Showing 75001 words to 78000 words out of 182697 words
ta kalli takawa ta ce "Wallahi ban yafe ba ku....."
"Ke wuce mu tafi, kin samu an ?yaleki kuma kina yi wa mutane iskanci, mara tarbiyya"
Cikin dakiya ta ce "Eh bani da tarbiyyar, ku tarbiyyar ce ta saka kuka ?auko ni ba da sanin iyayena ba ku ka kawo ni nan, cikin maza Allah sai ya saka mini"
Jabir ya ce "Kar ka kuma tankawa yarinyar nan, mayar da ita"
Jabir ya zauna a kusa da takawa ya ce "Takawa, wa me yake faruwa ne, ka san ta ne?"
Adam yayi shiru bai motsa ba, kuma bai ce komai ba, Jabir ya yi masa tambayoyi har ya gaji, amma bai amsa masa ba.
Ruma kuwa suna zuwa unguwar su, suka ajiyeta suka tafi, ta samu wani borehole ta wanke fuskarta, sannan ta tafi gida.
A tsakar gida ta tarar da Yaya Aliyu, ya kalleta ya ce "daga ina ki ke?"
"Makaranta" ta bashi amsa tana ?ata rai.
"Ba jarrabawa ku ke yi ba?"
"Laifi muka yi aka saka mu punishment" ta bashi amsar tana tsoron kar ya ganota.
"Haka dai ki ka iya, kullum cikin laifi kamar ke ka?aice ?aliba a makarantar"
Ganin bai ganota ba, ya sanya ta shiga ?aki, ta ajiye jakarta ta tafi gaban mudubi ta tsaya, ta ?arewa kanta kallo, ta tuna yadda takawa ya sha?eta hannunsa har yana ta?o ?irjinta.
Wasu hawayen ne suka shiga ziraro mata. "Wallahi sai ka gane baka da wayo, ka zunguro sama da kara, ni za a ciwa mutunci? Wallahi sai na kuma rubutawa, zaka gane ba ka da wayo, ai talauci ba hauka bane, mai kyan banza" haka ta tsaya a gaban mudubi, ta cigaba da kuka.
Kamar zararriya ta ?auko jakarta, ta ?auko wayar ta kuma komawa kan account ?in da Jabir ya saka hoton takawa, ta sake rubuta "Wallahi Allah ban yafe ba, sai na kai ?ararka wurin 'yan sanda, zaka san da ni kake yi" ta ajiye wayar tana fatan Allah ya sa kar idan mama ta dawo ta fuskanci wani abu.
****
Baba uwani ce ta shiga kitchen ta tarar da iman tana faten dankali.
"A'a mutuniyar ba kya gajiya da aiki, Ammin ake yiwa girki ne?"
Iman ta yi murmushi ta ce "A'a baba uwani, nice zan ci"
"Au yau ba za a ci abincin namu ba ne?"
Iman ta yi murmushi ta ce "Ba haka bane, kawai da wannan ?in nake sha'awa bana son takura muku ne"
"A'a ai da kin fa?a ma babu wani abu, sai ayi miki, ni kuwa na ce takawa lafiya ?alau kuwa yake?"
Cikin rashin fahimta iman ta ce "Me ki ka gani?"
"Ganinsa na yi duk wani iri"
"A'a lafiyarsa ?alau, ina ga hakan ya na da ala?a da yanayin aikinsa, kin san abubuwa su kan yi masa yawa"
Baba uwani ta ce "haka ne wallahi, ina tausayawa takawa yadda al'amura suke shan kansa Allah ya yi masa jagora"
Iman ta ce "Amin" a dai-dai lokacin ta juye dankalin a plate ta ?auka ta fice.
Baba uwani ta yi tsaki ta ce "Kai wannan yarinyar kininabbiya ce ba wani abu da zaka samu daga wurinta".
Takawa fa abubuwa suka sake rikice masa, tun bayan ha?uwarsa da ruma, da ya ji muryarta da take masa yawo a kunne, yana ta tuntuntuni, mutum ce ko akasin haka, dan iya ?warin gwiwar ta, da rashin kunya da ayar tambaya a kanta.
Yau gaba ?aya bai koma gida ba, ya wuce gidansa ya tura wa Ammi message a kan ba zai shigo gida ba, a gidansa zai kwana.
Bayan ya turawa Ammi sa?on, ya kuma komawa Instagram, ya duba comment ?in da ruma ta yi a kansa, kawai ya ci karo da sabon sa?onta, ya tabatta kenan ita ?in ce dai ta yi comment ?in farko.
Kiran Ammi ne ya shigo wayarsa, ya saita nutsuwarsa ya ?aga tare da yin sallama.
Ammi ta amsa sanna ta ce "Yanzu na ga sa?onka, ka sam yadda yanayin jikinka yake, amma ka ce zaka kwana a gidanka kai ka?ai, kar wani abu ya sameka fa"
"Ammi kar ki damu, babu abin da zai sameni in sha Allah, ina son gabatar da wani aiki ne"
"To shikenan, amma dai da ka ji wani abu ka kirani a waya".
Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, in sha Allah sai da safe" suka yi sallama ya katse kiran.
Ya rintse ido, yana jin muryar ruma na sake amsa kuwwa a kunnuwansa, ya tuna yadda ta danganta shi da sata, take ya ji ya tsani yarinyar, kuma daga uniform ?in jikinta zaka gane 'yar talakwa ce, amma sai ?arfin hali da rashin mutunci, to yayi fa?a da wannan 'yar ma ya ce ya yi da wa? Wani uban tsaki ya ja, ya koma ya kwanta yana ?wafa. Ya kuma komawa ya na duba comment ?in ruma, amma ya tarar Jabir ya goge posting ?in gaba ?aya.
***
Ko da mama ta dawo, ta tarar gaba ?aya ruma ba ta da walwala, duk tayi wani iri, mama ta tambayeta ko ba ta da lafiya, ta ce ita lafiyarta ?alau kan ta me yake ciwo, mama kuwa ta ?ayleta, amma ta cigaba da monitoring ?in ta.
Yau ko wannan uban surutun da take kamar an jefeta a ka, babu ta yi shiru sai tunane-tunane take a ranta, a kan me za ta yi wa wannan ?an tahalikin ta huce, gashi ita ba ta san a ina ma za ta sake ganinsa ba, balle ta gaggaya masa magana ta huce da abin da yayi mata.
Mama suna ta hira suna tsara yadda bikin saukar su Yasir zata kasance, ruma ta koma kusa sa Abdallah ta ?an yi ?asa da muryarta ta ce "Yaya Abdallah, dan Allah waye galadiman Kano?"
Ya dubeta ya ce "Basarake ne a Kano, ba shi ne aka ce yana Germany ba bashi da lafiya, meyasa ki ke tambaya?"
"Babu komai kawai tamabaya na yi, amma ba ya mutu ba?"
"Anya, gaskiya ban sani ba, na ji dai an ce yana Germany babu lafiya"
?an shiru ta yi ta na tunani, a wurin Hauwwaliya kawai za ta samu abin da take so, dan haka ta sake gyara zama ta ce "Yaya dan Allah ranar juma'a mu je cikin gari"
"Ba zani ba, ina da abin yi ranar"
"Dan Allah, na ji mama tana waya da mamansu, an ce Hauwwaliya babu lafiya dan Allah ka kaini na ganta"
"Ke na ce miki ina da abin yi ranar"
"Ai Allah na ce, ka taimaka" ta yi maganar cikin magiya.
Abdallah ya ?an yi tsaki ya ce "Zan yi tunani"
Ta ce "Dan Allah ka kaini"
Bai sake kulata ba, saboda baya son magiya, ruma kuwa ta ?ware a kanta.
***
Kamar wasa Samha ta kira Khalifa a waya, kamar dama jiran kiranta yaje, tana kira ya ?aga.
"Adon gari ya kike?"
"Ba dogon surutu ba, ina son sanin deal ?in da kake son mu yi, na gani idan zan iya"
Murmushi ya yi, tare da kashe sigarin hannunsa ya ce "Kin yi tunani kin ga ni ke da mafita dai kenan? Sai dai kin so ki makara dan na samu wanda ya kawo tayin shiga deal ?in, ban sani ba ko ta wurnki aka samu bayani, amma duk da haka kema akwai role ?in da zaki taka, a ina zamu ha?u?"
Cikin mamaki Samha ta ce "Amma waye haka, da har ka ke tunani ta hanyata ya ji labarin deal ?in nan?".
"Kar ki damu da sanin waye, mu ha?u a hotel ?in da muka ha?u last"
Ta girgiza kai ta ce "No, kar ka manta ni 'yar babban gida ce, ba zai yiwu ma din ga yawon hotel ba, ka sama mana wani wurin kawai".
"To Shikenan, zan turo miki wani address ?in, ki huta lafiya" ta sauke wayar daga kunnenta, tana tunanin anya ba ta yi garaje ba wurin amincewa da Khalifa ba tare da ta san aikin sa za ta yi masa ba?.
***
Ranar juma'a ana tashi daga makaranta ruma ta taho gida, saboda ta tirke Abdallah ya cika mata al?awarin kai ta cikin gari, dan tuni ta tambayi mama, mama ta barta Abdallah ya kaita, musamman da ta ji ta ce Hauwwaliya zata duba.
?asan zuciyarta kuwa, so take ta sake ha?uwa da takawa, ta yi rashin kunya ko ta huce abin da ya yi mata.
Duk wani hoton Adam yake kan account ?in Jabir, sai da Jabir ya sauke shi, ?arshe ma yayi blocking ?in ruma, bayan yayi reporting account ?in ta an rufe mata shi.
Abdallah ya ce "Sai dai ruma ta yi ha?uri, dan wani wurin za shi, amma mama ta ce ya daure ya kaita, dan ruma a zahiri damuwa ta nuna da rashin lafiyar Hauwwaliya.
Ba dan ya so ba ya tasa ruma a gaba zuwa mandawari, Hauwwaliyarma ta samu sau?i, bayan sun gaisa da mutanen gidan, Abdallah ya ce da yamma zai zo ya ?au ruma.
Hauwwaliya ta yi ta murna da ganin ruma, dan rabon da su ha?u tun wancan zuwan.
Bayan ruma ta ?an jima, ta fara ?o?arin aiwatar da abin da ya kawota.
"Hauwwaliya, ina ne gidan Galadima ne?"
Hauwwaliya ta ce "Wai makaranta?"
Ruma ta yi tsaki ta ce "Galadiman kano"
"Wanne?"
"Au biyu ne?"
Hauwwaliya ta ce "Ai akwai Galadima na yanzu, wanda ba shi da lafiya yana Germany, sannan akwai gidan Galadiman kano wanda ya rasu"
Ruma ta ce "Wanda ya mutun"
Hauwwaliya ta yi dariya ta ce "Ke ai wan baban su Janna ne, jikar turakin nan da muka je gidan su biki ta bamu kaya, kuma yayan Galadiman kano na yanzu ne duk fa 'yan uwa ne, sarautar ba a rabawa a bawa bare dole sai su"
Ruma ta yi tsaki ta ce "Ni fa ba nasaba na tambayeki ba, ina ne gidan na sa"
Hauwwaliya ta ce "Shi wa?"
"Ke wai ya ina magana kina raina mini hankali, maganar wa muke ne?"
"To ke meye ala?arki da su da ki ke tambayata?"
Ruma ta ce "Assignment aka bamu a makaranta"
"Aka ce me?" Ruma ta ?ata fuska ta ce "Hauwwaliya, ni zaki wula?anta?".
Hauwwaliya ta kwashe da dariya ta ce "Yi ha?uri, Galadiman da ya rasu gidansa a bayan gidan sarki yake, wani ?aton gida gari guda, baki ga katangar gidan ba, doguwa sosai a nan dai gidan yake"
"To kin san 'ya'yan gidan?"
"To meye ala?ata sa su da zan san 'ya'yan gidan, suma 'ya'yan gidan duk a cikin assignment ?in suke?"
Ruma ta yi murmushi ta ce "A'a dan Allah in anjima mu je, ina son in ga dokuna"
Haka ruma ta din ga lalla?a Hauwwaliya, suka tafi yakasai, har family house ?in su Takawa.
Ruma ta yi mamakin girman gidan, ya fi na Turaki da suka je rannan, suka gama yawonsu suka koma gida.
Yau ma sai magariba sannan Abdallah ya ?auketa, suka koma gida, sai dai tun da suka koma gida, ruma take tunanin ta ina za ta ga Takawa, dan ta ?udirce a ranta ba zata ha?ura ba.
Sai dai gate ?in gidan na su kawai girmansa abin mamaki ne, babu wata 'yar kafa da za ta bi ta shiga, ga masu gadi a zaune a ?ofar gidan, da alama shiga gidan ba zai zama abu mai sau?i ba.
***
Tun da Samha ta koma gida, take tunani a kan abin da Khalifa ya zo mata da shi, dan ba abu ne mai sau?i ba. Amma duk tunanin da ya kamata ta yi ta yi, shika?ai me mafitar da ya rage mata, dan takawa hankalinsa sam ba ya kanta, idan har ba kawar da ala?ar nan ta yi ba, to ita da Adam sai dai kallo daga nesa, haka zalika sai ta yi ?o?ari wurin takawa su Hajiya Jamila burki a wasu ?angarorin dan idan suka nakasta shi, to ita suka yi wa.
***
Mama ta zauna ta tattauna da yaranta, a ?arshe suka amince da a sayar gonar mahaifinsu ta can katsina a garin ?an?ara, domin yin hidimomin da suke gabansu, masu registration ayi musu, masu exam a biya musu, masu bu?atar jari duk ayi musu. Sannan still akwai filinsu da aikin gwamnati ya bi ta kai, za a basu diyya.
Sai dai mama ta ce ita tsoron garin nan take ji, kawai ayi waya su sayar ?an abin da ya samu da na diyyar a aiko musu, can dangin babansu suka hau mitar cewa mama ta mallake yaran ba ga son su je in da suje, ?arshe aka yanke Aliyu zai je.
Yaya Abubakar ya ce "Dan Allah mama idan zai je, ya kai musu ruma, tun da dama exam za su yi, su yi hutu, ko a samu su daina surutun nan da suke yi na rashin zumunci, rabon da aje da ita garin fa tun yaye, rannan da na je baki ga mita da fa?an da suka din ga yi ba, wai kin fiye son 'ya'ya, wayar da muka yi da baba Habu shekaranjiya a kan biyan diyyar nan shi ma ba ki ji fa?an da ya yi ba".
Mama ta ce "Ba ?i nake ba, ka san halin rashin jin yarinyar nan shi nake tsoro, ga yanayin garin babu lafiya".
"Mama ai a cikin ido ake tsawurya, in Allah ya yadda babu abin da zai faru sai alkhairi"
Mama ta ce "To, Allah ya sa"
Ruma ta ji dadin batun tafiya da ita garin mahaifinta, amma gefe ?aya ta fi son sai ta tafkawa takawa ?arna, sannan su tafi yadda zai nemeta ya rasa.
***
Zaune take a kan kujerar da ke gaban mudubi, tana ta shafe-shafen turare, ?amshi duk ya gauraye ?akin, sannu a hankali ya tako gabanta yana kallonta.
"Mutum kwalliya sai ka ce aljana" dariya ta yi har sai da dimples ?in ta suka lotsa, ta ce "To idan ban kwalliya ba me zan yi?"
Ya saka hannu ya fara jan kumatunta ya ce "Kai na yi missing kumatun nan naki sosai da sosai" ?ata fuska ta yi tana sake tura kumatun, shi kuma ya cigaba da ja yana dariya yana fa?in "My Chubby girl".
***
Tun da aka ce za ayi tafiyar nan da ruma, mama take mata nasiha da ja mata kunne a kan tafiyar da za ayi da ita, a kan nutsuwa da kama kanta, musamman saboda rashin tsaron da yake garin.
Gaba ?aya Instagram sun yi banning account ?in ruma, dan haka yanzu ba ta hawa Instagram ?in sam.
Mama har mamaki take, duk wanda ya ce za shi cikin gari sai ta ce za ta bishi, mama dai ba ta yi magana ba, ta cigaba da zira mata ido, ta gano sintirin me take yi haka a cikin garin nan.
Yau ma haka ta dage sai ta bi Aliyu, Allah ya taimaketa ya tafi da ita.
Bayan sun je, ruma ta faki ido ta fice, ta tafi gidan Galadima, domin aiwatar da abin da ta yi niyya, ta samu napep daga nan mandawari zuwa cikin yakasai.
A ?ofar gidan ta tsaya, tana kallo tana tunanin ta ina za ta shiga? Cikin dakiya ta tunkari ?ofar gidan, masu gadin suka zubo mata ido su ga iya gudun ruwanta.
Gadan-gadan ta nufi shiga, wani ?an sanda yayi mata tsawa ya ce "Ke wurin wa ki ka zo?"
Ta ?an yi jimm sannan ta ce "Wurin wani"
"Waye wanin?".
"Sunanshi Adamu"
Wado ido suka yi gaba ?aya suna kallon ruma "Ke! Baki da hankali?" Saroro ta yi tana tunanin me ta yi kuma?
"Ke haka ki ka ji ana kiransa da shi, zaki zo ki fa?i wannan sunan haka? Zaki bar wurin nan ko sai mun saka dogarai sun zane miki jikinki"
"Ai ni ban san me ake ce masa ba, dan Allah ku barni na shiga"
"Ke, ba a zuwa gidan nan sai da izini, wuce ki bar nan ko ki jira idan kin nemi izini sai ki shiga".
"To a wurin wa zan nemi iznin?"
?aya daga cikin su ya ce "Ke bar nan ko na yi miki duka a wurin nan, ji mini shegiyar 'ya da baki fil-fil kamar robot"
Ta kalleshi ta ce "Ni ba shegiya bace ba, ka daina zagina" tayi maganar idonta ?yar a cikin nasa.
Girgiza kai kawai yayi, dan idan ya tunzura sai ya ji?awa yarinyar nan jikinta.
Ta samu wani ?an tudu ta zauna, tana kallon hanya. Suka kunna sigari suna sha, ruma ta kallesu ta ta?e baki a hankali ta ce "An yi asara"
"Ke ki ka kuma hararata sai na miki duka, ki tashi ki tafi ko?"
"Ni dai ba a kanku nake ba, ku ?yaleni mana" ta yi maganar tana kawar da kai, tana ji a jikinta ko zata wuni a nan, sai ta ga abin da ya turewa buzu na?i.
Wata dattijiuwa ce ta nufo gidan, suna gainta da fara'arsu suka fara mata magana "Baba Sabuwa, kin dawo?"
"Wallahi kuwa, kun ganni sai yanzu ya aiki?"
Suka amsa mata da Alhamdilillah.
Ruma ce ta taso da sauri tana fa?in "Baba" baba sabuwa ta tsaya ta kalli ruma ta ce "Yarinya ya aka yi?"
"Dan Allah gidan nan zaki shiga?"
Ta ce "Eh, a gidan nake aiki"
"Kin san wani Adamu a cikin gidan?" Hangame baki baba Sabuwa ta yi, tana waige-waige da fatan Allah ya sa wani bai ji ba.
"Ke 'ya ta ai ba a fa?ar wannan sunan a gidajen sarautar kano, takawa ake ce masa, eh na san shi"
Ruma ta yi ?asa da muryarta ta ce "Dan Allah abu zan baki, ki kai masa, so nake na ganshi an hanani shiga, amma dan Allah ki bashi wannan takardar hannu da hannu babata"
Baba uwani ta ce "To shikenan, amma in ji wa zan ce masa?"
"Idan ya ga takardar shi zai gane, dan Allah ki bashi "
Baba sabuwa ta ce "to shikenan, zan bashi in Allah ya yarda".
"Ku kuma da baku barni na shiga ba kwa ci kanku"
"Zo mu baki sigari " ?ayan ya fa?a cikin iya shege.
"Sai dai uwar sigari" ta fa?a a hankali.
Tutsiye Baba sabuwa suka yi, a kan lallai ta basu takardar nan su duba, kar a shiga da wani mugun abu gidan, amma ta ce ba zata bayar ba.
Baba sabuwa, hadima ce a cikin gidan ita ma, ita ce shugabar hadimai a ?angaren Mummy, kuma tana ?aya daga cikin masu bata rahotanni a kan abubuwan da suke wakana a gidan.
Tun da baba sabuwa ta shiga gidan, take tunani ta kai wa uwar ?akinta takardar su fara dubawa ko kuwa? Sai dai mummy ba ta nan, dan haka ta sanya takardar a ?an tofinta, ta cigaba da ayyukanta.
Ruma kuwa jinta take wasai, kamar an yaye mata wata damuwa da take damunta, tana komawa maman su Hauwwaliya da yaya Aliyu suka rufeta da fa?a, dan babu wanda ya san ta fita, ko a jikinta kasancewar yau tana lissafin sa?onta zai je in da take so, sai Addu'a take Allah ya sa baba Sabuwa ta bayar da sa?onta. Aliyu ya tasa ta