayar mama kina fulashin, ki yi da wannan, saura ki lalata kuma akwai lokacin da zan dinga kar?a, dan ba bar miki na yi ba. Na bu?e miki account amma ban saka sunanki ba, ?anwar maza na saka na ?ora miki hoton flower a dp kar a gano mu".
Ruma tamkar ta goya Yasir dan murna da farin ciki, ta gurfana ta dinga yi masa godiya, tare da sanya masa albarka.
"Amma ki ja bakinki ki yi shiru, kar ki gayawa kowa"
"In Allah ya yarda ba zan gaya wa kowa ba, bakina ?anin ?afata, amma me yasa ba zaka saka mini sunana ba da hotuna na nima?"
"Dan ubanki gidanku kuna da background ?in da zaki dinga hoto ne? Kuma ni ban baki dan ki saka hotunanki ba, dan wallahi kin san idan suka gano kashinmu ya bushe, idan kin san ba zaki bi abin da nace ba, to tun wuri na kar?e kowa ma ya huta"
"A'a Allah ya baka ha?uri, da wasa nake maka nima, idan bana komai sai ka dinga bani ina ganin duniya nima, a daina hantarata dan na le?a waya".
Tun da Yasir ya bata wayar nan, aka samu sau?in neman magana a cikin gida, kusan koda yaushe tana kan wannan jagwal ?in wayar, kuma Yasir abubuwan karatu yayi mata following, dan haka su tafi gani, kuma sosai suke ?auke mata hankali, ya fi bata da daddare idan ya tabattar ta gama ayyukanta, da assignment, sai ya bata ta zauna a kusa da shi ta kalla, da lokacin kwanciya ya yi ya ?wace wayar ya korata ta kwanta.
***
Zuwa la'asar Ammi ta ?an samu nutsuwa, sai dai kallo ?aya zaka yi mata ka san tana cikin damuwa.
Takawa ya fuskanci damuwa ?arara a fuskar ta, sai dai ganin yadda take basarwa ba ta son magana, ya sanya shi yin shiru bai yi ?o?arin tilasta mata jin abin da yake damunta ba.
Wurin Jabir ya tafi, domin samun sau?in wasu damuwoyin da suke damunsa, kasancewar sa ?an uwa ?aya tilo da ya fi yarda da shi.
Jabir na ganinsa ya ce "Sarkin matsala, tun kafin ka yi magana, fuskarka ta nuna akwai damuwa, yau kuma menene?"
Takawa ya ?an yi shiru, sannan ya ce "Khalifa Usman wakili"
Jabir ya tsuke fuska ya ce "Ba zaka rabu da sabgar wannan yaron da ahalinsa ba ko?"
A hankali Adam ya ?an lumshe idonsa, ba ya son yin dogon jawabi da ga Jabir, tun da shi jabir haryanzu ya kasa gane abin da yake nufi game da khalifa, dan haka kawai yayi shiru ya cigaba da tunani.
"Ina Ammi?"
Adam ya bu?e idonsa ya kalli jabir, amma bai yi magana ba, so yake yayi masa zancen muryar nan da yake ji, wadda haryanzu ya kasa daina jinta a kunnuwansa, amma ya san da ya ?ago zancen Jabir zai yi masa wata fassarar. Bai gama fahimtar mai Jabir ya cigaba da cewa ba, sai jin sunan Iman da yayi Jabir ya furta.
Ya ce "Me ka ce ne?"
"Ni fa matsalata da kai wula?anci, duk surutun da nake ba ka ma gane me nace ba?"
"Sorry" ya fa?a a ta?aice yana tsare Jabir da ido alamar yana son ya maimaita masa me ya ce.
Jabir ya ce "Well, cewa na yi, wai me ?aninka yake nufi da Iman ne, yana takura mata da yawa fa"
"And so...?"
"Kana nufin ba ka damu ba kenan?"
"Kaga ni ka ?yaleni da sabgar gidan nan, bana iya tunanin komai a kai, ko na fara ma kaina ciwo yake yi, gaba ?aya bana son yin tunani a kan matsalolin gidan nan ".
Jabir ya yi ajiyar zuciya ya ce "Haka ne, ni auren Iman nake son ku bani, ka wuce mini gaba zuwa wurin Ammi mana".
Wani irin kallo Adam ya yiwa Jabir ya ce "Ba ka da hankali ne?"
"Ban gane ba ni da hankali ba?"
"Amma ka san ba abu ne da zai yiwu ba ko?"
Jabir ya ce "Saboda me, wai ni ko dai kai ne ka ke son ta ne?"
Tsaki Adam ya yi ya tashi ya ce "Ka san idan har zan auri Iman, zan iya auren su Nusaiba ko Fauziyya, kai ma ka san ba zan bari ka auri Iman ba, kuma ka san dalili".
"Amma a tunanina wannan bai kai hujjar da za a hanani aure ba"
A ?an hasalae takawa ya ce "A ganinka ba"
"Amma....." Bai jira jabir ya gama maganar ba, ya fice ya bar Jabir.
****
Ruma ce a tsakar gida, ta zage tana ta dakan ?uli-?uli, zata yiwa Yasir kafi kaza, dan ya ?ara samun ?warin gwiwar bata waya tana jagwalgwalo, dan wayar ta fara shiga ranta sosai, ga cacar ku?in data yana yi mata, da na caji wasu lokutan, tayi kiran ?awayenta a wayar iyayesu su yi ta shashashanci ta daina ?aukar ta mama.
Mama tana ganin wayar a hannun ruma, tana mitar ba ta son yawan duba wayar nan da take yi, a zatonta wayar Yasir ce kawai yake bata ta yi game da wasanta ta bashi kayarsa.
Mai sunan Baba ya nutsu ya tattara hankalinsa a kan litattafansa, sai dai hankalinsa ba a kan litattafan yake ba, damuwa da tunani ne fal a ransa, zuwa yanzu yakamata a sake aikawa da Abubakar ku?i ko babu yawa ne, dan har zuwa yanzu ya ce masa bai samu wani aikin ba, leburanci ne ya kan shiga cikin gari ya nema idan ba shi da lectures, kuma gashi ?an abin da za a baka na leburancin nan, bashi da wani yawa ga wuni ana aikin ?arfi.
Ga ku?in saukar su Yasir, ga ku?in Necon su, dan dai suma yaran suna da ?o?arin neman na kai, da karambani Yasir ya koyi gyaran fitila, da wayoyi gashi ya san kan computer sosai, yanzu zai kashe wata wayar ya tashi wata yana da kai a wannan fannin.
Shi kuma Huzaifa big boy ne, shi baya tanadi, idan ya samu ku?i kawai ya kashe su, a huta. Sai dai bashi da rowa, yana zuwa shagon ?inki da na aski, amma mugun mashiririci ne na gaske.
Sallamar da aka yi ne, ta dawo da mai sunan Baba daga tunanin da ya tafi.
Wata yarinya ce sa'ar ruma, sai kuma wata 'yar budurwa suka yi sallamar.
Fuskarsu kawai ya kalla, ya san da ?uyar idan ba ruma ce, ta yi wata tsiyar ba.
Suka gaida mama cikin ladabi, shi kuma ya mayar da hankali a kan littafin gabansa kamar bai san da zuwansu ba.
Zumbur ruma ta mi?e, za ta janye su, mama ta ce musu yaya aka yi, saboda ita mama a tarbiyyar ta ?awaye ba sa biyo ruma gida, idan ba wani abu ne mai matu?ar muhimmanci ya kawo su ba.
'yar babbar ta ce "Ku?in da ?anwata take bin ruma, muka zo kar?a".
Cikin mamaki Mama ta ce "wane ku?i kuma?"
Yarinyar ta ce "Ranar an aiki ?anwata, suka ha?u da ruma, shi ne a canjin mamanmu, ruma ta ranci naira ?ari biyu ta bawa wani tsoho almajiri, wai ya bata tausayi da ga gani yunwa yake ji, wai zata bata ku?in kuma haryanzu ba ta bayar ba, mamanmu kuma so take ta yi amfani da ku?inta"
Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ita ruman? Uban waye ya ce ki kar?ar musu ku?i kiyi sadaka da su?"
"Wallahi mama tausayi ya bani, cewa yayi na taimaka masa, kuma idan na bayar da ku?inki zaki yi mini fa?a, shi ne na ranci canjin babarsu, kuma malam ne ya ce mana sadaka maganin masifa ce"
"Ke a cikin wace masifar ki ke? Ko da yake akwai masifar da ta wuce ?auko mini magana da ki ke yi ba yau ba gobe, baki yi sadaka da ku?in uwarki ba sai na uwar wasu, saboda tsabar rashin ji?"
Abdallah ya ce "Wallahi mama yarinyar nan da ?yar idan ba ta da ta?in hankali".
Mama rasa me zata yiwa ruma ta huce ta yi, saboda yadda take caza mata kai abin ya wuce hankali, sai ?ifta ido take kamar an kwashewa karya 'ya'ya, gefe ?aya kuma tana hararar yaran.
Mai sunan baba ya kalli Ruma, ya ga tana yiwa yarinyar alamar idan suka ha?u sai ta yankata.
gashi yau Mama ba ta da wani ku?in kirki, ga ruma zata ja mata fitar naira ?ari biyu ba dalili.
Mai sunan Baba ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro naira ?ari biyu ya ajiye ya kalli yaran ya ce "zo ki ?auka"
Cikin fargaba da tsoro yarinyar ta tafi ?aukar ku?in, dan fuskarsa ma kawai abar tsoro ce saboda kwarjini.
Har ta dur?usa ta ?au ?arin, ya kalleta sai da hantar cikinta ta ka?a, ta dakata da ?aukar ku?in.
"Ke shashashar ina ce da wata za ta ce ki bata aron ku?in babarki, ki bata ta bayar kina tsaye san sokwanci"
Jiki na rawa ta ce "Idan ban bata ba zata iya dukana"
"Idan ta dakekin ba zaki iya ramawa ba, ko ?arfinki ta fi? Daga yau idan kuka kuma bata wani abinku, ku ka biyota gida kawo ?ara, da ku da ita zan ha?a na zane, ?auki ki tashi ki bani wuri"
Kamar mai shirin ?auko wani abu a wuta, haka ta mi?a hannu ta ?auko ku?in, ta tashi suka fice da sauri.
"Ke kuma zo nan" yayi ya yana kallon inda ruma take.
Jikinta har wata tsuma yake, ta taso ta zo in da yake ta dur?usa.
Ya ?are mata kallo ya ce 'har kin manta shara?inmu ko?" Ta girgiza kai.
"Da kyau, nan da gobe in Allah ya ki nemo ku?ina da na bayar ki biyani, dan ba zan ?au asara ba, kuma ban yarda ki tambayi wani a gidan nan ya baki ba, kuma ki ka je waje ki ka ?auko magana sai na takaki a gidan nan, mara kan gado tashi ki bani wuri" da sauri ta zabura ta bar gabansa tana tsuma, ita yanzu a gidan uban wa za ta samo ku?in da zata biya shi?.
Haka ta koma tayi zuruuu, kamar ruwa ya ji?a mage, tana ji a ranta idan ta kama yarinyar nan sai ta daku, saboda ja mata damuwa da ta yi.
****
Samha ce zaune a falo, tana shan twa da biscuit tana yi tana kallon tv, tare da ka?a ?afa.
Wayarta ce ta fara ringing, dan haka ta ajiye kofin tean, ta ?au wayar ta kara a kunnenta.
"Samha" ya kira sunanta a ta?aice.
"Waye?" Tayi maganar cikin ?osawa.
"Khalifa Usman wakili"
"Wai meye ha?ina da kai ne? Me ka ke so kuma?"
"Easy mana, a kan